Sashe 61
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawaye ne suka zubo mata yanzu da badan yana gidan ba Halisa zata iya yi mata mummunan rauni kuma karshe babu wani mataki da zai dauka sai dai ace tayi hakuri.....Yace."Ki sanjo hijab tunda wannan ya 'baci da jini sai muje asibiti a duba miki gurin, a sanyaye taje ta sake hijabi ta fito, Tarar dashi da Baba larai suna maganar Halisa inda yake cewa zai kira malaman rukiya suyi mata dan ya fahimci iskokin dake damunta masu cutarwa ne, Baba larai tace"To Allah yasa ayi cikin nasara." Naja'atu ta d'aya gefan ta wuce tana waiwayen inda Halisan ke kwance gabadaya yanzu masifar tsoranta take ji........To Da yake tayi saurin kaucewa yasa Halisa bata samu nasarar illata mata fuskarta ba d'an gurin daya tsage aka wanke sannan aka bata magunguna masu kyau wanda zasu taimaka gurin dusashewar ciwon......Bakin gate ya ajiye ta yace ta shiga gida zai wuce kasuwa, kuka tasa wai ita ba zata shiga gidan ba tsoron Halisa takeji sai dai ta shiga gidan aunty Maryam idan ya dawo da yamma ta dawo gidan.A take ya nuna mata rashin amincewarsa yace lallai sai ta shiga gidan Halisa bata isa tayi mata wani abun cutarwa ba, Tasa gaddama hade da fad'in "Gashinan ta tsaga mata fuska da makami ai idan ta farfado ta ganta a gidan zata sake d'aukar makami a kanta!
Suka dinga tababa ita dashi a motar Abbah bai ta'ba tsammanin yarinyar nada taurin kai irin hakaba, ita kuwa Naja'atu da biyu take masa haka dan kawai ta d'aga masa hankali ne ya za'bi zama da Halisa ita ya rabu da ita
Ganin tana 'bata masa lokaci ne yasa yace"Ta fitar masa a mota tunda ita bata jin magana, aikuwa ta bude motar ta fita tana kuka kamar wacce aka aikowa da mutuwar iyayenta, yasa mata ido kawai yana kallon inda ta nufa, sai yaga ta dauki hanya tana tafiya tama wuce gidan aunty Maryam din da alama kofar na'isa zata nufa...Da sauri ya tari gabanta da mota taja ta tsaya tana kallonsa da idanunta da sukayi jawur! duk tana sane take wannan kukan iskancin...Gilashin motar ya sauke babu fara'a a tare dashi yace." Ki shiga gidan aunty Maryam din amma kada ki sake kije kofar na'isa ki fada musu wata magana akan al'amarin nan daya faru.
Ba tare da tace masa komai ba ta juya da niyyar zuwa gidan anty maryam, bai ja motar ba sai da ya tabbatar da cewar ta shiga cikin gidan sannan yaja motar...Yana dab da fita daga layin Salim ya shigo da mota da niyar daukarsa bayan ya ajiye yara a skull Ganin kamar Kawun nasa na cikin damuwa yasa baiyi magana ba yayi saurin bin bayan motarsa data fice daga layin gidan.
Aunty Maryam na ganin Naja'atu wujiga wujiga ga gefan fuskarta manne da plasta sai gabanta ya fadi tana rawar baki take tambayarta abinda ya sameta.
Cike da neman fitina gami da 'kara rura wutar al'amarin da ya faru tace"Halisa ce haka kawai ta dauki kwalabar turare tace sai ta burma mata ta kashe to da bata samu damar caka mata ba sai ta yanke ta a fuskarta, tana kuka ta cigaba da cewa kuma Abbah Abbas din bai dauki mataki ba karshe ma cewa yayi wai tayi hakuri Halisan bata cikin hayyacinta.
Anty Maryam ranta ya 'baci mutuka tace"To a gaskiya wannan al'amarin ba zai yuwu ba tunda har Halisa takai ga matakin daukar makami a kanki to kuwa dole a dauki mataki a kan al'amarin! dan dama Abbah Abbas din ya saba goyawa Halisa baya ko lokacin da Halimatu take raye sau nawa Halisa za tayi mata abu baya daukar mataki sai dai kawai ya bata hakuri, dan kawai ya samu mace mai hakuri suka hadu suka dinga cutar da ita bakin cikinsu ya kasheta to gaskiya a wannan karon dole manya su shigo cikin maganar.
Naja'atu tace"Shiyasa tun farko nake fada muku cewar wannan al'amarin da kuka k'ulla akwai cutarwa a cikinsa ina zan iya zama da Halisa muguwar macace babu irin sharrin da ba tayi min a gidan kuma ya goyi da bayanta gashi yanzu ta kai har ta dauki abu zata kasheni wallahi idan baku raba auran nan ba to zan gudu na bar muku garin kowa ya huta." Cikin kuka na fitar hankali ta kare maganar
Anty maryam jin maganar guduwa yasa hankalinta ya tashi tace"Daina kuka nima ban goyi da bayan ki cigaba da zama a gidan ba, bayan gagarimar matsalar da kike fuskanta ta rashin biyan bukata kuma a dinga barazana da rayuwarki, gwara tun kafin tafiya tayi nisa a san yanda za'ayi.
Dakinta ta shiga ta dauko wayarta ta dawo ta zauna kusa da Naja'atun.
