Sashe 16
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halisa ta zabura! ta dafe kirjinta gabanta na wani irin buguwa tace"Aure kika ce Yaya Ramlatu.""?
Tace"Kwarai kuwa." Tafada tana tabbatar mata da gaskiyar magana
Wani irin gumi ne ya shiga tsiyaya daga jikin Halisa!
"Aure!aure! kalmar ma ba babu dadin ji a kunnanta, wato duk ladabi da biyayyar da take masa da nuna masa kulawar da Halimatu take masa bai sa yaji sha'awar aure ya fita daga ransa ba? ashe duk abinda takeyi masa na kulawa a banza take mutuwar Halima ko sati biyu ba'ayi ba amma har ya fara kokarin aure, shin wai dame ta gaza ne a gurinsa......wasu hawayen takaici da bakin ciki ne suka shiga sauka a kumatunta.....Yaya Ramlatu tace." Ai ba kiyi kuka ba ma tukkuna sai kinji yarinyar da zai aure."!
Bakinta na rawa tace."Wacece."?
Kai tsaye Yaya Ramlatu tace"Naja'atu ce.'' Sai tayi kasa'ke tana kallonta tunani takeyi wacece ma Naja'atu! dan a lokacin gabadaya kwakwalwarta ce ta toshe ta mance a inda tasan mai irin sunan."
Yaya Ramlatu tace''Kina mamaki! ko da jin wacce mijinki zai aura bari na 'kara tabbatar miki da maganar, Abbas zai auri Naja'atu kanwar matarsa Halimatu yarinyar da ya ri'keta tun tana 'karama yayi mata komai tamkar 'yar cikinsa! shine yanzu zai maye gurbin 'yar uwarta da ita." Halisa ta dinga jin hajijiya tana daga xaune! rintse idonta tayi tana tunano siffofin Naja'atu a idonta!!! a gigice ta bude idonta ta zabura ta mike tsaye tare da cewar "Wallahi ba zaiyi wuba !! ba zan yarda da wannan cin amanar ba!
Ni Abbas zaiyi wa haka? me nayi masa a duniya zai had'ani kishi da yarinya 'karama 'yar cikina! kutumar uban nan kayyasa!! sai ta zube kasan kafet ta fashe da wani mahaucin kuka tare d'ora dukkanin hannuwata a kanta.
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*10*
Wani irin kuka Halisa takeyi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwar iyayenta, ta d'ago kanta tana kallon Yaya Ramlatun fuskarta gaje-gaja da hawaye tace"Yaya Ramlatu ina zan saka kaina da wannan abun kunyar! shin wai me yake damun d'an uwanki ne?
Ya rasa wacce zai aura sai 'yar cikinsa yarinyar da ya ri'ke tamkar shi ya haifeta amma saboda tsabar abun kunya yace zai aureta tsofai-tsofai dashi zai auri 'yar 'karamar yarinya babu shakka wannan karon komai zai faru tsakanina dashi sai dai ya faru dan na rantse da Allah ba zan bari ya tozartani ya had'ani kishi da matsiyaciyar yarinyar nan da na riga nasan matsayinta a zuciyarsa ba."
Ya Ramlatu ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Ai shiyasa nima dana ji labarin hankalina ya tashi sosai!
Kishi da irin jinin Malam Baba ai bala'i ne wane irin daurin gindi ne Halimatu bata samu ba a gurin Abbas din, ai wallahi kece abar tausayi mutukar kika bari ya auri yarinyar nan to ki rubuta ki ajiye auran ki ya 'kare tsakaninki da mijinki."
Yaya Ramlatu ta 'kare maganarta cikin karfafa maganar ta gami da 'kokarin 'kara ingiza zuciyarta.
Goge fuskarta tayi tace"Yaya Ramlatu ai na fad'a miki wallahi tallahi sai dai ya za'ba ko ni ko yarinyar nan dan ni ba zanyi kishi da Yayarta ba itama nazo nayi da ita ba, wannan karon duk abinda yake ji dashi dai-dai nake dashi zai dawo gidan ya same ni.''
