← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 44 OF 65

Sashe 44

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Aguje In'am ta fita dg cikin d'akin"gaba d'aya bata cikin nutsuwarta"nafeesa data hangeta tana gudu tayi bakin get itama saita biyota"tun kafin ta shigo cikin parlourn take k'walama ummi kira"ummi ! ummi!! lafiya kikemun irin wannan kiran haka?"cewar ummin tana fitowa dg cikin kitchen"In'am tafad'a jikinta ta fashe da kuka tana fad'in ummi yaya bashida lafiya "harda Aman jini yakeyi yanzun ko numfashi baya yi"dan Allah ki kira yaya sulaiman mu kaisa Asibiti kar yaya Aliyu nah ya mutu ummi"ta k'are maganar cikin gunjin kuka"wanda nafeesa data biyota taji komai"da hanzari ta juya ta fita"ummi kuwa salati tayi tana fad'in yana ina?"kafin In'am tayi mgn yaya sulaiman yashigo cikin parlourn da nufin yagaida ummi"yadda yagansu kuma yanzun yaga nafeesa tana tafiya da sauri bedai tsaida taba yatabbatar masa da cewar bbu lafiya....tun kafin yayi mgn koyayi k'ok'arin zama In'am ta iso gefensa ta rik'e hannunsa tana fad'in dan Allah yaya sulaiman muje ka kai yaya Aliyu Asibiti bashida lafiya"tafad'a tana kuka"be iya cewa komai ba"sai ummi datace maza sulaiman kuje can Asibitin nashi"dato ya Amsa yafita"In'am zata bishi ummi ta tsaidata"bata tsayaba ta fito Aguje"Atare da yaya sulaiman suka shiga d'akin yaya Aliyu"yana kwance Asume"yaya sulaiman yayi k'ok'arin gwada ya d'aukesa Amma yakasa"In'am dai na tsaye tana ta kuka gwanin ban tausayi"Ahaka sukaji muryar Abba da nafeesa zasu shigo cikin d'akin"Abba ne Agaba nafeesa na bayansa"yayi sallama yana fad'in subahanallahi! wai baya numfashi ne?"Eh Abba dama ummi tace nazo nakaisa Asibiti"na gwada d'aukarsa nakaishi cikin mota Amma yamun nauyi"to bara nakama maka"yafad'a suna d'aukar yaya Aliyun suka fita dashi" In'am ta fad'a jikin nafeesa tana kuka"kiyi hak'uri insha Allah zai sami lafiya"yanzun mu gyara masa d'akin kafin su dawo ko?"mudai gyara Amma ko saman Adaidaita ni sai naje nafeesa"bazan iya jure har sai sun dawo ba batare danasan wane Hali yakeba"yah Allah ka bama yaya Aliyu nah lafiya"nafeesa ta Amsa da Ameen tana jin tausayin In'am"Atare suka gyara ko ina"kowaccensu na lura da k'aton pic d'in in'am dake cikin bed room d'in basudai tankaba sbd suna cikin jimami"wayoyinsa In'am ta d'auka suka rufe d'akin ta Amshi key d'in"part d'in mommy sukaje ta d'auki hand bag d'in nafeesa da kud'in transport "sannan ta fito ta tari nafef ta shiga suka nufi Asibitin....
su yaya sulaiman na isowa Asibitin shida yaya yusuf Aka nufi emergency room da yaya Aliyu"yayinda Abba yana gida be biyosuba"tsai tsaye sukayi bakin k'ofar shiga emergency d'in"kusan mintina 45 da shigarsu ciki In'am ta iso wajen"kallo d'aya yaya sulaiman yamata ya fahimci taci kuka ta godema Allah"yaya sulaiman ina yaya Aliyun yake? ta fad'a Idonta cike da k'wallah"fuskarsa Ad'aure yace"suna ciki Ana dubasa"miye Abin ki wani kwaso jiki kizo mana nan?"wuce ki koma gida kina jina??"kukan data rik'e ta fashe dashi tabar wajen tana shan Alwashin bbu Inda zataje"Acan bakin get taje ta zauna ta lalubo number d'in tasleem matar brr Ahmed "bayan ta kirata tasanar mata idan yaya Ahmed na nan tafad'a masa yaya Aliyu bashida lafiya yana Asibitin sa"bayan sunyi sallama tayi tagumi..... doctor marwaan da dr Amaan sune sukayi tsaye kan yaya Aliyu kusan awa guda sannan numfashinsa ya daidai ta"suka masa Allurai