Sashe 111
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah bakinsa yasa kunnan yaron dama da hagu yayi masa kiransa sallah sau uku sannan yasa masa kalmar shahada duk dai a kunnuwan nasa ya d'ago kanshi cikin nutsuwa ya tsirawa fuskar yaron ido..........Hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska ni kaina a lokacin dana kalli fuskarsa sai dana tausayawa masa, dan kallon fuskar yaron tasa yasa ya tuno da abubuwan da suka shud'e yana tunanin da Naja'atu na gidansa da tuni wannan yaron dake riqe a hannunsa nasa ne, kallon fuskar yaron tasa ya tuno da fuskar ubansa duk da sau daya ya ta'ba ganin Bash amma baya ta'ba tunanin zai mance kammaninsa,
Tamaza! yayi yayi saurin aro dauriya da jarumta ya kalleta tare da fad'in "Sannu ina fatan babu abunda ke damunki."! shuru tayi masa ta kasa magana saboda kukan da yaci karfinta
Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunanta." Naja'atu." Dago kanta tayi tana kallonsa hawaye na sake zubowa, "Kukan me kikeyi bayan Allah ya sauke ki lafiya ai sai ki gode masa."
Murya na rawa tace"Abbah tausayin ka nake ji wallahi dan Allah ka gafarta min abunda nayi maka wallahi ban zubar maka da ciki ba." Kawai sai ya tsaya yana kallonta, Kafin yayi murmushi ya dan sunkuyar da kansa yana nazarin maganarta, wai tausayi shi maganar ma dariya ta bashi
Yace."Cikina daya zube a jikinki dama haka Allah ya hukunta, maganar tausayi kuma ki daina nima na kusa samun k'aruwa ko baki da labarin amaryata nada ciki." Yafad'a yana kallonta ido da ido
Sai taga maganar tasa kamar akwai cin fuska a ciki, a sanyaye tace"Na sani Allah ya rabasu lafiya." Ya amsa da ''ameen ya Allah Wane suna kike so a sakawa yaron ki."Da sauri ta kalleshi, yace."Eh inaso nayi masa hud'uba ne kafin na tashi.
Tace"Ko wane suna asa masa.
"A'a kina da ikon ki za'bi sunan da kike so a saka masa dan haka ki duba dai.
Kai tsaye tace" Kasa masa sunanka tunda a yanzu kai ka zame masa uba."
Girgiza kansa yayi yace."Kece 'Yata shi wannan sai dai a kirasa da jika na, dan haka ba sunana ya kamata a saka masa ba na Malam za'asa masa ko kuma a saka masa sunan babansa Bashir."
Da sauri tace"Abbah dan Allah kada kasa masa sunan wannan mugun mutumin azzalimi wanda ya kwashe kayansa daga gaban ma'aiki, ni sunanka nakeso kawai kasa masa.
Yace."Ki daina tsine masa kina kwashe masa albarka yana a matsayin uban danki sannan ita shiriya ta Allah ce watakila Allah ya shiryeshi ya dawo ku daidaita kanku........Fad'ar wannan magana da yayi sai ta sake tunzura ta dinga zazzagin Bash din tana tsine masa albarka da fadin Sai dai ta mutu babu aure akan ta koma gidan Bash har da cewa insha Allahu ba zaiga annabi ba.
Abbah da kyar ya sata tayi shuru a maimakon ta tsaya ta cigaba da sauraran nasihar da yake mata kawai sai ta kwanta ta juya masa baya zafafan hawaye na zubo mata
Yaron ya ajiye mata a kusa da ita ya fita daga dakin yana mamakin al'amarin.....Kafin ya tafi harkokinsa sai ya tsaya ta tambayi hajia ko da akwai abinda ake bukata, hajia ta fad'a masa duk abinda ake bukata yace insha Allahu zai turo yaronsa
Aikuwa wajejan sha biyu na rana Abdulhamid ya kawo uban naman rago gami da kaji gyararru da kayan tea da uban cefane mai yawa...........A take Hajia ta umarci Yaya Ramlatu data taimakwa Jummai mai aiki da suyi wa Naja'atu miya irin ta masu jego.
Sai bayan la'asar iyalin Abbah Abbas suka sauka a gidan dukkaninsu har da yaran tinda washe garin ranar haihuwar jumaa ce sun taso daga makaranta da wuri yaran sai murna sukeyi zasuje suga d'an jinjiri......To bayan sun gaisa da hajia kai tsaye dakin da maijego take suka nufa...Naja'atu da aunty Maryam suna hira sukaji sallamarsu, halisa kamar ba itaba ta karasa cikin dakin da faraa a tare da ita take fadin"Lallai haihuwa da lafiya abar alfahari ce gaskiya na taya ki murna naja'atu Allah ya raya ya baki lafiya."
Aunty maryam ta amsa da ameen tana miqa mata yaron, Halisa ta karba tana dariya kamar ba itaba suka gaisa da Aunty maryam din cikin sakin fuska, aunty maryam ta dinga mamakin al'amarin, Zainab kuwa sai dauke kai take tana ya mutsa fuska, aunty maryam tace "Sannu uwar biyu kema ai kin kusa Allah dai ya raba lafiya."
A hankali ta amsa da "Ameen." Najaatu ta dan kalleta na minti biyu ta kau da kanta ta rasa me yasa gabad'aya Zainab din ke bata haushi iyayinta shine abinda tafi tsana a tare da ita
Halisa ta gama duba yaron ta miqawa Zainab da fad'in ''Gashi ki daukeshi kema kisa albarka." Zainab ta ya mutsa fuska da fad'in aunt Halisa bana iya daukarsa ni kai dai nasan abunda ke damuna Allah yasa masa albarka."
