← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 40 OF 65

Sashe 40

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 7 min read

Dr Aliyu kuwa ikon Allah kawai yakawosa gida"sai bayan kuma ya iso yayi dana sanin tafiya ya barta"sbd gudun kar wannan muddansir d'in ya kulata"be shiga da motar ciki ba"sai yayi parking Anan waje yayi zamansa ciki yana tunani"idanuwansa sunyi jajir zuciyarsa na zafi"yana jin haushin kansa dabai saita yaron nan ba koma waye shi Awajen brr Ahmed"yana Anan cikin motar ya hango motar brr Ahmed" kasancewar motarsa me tinted ce bbu wanda zai d'auka da mutum Aciki"yayi shiru yana kallon motar sbd jikinsa yabashi brr Ahmed In'am ce ya maido gida"dama kuma zaman da yayi kenan yaga waye zai maidota?"Akan idonsa ta fito ta harari motarsa ta wuce ciki....d'an murmushi yasaki da yaga tayi hakan"gaba d'aya sai yaga be kyautaba"ya fahimci kuma Angel tashi tayi fushi dashi"be gama wannan tunanin ba ya hango brr Ahmed yaja motar yabar wajen"hakan yakoma tabbatar masa da cewa shima fushi yakeyi dashi"zuciyarsa bbu dad'i yanufi Asibiti sbd yaduba wad'anda yayima Aiki jiya Friday"tunda yashigo cikin Asibitin yake tafiyarsa cikin izzah baya tanka kowa"kyakykyawar fuskar nan tasa A murtuke take bbu fara'a ko kad'an Acikinta"Abinda yaka mata yayiwa duk wani patient yayi yabar sauran doctors na Acikinsu"dukda week end ne kuwa.....cikin nutsuwa yanufi office nashi yaturo k'ofar yashiga"ko ina fes Angyara sai k'amshin turarensa ke tashi Aciki"gefen fridge yanufa yabud'e"yazaro goran ruwa ya b'alle murfin yakafa Abakinsa"tas ya shanye ya jefar da robar cikin dustbin yana maida numfashi"yaje ya zauna samqn kujerarsa tana lulawa dashi"ya lumshe idanuwansa yana hango In'am cikin zuciyarsa da yadda take tafiya cikin nutsuwa"yana kuma jiyo sautin shagwab'ar ta.....wani iri tsikar jikinsa yaji ta tashi yarrrrrrrrr!"ya bud'e lumsassun idanuwansa da sukayi jaa yana kallon fuskar wayarsa yafara k'ok'arin kiran In'am.....k'irjinsa yabuga da suka sanar masa tayi blocking nasa....ni maryam zatayi blocking nawa??"ya tambayi kansa yana tashi zaune"kiranta yakomayi da wani sabon sim card nashi dabata sanshi dashiba"saidai har tayi ringing ta gama yakoma wani kiran bata d'auka ba"kuma badan bata kusaba"jikinta yabata ko farooq ne yakirata da bak'uwar number....

Ajiye wayar yayi hakan yayi daidai da Anturo k'ofar"wata nurse ta shigo da sallama tana fad'in pls doctor Akwai me labour tana jin.....wata rikitacciyar tsawa yadaka mata yana fad'in kin tab'a ganin na Amshi haihuwa??"jikinta na kirma tana k'ok'arin mgn yaja tsaki yana fad'in you are fire!

