Sashe 33
So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 10 min read
Lallai kai ba mutum nagari bane safwaan"idan kayi tunanin dan gan takata da yaya Aliyu bame k'arfi bace kayi kuskure"kana buk'atar komawa islamiya kaje ka tambayo minene hak'ik'anin hakk'in mak'otaka??wani k'aulin sunce ma mak'oci na gari yafi d'an uwa na jini"sbd kafin d'an uwanka yazo yataimaka maka shi mak'oci yataimaka maka"inaso kasani! yaya Aliyu yafimun ko wane namiji Aduniya idan Ancire mahaifinah!! koda yaya Aliyu baya nan kai baka isa na kulaka ba.....iya nan In'am tayi shiru sbd lura datayi mutane nata kallonsu"wasu na mgn k'asa k'asa suna dariya"yaya Aliyu tsaye yayi k'ikam kamar Andasa A wajen"sbd ba k'aramin mamakin kalaman In'am yayi ba"yak'ara tabbatar wa tanada wayo sosai" tana kuma Amfani da Iliminta"da ido yabi safwan yana murmushi yace"baka buk'atar nakoma yi maka wani bayani"saidai inaso kasani har gobe idan mutum yana Aikata Abu me muni tofa gani yakeyi kowama haka yakeyi....yaya Aliyu be kai Aya Azancen saba"safwaan dake tsaye yana huci yad'aga hannu da nufin ya mari In'am dake zaune"sbd yaji zafin ta tsinkasa cikin jama'a"yaya Aliyu ya rik'e hannun nasa da sauri yana bashi wasu punches A gefen fuska cikin zafin rai"In'am ta d'ago kanta tana kallonsu"wuri ya d'auki hayaniya"safwaan yadafe gefen fuskarsa yana tab'o bakinsa yaga jini"cikin tsananin b'acin rai yana girgiza kansa yace"nika fitarma da jini?"yaya Aliyu beyi mgn ba yamasa wata wawar chakuma yana fad'in" ka isa kace zaka dokarmun maryam ne?"nace ka isa? yafad'a Atsawace yana cigaba da kaimasa duka"kasancewar k'arfinsu ba d'aya ba"duk yadda safwaan yaso yarama Abin yaci tura"body guards nasa suka finciko yaya Aliyu da nufin su dakesa"In'am ta saki k'ara tana d'aukar wayoyinsu sbd ta lura wajen ya hargitse da hayaniya"harbin bindiga security sukayi"hakan yasa aka nutsu"Amma yaya Aliyu yahau d'okin zuciya dukan body guards d'in safwan yakeyi tako ina"saida security sukazo suka raba"safwan na tsaye yana huci"yanashan mugun Alwashi a zuciyarsa game da yaya Aliyu da In'am....In'am na kuka tazo ta fad'a jikinsa ta rungumesa tace"dan Allah yaya kayi hak'uri kabarsa mu tafi gida kaji?"shiru yayi yana maida numfashi"yana jin tsananin k'aunar In'am da zazzafar soyayyar ta na k'aruwa Azuciyarsa"saidai duk jikinsa ya mutu murus"yana lura Ana kallonsu"hannunsa guda yasaka ya janyeta dg jikinsa"yarik'e hannunta ya d'auki ledar take Away nata sukayi waje"sbd tuni safwaan da yaransa sunbar wajen"In'am dukta tsorata tayi dai shiru"sai bayan sun shiga mota yana driving d'in ya kalleta yace"my Angel karki sanarwa kowa Abinda yafaru"to yaya Amma da Alama mutumin nan bashida kirki kuma mak'iyinkane ?bayan Abaya kuma Abokin kane"ko Abaya my Angel nasan makiyinane kawai ina basarwa ne bana nuna masa nagane"sai yanzun yafito zahiri yanunamun k'ina yakeyi"to shiyasa sani Allah ya shiryasa"Ameen idan zai shiryu"canza topic d'in tayi da cewa"lahh yaya har la'asar tayi fa"yes Amma ke Ai bakya yin sallar ko?"zaro ido tayi tace"banganeba?"shiru yayi yana d'an murmushi yana tsotsar lip nasa na kasa"itama kunya taji