Sashe 38
So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 5 min read
Acikin mintina 35 yaya Aliyu ya gama shiryawa cikin sabbin k'ananun kaya"red d'in t shirt da bak'in trouser"takalmi,Agogo, glass duk bak'ak'e yasaka"jikinsa na fitar da wani irin ni'imtaccen k'amshi me tsayawa Azuciya...duk macen datayi Arba da dr Aliyu me tubarau indai batada Aure dole ta k'yasa...lolx"ba k'aramin kyau wankan yamasa ba"yafito masa da kamalarsa da zatinsa"d'an murmushin gefen baki yasaki yana shafa bak'in sajensa daya kwanta lub"ya lumshe ido yana tuna k'ananun pink lips d'in In'am"wayoyinsa guda 2 ya d'auka dake samqn mirror yafito dg cikin bed room d'in"yasoma saiya gyara sashen nasa sannan yafita Amma zuciyarsa nason kasancewa da In'am"yanaso yakirata yana tunanin karta tambayesa meyasa d'azun yakashe mata waya??..."da wannan tunanin ya rufe part nasa yanufi part d'in hjy"sbd Abba yace"yaje yadubata tana fama da ciwon mara"had'e fuska yayi sosai sbd yasan tsab zata masa y'an surutai indai hjy ce"cikin nutsuwa yatura k'ofar parlourn ya shiga....yanzun fisabilillahi Abinda kikamun kenan nafeesa?"da wuya kiga Annabi S A W gaskiya"haba hjy wane irin bak'ar fata kikemun haka?"ban saniba"Akan me zaki cuceni ki b'atan parlou da shan rake?"kece kika gyaramun ko kuwa binta ce ta gyaramun??nafeesa na k'ok'arin mgn taji tattausan muryanshi yana yin sallama"hakan yasa tayi shiru tana fad'in yaya ina kwana?"lafiya qlau"kije ki kiramun MARYAM"iya Abinda yafad'a kenan ya zauna gefen hjy kan kujera"tanata hararar sa kamar yayi dariya Amma yadake....to zakin fama"ka shigo fuska bbu rahama kamar An sanar maka da sak'on mutuwa?"Ai dole kayi kwantai kak'i Auruwa sbd baka fara'a"to dama ina son ganinka"nayi lissafi shekaranka 35 Aduniya Amma bakayi Aureba"kodai bakada lafiya ne ko kuwa da gaske kwantai kayi???"yatsina fuska yayi yace"meke damunki?"Abba yacemun kina ciwon k'afa bayansa sai me??"Ai dama kai ba'a maka Abin Arzik'i"ina maka mgn me mahinmanci kai kanamun wata"okay idan lafiyarki qlau nizan iya tafiya"dan Allah idan katafi katashi sama kajiko"in bacin kanada sunan saiyadina Aliyu wlh dana d'ebe maka Albarka"girgiza kansa yayi domin har surutun hjy yafara isarsa"Ak'ule yace"idan baza kimun bayani ba zanyi tafiyata...."tab'e baki tayi ta shiga sanar masa Abinda ke damunta"sai bayan tayi shiru sannan yace"zan kawo miki magani"to Allah yabaka iko"Abinda nakeso dakai shine kayiwa hauwa uwarka fad'a ta nutsu"in bacin mutuncina da ubanka yasaketa jiya"na bashi hak'uri ka kwatanta mata"idan kuwa ta zab'i saki damuwartace babu Inda zataje ta tsugunna sbd iyayenta sun mutu"dandai kai kana matsayin jikana dole kaji mgn ta bazan bari kasiya mata gida ba....Agundure yaya Aliyu ya mik'e tsaye yafita bece komaiba"hjy ta raka bayansa da harara tana mita.... in'am bayan sun gama waya da yaya Aliyu ta tashi ta sauya kaya zuwa"riga da siket na Atamfa me golden pink &black colour ta saka"sosai kayan suka Amshi jikinta d'as"ta fito a kyakykyawar budurwarta"d'aurin d'an kwali ture kaga tsiya tayi har gashinta data d'aure ya sakko Abayanta"pink lipstick ta shafa"ta fesa turare tana kallon yadda tayi kyau Acikin mirror"wajen hand bag da shoes nata ta duba"ta d'akko pink"sannan ta d'akko mayafi pink"lokacin k'arfe goma saura"shiru tayi tana