Yaya Ramlatu ta dauki lemo ta kur'ba tace"To ai dik da haka ba zama za kiyi ba dole ki d'an nemi taimako dan baki san irin shirin da iyayen yarinyar suke a kan al'amarin ba, dan wannan tsinannan Malam Baba mugun mutumi ne babu irin surkullan da bayayi." Halisa tace"Yaya Ramlatu ni yanzu gabadaya ma banda kuzarin zuwa gurin wani malami da sunan taimako nifa gabad'aya auran Abbas ya fice min daga rai ya dawo ya sake ni." Ta'karasa maganar cikin rawar murya.
Yaya Ramlatu tace"A'a ba za'ayi hakaba ke yanzu idan kika kashe auranki saboda wannan yarinyar ai kin cutar da kanki! kada kice ya sake ki kawai idan ya dawo ki daga masa hankali ke macece kin san hanyoyin da zaka hanashi nutsuwa da kwanciyar hankali gefe guda kuma zamu sa malamai su taimaka miki insha Allah sai zuciyarsa ta karye yaji sha'awar auran ya fita daga ransa da kansa zaice ya fasa."
Halisa tayi shuru tana tunani!
Yaya Ramlatu tace"Dole ki futo da kudi aje a taimaka miki ni gaskiya bazan so ki bar dakin ki ba, ki zauna kici ubansu daga shi har yarinyar idan Allah ma ya kaddara sai ta shigo gidan sharri kad'ai ya isheta.
Halisa taja ajiyar zuciya tare dayin 'kwafa, tace"Maganar ki haka take Yaya Ramlatu bari na kawo miki dan abinda ke hannuna dan Allah kiyi min kokari akan al'amarin." Yaya Ramlatu tace"Kada ki damu zan shiga na fita insha Allahu maganar auran zata rushe ke idan ma Allah ya kaddara auran to wallahi ba zamu k'yalesu suji dad'in rayuwa ba." Halisa ta gyada kanta tana dan jin sassauci acikin zuciyarta, bedroom dinta ta nufa, minti biyar ta fito hannunta rike da kudi 'yan dubu dubu.
Ta mikawa Yaya Ramalatun da fadin "Dubu ashirin ne zuwa gobe sai ki aiko a kar'bi dubu talatin din zanyi duk yanda zanyi na dauki key din gurin da yake ajiyar kudi na dauka."
Yaya Ramlatu ta mike tana gyara yafan mayafinta tace"Nima daga nan zan wuce gidan *'Yar shagamu* (wata hatsabibiyar 'kawar Ramlatun ce)Ta cigaba da cewa......"akwai wani malami da mukayi hirarsa kwanaki da ita tace ya iya aiki idan dare baiyi ba zamuje idan kuma dare yayi to da sassafe zamu buga sammako dan kada muje mu tarar da mutane." Halisa taji wani sanyi a ranta tace"Yaya Ramlatu nagode kawarai da kaunar da kike nuna min hakika ina alfahari dake a cikin 'yan uwan Abbas kina nuna min kaunar da mahaifiyarku ma bata nuna min."
Yaya Ramlatu ta dafa kafadarta tace"Kada ki damu cikin ko wane irin hali ina tare dake, maganar Hajiyarmu kuwa dama can tafi kaunar Halima a kanki saboda gidan Malam Baba sun riga sun gama dasu daga ita har Alhajin, dan baki ga yanda suke murna da wannan al'amarin ba, Hajiya har da kuka tana 'kokarin yi min baki akan nace auran Abbas da yarinyar bai dace ba, shine fa take kuka har dayi min gorin abinda Abbas din keyi wa Salim."
Halisa ta shiga girgiza kanta, cikin 'kunar zuciya tace"Ai ba sai kin fad'a mun ba dama tuntuni na san Hajiyarku bata sona ko lokacin Halimatu tafi nuna kulawarta a kanta, to kinga kuwa dole taso wannan al'amarin ni na rasa me nayi mata ta tsaneni."
Yaya Ramlatu tace"Wallahi duk sharrin daga gidan Malam Baba yake gabadaya fa sun gama da zuciyoyin jama'ar gidanmu nice kadai na gagaresu." Halisa na jin d'aci a ma'kogwaronta tace"Insha Allahu sai mun karya alkadarinsu."
