← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 143

Sashe 99

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin kice kwabo labari ya bazu a gari, tuni masu rumfuna a wajan gurin suka bazamo domin duba dokiyoyinsu...Salim yazo gurin hankalinsa a tashe yana ihu! kamar gaske ya durfafi gate din rumfar da yayi wani irin ja saboda wutar dake cinsa, ihu! yake da wai sai yaje ya bud'e! a take aka rirri'keshi Abbah Magaji da Abbah Alhassan suka janyeshi su kaishi can gefe guda suka ajiye!

Kasuwar ta cika da 'yan a gaji kowa na iya bakin kokarinsa....a takaice dai sai da wuta taci ta cinye komai na cikin rumfar kasuwar Abbah sannan suka samu nasarar tunkarar gate din suka bud'e, nan ma sai da mutane uku suka fad'i suka suma! sakamakon shaqar hayakin da sukayi.........Ganin haka yasa jama'a da dama suka tsorata sai kowa yaja da baya haya'ki ba'kikkirinn ya dinga fitowa daga cikin rumfar..

Gidan Mmn Sajida baiyi wa Abbah wahala ba,dan da kansa yaje gidan bayan yayi tambaya a farkon layin wani matashin saurayi ya kwatanta masa, da yake akwai wutar nepa yasa hankulan Mutanan dake gurin ya dauke gurin kallon motar Abbah dake kokarin samun gurin yin parking.

"Alhamdullhi ya furta a fili a nutse ya bud'e murfin motar ya fito, karaf! idanunsa ya sauka kan Naja'atu dake zaune kusa da Mmn Sajida da Plate din abinci a hannunta tana ci, ga wasu zaratan samari a tsaye a kansu da alama abinci zasu siya.

Ya dinga jin wani tsantsar bacin rai da takaici na kokarin fasa masa zuciyarsa, mutum ne shi mai tsananin kishi mussaman a kan abinda yake so, yaushe Naja'atu ta lalace haka? har take zama a kan hanya gaban maza tana cin abinci kamar tunkiya, gaskiya bai ji dadin wannan al'amari ba....Taku d'aya yayi da niyyar isa gurin sai kira ya shigo wayarsa, a nutse ya fito da ita yana dubawa ganin abokinsa ne yasa yaki dagawa, ya cigaba da tafiyarsa yana jin wani kiran na shigowa, dubawa yayi sai yaga Salim ne, sai ya kara wayar a kunnansa tare da yin sallama..........." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un."!!

Wannan kalmar daya ambata itace ta dauki hankulan jama'ar dake gurin, Naja'atu ta miqe zumbur!! tana kallonsa tana so ta tabbatar da shi ne ko ba shi bane!!

Jin muryarsa rad'au! na fad'in "Ina fatan wutar ba taci kowa ba." Salim yace babu wanda taci amma mutum uku sun suma sannan komai dake cikin rumfar ya kone harda kudin da muka shiryasu a cikin drowar.

Yace."Salim daina maganar kudi da sauran wasu abubuwa wannan duk a duniya na samesu nasan tunda me nema ne ni Allah zai mayar min da gurbin abinda na rasa babban farin ciki na shine wutar bata ci wani ba,nagode Allah da yasa wutar ta tsaya iya kan dukiya bata ta'ba wani ba.

Salim jikinsa ne yayi sanyi baiso yaji haka daga gurinsa ba ya dauka zai gigice koma sitiyarin mota ya k'wace daga hannunsa yayi hatsari! sai kawai yaji shi yana godewa Allah.A sanyaye yace."To kawu Allah ya mayar maka da alkairi sai ka dawo kenan.?

