Sashe 82
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halisa ta kai awa guda a toilet tana aikin abu daya da ta yunkurin mayar da abunda yake kokarin fitowa daga gabanta sai ya sake dawowa haka ta dinga yi tana kuka da kiran sunan Allah dan gabadaya ta tsorata da al'amarin! wannan karon maganin gurin 'Yar Sa'adu na nema ya janyo mata matsala babbah! .....Da kyar tayi wanka ta shiga ruwan zafi ta dade wai ko abun zai koma sai dai har ta gama zamanta a ruwan d'umin ta fito abun bai motsa daga inda yake ba, cikin wata iriyar tafiya ta fito daga toilet din ta kwanta bed dinta cike da alhini da damuwar bala'in da yake shirin rikito mata.
Har yara suka tafi skull Halisa na cikin daki bata fito ba, baba larai na ganin maigidan ya fito ta gaishe shi a nutse ta bar palon, Abbah Abbas ya zauna gurin cin abinci da wayarsa a hannunsa, Salim ya kira yace maza yazo ya daukeshi da wuri yake so ya fita....Bayan sun gama waya da Salim a nutse ya karya ya mike ya nufi dakin Halisa, nan ya tarar da ita tana kuka ta takure jikinta a guri guda.
Cike da mamaki yake tambayarta abinda yake faruwa take kuka da safe dan shi gabad'aya ma ya manta da abunda ya faru da ita a jiya....Kasa fada masa tayi saboda tana jin tsoro kada yayi mata fad'a!
Yace"Ba zaki fad'a min abinda ke da akwai ba kin zauna kina kuka meye amfanin hakan da kikeyi ke ba yarinyar kankanuwa ba ki zauna kina aikata abu irin na yara.
Da kyar tace"Wallahi tun jiya wani abu yayi tsiro daga gabana na rasa kome ye nayi nayi ya koma ya'ki komawa." Cike da mamaki yace."Wane abu ne zaiyi tsiro ya fito daga matuncinki sai kace wanda akayi shuka gurin Kinga kiyi min bayani yanda zan fahimta.'' Hawaye ta share tace"Wallahi Abban Mufida ba karya nake ba nima na tsorata mutuka wata 'Yar tsokace ta bullutso daga gurin.....!
'Yar dariya yayi domin shi abun ma dariya ya bashi Kai tsaye yace"Bud'e min naga tsokar naman data bullutso." Yafad'a yana nufar inda take....
Halisa a tsorace take kallonsa dan gabadaya bata so yaga abin tana jin tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo
Zama yayi kusa da ita yana jan kafafunta had'e da so ya yaye zanin dake jikinta, jikinta ne ya dinga rawa cike da fargaba da tsoro tace"Abban mufida ka bari dan Allah ba sai ka gani ba.
Yace."Aikuwa dole sai naga wannan tsokar data bullutso komai 'boye 'boyen ki sai na duba nagaji." Cike da zolaya yake maganar dan gabadaya ma ya mayar da abun wasa da dariya!
Halisa hakura kawai tayi ta kyaleshi ya bude mata jikinta yana duba headquarter dinta yana laluben abun da idonsa
Lokacin da idonsa yayi masa tozali da abinda halisa ke fada masa sai da gabansa ya fadi! da sauri ya kalleta cikin wani irin yanayi na tashin hankali yace."Wannan wane irin abune ya fito miki a matunci gashinan har yana kokarin rufe miki kofa shin tun yaushe ne hakan ya kasance dake."?
Halisa data muzanta! mirya na rawa tace"Jiya ne bayan abunda ya faru tsakaninmu sai kawai naji kamar ana caccaka min allurai a ciki ga kaikyayin da gurin ya dinga yi bayan na gama sosawa ina shiga bandaki naga abun ya fito.
Kici kici da fuska yayi yana mata wani irin kallo yace."Ki dauko min maganin da kika sa wanda ya janyo miki wannan masifar."!
Rantse rantse ta shaga yi ita wallahi bata sa komai ba...Yace."Halisa kome ki keyi fa na sani nasan irin shaye shayen magunan da kikeyi akaina kuma watarana ina ganinsu da idona na tabbata akwai abinda kikasa a gabanki wanda ya janyo miki wannan abu saboda haka tun kafin ranki ya 'baci ki tashi ki dauko min maganin." !
Halisa ganin yanda yasha kunu ne yasa ta mike a sanyaye ta bude wardrobe inda take ajiye ajiyen magungunanta ta laluba ta dauko kwalbar maganin saboda haukanta sai da ta kusa sanya maganin gabadayansa kadan ta rage bayan kuma ba haka 'Yar sa'adu tace mata ba!
Mika masa tayi ya kar'ba yana dubawa!
Bude kwalbar yayi ya shanshana maganin yaji yana wani irin kamshi tabbas idan bai manta ba jiya yaji kamshin maganin a jikinsa dangwalar maganin yayi a hannunsa yaji wani irin danqo tamkar cingum!! yatsun hannunsa suka had'u da maganin suka manne guri guda!
Yace."A ina kika samo shi."?
Shuru tayi gabanta na faduwa!
Tambayar ya sake maimaitawa babu rahama ko kadan a tare dashi!.....Halisa dake neman mafita tana kuka ta shiga fad'a masa cewa a gurin wata matane da Yaya Ramlatu take kaita gurinta....Jin ta kira sunan Ramaltu sai abin ya bashi mamaki yace." Me yasa ko Yaya Ramlatu a cikin shirmen ki? ko dama ita take saki kina shaye shayen maganin mata bana son kiyi mata sharri dan ganin matsala na kokarin afkuwa dake."
