Sashe 137
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu meye ribar abinda kuka aikata keda muktar ashe kenan ba Daddy ne abin tausayi ba tunda shi kowa yasan sai da aka shafa fatiha aka haifeshi wannan yaron da kika haifa shine abin tausayi idan ya tashi yasan hanyar da akabi aka samar dashi dole ya shiga halin damuwa da tashin hankali.
Munira na kuka tace" Hakane maganarki Najaatu wallahi naso tun yaron na ciki ya mutu ko kuma na haifeshi babu rai, ke har fatan mutuwa nake wa kaina a lokacin dana nake da cikin amma duk hakan bata samu ba."
"Ki daina wannan maganar Munira dan shi Ubangiji babu ruwansa saboda kune kuka sa'bawa dokokinsa ba yaro ba Allah na iya raya shi kodan ya nuna muku ishara daku da masu irin halin ku." Amma yana da kyau ki sake neman Muktar din idan da hali ki kaishi koton musulunci."
Munira girgiza kai tayi tace"A'ina zanga Muktar? yau watansa uku da aure yana can legos tare matarsa amma kowa yaga Ahmad yasan d'ansa ne saboda suna kama sosai.
Najaatu tace"Kin sanya masa suna mai ma'ana kuwa to Ubangiji Allah ya raya shi tafarkin addinin musulunci Allah kuma ya karkato da hankalin mahaifinsa kansa yazo ya dube shi da idon rahama." A sanyaye munira ta amsa da ameen ya Allah.......Haka suka kasance har yamma suna hirar yaushe gamo gami da jajantawa junansu, Najaatu ganin biyar ta wuce yasa ta shiga kicin domin d'ora girki duk da ba itake da girki ba a ranar watarana idan yazo yakan ci abinci a gurinta kafin ya tafi.........Munira ta dinga sha'awar gidan Najaatu tana ta 'kiyasta abubuwa da yawa a zuciyarta hakika Allah ya musanyawa k'awarta da nagartaccan miji irin wanda yake da wahalar samu a duniya tana rokon Allah ya bata kwatankacinsa.
Najaatu wanka tayi ta kintsa jikinta tsaf ta fito falon ta zauna suna hira kafin lokacin sallar magariba yayi.........Bayan sunyi sallar ishai sai suka ci abinci tare, bayan sun gama Najaatu tace yana da kyau tayi wanka ko taji dadin jikinta, wani bedroom ta bude mata tace ta shiga akwai komai na bukata a ciki, a cikin kayan sawarta ta daukar mata riga da zani na atamfa ta kai mata dakin ta ajiye mata kan gado, ta fito ta zauna kan kujera tana sa'ke sa'ke gaskiya bata kaunar zaman Munira a gidanta saboda hausawa nacewa ruwan da ya dake ka shine ruwa Tsoron wani abu takeyi gashi tana jin nauyin tace mata ta koma gidan hajia ta kwana a can.
Tana can cikin tunanin mafita Munira ta fito cikin atamfar data ajiye mata, Najaatu saurin gyara fuskarta tayi tana kallonta har ta karaso kusa da ita ta zauna, a sanyaye tace"Najaatu da zan samu aikin aikatau dana zauna nayi na tara kudi kafin na tafi."
Gabanta ne ya fad'i jin abinda Munirar ke fad'a!
Tace" A gaskiya da kamar wuya ki sami aikatau anan area ki bari zan baki jari idan zaki tafi sai kije can ki kama sanaa har Allah ya fito miki da mijin aure....Munira tace"Nagode sosai Najaatu hakika ina alfaharin kasancewar ki a matsayin aminiyata Allah ya 'kara miki rufin asiri da wadata."
A hankali ta amsa da amin gefe guda tana nazarin maganarta shin wai har kwana nawa za tayi mata a gida itafa Munira tsoro take bata bata bukatar zamanta a gidanta to amma yanda za tayi ta fad'a mata ne bata sani ba .....Hira sukeyi sama sama Munira na sake bata labarin irin wuyar da tasha a hannun kanwar mamanta, ita dai jinta kawai take tana tunanin mafita.
Cikin wannan yanayi ya shigo gidan, Najaatu ta miqe da sauri tana masa barka da zuwa. ..........
Amsawa yayi ya tsaya yana kallon Munira da fad'in "Bakuwa kikayi ne."?
Munira ta zube har kasa tana gaisheshi, Yace." Wannan fuskar kamar na santa."?
Munira sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, Ita kuwa Najaatu a cunkushe tace"Kawata ce Munira 'kanwar Marigayi." Yayi jim yana kallonta kafin yace "Tazo ganin Daddy kenan."?
" Umm." Tace ba tare data kalleshi ba babban burinta ya bar gurin dan ita ba taga amfanin tsayuwarsa a gurin ba.
Shi kuwa gyara tsayuwa yay ba tare da wata Manufa ba yace."Munira ina mutanan gida ina fatan duk kuna nan lafiya." Tace."Kowa lafiya Abbah suna gaisheku da kyau." Yace."Muna amsawa ." yana gama maganar ya wuce ciki, Najaatu ajiyar zuciya ta sauke minti biyu tabi bayansa, Yana zaune a gefan gado ta shiga dakin, zama tayi a nutse ta gaisheshi tare da tambayarsa yanayin kasuwa, yace komai alhamdullih....Shuru dakin yay kafin yace."Naji dadin zuwan Munira ko babu komai sun nuna damuwarsu akan yaron dan dama abin yana damuna ganin daga b'angaransu babu wanda ya ta'ba zuwa da sunanan yazo ganin yaron amma zuwanta ya nuna mana cewar sun san da zaman yaro a hannuki."