sosai"dukda ta fahimci ko period yake zaton takeyi"kuma A lissafinta sai jibi satday sannan bak'onta zaizo...duk yaya Aliyu na lura da ita beyi dai mgn ba"suna shigowa cikin layin ya kalleta"tayi k'asa da kanta"shikenan zaki tafi ki barni ko my Angel?"kai yaya kamar wacce zata mutu?"bazaka shigo Anjima ba ku gaisa da ummi sbd ta.....sai kuma tayi shiru sbd ta tuna umma ta hanashi zuwa"shi kansa yafahimci Abinda ta tuna yasaka bata Ida maganar taba"kije zan kiraki"yanzun wanka zanyi naje nayi salla"yafad'a Ahankali yana kallonta"to yaya Amma ka kwanta ka huta ko?"zan huta d'in my Angel"gobe k'arfe nawa kuke da paper? 8 am ne ai"okay yafad'a yana gyara parking"ta bud'e k'ofar ta juyo ta kallesa"yayi saurin janye idanuwansa dg barin kallon ta"yaya zan tafi to"kije my Angel Amma ina jin kamar karki tafi"Anjima zan zo Ai part d'in mommy"to shikenan"me kikeso na siya miki da dare?"bbu komai fa yaya"dg haka ta fita tana murmushi ta rufe k'ofar"be wuce ba saida yaga ta shige gida....da sallama in'am ta shigo cikin parlourn"fuskarta cike da Annuri"ummi dake zaune A parlourn tana lazimi ta Amsa sallamarta"fuskarta Ad'aura tace"dg ina kike?"gaskiya zaki fad'amun sbd bakije wajen nafeesa ba"natura Auwal yakiraki mintina 15 da suka wuce Akace baki zoba"Ayya ummi muna fa Asibiti wajen matar yaya Ahmed Abokin yaya Aliyu"ta haihu ne mukaje nida yaya"shiru ummi tayi tana kallon ledar hannunta"kafin tace"yaushe ne Aka haihun"yaune ta sami namiji"Allah yaraya zanje zuwa ko jibi nayi mata barka"ta k'are maganar tana tunanin dama tunda taji In'am shiru ranta yabata tana tare da Aliyu"Ajiye ledar in'am tayi ta nufi kitchen"bata jimaba tadawo da plate da robar lemo"ummi dai nata kallonta harta zuba Abincin k'amshinsa nata tashi"kazar kuma d'iba tayi ta zuba Asama"ina kika sami wannan Abincin??"yaya ne yasiyamun da mukaje gidan cin Abinci"nace nidai bazan ciba ga mutane Amun take Away"bazaki dena cemasa yasiya miki Abuba ko?"kai ummi shinefa yasiyamun daya fahimci banci Abinciba"ta k'are maganar tana bissimilah tafara cin Abincin"Auwal yashigo yabita da kallo yana tab'e baki yazauna yana cewa"kefa kurace game da nama"ina kika sami wannan Abincin nasan dai bashine Aka dafa nan gidan ba??"kin ganshi ko ummi?"wlh koka k'yaleni kona sanarwa da yaya"tamkar yakai mata duka haka yaji yaja kwafa bece komaiba"ummi dai na kallonsu bata saka musu bakiba A maganar tasu"ummi ga wannan saiki ciko?"nidai na k'oshi Auta"ki bama Auwal dai....bana ci ummi niba bak'on kaza bane"idan yanzun naga dama zanje bakin hanya na siyo naci harna ture"dad'in Abun siya miki yaya Aliyu yayi bada guminki kika siya ba"dan nasan idan bashiba babu wanda zai siya miki....kukan shagwab'a tasaka"ummi taja tsaki tana fad'in bazaka dena jantaba ko Auwal?"haka kawai kuyita sakani mgn sai kace ku k'ananun yara ne?"shiru duk sukayi sbd shigowar yaya sulaiman"In'am na ganinsa tace"yauwa yaya sulaiman yaushe zamuje na zab'i kayan??yaya yace mun munje ne?"nasanar masa ah ah"harara ya ballah mata yana zama kan kujera yace"kina jinta ummi?"inaji sulaiman meye zance?"kaje ka kaita d'in ta zab'a"ka maida masa cikon 200k