Sashe 89
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maigadin gidan ne taga ya bude gate mota ta shigo gabanta ya yanke ya fad'i dan a tunaninta ko Bash ne har tana mamakin abinda ya dawo dashi kuma! sai taga bashi bane mahaifinsa ne ya fito daga motar yana sanye da 'kananun kaya shart da jins da farin gilashi a idonsa, dama bata ta'ba ganinsa ba sai a hoto kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana jin faduwar gaba! wani irin kallo Alhaji Aminu yake mata, da sauri ta tsuguna har kasa tana gaisheshi.
Yana wani murmushi irin na shegun 'yan duniya ya amsa yana shafa gemunsa ta mike tana kokarin komawa gurinsu....Yace."Doghtar zo muje akwai muhimiyar maganar da nake so nayi dake." A sanyaye ta kalleshi tana mamakin maganarsa wace irin magana zaiyi da ita, cikin zuciyarta tace ko dai ya samu labarin bakar wahalar da muta nan gidan suke baki zai rarrasheki!
A jiyar zuciya ta sauke tabi bayansa cikin gidan tana jin faduwar gaba kad'an.
Kasa nutsuwa tayi a palon sanin da tayi cewar babu kowa hatta da mai aiki bata zauna ba itama ta tafi sabgoginta tunda tasan da cewar masu gidan basa nan tayi tafiyar ta sai da yamma zata dawo tayi aikace aikacenta.
Tana zaune a inda take taji muryarsa yana kiranta daga cikin dakinsa...Ta amsa da sauri ta mike ta nufi dakin....Gabanta ne yayi wani irin faduwa ganinsa daga shi sai gajeran wando a tsaye a bakin kofar dakin...Da sauri ta juya zata fita kawai taji ya ri'ki hannunta ya janyota ta fad'o jikinsa! taji yana kici kicin kulle kofar...."Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!
Abinda ta ambata kenan tayi kukan kura ta bangaje shi da mugun gudu ta fita daga dakin tana gyaran hijabinta daya tattare!
A sukwane ta fito a harabar gidan tana rarrabawa idonta sai haki! take tana waige waige! can ta nufi bakin gate gabanta na dukan uku uku! tana kokarin bude karamar kofa maigadi ya fito daga dakinsa ai kafin ma ya karaso ta bude ta fice daga gidan....maigadi daya fuskanci cewa itace sai ya mayar da kofar ya rufe ya koma ya zauna hankalinsa kwance dan baiyi tunanin guduwa tayi ba...
Hanya ta kama ta dingi tafiya tanayi tana goge hawaye gami da nanata kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! jama'a wane irin gida Allah ya kaita Ashe shima maigidan d'an busuru ne? wai shin to da yake kokarin kulleta a dakinsa me yake shirin yi mata.
Tsayin wata uku da tayi a gidan bata ta'ba ganinsa ba saboda washe garin daurin su yayi tafiya, a tunaninta dawowarsa kenan! amma saboda tsabar shi mara mutunci ne zai haike mata a matsayinta na matar d'ansa!
Babu shakka rayuwarta na cikin gagarimin had'ari! dole ne ta nemawa kanta mafita tun kafin wata mummunar qaddara ta afka mata.
Taci bakar wuya kafin ta kai kanta gidan mmn sajida, lokacin ma da taje bata nan ta tafi kasuwa cefena, sai ta samu rumfar kwanon da jama'a ke zama ta zauna tana wani irin nishi mai wahalar gaske........Duk wanda zai wuce sai ya kalleta kai wasu ma har tsayawa suke suyi mata magana, ganin haka yasa tayi shahadar shiga gidan mmn ladi! tana shiga soron gidan ta soma jin muryar mmn ladi sai zage zage takeyi! kafin tayi wani yunkuri taga mutum ya fito yana gyara kwalar rigarsa sai zabga tsaki yake, da yake Saleh ba a cikin hayyacinsa yake ba bai ma ganta ba yasa kai ya fita daga gidan....Naja'atu tayi kasaqe tana jiyo mmn ladi na fad'in "Shege tsinanne wallahi na daina yarda kana yi min hawan qawara kullum sai kazo kana cikani da dad'in baki da daddare ka haye kaina kayi ta suburbudata amma washe gari idan na tambayi kudin cefane kace baka dashi to wallahi na daina yarda da kai tunda abun ya zama rashin mutunci to kwanan auran ma siyarwa zanyi idan kana bukata sai ka biya kudin zan barka kayi aikin banza kawai."!!