Dan Allah kayi hak'uri kaceci rayuwa kark.....get out of my office now! yafad'a da k'arfi"batace komaiba ta fita"yadinga jan tsaki bbu k'akk'autawa"ya mik'e tsaye ya fita dg cikin office d'in"da yawan mutane duk sunsha jinin jikinsu dashi sbd yadda suka yanayinsa"parking lot yanufa yashiga mota yabar wajen"kai tsaye super market yanufa yayima In'am shopping na fitar hankali"ya siyo mata harda su ice cream dasu kilishi da snacks"yanufo gida"lokacin kuma har Azahar tayi"bayan ya iso yayi parking yabar komai Acikin motar ya rufe"yana k'ok'arin tafiya ya hango Auwal da mahmood zasu fita get"da hannu yamusu Alamar suzo"babu musu sukazo suka gaishesa"yabud'e motar yanata fitowa da ledoji manya yana fad'in ku d'auka kubama maryam"iya Abinda yafad'a kenan yayi shiru"Aladabce suka Amsa dato suna d'aukar ledojin suka tafi....lokacin da suka shigo cikin parlourn ummi"In'am na kwance samqn 3 seeter kanta samqn cinyar ummi"da doguwar riga bubu ta material Ajikinta"tana ta bak'in rai ummi na mata fad'an ta d'aga mata cinya ta tashi tayi sallah taci Abinci"saidai dg ummin har In'am d'in kallon kayan da su Auwal d'in suka shigo dasu sukeyi"wanda Atake in'am ranta yabata natane kayan"Autar ummi kuma y'ar gatan yaya Aliyu gashi yace"mu kawo miki"cewar Auwal yana murmushi kodan yasami babban kaso"hararar ledojin da kayan In'am tayi ta d'auke kanta"mahmood yafita yana fad'in Auwal natafi masallaci nidai"okay jirani mu wuce"kai ina kukaga Aliyun yace"ku kawo kayan nan??"cewar ummi"yanzun Agida muka gansa ummi....ni wlh bana so bazan Amsaba"bayan Abinda yamun d'azun shine zai wani kamun kaya gamai son Abin duniya ko? to banaso kama mai....bige mata bakin da ummi tayi yasaka tayi shiru"Aikuwa ta tashi zaune tana kuka ita bataso bazata Amsaba kuma bbu ruwanta dashi"shidai Auwal mamakin In'am dake hakan yakeyi ,dan ya fahimci yanzun bata tsoron yaya Aliyu"kuma shima ransa yabashi soyayya sukeyi itada yaya Aliyun"kinga nidai wlh bbu ruwana iyakata isarda sak'o na kuma isar"kai jeka kayi sallah"cewar ummi fuska Ad'aure"beyi mgn ba yafita dg cikin parlourn"ummi na hararanta tace"d'auki kayan ki shiga ciki dasu"batayi mgn ba ta d'auka ta nufi d'aki"ummi jikinta Asanyaye ta d'auki sauran ta biyota dasu...Auwal na fitowa suka had'u da yaya Aliyu da jallabiya Ajikinsa red colour zai tafi masallaci"yayi saurin cewa"yaya munkai mata"Amma sai wata shagwab'a takeyi da kuka ita bata so"ummi na mata fad'a....

Amamakin sa sai yaji yace"metake so to?"nima yaya bansaniba"to idan ka koma ka tambayar mun ita metakeso kana jina?"dato Auwal ya Amsa yana mamaki yayi gaba..... in'am kuwa saida ummi ta mata jan ido sannan ta Amince ta d'auki kayan"ta raba ice cream d'in da snacks"aka kaima nafeesa"ta d'ibarwa Auwal sauran"tanata b'ata rai ta sha ice cream d'in da snacks"ko Abinci bata nema ba"k'asan zuciyarta kuma tanaso yaya Aliyu yane meta yabata hak'uri...ummi kuma tasha Alwashin zata kirashi ta waya tasanar masa yadena wannan hidimarwa In'am sbd Abinda zaije yadawo...