To sallama sukayi da juna inda Yaya Ramlatu take sake tabbatar mata da cewar yanzu idan ta fita gidan *'Yar Shagamu* zata nufa domin su tattauna yanda al'amarin tafiya gidan malam zai kasance.
Koda Naja'atu ta koma gidan Malam kai tsaye dakinsu ta shige taje ta kwanta kan katifa, ta dinga kuka tana birgima kan katifar! sai sambatun surutai take da kiran sunan Halimatu wai ta mutu ta bar baya da 'kura mutuwarta tana nema ta zame mata barazana ga rayuwarta...........Sautin kukan tane ya cikawa Baba Talatu kunne da sauri ta fito daga kicin ta nufi dakin, nan ta tarar da ita sai burgima take kan katifa tana dukan kanta da kanta kamar wata mahaukaciya sai surutai takeyi da fad'in in dai aka daura mata aure da wani ba Salim ba to sai ta kashe kanta ta kashe wanda aka aura mata......Baba Talatu ta shiga dakin hankalinta a tashe ta birkitota wani wawan mari ta kifa mata a fuskarta tana wani irin huci!!
Rintse idonta tayi ta mike zaune hannunta kan kuncinta idanunta a rufe amma hawaye ne kawai yake zurara.
Murya na rawa Baba Talatu tace"Naja'atu idan baki kashe kanki kin kashe Alhaji Abbas ba bakya kaunar Allah!
Wai shin ke d'in wace irin yarinya ce butulu mai manta alkairi! yanzu da abinda zaki sakawa da wannan bawan Allahn kenan? wannan wace irin 'kiyayyace kike nuna masa 'karara? meye bai miki ba? ki sani idan da mutuwa bata ratsa tsakaninsa da matarsa ba ke baki isa ya kalleki ba ballanta yace zai aure ki dan saboda baki dace daki auri nagartaccen namiji kamar wannan ba! meye laifinsa? meye kuma illarsa!?
Muna tsaka da alhani gami da rad'ad'in mutuwar 'yar mu mai biyayya kina nema ki d'ora mana ciwo! ashe bamu isa dake ba? ashe kuma Halima bata cancanci sakayya al'kairi a gurinki ba?
Idan kin auri mijin Halimatu babu wanda zai kai ki Jin dad'i itama kuma zata samu farin ciki alkairin da kikayi mata kin auri mijinta bayan babu ranta kin tallafi 'yayanta! to wallahi duk sanda na kara jin kinyi wani mummunan furuci kan wannan bawan Allahn sai ranki ya 'baci! sai na fad'awa Magaji duk abinda kike yi tunda ni da malam kin raina mu bakya ganin mutuncin mu."!!
Baba Talatu ta kare maganarta cikin tsantsar 'bacin rai gami da jin takaicin abinda 'yar tata takeyi.
Baba Talatu fita tayi daga dakin ranta a 'bace! hakika yarinyar bata ta'ba 'bata mata rai ba irin yau! ita rasa gane meye abin gudu a game da wannan auran da suke kokarin had'awa, a iya tunaninta da tsinkayen ta tana ganin kamar gata sukayi wa yarinyar har indai sun had'ata aure da mijin 'yar uwartata dan hausawa na cewa Naji dad'i shine gari ba nasa baba........Baba Talatu na fita daga d'akin ta zame a hankali ta kwanta kasan ledar dakin tana takure jikinta ta cigaba da kukan rashin mafita, a lokacin ji take yi dama Allah zai dauki ranta ta huta daganin wannan masifar..........
Koda Saddiqa da Mussadiq suka shiga dakin suka sameta a kwance tana kuka!
Mussadiq ne kawai ya tsaya a kanta yana mata magana ita kuwa Saddiqa saboda tasan ko kukan me takeyi yasa ta juya ta fita daga d'akinta ranta a 'bace! hakika tana jin ba'kin ciki da takaicin irin 'kiyayyar da take nunawa mahaifinta, shiyasa itama ta soma jin haushinta akan irin abinda takeyi kan al'amarin.