Naja'atu gabanta ya tsananta fad'uwa shin wane irin zaman aure mmn ladi takeyi da mijinta? idan akwai matsala su rabu ai babu dole mai zai sanya kullum su dinga tsinewa junansu....Gidan ta shiga da sallama a bakinta, mmn ladi na huci! tace" Ke kuma daga ina? dama baki tafi garinku ba."? a sanyaye tace"Na tafi qaddara ta sake dawo dani."
Mmn ladi taja tsaki mai qarfi tace"Ke! kowa da kika gani yana da matsala dan Allah kada kice zaki fad'a min matsalarki ki rabu dani naji da matsalar da ta dameni.
Zama tayi kan tabarma tace"Mmn ladi dan Allah zauna mu fuskanci juna." Mmmn ladi tayi mata wani irin kallo kafin ta zauna tana kallonta tace me kike shirin fad'a min ne."?
Murya na rawa tace"Mmn ladi dan Allah ki dinga sawa zuciyarki ruwan sanyi kafin na shigo gidan nan duk naji irin xage zagen kikeyi dan Allah ki daina babu kyau zagin miji da tsiyatashi ko banza kun haihu da juna idan ya lalace zaki fi kowa jin ciwo saboda yayan da kuka haifa tare.
Mmn ladi ta sauke gwaron numfashi kafin tace"Wallahi naja'atu mutumin nan bashi da mutunci tunda ya aureni yake bani wuya, gabadaya baya sauke hakkina da yake kansa kin dai zauna kwana biyu kinga irin rayuwar da nakeyi abinci ma da kyar yake bani! da farko na dauka babu ce sai da nayi bunkice na gane cewar yana samun kudi kawai yana bakin cikin ya kawo gida sai dai yaje ya lalatar a waje da daddare kuma ya isheni da jaraba shiyasa na yanke shawara kan cewa duk ranar da ya nemi yayi wani abu dani sai ya biya ni dan ni ba shashar mace bace.'' Naja'atu shuru tayi tana nazarin maganar matar tace"Mmn ladi ki daina wannan maganar dan Allah musulunci bai hallata hakan ba, ki amince da mijinki a duk lokacin daya bukace ki mutukar ba a cikin tsarki kike ba, sannan dan Allah ki daina kama mijinki da kokawa kuna dambe a gaban yara kinga karfin ku ba daya bane kuma kina da 'ya mace watarana abinda kika aikatawa akan babanta itama shi zata aikatawa mijinta, kuma idan ban manta ba kwanaki naji mmn sajida na yi miki nasiha kan cewar ki dinga hakuri da kad'an! idan ba zaki iya ba to ki kama sa'ana shi kuma ki kyaleshi da halinsa mutukar yana zalintarki sai ubangiji ya saka miki wannan tashin hankalin da kikeyi da masifa ba shine zai kawo miki kwanciyar hankali ba.
Mmn ladi jikinta yayi sanyi jin nasihar da naja'atu tayi mata tace"Shikkenan na'ajatu zanyi kokarin ganin na dauki shawararki amma wallahi abin ne da ciwo ace dari biyu shine kudin cefanan gida ki duba kiga yanda rayuwar nan ta koma komai yayi tsanani!! kuma yanzu da kike maganar na kama sana'a ina naga jarin da zanyi sana'ar dashi." ?
