← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 46 OF 65

Sashe 46

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Abba na isowa gida yanufi parlourn sa ya zauna yana nazarin soyayyar Aliyu da maryam"yakuma san tabbas Alh d'ahiru yaji Aliyu keson maryam koda kud'in wani Aka kawo saiya mayar yabama Aliyu ita"to ballema ba'a kawo ba"yana wannan tunanin yaji sallamar umma"wacce gaba d'aya bbu ruwanshi da ita"saiya kama yake mata mgn"yana ganin itace ya had'e rai"zama nesa dashi tayi tana fad'in Alh yaya jikin Aliyu d'in?"tun jiya da baizo yamun saida safe ba nafara zaton bbu lafiya"toda safen nan sai nafeesa ta shigo ta sanarmun bashida lafiya yana Asibiti"ga kayan kari can na had'a zanje na dubasa.....hmmm! kin makara hauwa! domin dai ita maimunar wacce kika tsana itace zuri'arta kecan ke kulawa dashi"yanzun haka ta bayar da break fast yusuf yakai tun d'azun"inaso ki sani ciwon Aliyu nada Alak'a da maryam sbd irin son dayake mata"sbd tsoronki yak'i furtawa"yara nason juna mugun halinki zai sakq d'ana yaje yarasa ransa koya kamu da wata lalura"inaso kisani idan Allah yatashi zai iya d'aukar ranki maryam da Aliyu su rayu Acikin inuwar Aure"d'ana yakamu da ciwon zuciya ga ulcer dukdan sbd damuwa"yana kumayi danke"Amma ke baki san ciwon saba"miye ribar k'iyayyar da kike nuna wa maimuna da zuri'arta??"to Aliyu nasami labarin sbd in'am ya kwanta ciwo"nakuma tambayeta tana sonsa ta Amsamun"sbd zan iya komai sbd farin cikin d'ana"nanda sati 1 insha Allah zan sakq ranar Aurensu"ya miki dad'i kokar yamiki banida matsala"saidai inaso ki sani muddin kika tado mana fitinah wlh zan iya rabuwa dake har Abada"ko A kwanaki darajar mahaifiyata kikaci na barki"dubiya kuma kije bazan shiga tsakanin d'a da uwa ba" yana fad'in hakan yaja tsaki yatashi ya shige bed room d'insa"umma ta mik'e tsaye ta fita jikinta Asanyaye"yyinda kalaman Abba ke Amsa kuwa Acikin kunnanta"part nata ta koma ta d'akko hand bag nata da hijab tabar masu Aiki ta fita batare data d'auki Abin break fast data had'a ba" bayan driver yafito da motar umma ta zauna back sit suka nufi Asibitin"bayan sun iso ta fito ta wuce ciki"tana shigowa a reception taga yaya sulaiman zaune kan kujera yana danna waya"shi bema lura da itaba"saida yaji tace"sulaiman inane d'akin da Aliyun yake ne?juyowa yayi da sauri suka had'a ido"ina kwana umma?"yafad'a dukda bata cika Amsawa ba idan sun gaisheta"yana dai cigaba da gaishetane koda bazata Amsaba bisa bin umarnin ummi"lafiya qlau"mik'ewa tsaye yayi yace"muje ga d'akin can gaba"yafad'a yana yin gaba tana biye dashi Abaya"suna isowa bakin k'ofar d'akin yanuna mata shi kuma yakoma Inda yake zaune.....