Yace."Insha Allah gani a inda Naja'atu take kuma komai dare zan dauko hanya tare da ita." Salim cikin zuciyarsa cewa yayi Allah yasa gurin hanyarka ta dawowa kayi accident kowa ya huta, a zahiri sai yace."To Allah ya kawo ku lafiya Kawu." Abbah Abbas ya amsa da amin kafin ya kashe wayarsa.....Yana kallon gabansa yaga Naja'atu a durkushe kasan k'afafunsa tana shashshekar kukan da yayi mugun d'aga masa hankalinsa, damuwarsa a yanzu ganinta da yayi a tsakiyar maza tsakiyar hanya gaban mai abinci ba wai damuwarsa wutar data cinye masa dukiya ba babban damuwarsa wannan hawayen da take zubarwa..........

IKON ALLAH WAI DUK DUBARAR DA NAKE AKAN KADA A GANE BOOK DIN NAN KODA YA FITA SAI DA AKA GANE
TO NA DAINA WAHALAR DA KAINA A BANZA WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA ALLAH Y............
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip gruop#600 normal group #300 account....

Binta umar gtbank idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Mddbhrmbn63*******Kuka take sosai kukan da ya dinga jinsa har tsakiyar kwakwalwarsa, Cikin wani irin yanayi ya miqa hannunsa a hankali ya kamo hannunta ya miqar da ita tsaye suka tsirawa juna ido ita dashi dalilin hasken wutar lantarkin daya haske gurin yasa ya dinga kare mata kallo yana jin wani irin d'aci! a maqogwaronsa, Naja'atunsa lafiyayya mai san girma itace ta lalace ta zama tamkar qashi da rai ga wani irin haske da tayi tamkar mara jini a jiki, k'wayar idanunta kawai daya kalla shine ya nuna masa da cewar tana cikin jerin mutanan dake da bukatar jini a jikinsu, komai nata ya sanja a idonsa, wani irin kallo yake mata wanda kai kana ganinsa kasan na tsantsar tausayi da jin kai ne............Kanta ta sunkuyar qasa murya irin na wanda yaci kuka ya qoshi tace"Abbah Sannu da zuwa ya hanya."?

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya amsa kafin ya kalli agogon hannunsa yace."Muje kiyi min jagora zuwa gurin uwar dakinki." A sanyaye ta kalleshi tana so tayi magana ya rigata da fad'in "Naja'atu nazo garin nan ne da niyyar na tafi dake bana so naji wata magana daga bakinki uwar ri'kon ki ta kira ni a waya kwanaki hudu da suka wuce ta sanar min da halin da kike ciki wannan dalilin yasa na yanke wannan shawarar a kanki."
"Abbah dan......Katse ta yayi ta hanyar daga mata hannu yace." Meye amfanin zaman da kike a garin mutane bayan wanda kike zaune dominsa ya sake ki wace irin rayuwa kike tunanin zakiyi a inda baki da kowa! sannan kinzo kin d'orawa wata nauyi a wannan zamanin da yayi wahala wa kike tunanin zai dauki lalurar ki kamar yanda wannan matar ta dauka! kiyi wa kanki fad'a Naja'atu duk rayuwar da kike tunanin za kiyi a garin nan ba kamar kina gaban iyayenki ba."
Wani irin kuka takeyi mara sauti! tana so tayi magana amma ta kasa saboda kukan daya ci karfinta sai kawai ta kama hannunsa ta riqe gam a cikin nata....a haka suka isa inda Mmn Sajida take zaune....Jama'ar dake gurin duk suka zubo idanunsu suna kallonsu har suka karaso gurin, Mmn Sajida ta miqe tsaye cikin karramawa takewa Abba barka da zuwa sai washe bakinta takeyi tana fad'in ya shigo cikin gidan su gaisa sosai.'' Abbah cikin kulawa yace."Tayi hakuri ba sai ya shiga ba tunda a kan hanya yake, ya umarci Naja'atu ta shiga gidan ta dauki abinda take ganin zata dauka ta fito su tafi!

