← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 6 OF 65

Sashe 6

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 6 min read

In'am na fitowa Aguje yaya Aliyu na kawowa zai fita"yakuma sha alwashin zata sani tunda ta gudu"da sauri ta nutsu tana kallon kyakykyawar fuskarsa yajuyo suka had'a ido"da sauri tayi k'asa da kanta"ban hanaki guje guje ba?"inafa sauri zan fito karkaga na dad'e ko?"shine akace kiyi gudu?"shiru tayi"yabi kayan jikin ta kallo ya d'auke kansa yana fad'in anjima karki bari na jiraki"naga akwai hadari bama sai nace karki shiga ruwa ba"yana fad'in hakan yayi gaba be jira amsartaba"ta raka bayansa da harara tana murgud'a baki tana kwaikwayon maganarsa"sannan ta nufi dining area d'in"kasancewar bbu kowa parlourn"tea kawai da k'wai taci tabar parlourn taje kitchen ta dafa indomie ta zabga Attarugu"ta fito ta zauna tana ci"Ahaka mahmood yashigo parlourn da leda Ahannunsa yamik'a mata yana fad'in yaya yace gashi"fuskarta ad'aure ta Amsa"shi kuma yafita"shiru tayi tana kallon kayan gogaggu"tambayar kanta takeyi shine yagoge ko kuwa sawa yayi aka goge??"ganin batada Amsar tambayar yasaka ta hak'ura taci gaba da cin Abincin"taji An fara yayyafi"ummi ta fito tana kallonta"wato shan yajin bazaki denaba ko?"nidai ummi an fara ruwa kuma yaya yace" karna shiga"wlh kuma inaso na shiga"to shikenan Allah yabaki sa'ar shiga d'in ta fad'a tana k'ok'arin zama kan kujera tana duba ledar kayan"tana kallon in'am tace"sune yunifoam d'in?"Eh yanzun yaya yakamun"shiru kawai ummi tayi tana tunani.....
mama gaje da sallama ta shigo parlourn umma"yaya isma'il na zaune yana kallo umma na bed room d'in ta"gaida ita yayi ta Amsa ta wuce ciki"umma na'a tsaye tana shirya kayanta cikin ward rope mama gaje ta shigo"juyowa tayi ta Amsa sallamarta"ta zauna suka gaisa"cikin b'acin rai mama gaje tace"gaskiya in kika zauna Ahaka kina ji kina gani maimuna zata rabaki da d'anki da mijinki"banganeba?....sanar mata k'arya da gaskiya tayi na ganin Aliyu da In'am"kafin ta d'ora da fad'in miye daga yadawo yakama yawo da yarinya Amota?ko kuwa manna masa y'ar tata zatayi ya aura?"su mallakesa da Abinda yatara tunda Anga yanada abin hannunsa....bana fatan hakan har Abada gaje"kima dena wannan maganar"shi kuma Aliyun zan ganshi"na rabashi da maimuna da shegiyar y'arta Amma yak'i ji ko?"to ki barni dashi zan masa mgn ya fito da wacce yakeso yayi Aure"inma burunta kenan na cusa y'arta wajensa to hakan bazai cikaba in sha Allah"to nima Abinda nagani kenan"yanzun dai tunda ga zubaida yaya hauwa Ai sai Ayi tuwona maina ko?"d'aure fuska umma tayi tana fad'in Atsarinna bana son Auren zumunci sbd kar Asami matsala zumunci ya lalace"sannan banida burun Aliyu ya Auri wacce beso ko bata sonsa"inada tabbacin Aliyu beson zubaida da Aure garama kibar zancen nan anan"hmm! kikace ba?"sbd kin gammu talaka shiyasa zaki guji had'a zuri'a ta da taki"to shikenan bbu komai ai arzik'i na Allah ne"ta fad'a tana matsar k'wallah"umma da mamaki take kallonta"kafin tayi mgn zubaida ta shigo d'akin da sallama"umma ta Amsa"mama gaje tayi saurin mik'ewa tsaye tana fad'in ke zubaida tashi muje gida"bangane kujeba?

