← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 23 OF 65

Sashe 23

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Tunda yaya Aliyu yabar shashensu In'am yakoma d'akinsa yaketa bacci sai wajen k'arfe 10 na safe yatashi"bayan yayi wanka ya shirya cikin suit red colour"yayi wani irin mugun kyau"tamkar irin black America d'in nan haka yayi"cikin takunsa na kasaita da nutsuwa daya zamar masa jiki yanufi part d'in umma sbd yayi break fast....in'am kuwa bacci tasha sosai tama manta da wani yaya Aliyu yace k'arfe 10 zasu fita"tajima tana bacci A parlourn ummi"tana baccin taji Ana dukan center table d'in dake a tsakkiyar parlourn"ta bud'e idanuwanta tana hamma" mahmood tagani tsaye" ya mik'a mata leda bak'a yana fad'in gashi inji yaya yace"minitina 10 yabaki ki fito"batayi mgn ba ta Amshi ledar"bayan ya fita ta duba ledar"tana tunanin idan yaya Aliyu be takura mata ba baya jin dad'i Arayuwar sa....cak tunaninta yatsaya sakamakon babbar robar butter data gani Acikin ledar"bata gama dawowa nutsuwarta ba taji muryar ummi na fad'in ki tashi kije ki wanke kayanki tunda bbu Abinda kikeyi"bazan koma biya miki kud'in wanki ba"wayyo Allah ummi saloon fa zanje"harma nacema yaya Aliyu yajira yasaukeni"kumafa yana waje"keda kina Anan ina kika gansa?? mahmood ya Aiko yakamun butter"kallon butter d'in ummi tayi kafin tace"Aidai kafin Azahar kin dawo ko?"shiru tayi tana b'ata fuska ta Ajiye butter d'in ta shige ciki da sauri sbd kar yayita jiranta"brush tayi ta fesa turare" kasancewar da wankanta tun d'azun"doguwar riga ta Atamfa red da mayafi red ta saka ta yane kanta"ta rataye hand bag nata Agefen kafad'ar ta tana yatsina fuska ta fito....tana fitowa dg cikin d'akin shi kuma yana shigowa"fuskarsa Amatukar d'aure....da sauri tayi baya murya na rawa tace"wlh inata sauri yaya karka gaji da jirana"ta fad'a kanta Ak'asa"beyi mgn ba yafita yana jin dad'in sun saka kaya kala iri d'aya"in'am kuwa ummi taje tayima sallama sannan ta fito waje"tunda ta fito dg get d'in gidan idanuwansa ke Akanta harta bud'e gaban motar ta shigo ta zauna" yaya! beyi mgn ba yadai kalleta"nagode sosai da sak'on dana gani"shiru yayi bece komaiba yana driving d'in nasa"ita kuma tana kallon waje"ina muka nufa?"Ahankali tajuyo tace" zainab saloon zamuje"da wane relaxser kike using?" Organic ne"okay yafad'a be koma mgn ba"in'am dai tunani takeyi meyasa yake mata haka bayama nafeesa??bayan ita bbu wata Aalak'a ta jini tsakaninsu sai zumuncin daya had'a iyayensu....daga yau karna koma ganin kin fito bbu d'an kwali"nidai yaya kaina ke ciwo idan na d'aura saidai nafi gane mayafi ko hula"bbu ruwana idan nakoma ganinki zaki Amshi hukunci ne"turo baki tayi tak'i mgn"har suka iso Adaidai shagon"bayan yayi parking ya kalleta yana fad'in Awa nawa zakiyi Aciki?"idan bbu layi minti 40 nagama"idan Akwai layi zanfi Awa guda"kud'i yazaro bema san ko nawa bane y'an 1k ya mik'a mata"yaya wa'annan kud'in sunyi yawa"be wuce ta Amshi 4k na mai da sallamarta ba"kuma ni Inda kud'i a hand bag nawa"muga hand bag d'in naki"yafad'a yana kallon ta"gaba d'aya duk ta daburce sbd yadda taga yanata kallonta"sai taga idanuwansa sun cika wajen" mik'a masa tayi tayi k'asa da kanta"bud'a jakar yayi ya saka kud'in hannunsa yana fad'in idan kin fita saiki yar ko?"kije ki gani idan bbu layi"to nika d'ai zanje?"Amamakinta sai taji yace"kinaso na rakaki?"kanta ta gyad'a masa"Amma tak'i yarda ta kallesa"sai kuwa taga yafito dg cikin motar"itama fitowa tayi tana tunanin Anya yaya Aliyun data sanine yau??"ji yadda yaketa son faranta mata....kin tabbatar maza na shiga har ciki?"tattausan muryanshi ta katse mata tunani" ah ah nama manta ba'a shiga"beyi mgn ba suka tsaya Abakin k'ofar shagon me tubarau yayi knocking....Ihu In'am dake tsaye