Babu wanda yaji dadin abinda tayi ai ko yaya ne ta daukeshi koda kuwa bata jin dadin jikinta...Naja'atu taji haushi sosai sai dai ta bawa zuciyarta hakuri ta cigaba da amsawa Halisa maganar da suke......Su Saddiqa ne suka shigo dakin suna murmushi.
Aunty Maryam tace"Yawwa dama tun dazu 'kaninku yake neman ku da har yayi fushi na bashi hakuri." Da sauri mussadiq ya karasa kusa da Halisa yana dariya yana leqa fuskar yaron, Halisa tace zauna nasa maka shi a jikinka.
Ya zauna da sauri tasa masa yaron ya rungumeshi su Saddiqa na leqen fuskarsa!
Aunty Maryam ta kalli Mufida da fad'in "Albishirin ku." Mufida tace"Goro." Aunty maryam na dariya tace"To dai yaro yaci sunan Abbanku dan sunan da mamansa ta za'ba masa kenan." Ai gabad'aya sai yaran suka shiga murna da farin ciki Halisa na 'yar dariya tace"To ikon Allah ashe sunan maigida aka saka masa gaskiya dole na fito da kyau ranar suna." Aunty Maryam ta dinga dariya tana fad'in "Aikuwa hakan nada kyau.
Zainab kamar ruwa ya cinyeta a dakin tayi d'if bakin ciki kamar ya kasheta jin wai
sunan mjinta ta sakawa yaronta yasa ta sake jin wani sabon kishi na taso mata....Gabadaya zaman dakin ne ya gundureta mutukar zata waiwaya ta kalli Naja'atu shar da ita tana dariya da farin ciki to ji take kamar zata mutu saboda bakin ciki....Miqewa kawai tayi ta kama hanya fita, dukkaninsu suka bita da kallo har ta futa babu wanda yayi mata magana a cikinsu.....To aunty maryam dai da Halisa ba yara bane dukkaninsu sun gane abinda ke damun yarinyar itama Naja'atun taso ta fahimci wani abu kawai ta share abun ne dan a zauna lafiya amma zahirin gaskiya irin halin ko in kulan da Zainab ke nuna mata yana yi mata ciwo.
Zainab falo ta fito ta zauna ita kadai abun duniya ya isheta, ita kuwa Yaya Ramlatu sai shige da fuce takeyi a tsakanin Dakin maijego da kicin tana sakin habaici ga Zainab din(
mai hali baya fasa halinsa hausawa suka ce idan ka kwana biyu ba kaga mutum ba to kana ganinsa ka fara tambayarsa halinsa) Zainab muzanta tayi kwarai da gaske sai ta shiga data sanin fitowa falon , sunkuyar da kanta tayi kuka na kokarin kufce mata....Yaya Ramlatu bata qyale Zainab ta sarara ba sai da taga hajia ta sakko tukkuna ta rabu da ita.
Har yamma suna gidan aunty maryam kuwa ganin yamma tayi yasa tayi musu sallama ta tafi gidanta......Halisa da Zainab suka zauna jiran zuwan mijinsu domin haka yace su zauna su jirashi idan yazo sai su tafi tare.....Daf da magariba Abbah da Abbah magaji suka shiga gidan Alhajin Abbah Abbas da kansa ya jagoranci Abokin nasa har dakin da maijegon take ya shiga ya duba yaro da mamansa, Naja'atu kasa hada ido tayi dashi sabida kunya kuma tayi mamakin yanda ya dauki yaron nata yayi masa addua sosai, ta dinga jin wani iri a jikinta tana tuno irin rashin arzikin da dinga yi musu a lokacin auranta da Bash! tana can tunanin abinda ya shud'e suka fita daga dakin ba tare da ta sani ba.
*Littafin na kudi ne.....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karantawa ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank...
Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Takwara nima ina bayanki gaskiya abun na Abbah Abbas yayi yawa, haba yace shi ba mayar da ita zaiyi ba to me yasa yake damun kansa a kan al'amuranta hidimar tayi yawa
kuma Zainab macace dole tayi kishi tunda halak ne! itama Halisa ruwa ne ya daki babban zakara shiyasa tayi sanyi......gaskiya Zainab da Halisa suna da hakuri
...........Nafisat maganarki haka take Najaatu dawa ta dogara da har takewa wata al'kawarin zata bata jari
Kawai ta samu mutum sai tatikeshi take koda yake ai yace saboda Allah da Annabi yake mata hidima! hummm! to maji ma gani dai wai an bunne tsuhowa da ranta
*MADADI*
72*****Naja'atu sai wajajen tara na dare da samu sukunin kiran wayar su Mmn Sajida ta fad'a musu ta haihu!
Mmn Sajida kamar ta fasa wayar dan murna a gurguje ta shiga gidan Mmn Ladi ta sheda mata, Mmn Ladi na murna da farin ciki ta kar'bi wayar tana mata barka tare da fatan Allah ya raya abunda aka samu.....Sun juma suna hira da juna kafin tayi musu sallama cike da jin kaunarsu a cikin ranta.
To a takaice dai
Sai da Naja'atu ta kwana uku da haihuwa tukkuna Baba Talatu tazo ta duba taga abinda ta haifa daukar yaron tayi tai masa addua daidai gwargwado tabbas komai qinka da abu idan Allah ya qaddara faruwarsa babu yanda za'akayi, babu shakka rabon wannan yaro ne ya raba auran *MADADIN* da suka daura amma suna fatan Allah ya mayar dashi da alkairi...............Bayan ta gama zancan zucci da take sai ta kalli Naja'atun a nutse tace" 'Dazu Magaji yake fad'a min cewar wai kin za'bawa yaro suna hakane ko."?