Eh zamu tafi mubar miki gidanki tunda guduna kikeyi"tana fad'in hakan taja hannun zubaida suka fita"umma ta tab'e baki tana fad'in Allah ya kyauta"k'asan ranta tana dakon Aliyun yazo taji gidan ubanwa yaje da in'am??....
da marece misalin k'arfe 3:45 pm"in'am ta gama shiryawa cikin sabbin yunifoam d'inta pink colour"ta saka takalmi cover bak'ak'e sawu ciki"sannan saida tasaka bra"ba k'aramin kyau yunifoam d'in suka mata ba"sbd colour d'in pink akwai haska farin mutum"turaruka ta fesa ta fito da jakarta a hannunta da nufin ta zauna a parlour kafin Almasifatu ya aiko tazo..... k'ok'arin zama kan kujera takeyi"ni'imtaccen k'amshin turaren yaya Aliyu ya kaima k'ofofin hancinta ziyara"ta juyo da sauri ta kallesa yana k'ok'arin shigowa cikin parlourn"yana sanye da farar shadda giznah"kansa bbu hula"bak'ar suman kansa zuwa lallausan sajensa daya zagaye fuskarsa sunsha gyara sun kwanta lub....yana sanye da takalmi sawu ciki bak'i"da Agogon fata bak'a d'aure A damtsan hannunsa"fuskarsa Ad'aure bbu Alamar wasa"saidai bbu glass a fuskarsa"ba k'aramin kyau yayiba"cikin second 30 in'am ta k'are masa kallo Azuciyarta tana fad'in kayi kyau dai badan halin kaba"yaya na shirya....waike baki iya gaisuwa ba?"d'azun fa da safe na gaidakai kuma baka Amsaba"tuhumata kikeyi?"yafad'a yanata kallon"tana k'ok'arin mgn ummi ta shigo parlourn ta dubesu Aranta tana fad'in masha Allah!

Afili tace"bakiyi latti ba?"ai 4 d'in bata idaba ummi"cewar yaya Aliyu yana fita"in'am tak'i mgn tana b'ata rai"ummi tayi murmushi kawai tana fad'in Allah yatsare"ta Amsa tana barin parlourn"sadda ta fito waje harma yaya Aliyu yashiga mota"hakan yasa ta nufi motar zata shiga ta lura da Auwal da mahmood zasu tafi islamiya"wani haushi taji na'an rabata da y'an uwanta an kaita wani wajen daban"Auwal kuwa gwalo yamata yayi gaba"bud'e k'ofar tayi ta shigo ta kallesa tana fad'in yaya kaga Auwal yamun dariya ko?"shiru yayi yak'i mgn yana driving d'insa"itama dataga haka sai tayi shiru tana jin haushin shirun da yayi...."can suna tafiya yatsaya wajen me siyar da gwaba da rake yadubeta fuska ad'aure yace"zaki sha?"k'in mgn tayi ta kauda kanta"ba dake nake mgn ba?"ni bana ci"bece komaiba yaci gaba da driving nasa har suka iso islamiyar yyi parking"big bom guda biyu manya yafito dasu agaban Aljihun rigarsa.....saidai kawai taji yakamo hannunta guda yasaka mata aciki"turo baki tayi data kalli Abinda yasaka mata d'in"ni yaya bana so"yanzun dan Allah nasanar maka Abinda Auwal yamun sai kayi shiru ko?"kuma sune suke tsokanata "ta fad'a tana sakin kukan da bbu hawaye"cika mata hannu yayi da sauri yana fad'in ramawa kikayi kenan sbd ga sa'anki ko?"nifa ba haka bane"shiru yayi yazaro kud'i dubu biyar yasaka mata cikin hannunta"ta kalli hannun taga kud'i ne"yatsareta da firgitattun idanuwansa"yaya kud'in meye ?"bakiso?"yajefo mata tambayar"shiru tayi kanta Ak'asa tak'i mgn"shima bece komaiba saidai yafahimci Akwai Abinda takeso ta sanar masa ko nauyi takeji....kusan second 30 bbu me mgn acikin su"can ya kalleta yana fad'in menene?"d'ago kanta tayi ta marairaice murya tana cewa "dama Ance muyi waya A skul kafin akoma hutu sbd exams....shiru yayi kamar ma bazaice wani abu ba"kaji yaya? tab'e baki yayi yace"har yanzun Aike k'aramar yarinya ce ki bari sai kinyi hankali kin nutsu sannan saina siya miki wayar"wayyo yaya wlh na nutsu tun tuni"ta fad'a cikin yarinta"yaya Aliyu yatab'e baki yana fad'in *me tubarau* d'in da kike murna zai tafi ku huta shine yadawo yanxun kikeso yasiya miki waya?"zaro ido tayi tana tambayar kanta ta yaya yasani??"ke tashi ki wuce aji kina b'atamun lokaci"batace komaiba ta bud'e k'ofar tana rik'e da kud'in sai b'ata fuska takeyi"fitowa yayi yana fad'in ki jira"tsaye tayi batace komaiba"yazo gefenta yatsaya yana fad'in muje har ajin naku"nidai yaya basai munje dakai bako?"ta fad'a cikin shagwab'a"d'aure fuska yayi yana fad'in wai yaushe na fara wasa dake MARYAM?"da sauri ta kallesa suka had'a ido"harara ya wurgo mata"batace komaiba ta fara tafiya itada dashi"har bakin k'ofar Ajin nasu suka iso"Anan nefa yaya"kiyi karatu sosai kina jina?"banda fad'a da friends naki"duk fa banayi ai"to wuce ki shiga"batace komaiba ta nufi cikin Ajin duk y'an matan dake Ajin nata hango dr Aliyu ta window sunata kallonsa"saida yaga ta zauna sannan yajuya cikin nutsawa yatafi.....
Chapter 6 · 0% Book details