gefensa ta saki tana fad'awa jikinsa ta chikwikwiyesa sbd bak'in k'adangare jan kwatakware data gani Ak'asa bakin k'ofar shagon"wayyo Allah yaya Aliyu k'adangare karya haumun samqn k'afata ni.....da sauri yaya Aliyu yadafe bakin k'ofar shagon da hannunsa guda"sbd hajijiyar dayaji ta d'aukesa"yayinda hannunsa guda ke saman kafad'ar In'am"mamaki yakeyi Aransa meyasa yanzun idan jikinsu danata ya had'u yakejin wani iri??...yaya kadubamin yatafi?"cewar In'am Atsorace tana k'ara b'oyewa Ajikinsa"hakan yayi daidai da wata mace ta fito dg cikin shagon"ta bisu da kallo sbd tasan in'am"yaya Aliyu janyeta dg jikinsa yayi ya rik'e hannun ta yana fad'in ki nutsu k'adangaren ya gudu ko?"Ayya ta tsorata ne ko?"Eh"ya Amsa Atak'aice"In'am ta kalleta ta gaisheta ta Amsa tana fad'in my costumer ki shigo mana"ogah ina wuni?"lafiya qlau ya Amsa yana kallon fuskar In'am"daya fahimci har yanzun Atsorace take"In'am tace"dama Akwai layine?Ah ah bbu kowa"kallon yaya Aliyu tayi dashima ita yake kallo ta cikin tubarau nasa"cikin shagwab'a tana b'ata fuska tace"yaya pls kajirani mintina 30 Angama fa"kansa kawai yagyad'a mata"matar ta tura k'ofar ta shiga"shi kuma yacika hannunta yana fad'in kije mana"k'asa ta kallah sannan ta tura k'ofar ta juyo ta kallesa sannan ta shiga ciki"yaya Aliyu yasaki Ajiyar zuciya jikinsa Amace yanufi cikin motar yashiga"tunani yakeyi Aransa tayaya zai nunawa in'am soyayyar sa ??yana wannan tunanin yaga wulgin wata mota tabiyo ta gabansa"kamar Ance ya kalli motar"kawai yaga kamar yasan motar"tana yin gaba yabi number d'in motar da kallo..da sauri yatashi motarsa yabi bayan motar"sbd yatuna motar daya gani ce kwanaki da Akazo d'aukar masa in'am da ita
ba'ayi nassara ba"Anutse yake bin motar sbd kar Agane yana binta.....Abin mamaki yaga motar nayin Anguwar da gidan safwaan yake"be gama mamaki ba saida motar ta shiga har cikin get d'in gidan safwaan"juya Akalar motar yayi zuwa Inda ya baro"yana tunanin zarginsa zai d'arsu Akaro na biyu Akan safwaan"Amma bara yanemi Ahmed koda zai gano wani abu Awajensa"yana driving d'in yakira brr Ahmed....hands free yasaka wayar yana cigaba da driving"dg d'ayan b'angaren brr Ahmed bugu 3 tayi ya d'auka cikin zolaya yana fad'in me tubarau na In'am....pls Ahmed kana ina?"lafiya dai ko?"ba lau ba"subahanallahi"ina gida kasan week end ne"okay gani nan zuwa yanzun"dg haka yakashe wayar"yanufi wajen saloon d'in"tun kafin ya Ida isowa ya hango In'am ta fito tana b'ata fuska tanata waige waige taga A ina zataga motarsa"d'an murmushi yasaki yana fad'in my Angel bazaki dena shagwab'a da rigima ba"gashi harkin girma baki dena ba"yazama dole na siya miki waya sbd nadinga kiranki in buk'atar hakan yataso...horn ya danna mata A bayanta da k'arfi"ta juyo da sauri"Ajiyar zuciya tasaki dataga motarsa" tana turo baki tak'i motsawa dg Inda take"zuge glass d'in motar yayi ya zuro kansa yana fad'in kizo muje kona barki Anan"Amma yaya shine kayi tafiyarka ko?"bece komaiba yamaida glass d'in yarufe"ita kuma tazo ta bud'e gaban motar ta shigo"saidai dataga kamar ba hanyar gida yayiba tayi mamaki"kanta ak'asa tace"yaya ina zamuje?"gidan Ahmed"to kuma kar ummi ta jirani"sbd tace idan na dawo zanyi wanki"wane irin wanki?"kasan yaya Ada badamun wanki Akeyi wai yanzun na girma nayi da kaina"ta fad'a kamar zatayi kuka"hmm! shiyasa nace kin cika rangonta"Inda zanje bazan fasa zuwaba garama ki hak'ura"shiru tayi batace komai ba"tana tunanin wata rana yanada kirki wata rana kuma sai Ahankali"zaki iya gane yaron dayazo kwanaki islamiyar ku yace nine naturosa ya d'aukeki?"Eh idan na ganshi zan ganeshi"shiru yayi bece komai ba yaci gaba da driving d'in yana tunani"har suka iso gidan brr Ahmed....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
25&26
........