Babu cikakkiyar walwala a tare da ita tace"Munira ba ganin yaro tazo ba hasalima bata san dashi ba sai da hajia ta sheda mata ita dai kawai tazo neman gafara akan abubuwan da suka faru.
Yace."Allah sarki ai sai ki yafe musu tunda sun gane kuskuransu ko babu komai kun had'u tunda ga Daddy nan a tsakaninku sai suci albarkacinsa......Shuru tayi tana kokarin mayar da kwallar idonta, Ya kalli agogon hannunsa tare da fadin"Yau me kika girka."
"Abinci ne mai sauki dan zuwan Munira yasa ban shiga kicin da wuri ba...jollop din macaroni nayi." Girgiza kansa yay yace."Bana jin zan iya ci." Ta kalleshi tare da son tayi masa tambayar da ta jima a cikin zuciyarta " Wai don Allah me yasa baka son cin abincin su Halisa da girkina da banawa ba sai kazo kaci abinci.
Yace." Babu wani dalili kawai dai inajin dadin duk abinda zai fito daga gurinki sannan kuma suma ba abincinsu ne bana ci ba, ina ci daidai gwargwado amma dai duk kin fisu iya girki shine dalilin daya sa nake so naci naki." girgiza kanta tayi tace"To yanzu da a guri guda muke haka zaka dinga yi kenan kasan rigima za'ayi.
Yace."Saboda me.'? kai tsaye tace"Saboda wannan dalilin ba kowace macace zata yarda ba dan Allah ka dinga kamanta adalci Abbah bana so ranar Lahira ka tashi da shanyayyan jiki."
Shuru yayi yana tunanin maganarta kafin yace." Dan nazo gidanki kin bani abinci naci hakan ba zai sanya ranar lahira Allah ya tuhume ni ba, nasan akan abinda kike cewa nayi adalci sabida ina neman ki a lokotan da ba girkin ki ba shiyasa kike fadin cewa na dinga adalci to abincin ma na daina zuwa naci kamar yanda kika hanani kanki a lokacin da nake bukata.'' Mi'kewa yayi ya kama hanyar fita da fad'in sai da safe ina fatan babu matsala.'' Ta mike tana kallonsa sai wani Muzurai yake tace''Daga magana sai ka hasala bani na hanaka abinda kake magana akai ba wanda ya hallice kane yace kayi adalci a tsakanin matanka to me zai saka ka dinga d'aukar kwanan wannan kana kaiwa waccan."!
Hannu ya d'aga mata a murtuke yace."Kinga maganar ta isa haka ko kinga nazo miki da wata bukata ne."?
Da sauri ta girgixa kai Yace."To kada ki sake kawo min hadisai akan wannan maganar.Tace." Dama ai bani na fara maganar ba kaine." Tsaki yaja ya kama hanyar fita, ta bishi da kallon mamaki! itakam bata san me yasa zuciyarsa ke saurin hasala ba kwana biyu tunda ta hanashi biyan bukatarsa a ranar da ba girkinta ba yake mata magana sama sama.......A nasa 'bangaran kuwa haushi da takaici ne yake damunsa dan saboda yasan Zainab ba iyawa za tayi dashi ba, ita kuma Halisa ba cikakkiyar lafiya ba sam be ma fiye matsa mata ba dama Najaatun ce gwanarsa ita kuma ta kasa ta tsare tace bata yarda da wannan tsarin ba, idan ya gama kwana biyunsa a gurinta to haka yake shiga mugun yanayi a tsakanin kwanaki hud'un da zaiyi dasu Halisa ya galabaita mutuka abinka da wanda ya saba da sex duk sai ya fice daga hayaccinsa aikuwa ranar daya dawo gurinta tana raina kanta da farkon dare yayi asubah yayi da safe kafin ya fita kasuwa ma sai yayi, sai kace wani ayu!
Koda ta fito falon gani tayi yana sallama da Munira cikin sakin fuska kamar bashi ba yasa kai ya fita daga falon ba tare daya kalleta, danne damuwarta tayi ta zauna suka cigaba da hira da Munirar kafin dare ya shiga sukayi sallama kowa ya shiga daki domin kwanciya........Wanka tayi kamar koda yaushe ta shirya cikin shirin kwanciya, wayarta ta dauka tana dube dube gabadaya bata cikin nutsuwarta na farko zaman Munira a gidanta ya tsaya mata a rai na biyu kuma wannan matsalar da take fuskanta a gurin maigidan nata, tasan yasan gaskiya amma yake takewa yanzu meye laifinta dan ta tunasar dashi abinda ya dace, ashe shi 'kullatarta yayi a cikin zuciyarsa gaskiya al'amarin ya bata mamaki sosai...........Washe gari da safe da yazo take fad'a masa bukatarta naso ya bata kudi zata taimakawa da Munira idan zata tafi....Kai tsaye yace bashi dasu." Ta saki bakinta tana kallonsa har ya gama abinda yake a dakin ya tafi....Da wannan takaicin ta yini dan har sai da Munirar taso ta fahimci wani abun na faruwa........Da daddare da yazo bai bukaci cin abincinta ba ita tayi masa tayi tare da fad'a masa abinda yake so ta dafa..........Yace."A 'koshe yake da zai tafi ta dakatar dashi tare da fadin tana so tayi magana dashi, yace sai dai ta bari sai da safe dan yanzu sauri yake.....Koda ta fito falo samunsa tayi yana magana da Munira tana fad'a masa cewar gobe zata tafi da safe.