← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 48 OF 65

Sashe 48

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Bayan ya kimtsa yaci Abinci merai da lafiya"ya zauna parlourn sa"shida wani Abokinsa da yayi sanadin shigarsa k'ungiyar"Abokin nasa yadubi safwaan yana fad'in yanzun da gaske zaka iya bada bahbah Akashesa?gaban bahbah dayake k'ok'arin yaye labulen k'ofar yashigo yafad'i"ya lab'e sbd yaji meke faruwa? dan yasan safwan ba imani ne dashi ba"saida safwan yasaki wani shegen murmushi Agadarence yace"damisa ceni k'i sabo"waye bahbah Allah natuba?"duk matsayin dayake dashi Aguna yakai darajar mahaifina ne??

Ah ah be kaiba"Ashe ka gane?kaga kuwa tunda na iya bada ran mahaifina dan wani bahbah ai Abu ne me sauk'i"gashi Abin farin ciki babban mak'iyina dr Aliyu me tubarau shima k'anwar mahaifiyar sa datake a cikinmu zata bada mahaifiyarsa jibi zata kaita zuwa gata Afarka ta mace.... yak'are maganar yana dariya ko Ajikinsa"kai Abokina bala'ine kai"yanzun wai ina muhseen??"wlh bansan Inda yab'uyaba"bbu Inda ban turaba Amma ba'a ganinsa"shi kansa duk ranar dana gano Inda yake dodo zan bama jininsa yazuk'e"tunda Ance mutum 2 kawai kake badawa cikin shak'ikan ka.....iya nan bahbah yaji yabar wajen sbd gudun kar Aganshi"gabansa na wani irin dukan tara tara yabar gidan da wani irin mugun sauri"me gadi na masa mgn yace"yabari yadawo"yana fitowa dg get house d'in safwan Anata kiran sallar isha'i"acab'a yatara ya hau"suka nufi Anguwar G R A nassarawa"zuciyarsa Adake yana ganin bbu matsala idan yatona Asirin safwaan"tunda harshima zai iya ganin bayansa"lokacin da Aka Ajiyesa daidai k'ofar gidan Alh Ibrahim" yaya Aliyu na fitowa zai tafi masjeed sallar isha'i"kasancewar Anguwar da nefa k'anyar take da haske ko ina"hakan yasa yaya Aliyu kallon fuskar bahbah"haka nan yaji k'irjinsa yabuga"fasa tafiyar yayi yak'ara had'e rai yana kallon bahbah dake nufosa"dr barka da dare! cewar babah yana tsayawa gefensa"waye kai?"shine Abinda dr Aliyu ya tambaya murya Adake"kayi hak'uri ko zamu d'an zauna inada mgn me mahinmanci data kawoni Awajenka"na maka Alk'awari zan fad'a maka gaskiya koda zakaji zafinah"tab'e baki yaya Aliyu yayi yana fad'in bbu zancen jin zafi"saidai idan naji maganar batada mahinmanci ko Alak'a dani zamu kwashi y'an kallo dakai"yafad'a cikin izzah"sbd kallo d'aya yayima bahbah yaji be yarda dashiba" ga fuskarsa da lips nasa daya kallah yagano yana shaye shaye Abinka da likita....lolx"babu komai indai zakaji meke take dani"Amma inaso inhar kasan Inda muhseen yake ka kirashi yazo Ayi maganar gabansa"yatsina fuska dr Aliyu yayi zuciyarsa na masa wasu sak'e sak'e"yadubi bahbah yana fad'in zanje nayi sallah zaka iya jira nadawo?"Eh bbu damuwa zanjira Anan"yaya Aliyu beyi mgn ba yayi gaba yana zaro wayarsa yakira brr Ahmed"bugu 3 yad'auka yana fad'in zaka hanani bin jam'i"nima jam'in zanje nabi saidai Akwai matsala"yafad'a yana masa bayanin komai"brr Ahmed yayi murmushi yace"Akwai wata Ak'asa Abokina"Amma zan kira muhseen muzo yanzun idan munyi sallah saimu taho nan"saidai jikina yabani wannan mutum yanada Alak'a da safwan"Eh nima Abinda na zarga kenan Amma saidai kazo d'in"dg haka yakashe wayar yanufi masjeed d'in dake a cikin layin....