Numbar mijinta ta shiga kira, wanda a lokacin ma suna tare da Abbah Abbas din a kasuwa suna sake tattauna maganar jiya da naja'atu taje ta fadawa maryam din ta rashin gamsuwa...Abbah Magaji ya daga wayar da sallama a bakinsa, to da yake handsfree yasa babu abinda Abbah Abbas din baya ji....Anty maryam muryarta na rawa tace"Abban Ilham abubuwa fa suna nema su lalace! ga Naja'atu nan muna tare da ita ta shigo min hankalinta a tashe tana kuka ga wani irin rauni a fuskarta wai Halisa ce ta dauki makami zata caka mata da bata samu damar caka mata ba sai ta yanke ta a fuskarta wallahi baka ga abun ba babu kyawun gani, a gaskiya yarinyar nan na cikin tashin hankali mai girma, Aure kwana takwas duk ta lalace kullum babu nutsuwa a tare da ita ga wannan babbar matsalar da na fad'a maka jiya a gaskiya yana da kyau ku zauna gabadayanku ku duba al'amarin nan kada garin son zuciyarku ku cutar da yarinyar nan Dan gaskiya xaman gidan Abokinka sai wanda ya shirya Halisa ba a zaune take ba." Aunty maryam ta karashe maganar ta tana sauke numfashi.
Abbah Magaji ya dinga kallon abokin nasa ya rasa ma abunda zai cewa da matarsa dan duk ta daureshi da jijiyoyin jikinsa...Tace"Abban Ilham kana jina kuwa.'' Yace."Duk naji abinda kika fada idan na dawo gida zamuyi maganar insha Allahu kuma kada ki bari yarinyar taje ko ina sai na dawo."
Tace"To insha Allahu dama babu inda zan bari taje.
Kashe wayarsa yayi ya cigaba da kallon abokin nasa dan yasan yaji komai kawai yana bukatar karin bayani daga bakinsa
Abbah Abbas ya cire hular dake saman kansa yasa hankici ya goge zufar goshinsa ya kalli abokin nasa cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali yace."Duk abunda Naja'atu taje ta fa'dawa Maryam hakane!
Yau da safe kafin na fito al'amarin ya kasance tabbas Halisa ta dauki kwalbar turare da niyyar ta illatar dani kamar yanda tafad'a da bata samu nasara a kaina ba sai ta huce kan Naja'atu akan wani dalili nata na daban, amma Halisa bata dauki kwalbar turare da niyyar ta cakawa Naja'atu ta kasheta ba kamar yanda naji Maryam na fad'a maka yanzu..Sannan kuma inaso kasan da cewar abinda Halisan tayi bawai tayi shi bane a cikin hayyacinta ba ina kyautata zaton Halisa na tare da mugwayen aljanu wanda suke tunzura mata zuciyarta ta dinga kokarin aikata mummunan abu a kwanakin baya idan baka mance ba na fad'a maka cewar a ranar da Halisa ta samu labarin aurena da Naja'atu kwanana ne kawai a gaba dan wuka ta dauko zata kashe ni da ita da gaske caka min za tayi daba don nayi gaggawar murdeta na kwace wukar ba to da zata iya illatani kuma a ranar na tabbatar da cewar tana da aljanu dan a gurin suka bugeta."
Abbah Magaji ya jima kansa a kasa yana ta nazarin maganganun abokin nasa, to a gaskiya idan hakane zaman Halisa da Naja'atu a guri daya bai taso ba dole daya ta matsa ta bawa daya guri ma'ana ya zamana ko wacce na gidant
a tare da sharadin 'kin ziyartar juna domin a samu daidaito da zaman lafiya, dan mutukar d'aya na zuwa gidan d'aya to kuwa matsala zata cigaba da afkuwa....Abbah Magaji ya dago kansa a nutse yana kallon abokin nasa ya shiga fad'a masa shawarar da ya yanke a zuciyarsa wacce yake ganin kamar itace mafita a garesu
Abbah Abbas yace."Tun farko haka naso ya kasance to a tsakaninsu Halisan da Naja'atu babu wacce na isa nace ga yanda za'ayi tace to!
Halisa ganin ido Naja'atu taurin kai! amma tunda al'amarin nan ya kasance da haka insha Allahu bayan munje umara mun dawo zan dauke Naja'atu daga gidan gabad'aya zan sanja mata gida idan ma bata so ta zauna a tsohon gidana dake d'anbare zan dai samar mata gurin zama wanda ya dace!
Sannan ina k'ara baku hakuri a bisa abinda ya faru a yau insha Allah zan nemi malamai domin su zauna kan Halisa a sama mata lafiyarta."
Abbah Magaji ganin yanda hankalin abokin nashi ya tashi yasa ya sassauta zuciyarsa yace."Haba Alhaji Abbas meye abin bada hakuri ai ba wata matsala bace wannan insha Allahu Allah zai daidaita maka zamantakewar gidanka da iyalinka sannan kuma naji dadin kar'bar shawarata da kayi ina rokon Allah ya kawo zaman lafiya da daidato a tsakanin iyalinka." Abbah Abbas ya mika masa hannu da fad'in Ameen ya Allah nagode sosai abokina."
To 'bangaran Halisa kuwa sai kusan uku da rabi na rana ta farka da jan gindi ta shiga dakinta ta zabga tagumi tana kallon guri guda, tunda taji kanta yayi mata nauyi da kuma kasala da ciwon jiki yasa ta gane cewar aljanunta ne suka tashi, hawaye ta dinga sharewa tana jin wani irin daci a bakinta, shin wai ita a haka zata kare rayuwarta ne a duniya bukatarta ba zata biya bane.?