Adaidai bakin get d'in gidan dg waje yayi parking"ya saci kallon mutuniyar tasa yaga idanuwanta cike da k'wallah"yatab'e baki yabud'e k'ofar yana fad'in karki bari na ri gaki fitowa"dg haka yafita dg cikin motar yanufi bakin get"knocking yayi sau 2 sannan yajuyo yaga In'am ta fito tayi tsaye"beyi mgn ba yazo yayi lock d'in motar sannan yamatso dab da ita yakama hannunta"kukan shagwab'a tasaka tana fad'in nidai yaya ka barni na hau Adaidai ta ko?"shareta yayi yanufi ciki da ita"bayan sun gaisa dame gadi suka nufi interest d'in shiga cikin gidan....kinsan Allah koki nutsu kona b'ata miki rai"dg yanzun idan gulman fitarki yatashi karma ki koma cemun na kaiki"yak'are maganar yana yin knocking d'in k'ofar parlourn"in'am tana taso ta turje masa ya rik'e hannun nata gam"yakama fuska ya d'aure"Ahaka brr Ahmed yabud'e k'ofar"yana sanye da farar jallabiya Ajikinsa"yabisu da kallo"ba k'aramin kyau da burgesa sukayiba"Aransa yana yiwa Abokinsa fatan mallakar in'am Amatsayin matar Aurensa"irin yadda ya rik'eta tana son guduwa tana turo baki "shi kuma yana kallonta yana danne dariyarsa zaka fahimci ba k'aramin matching da juna sukayiba.....da Alama Abokina tursasa In'am kayi tabiyoka ko?"yafad'a yana murmushi"In'am tayi saurin gaishesa cikin girmamawa"yayinda me tubarau ya zabga masa harara"yayi dariya yana gyara musu suka shigo ciki"yana rik'e da hannun ta yayi sallama cikin k'asaitacciyar muryarsa me cike da haiba da dad'in Amo"tasleem dake zaune aparlourn ta Amsa sallamar tana fad'in gaskiya doctor ka koma"rabonka da gidan nan tun ina Amarya"In'am kawai nake murna da zuwanta"dr Aliyu na murmushi yakalli brr Ahmed yace"kasaka baki Abokina kasan yana yin Aikina"babu ruwana Anan"daka dawo tun last week ai baka lek'o zumunci ba ko?"cewar brr Ahmed yana zama gefen tasleem"me tubarau yaja In'am suka zauna kan 2 seeter"yana fad'in yanzun nazo na goge laifina ko?"ina baby hafsat?"tana bacci doctor ina kwana?"ya Amsa da tambayarta gida"In'am kanta Ak'asa ta gaisheta"ta Amsa tana dariya tace"oh In'am Autar ummi kin girma ko? tadai girman nan gaba"yanzun ma rigima takeyi batama so zuwanmu nan gidan ba"bafa haka bane Anty tasleem Akwai abinda zanyi Agida shima yaya yasani"ta fad'a tana zare hannunta dg cikin nashi"taso muje ciki mu gaisa"dato In'am ta Amsa suka bar parlourn"tasleem ta fito tazo ta Ajiyewa dr Aliyu drinks sannan ta koma d'aki"brr Ahmed na kallonsa yace"meyasa baka sakewa yarinyar nan fuska kodan sbd ta saba da kai?"hmm! maryam dakake ganinta idan ta botsare sai Addu'a"jiyafa wajen party sukaje saida jikinsu yagaya musu kuwa"bakada kirki me tubarau"ina jiye maka karkayi sake wlh"dan Allah mu dena wannan zancen "kasan meke tafe dani?"kansa ya girgiza beyi mgn ba.....

Abinda yafaru yasanar masa yana k'are maganar da cewa"miye ma'anar hakan Ahmed?"dama tunda nadawo dg london nake zargin safwaan ne yasace kud'in nan ta barauniyar hanya"dukda zargina game da turowa d'aukar Maryam be tabbata Akan saba saina gama bincike sosai......Abokina kenan!
Chapter 23 · 0% Book details