kimanin shud'ewar mintina 25"yaya Aliyu da brr Ahmed da muhseen suka iso k'ofar gidan su dr Aliyu Atare"kasancewar can bakin titi dr Aliyu yajirasu suka iso tare....bahbah! cewar muhseen da mamaki"bahbah dake tsaye ya Amsa"brr Ahmed ya kalli dr Aliyu yace muje ciki"bbu musu suka shiga cikin gidan suka zauna a compound d'in gidan kan resting chairs"fuskar dr Aliyu Agimtse ya kalli muhseen yana fad'in waye wannan?"bbu b'oye b'oye yasanar masa yaron safwan ne kuma shine safwan yasaka yasace In'am Abaya..... what?? yaya Aliyu yafad'a da k'arfi yana jifar bahbah da wani irin mugun kallon dayasaka hanjin cikinsa kad'awa"calm down Abokina"mubi komai daki daki muji meye dalilin zuwansa??"hakane kayi hak'uri ku saurareni"cewar bahbah"yaya Aliyu beyi mgn"bahbah yayi k'asa da kansa yana sanar musu Abinda yaji dg k'arshe ya zaro wayarsa ya kunnah recording d'in da yayi"saiga muryar safwan tiryan tiryan yana mgn.....
zazzafan sharhi
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
59&60
........... innalillahi wa inna ilaihir raju'un!! shine Abinda dr Aliyu me tubarau ya furta da k'arfi shida brr Ahmed Atare"ya mik'e tsaye cikin wani yanayi yana girgiza kansa Arikice yace"mama gaje ce Ahmed !....lallai biri yayi kama da mutum"yak'are maganar yana furzar da wani zazzafan huci dg bakinsa "wata wawar chakuma yayima bahbah yana bashi wasu zafafan punchers kota ina yana fad'in yau kaima a cell zaka kwana "in bacin yace"zaiga bayanka aida baza kazo kasanar ba ko?"yafad'a cikin karaji"brr Ahmed ya mik'e tsaye ya rik'esa yana fad'in kayi hak'uri kabarsa ka zauna muyi mgn kaga masu gadi sun fara lura dameke wakana"yafad'a yana janye bahbah dg ruk'on da dr Aliyu yamasa"Ahmed bbu zancen bi Ahankali Anan" zan iya komai sbd mahaifiyata"yana fad'in hakan yazaro wayarsa yana dannawa"bugu 3 tayi Hamza ya d'auka"ko gaisawa basuyi ba dr Aliyu yace"mama na nan?"Eh tana gida ni ina wani waje"okay "be jira Amsar shiba yakashe wayar"....brr Ahmed Anan yakira DPO yamasa bayanin Abinda ke faruwa Atak'aice"yaya Aliyu ya fisge wayar yana fad'in y'allabai ka shirya yaranka su nufi Anguwar kabara kwanar gidan bread zamu had'u dasu"okay DPO yafad'a"yaya Aliyu beyi mgn ba yanufi wajen motarsa"shida bahbah suka shiga"yayinda brr Ahmed da muhseen suka fita waje Inda sukayi parking suka shiga cikin motar"gaba d'aya suka d'auki hanyar gidan mama gaje"lokacin da suka iso Anguwar"saima suka sami police d'in har sun rugasu isowa ma"yaya Aliyu ne da police guda 2 suka shiga cikin gidan"yayi bala'in had'e rai bbu Alamar tausayi ko mutunci samqn fuskar yaya Aliyu"yana tunanin koda beji recording d'in ba zai yadda mama gaje ta Aikata"sbd rana guda mijinta da mahaifin safwan suka mutu"kuma yaganta Acikin motar dayake zargi An Ajiyeta Ak'ofar gidan su"gashi uwa uba canzawar da mama gaje tayi lokaci guda"wannan kawai ya isar masa shaidar cewa ta shiga k'ungiyar Asiri"shine sbd tana butulu zata bada ran mahaifiyarsa duk irin Alkhairin data yimata Arayuwa.....tunaninsa yatsaya cak sbd yadda yaga An gyara gidan mama gaje ko ina tiles har jikin bango....kai lafiya su waye haka bbu ko sallama?"cewar mama gaje dake tsakar gidan zaune tana shan Iska itada zubaida"torch lighte d'in da police suka kunnah me mugun haske yasaka mama gaje ganin fuskar yaya Aliyu da kuma y'an sandan....gabanta yayi mugun fad'uwa murya na