yaya Aliyu na shiga toilet d'in in'am ta kama dariya taje ta tsugunnah gaban basket d'in"cikin nutsuwa da tunanin wai dama tun tuni yaya Aliyu ke sonta?"wanda ada ita tana ma Abinda yake mata kallon K'IYAYYA"da wannan tunanin ta had'a masa tea me kauri me zafi"ta Ajiye samqn loka"sannan ta zuba masa farfesun kayan ciki da doya da k'wai Agefe"itama kanta yunwar takeji Amma wata iriyar kunyarsa yanzun takeji"bata jin zata iya cin Abinci Agabansa"tana k'ok'arin zama gefen bed d'in yafito dg cikin toilet d'in"saida k'irjin In'am yabuga"tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta"yarfo mata sauran ruwan hannunsa yayi yana fad'in my Angel kinga jikin nawa da d'an k'arfi ba kamar jiyaba"saidai kan har yanzun yana mun ciwo"Ayya sannu"yanzun kaci Abinci saika sha magani zakaji normal "to dr maryam"yak'are maganar cikin zolaya yana zama gefenta"murya can k'asa yace"wai k'auyanci meye haka?"karfa Ace kunyata kikeji?....nidai kayi shiru kayi break fast dan Allah"ta fad'a cikin shagwab'a batare data kallesaba"bazan yiba bayan kema bazaki ciba" kuma bakice kina sona ba....wai haka yaya Aliyu dama yake?"matsowa gefenta yayi yana danna wayarsa yace"zo kiga pics namu na jiya"ka bari kayi break fast saimu gani"kuma banace I love you ba"tafad'a tana saka tafikan hannayenta ta rufe fuskarta dashi tana murmushi"yaya Aliyu yace"wow banyi zaton hakan ba my Angel"I love you too! nasan saura kiris ki zama matar yaya Aliyu"shi kuma yazama mijin ki....shiru tayi Aranta tace bashida kunya"ki tashi ki had'a wani tea d'in kinsan bansan musu ko?"batayi mgn ba taje ta had'a ta sheka yarage zafi"tana dg zaune ta bashi baya ta kafa kai ta shanye ta Ajiye cup d'in"sannan tajawo farar kujera ta zauna dg gaban gadon tana fad'in to yaya nika dena kallonah kaci Abinci ga magani nan najiranka...yana k'ok'arin mgn umma ta turo k'ofar d'akin ta shigo da sallama"Atare k'irjin In'am dana yaya Aliyu yabuga!"kallo d'aya ta musu ta d'auke kanta"yaya Aliyu ne yayi jarumtar Amsa sallamar tata yana k'ak'aro fara'ar dole"da sauri in'am ta duk'a ta gaisheta jikinta har kirma yakeyi"ta Amsa fuska bbu yabo bbu fallasa"In'am ta sauka dg samqn kujerar tana fad'in umma ki zauna"ita kuma ta nufi k'ofa da nufin taje reception ta zauna kafin ummar ta fito"yaya Aliyu yabita da kallo tamkar yatsayar da ita saidai yana shakkar umma"In'am dawo kiyi zamanki ni tafiya zanyi driver na jirana"juyowa tayi Ahankali tana mamakin yau umma ta Ambaci sunanta bayan da K take kiranta dashi"umma ina kwana?"lafiya qlau ya jikin naka?"Alhamdllh da sauk'i yafad'a yana kurban tea d'in"In'am ta d'akko plate d'in farfesun ta ajiye masa gabansa ta zauna can k'arshen gadon"yaya Aliyu na satar kallonta ya d'auki wayarsa yakira sulaiman yasanar masa yasiyo masa robar ruwa biyu"bayan yagama wayar ya Ida shanye tea d'in yafara cin farfesun"yana tambayar umma ina isma'il?"yana office bemasan baka lafiya ba"nima nafeesa tazo ta sanar mun d'azun"Amma dai da sauk'i ko?"Eh zuwa azahar zan dawo gida insha Allah"to shikenan Allah yakaimu"ta fad'a hakan nayin daidai da shigowar yaya sulaiman da roban ruwan Aleda"yayi sallama yana mik'a ma In'am"bayan ta Amsa yafita"itama umma tashi tsaye tayi tana fad'in bara na tafi Aliyu sai kundawo d'in"to umma Allah yatsare"ta Amsa da Ameen ta fita"yaya Aliyu yayi saurin cewa matso kiji my Angel"nidai kabari ka idar mana"bece komaiba yaci gaba da cin abincin harya gama"ya Ajiye plate d'in da sauran kad'an daya rage"beyi mgn ba yana dai ta kallonta Azuciyarsa yana godiya ga Allah daya saka In'am ta Amince dashi Amatsayin masoyi"wanda yasan sbd soyayyar ta ya kwanta ciwo"gashi kuma ta Amince yasami lafiya....gashi yaya Aliyu"yaji siririyar muryarta tana katse masa tunani"yatsurama baby face nata ido beyi mgn ba"saidai ya Amshi robar ruwan da maganin data b'allo masa"yana mamakin yaushe ta tashi ko motsinta bejiba sbd