Sashe 103
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To bayan tafiyar Abbah Abbas da iyalinsa Hajia ta kalli Yaya Ramlatu cikin bakin ciki da takaici tace" Ramlatu bana tunanin zan zauna dake a gidan nan sabida haka tun wuri ki nemi inda zaki je ki zauna, Idan ya kama dole sai kin zauna to ni ina iya bar miki gidan dan ni wallahi sharrin ki tsoro yake bani."
Ramlata cikin sarewa da al'amarin ta nufi mahaifiyar tata murya na rawa tace"Hajia dan darajar Allah kada kije ko ina a kaina kiyi zamanki a dakinki wallahi na tuba nabi Allah na gane abinda nayi ban kyauta ba insha Allah ba zan sake ba ki yafe min Naja'atu kema ki yafe min abubuwan da nayi miki." Naja'atu ta goge hawayen idonta ta kalli hajia murya na rawa tace"Hajia dan Allah ki yafe mata tunda ta gane kuskuranta kin san adan adam ajizi ne kowa yana kuskure a duniya kinga shima wanda akayi wa laifi kafin ya tafi sai da ya yafe mata tukkuna." Hajia tace"Humm!
Naja'atu kenan har yanzu ke yarinya ce kina ganin kamar abinda take fada har zuciyarta ne nafi kowa sanin halin Ramlatu da rantsuwa kan karya."
Hajia Rabi dake kokarin shigowa dakin tace"Ke kuwa Hajia ki daina wannan maganar mana, kiyi addua kan Allah yasa tuban Ramlatu na gaskiya ne ni a jikina ina jin cewar karshen matsalarta ne yazo akwai mutane da dama da suke aikata mummunan abu wanda yafi nata su tuba su nemi gafarar Allah ya gafarta musu, kema don Allah ki yafe mata tunda shi Abbas din ya nuna komai ya wuce kuma dan Allah ki daina fad'in zaki fita ki bar mata gida wannan maganar bata dace ba." Hajia tace"To shikkenan tunda kunce haka na hakura na barku da ita gatanan ta zauna idan halinta ne zaku gani ni tuntuni na dawo da rakiyar Ramltu shiyasa nake so tayi nesa dani da zuria ta."
Ramlatu tace"Hajia ashe har kin cire ni daga cikin zuriarki me yayi zafi hajia ki duba halin da nake ciki nice fa babbar 'yarki." Hajia taja tsaki gami da miqewa da fad'in "Kece babba kuma kece fitinanniya wacce bata kaunar zaman lafiya Allah dai ya shiryeki." Tana kare maganarta ta mike tare da kallon kishiyarta tace"Hajia gobe idan Allah ya kaimu da safe zakuje asibiti da Naja'atu a dubata." Hajia Rabi tace"To Allah y kaimu goben lafiya." Hajia sama ta nufa ba tare da ta saurari magiyar da Ramlatu take mata ba.....Hajia Rabi ta kalleta a nutse tace"Hakuri zakiyi Ramaltu ki cigaba da rarrashinta har ta sakko amma hakikanin gaskiya ke da d'anki kun aikata mummunan aiki sai dai kawai ace Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba."
Ramlatu tasa gefan zaninta ta share hawayen idonta jingina tayi jikin kujera tare da tsirawa kasan kafet ido tana tunanin yanda rayuwa ta juya mata baya.....Naja'atu kuwa miqewa tayi ta shiga daki ta kwanta tana zubar da hawayen bakin ciki, tana kallon Abbah Abbas ya tattara iyalinsa suka tafi banda ita wannan al'amarin yayi masifar tsaya mata a rai! sai ta shiga tunanin ita yanzu mecece makomarta.
To washe garin ranar da wuri Naja'atu da hajia Rabi suka shirya direba ya daukesu suka nufi asibiti da yake pravite ne basu sha wahalar ganin likita ba.........Dr ya tabbatarwa Da hajia Rabi cewar Naja'atu ita da babyn dake jikinta lafiyarsu lau, hasken da fatar tayi ba matsala bane mafi akasari masu karamin ciki nayin irinsa, har scanning sai da yayi mata ya nuna musu tare da tabbatar musu da lafiyar babyn magunguna masu kyau ya rubuta a takarda sannan yace suna fita zasu ga gurin saida magani sai su siya...........Hajia Rabi taji dadin bayanin da Dr yayi kan lafiyar Naja'atu da cikin jikinta, dan haka kafin su nufi gida sai da suka tsaya a Pharmacy (gurun siyar da magani) suka siya kana suka shiga mota direba yaja suka nufi gida.
Koda suka isa gida hajia rabi bata bari direba ya shiga da motar cikin gidan ba ta umarce shi daya saukesu....Suna fitowa ta kalli Naja'atu a nutse tace"Zamu shiga gidan Baba malam ku gaisa ko."?
Naja'atu tayi kwal kwal tana shirin yin kuka tace"Hajia ina jin tsoron haduwata da Baba Talatu." Hajia Rabi tayi murmushi tare da girgiza kanta tace"Ki saki jikinki kada ki damu bazan bari tayi miki fad'a ba!
Baba Talatu macace mai ilimi tasan qaddara daidai gwargwado saboda haka ki kwantar da hankalinki nayi niyyar kaiki gurinta ku gaisa ba da wata munufa ba." Naja'atu ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace"Nagode hajia." Hajia rabi tace"Babu komai ai." Hannunta ta riqe kai tsaye suka nufi gidan baba malam d'in.........
