Sashe 21
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*14*
Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar ya'ke tayi tace"To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk d'aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had'a neman aure da kai."" Abba Abbas yayi murmushi yace."Kwana biyu ma bana ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d'auka nasan duk akan hakane." Tace."Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi cancanta daka auri yarinyar." Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.
Yaya Ramlatu a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna 'kulle-'kullensu, Halisa ta fad'a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had'o lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so zai bata kudi ta siya.....Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace"Kinga aikin malam ya fara yi ko ai dama na fad'a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d'aga hankalin ki kan auransa da yarinyar nan nasan idan muka ri'ke Malam mai al'mutsutsai! a hannunmu to bukatar mu zata biya dama kuma babban burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da 'kan'kanin lokaci zaki mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud'e bakinsa yace miki dashi da duk wani wanda yake 'kar'karshinsa a 'kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga aikin alherin da yayi miki." Halisa tace."Nifa Yaya Ramlatu sai nake gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu."
Yaya Ramlatu ta 'bara rai tace"Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake miki bakya gani sai kin 'karya ta ni! kin 'karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba'ka'ken aljanu yake aikinsa, to shi mai al'mutsutsai da ba'kaken aljanu yake aikinsa, idan kin san ba'kar wuyar da muka sha nida 'Yar shagamu kafin mu je zauren malam d'in sai kin tausaya mana, amma kin samu aiki yayi shine kike 'karyata wa to wallahi babu ruwana."
Halisa ganin ran Yaya Ramlatu ya 'baci sai ta shiga bata hakuri tace"Ba wai ina karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah." Yaya Ramlatu tace"Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya bar jikinsa."
Halisa ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "To shikkenan insha Allahu zanyi kokarin ganin na kauda duk wani abu dake raina dangane da auran, ammafa nace ban yarda ya raba mana gida ba dan ina ganin kamar za'a cutar dani, sannan kuma wa 'yan nan 'ya'yan nasa daya kawo min sam bana son ganinsu wallahi."
Yaya Ramlatu tace"Eh kina da gaskiya gwara ya had'aku a gida d'aya duk da nasan ba wani d'okin auran yarinyar yake ba amma hausawa nace wa amarya ko mahaukaciya ce dole ayi d'okinta, dan haka tana tarewa ya kwashe yara ya kai mata dama ai saboda ta zama *Madadin* Uwarsu ya aureta."
Halisa tace"Yace idan an d'aura auran sai bayan sati biyu zata tare." Yaya Ramlatu tayi shuru tana nazarin maganar tace"To shikkenan sai ki hakura ki ri'kesu kafin lokacin amma ban amince ki zalince su ba tunda basu ne sukayi miki laifi ba." Cike da mamaki Halisa ke kallon Yaya Ramlatun wato idan ta fahimta tana so ta nuna mata cewar ita tana 'kaunar 'ya'yan d'an uwanta, Halimatu da Naja'atu ne bata kauna!
To idan hakane kuwa 'kiyayyar da take musu ba takai har zuciyarta ba tunda ba zata bari a zalinci jininsu ba.
To Duk abinda Allah ya tsara ya hukunta sai ya kasance dama haka al'amarin yake mutum baya ta'ba tsarawa kansa rayuwa sai irin wacce Allah ya tsara masa, Abba Abbas da Naja'atu ko a mafarki basu ta'ba tsammanin zasu zauna a inuwar ma'aurata ba, sai gashi Ubangiji ya zartar da ikonsa a kansu, Sai gashi a yau jama'a masu yawa suka sheda daurin auransu, kowa sai fatan alkairi yake gami da fatan zaman lafiya, Alhaji Sama'ila da Baba Malam da Abba Magaji bakin su ya'ki rufuwa sai gaisawa suke da jama'a Abba Magaji na raba goro da alawa fuskarsa tamkar gonar audiga........Shi kuwa ango fuskarsa kadaran kadahan yana ta mi'kawa abokanshi hannu suna gaisawa suna taya shi murna da fatan alkairi yana amsawa fuska d'auke da murmushi.
Cikin gida kuwa, Naja'atu kasa gane kanta akayi ta rufe d'aki! da sakata, sai kuka take tana kiran mutuwa tazo ta dauketa, Baba Talatu da 'yan uwanta da suka cika gidan hankalinsu ya tashi suka dinga buga 'kofa suna kiran sunanta, tana jinsu tayi shuru sai ihu! take tana birgima 'kasan d'akin.
Baba Talatu ta fashe da kuka tana fad'in "Wannan yarinya tana so ta jawo min abin kunya a idon jama'a innalilihi wa'ina ilahi raji'un!