yayi nisa atunani"duka maganin yajuye Abakinsa yabi da ruwa"bayan ya had'iye yasaki numfashi Ahankali"sannu! yana k'ok'arin yin mgn ummi da mommy suka shigo cikin d'akin"haka nan yau yaya Aliyu ya tsintsi kansa dajin nauyin ummi"In'am ta Amsa sallamarsu taje Aguje ta rungume ummi"shikenan tunda Abin wariyar launin fatane In'am"cewar mommy tana murmushi"ummi tace keda y'arkine mommy"ke kuma ki cikani karki kayar dani ko?"In'am tak'i mgn ta kwantar da kanta Agefen kafad'ar ummi tana yiwa yaya Aliyu dake kallonta ta k'asan ido gwalo"wanda sai a sannan yace"sannunku da zuwa"ummi ta Amsa da yauwa tana fad'in ya jikin naka Aliyu?"da sauk'i na warke zuwa Anjima zamu koma gida"Allah yak'ara lafiya"ya Amsa da Ameen"mommy ta zauna gefen bed d'in suka gaisa"ummi ta zauna gefen kujerar"mommy ina nafeesa?cewar In'am"tare muke da ita"Amma tana can wajen sulaiman naga ta tsaya"In'am tayi murmushi batace komaiba tana tsaye bayan ummi"saiga nafeesa da yaya sulaiman d'in sun shigo"In'am ta kallesu takama dariya"yaya Aliyu dai na danna waya"ke lafiya kike mana dariya haka?"cewar yaya sulaiman yana maka mata harara"nifa yaya badaku nakeba"kwafa yaja yana kallon nafeesa dake gaida yaya Aliyu da masa ya jiki"ummi ta mik'e tsaye tana fad'in to Aliyu Allah yak'ara lafiya"Ameen ummi"ke Autah dake zamu tafi ko?"da sauri in'am ta kalli yaya Aliyu ya kyafta mata ido"ta d'auke kanta tak'i mgn"yayinda mommy da yaya sulaiman da nafeesa suka fita"kizo muje kiyi wanka saiki dawo ko?"In'am batayi mgn ba ta d'auki hand bag d'in datazo da ita tabi ummi"saida tazo fita ta juyo suka had'a ido da yaya Aliyu taga ya kauda kansa Alamar yayi fushi"murmushi ya sub'uce mata ta had'e hannayenta tana nuna masa sama"sai yayi murmushi yayima tafin hannunsa kiss yahuro mata"wata iriyar kunya taji tayi gaba da sauri dan har su ummi sunyi gaba tuni....

Bayan sallar la'asar In'am ce zaune Amain parlour"tasha gayunta cikin Riga da siket na wani materia lace blue me zanen flowers pink"tayi kyau gwanin burgewa"dan harda lip stick ta shafa"tayi zaune tayi shiru tana tunanin wayar da sukayi da yaya Aliyu d'azun"jefi jefi tana sakin murmushi"tasan tun wajen 2:30 pm yadawo gida"Amma ummi tace"bbu Inda zata je Ai d'azun taje ta ganosa"ga girki ta masa na musammun"faten dankali da wake"yaji bushashshen kifi da Alaiyahu"motsin shigowar ummi da taji yasaka tadawo tunaninta"ummi tabita da kallo tana fad'in kinci Abincin?"Eh naci saura na yaya Aliyu ne bankai masaba"kuma ummi bbu dad'i dan Allah Amatsayinsa na babban Aminina nak'i zuwa koma dubasa ko??"baki galalah ummi tasaki tana k'ok'arin mgn yaya seif yashigo cikin parlourn da sallama"ummi ta Amsa ya gaisheta yana kallon In'am yace"yaya Aliyu yace"kizo yana bakin get d'in gida"kuma ki bada Abincin akai masa"cike da Aji In'am ta Amsa ta mik'e tsaye ta nufi dining area"bayan ta d'akko basket d'in data shirya Abincin Aciki ta mik'ama seif ya Amsa ya fita"ita kuma ta saci kallon ummi"taga ta had'e rai"In'am mutucinki da tarbiyyar ki nake kare miki ba wani abu ba"musammun tunda mahaifiyar Aliyu bata sonmu"idan kinje karki jima ki dawo"koso kike Adinga cewa koda yaushe kina manne dashi?"dama d'azun kafin muje Asibiti baffanku d'ahiru yazo yasanar mun Aliyu shine mijin daya zab'a miki sbd kuna son juna"ban damu da halin uwar saba na fawwalama Allah komai"fatana Azo Asanya ranar taku harda sulaiman ko hankalinah ya kwanta"sanya rana kuma ummi??"cewar In'am gabanta na fad'uwa data tuna da Abinda Akeyi idan Anyi Aure tsakanin miji da mata"ummi bata koma mgn ba ta zauna kan kujera"jikin In'am Asanyaye ta shiga d'akinta ta zumbula hijab pick colour"wacce tayi mata mugun kyau"dan yanzun ji tayi bata son yaya Aliyu yaganta bbu hijab"Anutse ta fita dg cikin parlourn ta nufi gidansu yaya Aliyu.....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
57&58
........
Chapter 46 · 0% Book details