d'in kabashi hak....ah ah ummi ki barshi Ayi cefanen tunda kinada kayan Abinci da Abba yasiya miki"bbu kyau maida Alkhairi"kawai dai kimasa mgn da kanki yadena sbd gudun Abinda zaije yadawo"nima Abinda na hanga kenan ai"In'am dai nata d'aure fuska ta tashi tana gyatsa ta d'auki sauran naman ta shige kitchen ta saka a fridge"sannan ta shiga d'aki tayi Alwalah tayi sallar la'asar"ta jima tana Azkhar"sannan ta shiga wanka"bayan ta fito ko mai bata shafaba sbd zafi"turaruka kawai ta shafa ta saka riga da wondo pencil ta saka hijab iya gwiwa ta fito parlourn"har sannan ummi dasu yaya sulaiman na zaune sunata kallo"ke ! jeki kiramun my nafee"cewar yaya sulaiman ko Ajikinsa"ummi ta girgiza kanta batace komaiba"in'am ta saka takalmi tana turo baki ta fita"saima Asannan ta tuna da yaya Aliyu da Abinda yafaru d'azun tsakaninsa da safwaan"wani irin zafin safwaan da k'insa taji Aranta"Afili tace"kai yaya Aliyu nah jarumine kuma bashida tsoro"tafad'a tana murmushi ta fito k'ofar gidan"tana shigowa cikin gidansu nafeesa ta hango yaya Aliyu zaune kan resting chairs a compound d'in gidan"yana sanye da fara k'al d'in t shirt da wondo 3 quarter bak'i"ba k'aramin kyau da burgeta taji yayiba"suna had'a Ido dashi yamata Alamar tazo da hannu yana d'an murmushi"nok'e kafard'arta tayi tana nuna masa part d'in mommy"d'aure fuska yayi yana nuna kansa wai shinefa?"kuma idan bata zoba sun b'ata ita dashi"yak'are nunal d'in yana juya mata baya Alamar yayi fushi"ta dinga dariya Ahankali ta nufosa cikin sand'a"tafi ta masa Agefen fuskarsa dg bayansa"yajuyo yana kallon yadda take dariya beauty point d'inta na lotsawa"my Angel yanzun kin kyauta kiga babban Amininki ki wuce??"bayan kuma kincemun Anjima zaki shigo?"Ayya yaya wlh ba haka bane"d'azun ma ummi fad'a tamun ta Aiko nan Ance bani nan"kuma yanzun yaya sulaiman ya Aiko na kira masa nafeesa karyaji shiru yayita mun fad'a"ta k'are maganar kanta ak'asa"yaya Aliyu na kallon d'an bakinta yace"zauna na kirata ta waya"dg haka yafara danna waya"ita kuma ta zauna Agefensa"kamar Ance ta d'ago kanta ta hango mama gaje zata wucesu tana jifarsu da mugun kallo"k'asa tayi da kanta tana jin tsoron kar mama gaje taje ta sanarwa umma ta gansu....yaya Aliyu dake waya da nafeesa duk yana lura da komai"shima Aransa beso ta gansuba"saidai yadda yafahimci In'am ta damu"sai yaji bbu dad'i"Ahankali yace"my Angel gata nan zuwa yanzun"to yaya bara naje gida"kawai dai kina guduna bakyason mu zauna na ganki ko?"nifa ba haka bane yaya Aliyu"tayi maganar cikin shagwab'a tana hango nafeesa"ya lumshe ido yana fad'in gata can ta fito tashi kuje"kicema ummi ina gai da ita"dg haka yayi shiru be bud'e ido ba"ita kuma ta tashi tsaye ta d'auki ruwan dake gabansa saman table"ta watsa masa Ajiki tana dariya"yabud'e idon yana kallon ta tattausan murmushi shimfid'e Asaman kyakykyawar fuskarsa"yana jin kamar ya janyota jikinsa ya rungume ta"murya can k'asa yace"my Angel nine kika jik'a?"gwalo ta masa batayi mgn ba tayi tafiyarta"yayi d'an murmushi yana tuna time d'in da take y'ar 4 yrs idan yana wanke musu kayansu shida ita tayita jik'ashi da ruwa tana dariya......