Bayan sallar la'asar In'am ta shirya cikin yunifoam nata gogaggu"tayi kyau sosai ta fito k'ofar gidan"sbd Auwal zai mik'ata islamiya da mashin nasa"tana fitowa dg gidan taga yaya Aliyu tsaye yana waya"yaci wani zazzafan wanka"k'amshin turarensa har nan Inda take tsaye tana jinsa"yadine bak'i Ajikinsa"kansa bbu hula"da plate shoes na maza A k'afafuwan sa"gaba d'aya tunda ta fito ransa yabashi tana wajen"sakamakon zuciyarsa data buga! baya jin kuma hakan sai idan yana tare da In'am"hakan yasa da sauri ya kalli bakin get d'in gidan su"idanuwa yatsurama baby face nata"yaga tayi mugun had'e rai tak'i kallon gefen dayake"saima k'ok'arin komawa cikin gidan takeyi"wai Abokina baka jinane??muryar brr Ahmed dasuke wayar ta katse masa tunani"zan kiraka Anjima"Abinda yafad'a kenan yana kashe wayar"yakoma kallon Inda in'am take tsaye yaga wayam"sai Auwal dake k'ok'arin shiga cikin gidan"wato sbd ganina yasaka my Angel komawa ciki??"yafad'a Ahankali yana kallon k'ofar gidan.....
yanaga kin dawo ina Auwal d'in??"cewar ummi tana kallon In'am"kanta Ak'asa tana b'ata fuska tace"ba wannan yaya Aliyun bane yana waje tsaye"In'am! ta kirata murya bbu wasa"kafin taci gaba da cewa"me yayan naku ya miki haka wai??"karkimun k'arya kina jina?"kanta ak'asa ta sanarwa ummi komai....dama ba keda nafeesa kuka tafi ba?"to Ai ummi nasan hanani zakiyi shinefa sai nace da ita"to yayi kyau"dg yanzun kika koma yimun k'arya sulaiman zan sakq yazane miki jikinki"dg yanzun ki kiyaye duk Abinda bayaso saiku zauna lafiya ko Autah?"nifa ummi bbu ruwana dashi har y'ar raba daidai da muka k'ullah dashi zan kwance"kuma duk yau ban kai masa komai ba....ummi dai na saurarenta tama kasa mgn"Auwal ya shigo yana fad'in ke dallah kizo muje konayi tafiyata yasin"ki wuce kibisa mana"cewar ummi"In'am batayi mgn ba tabishi suka fita"Abin mamaki yaya Aliyu na tsaye Inda ta barsa"yadad'e da eye glass bak'i"In'am nata cin magani ta hau mashin d'in"tak'i kallon Inda me tubarau yake tsaye..kamar yaya Aliyu yace"Amaidota yakaita da kansa Amma sai yabasar yana kallon su har suka tafi....yasaki Ajiyar zuciya yana tuna koma In'am taci Abinci?"danshi rabonsa da Abinci tun break fast na safe data bashi"yana wannan tunanin yaji horn d'in motar brr Ahmed"yatab'e baki yana kallon motar"bayan yagama parking yafito ya iso gefensa yatsaya yana fad'in"nazo muyi mgn Akan muhseen shiyasa ma nakiraka d'azun ka kashe"d'an murmushi me tubarau yasaki sbd ya lura har yanzun brr Ahmed haushinsa yakeji"haba Abokina uzuri zakamun"bana iya controlling d'in kaina idan kishin my Angel ya motsamun"garama kadena jin haushina"ko yanzun muna mgn dakai ita na hango tana ganina ta gudu Alamar fushi takeyi dani.....wannan kuma Ai laifin kane"koma miye tamaka yadace ka barta ka tafi??balle banga laifinta Anan ba"sannan wanda kakeyi danshi kuma nama sanar masa kai zata Aura yadena kallonta"nasan sbd tayi mgn yaji muryar ta shine ka fusata ko?

To Ashawarance ka Ajiye saurin fushi da zafin kishi"karka manta har yanzun bata san kana sontaba"kaga bazata gane kishi kakeyiba"Abinda tayi kuma tayi daidai kaine kayi fushi bbu k'wak'wk'waran dalili me k'arfi"haka kaine zaka rarrasheta"Allah yasa ta d'auke maka wuta na sati 2"dama tasleem d'azun na tambayata meyasa kuka fita bbu sallama??"nasanar mata komai"tace"dama ta jima tana zargin son yarinyar nan kakeyi....kace gulma kake koya mata kenan??"yafad'a zare eye glass d'in yatab'e baki yana nufar cikin gidan"brr Ahmed yabiyosu Abaya suka zauna kan resting chairs"me tubarau yadubesa beyi mgn ba"hakan yasa brr Ahmed yayi murmushi yana fad'in In'am tafara canza mana kai da yawan surutu"duk wannan miskilancin naka zaka Ajiye sa gefe....mlm pls kasanar mun meke faruwa da muhseen??"Ajiyar zuciya brr Ahmed yasaki yana fad'in zancen gaskiya safwan nason ganin bayansa sbd yasan sirrinsa"ko jiya da dare yatura y'an daba gidan kwansu Allah yasa baya nan sai samarin dake kwana kawai suka samu"suka tambayesu yana ina?
Chapter 40 · 0% Book details