rawa tace"Aliyu?"hmm! k'arshen munafuki shine jin kunya" kunganta nan itace"cewar yaya Aliyu yana binta da wani irin mugun kallo irin na tsana"mekake nufi Aliyu miye ma'anar zuwanka da police gidana??"banza yamata"suka matso suna fad'in ki tashi muje Acan station zakiji komai "saidai kika mana gaddama Ankwa zamu d'aura miki....yaya Aliyu dakai za'a zo har gida Aciwa mahaifiyar mu mutunci??cewar zubaida tana fashewa da kuka"wani banzan kallo yaya Aliyu yamata yana fad'in duk ranar da kikasan wacece ita da Abinda ta Aikata Agareku zakuyi nadamar kasancewarta mahaifiyarku....yana fad'in hakan yaja tsaki"su kuma suka matso suka d'aura mata Ankwa"gabanta na dukan tara tara tana tunanin kodai yaya Aliyu yagano wacece ita da kuma burin ganin bayan mahaifiyarsa datake dashi??"zubaida na kuka da komai suka iza k'aryar mama gaje aka fito da ita dg cikin gidan"danma da dare ne Amma dukda haka wasu mutan Anguwar sun gani"kai tsaye police station suka nufa....Abinka da wanda ke dashi yaya Aliyu yasakar musu naira"yabada umarni Atuhumi mama gaje dan baya tausayinta"kuma kotu yakeso Ashiga"suka Amsa dato"
sannan aka dawo zancen safwan"wanda yaya Aliyu da brr Ahmed suka kafe sai an kamashi"babu bata lokaci police mota guda dasu metubarau suka nufi gidan safwan"wanda Alokacin yaya Aliyu na lura da kiran In'am saidai bbu nutsuwar d'agawa"bayan sun iso gidan me gadi yaso yabasu matsala"yaya Aliyu yatureshi suka shiga ciki su kusan 8"kai tsaye parlourn safwan suka nufa.....

Abin tir da Allah wadai yana zaune tare da karuwai guda 2 kowace nason jan ra'ayin sa"d'aga shi sai boxer Ajikinsa"saidai kawai yaji motsin shigowar mutane danko sallama basuyiba"wasu tsakine dogaye yaya Aliyu keja yana yatsina fuska had'e da toshe dogon hancinsa"gaban safwan yayi mugun bugawa ya janye jikinsa"matan na saurin tashi suka shige wani d'aki"gaba d'aya kunya ta kama safwan"cikin k'arfin hali yace"malamai lafiya zaku shigomun parlour bbu sallama balle neman izini??"wani banzan kallo yaya Aliyu yamasa yana tab'e baki yak'arema parlourn kallo kafin Atare shida brr Ahmed suka saki wata iriyar dariya"tsaki safwan yaja yana fad'in da Alama wani sharri kuka k'ullomun tunda gashi kunzo da police?"dad'in Abun mutum be isa yamun komai ba saidai yaturo police d'in"yafad'a cikin tsananin jin zafin dr Aliyu"shi kuwa dr Aliyu zuciya tazo masa iya wuya"matsowa yayi yana fad'in sharri ai d'an Aikene meshi yake bi"kuma karshen munafuki jin kunya"kaima kasan ko waye ni"dalilai biyu suka saka bazan d'auki hukunci hannunaba dole sai hukuma zata d'auka...kana son kaga wani yatozarta kaine zaka tozarta tunda sbd Abin duniya kaga bayan mahaifinka"cewar brr Ahmed da dr Aliyu yayi shiru"k'irjin safwan yabuga Aransa yace"mahseen ne yasanar musu"be gama wannan tunanin ba muhseen ya shigo parlourn yana fad'in nine nan nasanar musu kabada ran mahaifinka"bahbah kuma yaji da kunnansa zaka ga bayansa shima.... wani kukan kura safwan yayi zai finciki mahseen dr Aliyu ya fusgosa yana kai masa duka kota ina sbd dama ba k'aramin mak'ura yakaishi ba.....police ne suka tsawata musu da cewar safwan yasaka kaya su wuce yana b'ata musu lokaci"beyi mgn ba zuciyarsa kamar zatayi bindiga"yanufi bed room nasa police 3 suka bishi da bindiga"agabansu yasaka jallabiya yana tunanin daya sakar musu kud'i zasu barshi.....
Chapter 48 · 0% Book details