aka kaisa wani room na mummunan suka d'aura masa drip"kafin doctor marwan ya kalli yaya sulaiman yace"idan babu damuwa ina son ganin wani babban makusancinsa"to shikenan insha Allah Abba zaizo sai kuyi mgn"daga haka dr marwan ya fita"shi kuma yaya sulaiman ya kira Abba yasanar masa komai"cikin y'an mintina ya iso Asibitin ya isa office d'in dr marwaan d'in"wanda yana ganinsa yafahimci mahaifin dr Aliyu ne sbd kama ta jini....bayan sun gama gaisawa dr marwan yayi gyaran murya yana fad'in zancen gaskiya Abba dr Aliyu yana cikin damuwa da fargaba daya saka Aransa"wanda binciken mu ne yasaka muka gano hakan"kuma ko shima idan yabinciki kansa hakan zai gani"yaka mata Abba kajashi Ajiki kaji meye damuwarsa dake barazanar shafar zuciyarsa??"sannan yanzun haka yakamu da ulcer"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! cewar Abba yana tunanin tabbas zancen da yamasa jiyane yak'ara sakashi shiga damuwa"wanda yad'auka ya hak'ura da in'am d'in ma"suna cikin maganar brr Ahmed yashigo cikin office d'in fuskarsa d'auke da damuwa"d'uk'awa yayi yagaishe da Abba"kafin yaja kujera ya zauna yana tambayar meke damun dr Aliyu?"bbu wani b'oye b'oye Abba ya sanar masa yadda suka ganshi da zuwan su Asibitin da bayanin da dr marwan yamasa yanxun"shiru yayi yana tunanin Anya ciwon dr Aliyu beda Alak'a da in'am?"Amma sai yayi shiru yana jin yadda dr marwan ke rok'ar Abba Aji meye damuwar dr Aliyu Amagance masa ita"bayan sun gama mgn Abba da brr Ahmed suka fito"Amma Abba dan Allah babu wani Abu daya faru cikin gida na rashin jin dad'i ko kuma Angaya masa wata mgn data saka yashiga damuwa??"tabbas Akwai Ahmed"cewar Abba yana masa bayani"Ajiyar zuciya brr Ahmed yasaki yana fad'in wlh Abba sbd in'am ne"tunda yaji zancen za'a bama wani ita"yasha fad'amun sbd damuwar cikin gidan yake b'oye furtawa yana sonta"to Ai gashi yana neman rasa ransa ko lafiyarsa sbd zurfin ciki ko?"dama can nasan zancen saidai da baiyi mgn ba na d'auka ya hak'ura ne"sbd haka bbu damuwa indai mamana tana sonsa"gaskiya tana sonsa Abba"to saidai naji ta bakin nata tukum"dg haka sukayi sallama Abba ya shige mota driver yajashi"brr Ahmed yawuce d'akin da dr Aliyu ke kwance yanata bacci"lokaci guda duk ya zabge yayi y'ar fuska"saidai yak'ara wani irin mugun kyau"har yanzun be farkaba?"Eh gsky Amma sunce bazai jimaba"cewar yaya yusuf da yaje ya Amso break fast d'in da ummi ta shirya "idan yaya Aliyu ya farka yayi yasha magani"bara naje nadawo tunda be farkaba"okay yaya sulaiman ya fad'a yana tuba time kusan k'arfe sha d'aya na safe da wasu y'an mintina"brr Ahmed befi mintina 5 da fitaba"yaya Aliyu yafara matsa zara zaran eye lashes nasa"kafin yabud'e duka manyan idanuwansa da har yanzun Akwai jaa Acikin su"iya lab'b'ansa yayi salati yana k'arewa cikin d'akin kallo"yaya katashi kenan?"sannu ya jikin naka?"cewar yaya sulaiman yana kallon sa"maimakon me tubarau ya Amsa masa" sai yayi shiru yana tunanin ina In'am ta tafi??"da k'yar ya iya motsa red lips nasa yana fad'in ina my Angel??"d'an murmushi yaya sulaiman yayi yana fad'in na koreta yaya Aliyu"sai kawai tazo tayita mana koke koken gulma....dukda har yanzun bayajin dad'in jikin nasa hakan be hanashi had'e rai ba cikin sanyayyar muryanshi yace"maza kaje duk Inda take kazomun da ita"Akan me zaka koreta??"