Tace"Wallahi tunda nake ban san hanyar gidan boka da malami ba sai ta hanyar 'Yar uwarka Ramaltu kome nakeyi itace take d'ora ni a hanya." Abbah Abbas bude bakinsa yayi kawai yana kallonta yace."Halisa da bakinki kike fad'a min kina zuwa gidajen bokaye."?
Wani irin kuka ya kwace mata tace"Abbah Mufida ka gafarce ni wallahi ba laifina ne ni kad'ai ba Yaya Ramaltu itace take sani a gaba muyi komai tare ni yanzu babbar matsalata wannan matsalar data tunkaro ni!
Girgixa kansa kawai yake yana mamakin al'amarin! ikon Allah 'Yar uwarsa uwa daya uba d'aya itace ke cutar dashi da iyalinsa yanzu meye amfanin d'ora Halisa a turba mara kyau da Ramlatu keyi! menene amfanin cutar dashi da takeyi? me yayi mata a rayuwa da har zata bada goyan baya a cutar dashi idan halisa tayi masa asiri matarsa ce zata iya aikatawa amma ita saboda k'arfin zumunci da 'yan uwantaka bai kamata tayi masa haka ba
Ya jima yana kallonta gabadaya kansa ya kulle ya rasa wane irin tunani zaiyi dangane da wannan mummunar maganar da yaji daga bakinta wai Ramlatu 'Yar uwarsa uwa daya uba daya itace take jagorantar matarsa domin xuwa gurin bokaye a asirce shi....Halisa ganin yanda ya zuba mata ido yana mata wani irin kallo yasa takasa tsayar da hawayen dake zubo mata sai yanzu ta fahimci wautar da ta tafka gabadaya bata cikin hayyacinta shiyasa tayi su'butar baki ta fad'a masa abinda suke shukawa shin yanzu idan yayi bunkice ya tabbatar da gaskiyar maganarta da wane ido zata kalleshi na farko dai ita da kanta ta fad'a masa tana zuwa gurin malamai da bokaye babu wanda yayi mata sharri ballantana ta kare kanta...Sunkuyar da kanta tayi ta cigaba da kuka tana murza yatsun hannuwanta!....
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya Mi'ke tare da duba agogon dake daure hannusa yace." Idan kina iyawa ki tashi muje asibiti domin a duba a ga abinda keda akwai amma ki sani bani kika cuta ba kanki kika cuta wallahi idan kina zuwa gurin boka domin ki mallake ni 'Karyar ki tasha 'karya ni ba irin mazajen da mata ke kaiwa gurin bokaye bane wai ko kunyata baki ji ba da bakin ki kika fada min cewar kina zuwa gurin malamai! shin me na rage ki dashi? meye bana miki a rayuwa zaki dinga biye biyen bokaye me kike nema a duniyar nan wanda bana miki?
Halisa tayi shuru sai kuka take....Ya girgiza kansa yana jin wani irin takaici da mugun haushinta yace."Kada kiga na rabu da Naja'atu ki dauka zan zauna dake ke kadai 'Karya kike koda baki kaini gurin malamanki ba sai na sake aure kuma budurwa zan aura in yaso sai ki sake d'aura d'amarar kai sunana gurin bokayenki.
Sannan kuma maganin banza da kike sha a kaina kada ki daina kanki kike cuta bani ba." Halisa kuka kawai take tana bashi hakuri wai wallahi tsautsayi ne ita bata kaishi gurin malami dan a cutar dashi ba!
Cikin tsawa mai tafe da hantara yace tayi masa shuru domin kwata kwata shi ba zai saurari maganarta ba da bakinta ta fada ba wani shege ne yayi mata qazafi ba.
Shuru tayi kamar ruwa ya cinyeta hawaye sai tsiyaya yake a kuncinta tana jinsa yana ta zabga mata cin mutunci tayi 'kus! da bakinta addua ma take ka da yace ya saketa!!
Da zai fita daga dakin a fusace! yace."Idan kinga dama kina iya fitowa na kaiki asibiti ba dan halinki ba." Yana gama maganarsa ya fita daga dakin rai a 'bace!
Sosai Dr Sa'adatu ta shiga tsananin tashin hankali ganin abinda ya zazzago daga cikin matuncin Halisa dake kwance a wani hado kafafunta a bud'e!
Dr Sa'adatu kasa aikin tayi ita kadai sai da ta kira 'Yar uwarta suka zo suna ta wagewa Halisa kafarta suna haska headquarter d'inta da wata 'yar 'karamar fitila irin tasu!
Dr Na'ima ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Halisa da cinyoyinta suke rawa tsabar tension hawayen ma sun daina zuba sai zazzare ido kawai take.....Dr Na'ima tace"Gaskiya Hajia Halisa kin bani mamaki wallahi! yanzu da girmanki da shekarunki kike aikata aiki irin na matasan yara kefa uwace ke zakiga yara na aikata abu mara kyau ki hanasu Fisabillilahi yanzu abinda kikayi ya kamata? ina amfanin cushe cushen maganin mata da kukeyi? kullum maganar da mukeyi kenan a kafafan sadarwa kancewar mata su daina irin wannan kwamacalar saboda muhimancin virginal d'insu ya wuce ace su had'a shi da komai!
Guri ne mai muhimanci a jikinki mace da ya kamata ta mutuntuna shi amma saboda cutar kai kawai sai kuje ku dinga siyan maganin da baku san da wace tsiyar aka had'ashi ba kuzo ku cusa a matuncinku wai duk dan ku mallaki namiji humm! wannan zalintar kaine dan a yayin da wata matsala ta afku dake shi wanda kikeyi dominsa bazai saurareki ba karshe ma kina zaune ya dallo miki amarya sabuwa dal kuma baki isa ki hanashi ya aikata abinda yake so da ita ba....Yanzu dan Allah wa gari ya waya?