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Insha Allahu ni idan na samu yanda nake so zan baki jari ki dinga sana'a domin ki rufawa kanki asiri amma dan Allah ki daina wannan mummunar d'abiar da kikeyi a gidan auranki." Allah sarki Naja'atu rayuwa ta koya mata hankali wai yau itace takeyi wa wata nasiha...Mmn Ladi tace"To nagode sosai Naja'atu Allah ya saka da alkairi." Naja'atu na kokarin yin magana mmn Sajida ta shigo gidan ganin naja'atu yasa ta tsaya tana mamaki! murmushi mai ciwo naja'atu tayi tace"kinyi mamakin ganina ko."?
Mmn sajida tace"Wallahi kuwa ai na dauka kin tafi." Naja'atu a sanyaye tace"Na tafi mummunar qaddara ce ta sake dawo dani.'' Mmn sajida ta rike bakinta had'e da fadin wace irin mummar qaddara kuma."?
Mmn Ladi tace"Nima mamakin maganar nake dama yanzu nake shirin tambayarta sai gashi kin shigo."
Mmn sajida ta zauna kusa da ita tace"Ni wallahi jikina yayi sanyi da jin wannan maganar naja'atu wace irin qaddara ce ta dawo dake garin jos."?
Zafafan hawaye ne suka shigo zubowa daga idonta tana kuka mai tsuma zuciya ta shiga basu labarin abinda yake faruwa, tun daga farkon al'amarin harkarshe bata 'boye musu komai ba sai da ta fad'a musu.
Maman Ladi ta rike baki cikin mamaki gami da al'ajabi tace Ikon Allah "Yanzu Naja'atu dama ashe kece matar da Bash ya aura? mu dai mun samu labarin cewar yayi aure ya auri yar kano kuma bazawara har a gari a kan dinga surutu da yawa mutane na cewa dama sai da yaje inda ba'asan halinsa ba ya nemi aure dan gabad'aya mu nan mun sanshi kuma mun san mummunar sana'arsa ta 419 (damfara) gami da sace sace a manya gurare uwa uba Harkar luwadi da yake yi........Gaskiya duk wanda yake da hankali ya kuma san waye bash to ba zai dauki 'yarsa ya aura masa ba dan a zahirin gaskiya bash ba mutumin arziki bane kuma ba mutumin da zakayi fatan ka had'a zuria dashi bane! sai kuma maganar mahaifinsa da kikace ya kulleki a daki yana neman lalata dake gaskiya nayi mamaki sosai dan a sanin da jamaar gari sukayi masa mutumin kirki ne! to amma babu mamaki Ubangiji ne yayi nufin tona masa asiri watakila ya dad'e yana lalata da 'ya'yan mutane sai yanxu asirinsa ya tuno gaskiya duniyar nan a bar tsoroce wallahi naja'atu na tausaya miki da tun farko kinzo ki fad'a min halin da ake ciki wallahi da bazan barki ki auri Bash ba(Allah sarki mmn sajida a lokacin da idanun naja'atu suka rufe kome zaki fada mata a kan auranta da bash ba zata dauka ba) Mmn Ladi tace"Ni wallahi abin ne ma yake bani mamaki na rasa abinda zance Allah dai yasa baki da ciki dan shine babbar matsalar a yanzu.
Naja'atu na goge hawaye tace"Bana tsammanin inada ciki mmn ladi ni tunani na yanda zanyi na ku'buta daga hannun wad'annan mugwayen mutanan."
Mmn Sajida tace"Gaskiya zamanki a tare dasu bai taso ba yana da kyau ki nemawa kanki mafita kije gida ki shedawa iyayenki halin da ake ciki."
"Mmn sajida ina jin kunyar tunkarar iyayena da wata magana wallahi mahaifiyata tayi min gargadi kancewar kada na sake nazo gida da wata matsala tunda dai ni naji na gani da auran bash to naje na zauna nayi hakuri.....Mmn Sajida tace" To ai wannan matsalar babbace dole su san da ita idan baso suke ki shiga cikin masifa ba." Shuru tayi tana kuka gami da tunanin yanda za tayi.