Daki ta shiga ta zauna gefan gado tana share hawaye babu shakka Naja'atu ta fita zakka a cikin 'yayanta.......Abba Magaji ne ya shigo gidan ya gansu tsaye a kofar d'akin!
Gashi sai gunjin kukan Naja'atun yake ji daga cikin d'akin, Ya karasa gurin da sauri yana tambayar ba'asi.........Baba Larai wacce ta kasance Yaya ga Baba Talatu itace tayi masa bayani duk abinda ke faruwa, Ya shiga bubbuga kofar yana kiran sunanta, tana jinsa taki kulashi.
Cikin rarrashi yace." Naja'atu bude kofa kinji ko duk kinsa hankalinmu ya tashi yi hakuri ki bude kofar zanyi magana dake.......Cikin dashashshiyar murya tace"Sai dai ku dau'ko gawa ta amma wallahi bazan bud'e 'kofar nan ba."
Abba Magaji ya kalli kofar 'kofa ce irin tada mai k'wari tabbas jijjige ta aikine babba amma yana ganin hakan shine mafita, yana kokarin fita Baba malam na kokarin shigowa ganinsa a fujajan! yasa ya tsaya tambayarsa, Baba malam ransa ya 'baci sosai babu shakka Naja'atu ta shirya tsaf! domin ta tozarta shi a cikin unguwa, nan ya umarci Abbah magajin ya samo matasa majiya karfi suzo su jijjige 'kofar......Gidan ya shiga ya tarar da jama'a sai surutai suke kowa na fad'in albarkacin bakinsa, har da masu cewa dama a warware auran tunda yarinyar bata so.......Baba malam ya tsaya a bakin tagar dakin ya daga labule yana le'kanta da kiran sunanta, duk da tasan shine bai sa ta amsa masa ba, juya baya tayi ta cigaba da kukanta...........Abba Abbas na tare da Dan uwanshi a bakin gate din gidan alhaji suna magana, kawai yaga abokin nashi tare da zaratan maza majiya 'karfi harda Salim a ciki zasu shiga gidan Malam......Ya bisu da kallo cikin mamaki!
Jikinsa ya bashi da akwai abinda ke faruwa..............Sai da suka fara sassa'ke 'kasan 'kofar da (diga) sannan suka sanya mata karfi! aikuwa a take suka cire ta.........Mi'kewa tayi tsaye! cikin firgici! tana rarraba idonta a kansu, ganin sun shigo dakin har Baba Malam d'in yasa ta takure jikinta a bango tana rawar jiki, Abba Magaji ya nufe ta a zafafe! da alama jibgarta zaiyi Baba Malam ya hanashi, a fusace ya bar dakin, su kuwa jama'a 'yan zuwa taya murna sai fad'ar albarkacin bakinsu suke a kanta........Baba Malam yace."Magana dai duk ta 'kare kowa yaje ya cigaba da sabgarsa aure tunda an daura babu zancan a warware shi.
Dakin ne yayi shuru na tsayin minti biyar kafin yayi gyaran murya a nutse ya kira sunanta."Naja'atu.'' Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya kalleta cikin yanayi na damuwa yace."Kina so jama'a su zage ni a unguwa ko? ashe a matsayina na mahaifinki ban isa na nemi alfarma a gurin ki kiyi min ba! kin shirya tozartani a cikin unguwar ko, ba'a ta'ba samun labarin yarinyar data fujirewa umarnin iyayenta a cikin unguwar nan ba sai ke! wato tun munayin abun nan a cikin gida sai ki janyo hankalin jama'ar dake waje sun gane cewa tilas mukayi miki ki auri mijin 'yar uwarki, Kina ji da kunnan ki irin surutan da jama'a keyi a kanki, kina so duniya ta zage tayi tur! dake kan 'kin bin iyaye meye aibun Alhaji Abbas da kike masa wannan 'kiyayya! idan da al'kawari da amana Abbas bai cancanci haka daga gare ki ba, to saboda haka ni wannan itace magana ta ta karshe a tsakanina dake, an daura auraki da Alhaji Abbas to kada naji kada na gani, mutukar kin daukeni a matsayin uba to ina so ki zauna da wannan bawan Allah zama na amana kamar yanda 'yar uwarki ta zauna dashi, idan aka kai ki dakin mijinki aka samu matsala ta 'bangaranki to babu shakka zan yafe wa duniya ke babu ni babu ke har abada."!!
Kallonsa kawai take tana shararar da hawaye bakinta sai rawa yake tana so tayi magana amma ta rasa ma ta ina zata fara.......Baba malam ya mike ya fita daga dakin ya barta cikin zullumi da tararrabi gami da neman mafita.