tunanin ta yaya zata sanarwa ummi zata fita??"tafi mintina 10 A tsaye"dg k'arshe ta fito tana rik'e da wayarta Ahannunta.....Auwal na zaune a parlourn yana kallon ball"yabita da kallo yana fad'in hjy mery babbar yarinya! irin wannan zazzafan wanka Ai saiki burkita mazan layin nan"wlh kinyi kyau sosai my lovely sis"yafad'a yana murmushi"In'am kuwa dariyar data fito mata da kyawun fuskarta ta saki"sbd tasan wani Abu Auwal keso wajenta"dan da taji yana yimata haka to kud'i yakeso"bayan ko jiya taji ummi na masa fad'an tunda yanzun yashiga har label 2 yadinga zuwa kasuwa wajen yusuf" shima yasamu na kansa bawai Abashi yakashe ba....hmm ! broth kenan"wlh da gaske nakeyi"kinfa had'u da yawa"naga Alamar kinfi kowa gidan nan kyau"bakai kad'ai ke fad'in hakan ba"ta fad'a tana k'ok'arin nufar d'akin ummi"zokiji mana my sis"juyowa tayi tana gallah masa harara"meye zan samu?"nasan dai yaya Aliyu yana cika miki jakarki"kona credit ki bani pls"nima dai zan koma shago zuwa gobe"murmushi In'am tayi sbd dama ita can batada rowa"wasu ragowar 6k ne cikin jakar"suma tun 20k d'in da yaya Aliyu yabasune sadda zai tafi k'asar Cairo"ga 4k nan ka rik'e"credit ina dashi bara na maka transfer yaya yasamun jiya "kai godiya nake Autar mu"yafad'a yana Amsar kud'in"hakan yafaru kan idon ummy data fito dg d'akinta"ta Aiko masa da harara tana fad'in wayon daka saba yimata shine kake mata ko?"sosa k'eya yayi yak'i mgn"ummy tabi Autar tata da kallo tana fad'in masha Allah Aranta"Afili kuwa d'aure fuska tayi tana fad'in ina zakije kika ci gayu haka??"kai ummi gidanfa yaya Ahmed zamuje da nafeesa"dg nan kuma naje na zab'o kayana wajensu yaya sulaiman ko? indai itama nafeesar be siya mataba basai kinjeba da ita sbd bbu dad'i yamiki Abu ita be mataba"in kuma dole sai kunje"zan kira sulaiman d'in itama ta zab'i irin naki saiya biya kud'in"dato In'am ta Amsa tana tunanin kar Anjima kuma yaya sulaiman yace"basu zo da nafeesar ba..... sallamar nafeesar yakatse mata tunani"ummy na murmushi ta Amsa"Akunyace suka gaisa da ummi"bayan ta Amsa ta wuce ciki tana sanarwa In'am karta wuce k'arfe 2 bata dawo ba.....beauty kinga yadda kikayi kyau kuwa??"cewar nafeesa"d'an murmushi In'am tayi tana fad'in dama wajenki zanje"to ni kuma yaya Aliyu yace"na kiraki...gabanta taji yafad'i ta saci kallon Auwal taga kallo yakeyi"dining Area ta wuce"ta d'auki wata food flux data Ajiye suka fita Atare"bayan sun fito tace"wai ina yaya Aliyun yake?"yana part d'in hjy"taff bazan jeba gaskiya nafee"kinsan halin hjy da mita tayita gaya maka mgn"karki damu muje kinsan dai halin yaya"dukda ke yanzun y'ar gatansa ce ko?"murmushi In'am tayi tana sanar mata gidan brr Ahmed zasuje"kuma harda ita zasuje...wlh indai bashine yace muje ba bazan jeba in'am"haka kawai ki jamun wajensa kinsan dai halin yaya beson shishshigi?"In'am na k'ok'arin mgn suka hango yaya Aliyu tsaye bakin k'ofar shiga parlourn mommy"ya tsare In'am da ido yana kallo tun dg tafin k'afarta har zuwa baby face nata"dukda A zahiri za'a zata ba ita yake kalloba sbd ya b'oye idanuwansa cikin glass d'insa...ba k'aramin kyau yau yaga tamasa ba"dukda yasan Angel d'insa beauty ce Amma bata tab'a yimasa kyau irin na yau ba"sai yaji kamar yaje yayi hugging nata"sai dai kuma k'asan zuciyarsa yana jin tsananin zafin kishinta.....