mama gaje Anfa samu duniya ta dad'e kunnuwanta da yawan zund'enta da mutanan Anguwa keyi tana hidimar gabanta"batada Aiki dg ta wanke goma saita tsoma biyar"tayi tafiyarta yawon bin garinta"ga masoya nata fitowa neman Auren zubaida Amma tak'i Amincewa "sbd tafi son me kud'i yafito idan har batayi nassarar Aliyu ya Auretaba.....bakinta cike da gulma ta nufi part d'in umma"wanda rabonta da gidan kusan wata 2 kenan"umman na zaune kan kujera tana kallo A sunnah tv mama gaje ta shigo"Amsa sallamarta tayi tana fad'in b'atan kai kikayi gaje? tab'e baki tayi tace"ah ah nadai dena zuwane sbd kema ai baki son zuwa Inda nake"saidai ki kirani ta waya kawai"bazaki gane halin danake ciki Agidan nan ba"ko fita yanzun Alh ya hanani .....ta shiga yimata bayani" hmmm! yo wacece ta rabaki da mijinki inba binta da memuna ba?"idan ya gaji dake sai Aliyu yabaki gida cikin gidajensa ki koma"kema Ai kin Haifa sai wata tsiya?"na rasa meyasa bazaki iya tashi tsaye kan mutanan nan ba?"yanzun haka wlh zaune na samu Aliyu da shegiyar yarinyar nan can nesa da get suna fira"ina zaton shi be ganni ba"idan nayi mgn kice kin rabashi da ita"to wlh yana nan tare da ita.....shigowar Abba cikin parlourn kamar An jehosa shiyasa duk sukayi shiru gaba d'aya....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
39&40
.........wani irin mugun kallo Abba ke jifarsu dashi su duka d'aya bayan d'aya"fuskarsa Ad'aure yana dg tsaye cikin b'acin rai yace" kwana 99 na barawo"rana guda tame kaya"tuni na jima da fahimtar kome takeyi na rashin daidai" kece kike mata Aza me kantu ruwa! dg yau nakoma ganinki Agida na hukuma ce zata rabamu"tunda kin zama bak'ar munafuka me had'a husuma"naji duk Abinda kike sanar mata"ke kuma sbd ta d'aukeki shashasha kina bin Abinda takeso ko??"innalillahi wa inna ilaihir raju'un"sharri zakamun Alh?"idan bakaso nadena zuwa maka gida Ai zahiri zaka sanar mun baka watsamun tsaba kaji su bini ba....cewar mama gaje tana sakin kukan munafurci"umma ta dubi Abba tana fad'in bakada hujjar rabani da y'ar uwata ka raba zumucin Allah"nagaji da irin wulak'ancin dakake mun"okay to shikenan tunda kin gaji kije gidanku saina nemeki"bazan jeba saida takarda ta"kasani duk Abinda kamun kaje kaida Allah"kana nuna banbanci tsakanina da binta"da wata banza da baka Aura ba....ga banza nan kusa dake da bata k'aunarki"kin kasa ki gane"Ayanzun ba zaki tab'a ganeba sai nan gaba idan ta kwab'e muku"ina me tabbatar miki da cewa nan gaba sai kin zubar da hawaye sbd wannan"yafad'a yana nuna mama gaje dake sharar k'wallah"yayinda kalamansa na k'arshe suka saka jikin umma yin sanyi"mama gaje ta mik'e tsaye tana fad'in nida gidanki har Abada tunda mijinki yafini"dg haka ta fita...ki tashi ki bita mana"bazan bitaba Ibrahim! ni kike kira da Ibrahim hauwa?"Eh nace kayi duk Abinda kada dama"bece komaiba ya juya yafita dg cikin parlourn ransa Ab'ace"umma ta fashe da kukan bak'in ciki"tana Ahaka yaya Aliyu yashigo da kayansa da in'am ta jik'e masa....gabansa yafad'i da yaji sautin kukan mahaifiyar tasa"jikinsa na rawa ya zauna kan kujera"cikin karya harshe yace"ummah! umma dan Allah kiyi shiru ki fad'amun meya faru??"ta d'ago kanta tana share hawayenta tace"Aliyu na gama zama da ubanka!