Mmn Sajida ta bita cikin gidan da sauri, shi kuma ya shiga nazarin gurin, matar na bukatar taimako ko ga yanayin sana'arta, barin gurin yayi saboda shi mutum ne da baya kaunar kallo a rayuwarsa sai yaje ya bude mota ya zauna yana jiran fitowarta.......Mmn Sajida na kuka Naja'atu na kuka a haka suka fito, suka shiga gidan Mmn Ladi sai gasu sun fito dukkaninsu su ukun suna kuka gwanin tausayi(sabo turken wawa ba) Mmn Sajida da Mmn Ladi sun shiga damuwa gami da alhinin tafiyar Naja'atu mutuka sun shaqu da ita mussaman Mmn Sajida gabadaya kasa magana tayi sai rintse hannun Naja'atu takeyi a cikin nata
A haka suka isa gurin motar, Abbah ya fito yana kallonsu sai kuka suke abun ya bashi mamaki sosai, yace."Kuyi hakuri ku daina kuka ba wai kun rabu da itaba har abada ba insha Allah zata dinga kawo muku ziyara sa'i da lokaci."
Mmn Ladi tace"Alhaji dole ne muyi kuka wallahi mun saba da yarinyar nan tana da hankali tana bani shawarwari masu amfani idan taga muna fad'a da mijina tayi ta bani hakuri tana kawo min misalai ni kam a rayuwar aurena ba zan ta'ba mancewa da wannan yarinyar ba." Abbah Abbas ya shiga mamaki mutuka Naja'atunsa har ta iya sulhun aure kai alhamdullhi ashe zamanta a garin ya haifar da alkairai amma yaji dadin wannan labarin.

Mmn Sajida tace"Ballantana kuma ni da muke kwana a guri daya mu tashi a guri daya kullum cikin nuna kulawarta take a kaina da 'ya'yana hakika ban ta'ba zama da mutum mai nutsuwa gami da iya mu'amula ba kamar wannan yarinyar kafin na saba da rashinta nasan zan sha fama."
Abbah yayi murmushi mai ma'ana kafin yace." Duk maganar da kuka fada akan Naja'atu naji dadinta kwarai da gaske inaso na sake jaddada muku kamar yanda na fada muku da farko cewar ba wai kun rabu da ita bane har abada insha Allah ni nayi muku alkawarin kawo muku ita a duk sanda ta bukaci hakan ina fatan zaku kwantar da hankalinku baku rabu da Naja'atu ba."
Naja'atu share hawaye tayi ta kallesu murya na rawa tace"Mmn Sajida kamar yanda Abbana ya fad'a muku cewar muna tare har abada hakane ku daina kuka da damuwa kuna ganin kamar kun rabu dani wallahi bamu rabu ba, domin ba zan ta'ba mance alkairinku a gare ni ba, kun tallafe ni a lokacin da nake bukatar taimako baku qyamace ni ba kun jani a jikinki kun bani kulawa ni kuwa me zance muku ai idan na cika 'yar halak baku cancanci na tsawar daku a rayuwata ba insha Allah zan dinga kawo muku ziyara kamar yanda Abbana ya fad'a muku."
To jin haka dasu Mmn Sajida sukayi sai hankalinsu ya kwanta suka daina kuke kuken da sukeyi...Abbah ya bude mota ya shiga minti biyu ya fito hannunsa ri'ke da kudi yan dubu dubu sun kai talatin ya miqa wa Naja'atu da fad'in ta basu." motar ya koma yana zauna yana qoqarin tashinta.....Mmn Sajida ta rungume Naja'atu tana zirarar da hawaye da kyar ta saketa Mmn Ladi ma tazo ta rungumeta sukayi sallama cike da alhini da damuwa Naja'atu ta bud'e mota ta shiga, suna tsaye a gurin suna daga musu hannu har sai da motar ta 'bace daga gurin.....Sannan suka juya da mataccen jiki, Mmn Sajida hada ido sukayi da Dantalle daya zubo mata ido yana kallonta shima tamkar yayi kuka!
Chapter 99 · 0% Book details