......yaya sulaiman na k'ok'arin mgn In'am da brr Ahmed suka shigo cikin d'akin"wanda bayan yafita ya ganta bakin get taci kukanta ta k'oshi idanuwanta duk sun kumbura"ta sanar masa yaya sulaiman ne yakoreta"tausayinta yaji yace"tazo suje yarakata d'akin"shine suka shigo a tare...In'am na shigowa sukayi ido hud'u da yaya Aliyu"wani kukan ta saki Aguje ta nufo gefen bed d'in"yaya Aliyu ya lallab'a yatashi zaune cikin k'arfin hali yana kallon ta bbu ko k'iftawa"saidai yatsorata da yadda yaga idanuwanta sunyi jajir sun kumbura"yaya Aliyu nah ka farka?"to ya jikin naka?ta fad'a tana duk'e gaban gadon ta kama hannun sa guda"beyi mgn ba sai jan hannun nata yayi ta dawo gefensa ta zauna"ya juyo Ahankali yana fuskan tarta yana jin kamar ya sanyata Ajikinsa "my Angel ina kika tafi kika barni??"yafad'a yanda itace kawai zata iya jin meyake fad'a"d'ago kanta tayi da nufin tayi mgn"sai sannan ta lura dasu yaya sulaiman da yusuf dake cikin d'akin"turo baki tayi tace"ba wancan yaya sulaiman d'in bane yakoreni
... lallai Auta zaki koma gida zamu had'u ai ko?"kamata Abinda kayi niya"cewar yaya Aliyu fuska Ad'aure yana makama brr Ahmed harara dayayi tsaye ya jingina jikinsa ga bango yanata kallonsu cike da burgewa" Abokina bani nakashe zomon ba"gata nan tambayeta kaji zan tafi naganta bakin get"bayan ta sanar mun sulaiman yakoreta nace tazo muje nan"kai ina kasan bana lafiya?"In'am ce takira tasleem tanata kuka"Allah sarki my Angel na warke karki koma yin kuka kinjiko?"yafad'a yana kallon ta"yayinda yaya yusuf da sulaiman ke kallon yaya Aliyu suna mamakinsa"sbd sunsanshi beda sakin fuska ko yawan mgn Amma sbd mace gashi yanayi duk Akan soyayya"lallai SO mugun wasa....yaka mata kayi brush kaci wani abu saika sha magani gasu can"cewar brr Ahmed"okay"sulaiman Amsomun brush da toothpaste a shop"okay"yafad'a suka fita shida yusuf"brr Ahmed ya kallesu yaga in'am tayi k'asa da kanta tayi shiru shi kuma uban gayyar yanata kallonta"zan wuce gida Abokina"Allah yak'ara Afuwa zuwa dare nasan ka koma gida ko?"yaya Aliyu na k'ok'arin mgn Abba yashigo cikin d'akin"driver na biye dashi da ledoji manya Ahannunsa"brr Ahmed yama Abba sannu da zuwa sannan yafita shida driver"Abba na murmushi yace"mamanah yayanki yasami lafiya ko?"yafad'a yana k'ok'arin zama kan farar kujera"In'am ta Amsa da Eh tana masa sannu da zuwa"ya amsa kafin ya kalli yaya Aliyu dayayi k'asa da kansa yana fad'in Abba sannu da zuwa"yauwa Aliyu me b'oyemun damuwarsa"ka bani mamaki da sbd hauwa ka b'oye Abinda ke ranka game da y'ar uwarka In'am"meyasa bazaka sanar niba ni?k'irjin yaya Aliyu yabuga"yad'ago kansa yasaci kallon In'am datayi shiru tana sauraren kalaman Abba"mamanah!

Abba yakira sunanta"na'am Abba"fad'amun kina son yayanki kamar yadda shima yake sonki??"kuma gaskiya zaki fad'amun karkimun k'arya.....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
55&56
...........kallon Abba In'am tayi yayinda ita kuma yaya Aliyu ke kallonta zuciyarsa na wani irin harbawa" yayi kasak'e yana jiran jin wace irin Amsa zata bama Abba"cike da yarinta tace"Eh ina sonshi fa Abba"sai kuma ta b'oye fuskarta da tafikan hannayenta Alamar jin kunya"yayinda yaya Aliyu yasaki wata iriyar Ajiyar zuciya Ab'oye yana furta Alhamdllh!

Abba na murmushi yace"masha Allah!

Ubangiji yayi muku Albarka yasaka Alkhairi Acikin wannan Alak'ar taku da juna"kan yaya Aliyu ak'asa ya Amsa da Ameen cikin tsantsar jin dad'in kalaman mahaifin nasa"yayinda kan In'am ke cikin cinyoyinta tanata murmushi.....
Chapter 44 · 0% Book details