*Wayyo hannuna
Ayi hakuri da typing error babu editing
Nagode
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.... *07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
66****Baba Talatu na zaune a kan tabarma da karamar redio a kusa da ita tana sauraran shirin barka da hantsi wanda tashar redio freedom ke gabatarwa a daidai irin wannan lokacin Baba Talatu ma'abociyar jin redio ce shiyasa kullum kanta yake a waye ta iya mu'amula da mutane bayan hakan kuma tana zuwa isilamiyya irin ta matan aure duk ranakun asabar da lahadi( sauraran redio nada mutukar tasiri a rayuwar d'an adam akwai muhimman shirye shiryen addini da wasu tashoshin gidajen redion ke gabatarwa wanda idan mutum na saurara zai qaru da wasu abubuwan masu amfani, redio tamkar makarantar ce ta wanni fanni domin suna ilimantarwa )
Tunda suka shiga gidan Naja'atu take ra'be ra'be ta kasa sakin jikinta sai 'buya take a bayan hajia Rabi tana jin tsoron had'a idonta da mahaifiyartata......Baba Talatu ta gyara zamanta fuskarta da fara'a takewa Hajia Rabi sannu da zuwa, redion kusa da ita ta dauke daga gurin ta sanja mata guri tana fad'in'' Hajia bisimillah zauna ga guri nan."
Hajia Rabi ta zauna a nutse Naja'atu ta zauna kusa da ita sai sunkuyar da kanta takeyi............Bayan sun gaisa da juna Hajia Rabi ta kalli Baba talatu tace''Naja'atu na kawo miki ku gaisa da juna." Baba Talatu tace'' Au ita bata da kafafu har sai anyi mata jagora."?
Hajia Rabi tace" Haba ba dai haka bane wallahi munje na kaita asibiti ne nace lallai sai na kawo ta ku gaisa da juna.
Baba Talatu ta ta'be bakinta taja bakinta tayi shuru har yanzu tana jin ciwo da takaicin abinda naja'atu tayi musu.....Naja'atu ta dago kanta a hankali ta kalli gurin da mahaifiyar tata take a sanyaye tace"Baba ina kwana kunanan lafiya."?
Ba tare data kalleta ba ta amsa da "lafiyarmu lau." A sanyaye ta mayar da kanta qasa jikinta duk ya mutu da yanayin kallon da mahaifiyar tata ke mata....Hajia Rabi tace"Baba don Allah ki yafewa yarinyar nan magana ta wuce nasan ke mai ilimin addini ce kin san qaddara daidai gwargwado dan haka ki sassautawa naja'atu taji da abu guda.
A sanyaye tace"Ai bani tayi wa laifi ba da kike wannan maganar ita tasan wanda tayi wa laifi shi zata nemi afuwarsa bani ba."
Hajia Rabi tace"Wallahi tuntuni Alhaji Abbas ya yafe mata da bai yafe mata ba ai ba zai tsaya a kan al'amuranta ba nasan kina sane da cewar shine yaje har can garin da take ya daukota ko.''
A sanyaye tace"Duk inada labarin komai wallahi ni kam na rasa wace zuciya ce da mutumin nan hajia Rabi ki duba kiga irin rashin arzikin da yarinyar nan tayi masa amma bai duba ba ba tare da yayi shawara da kowa ba yaje ya daukota daga wahala ai naso ya barta a can ta gane duniya ba rigar sanyawa bace."
Hajia Rabi tace"Haba Baba ya kike wannan maganar babu dadin ji idan rai ya 'baci hankali ake sawa ya nemo shi, kuma a duniyar nan babu wanda baya kuskure saboda haka dan Allah ki daina wannan maganar Baba kiyi hakuri da duk wasu abubuwa da suka faru a baya tunda shima wanda akayiwa laifin maganar ta wuce a gurinsa sai mu taru gabadayanmu muyi wa yarinyar nan adduar rabuwa da cikin jikinta lafiya shine babban abinda ke gabanmu
Baba Talatu ta share guntun hawayen idonta tace"Wallahi tuntuni magana ta wuce a gurina kuma na yafe mata har abadah sai dai duk sanda na tuna al'amarin nakan ji rashin dad'i a zuciyata nida malam munso yarinyar nan ta zauna zaman aure da Alhaji Abbas amma ta watsa mana qasa a ido duk sanda na tuno wannan al'amarin nakan shiga 'bacin rai mai tsanani."
Hajia rabi tace"Gaskiya da akwai rashin dadi a cikin al'amarin amma bakya tunanin rabo ne ya fitar da ita daga gidan Alhaji Abbas din, dukkaninmu fa bamu san gaibu ba sai Allah wannan cikin dake jikinta ya ishemu ishara gabad'ayan mu."
Baba Talatu tace"Eh nima bayyanar cikin jikinta yasa na jingina al'amarin a matsayin abinda kika fad'a yanzu babu shakka idan rabo ya rantse to babu mahalukin da ya isa ya dakatar dashi, san nan kuma wani baya ta'ba haihuwar d'an wani koda da akwai sauran zama a tsakanin Alhaji Abbas da yarinyar nan to tilas sai taje ta auri wani ta haihu sannan ta dawo hannunsa."
Hajia Rabi tace"Yawwa nima abinda nake taso ki fahimta kenan watakila akwai ragowar zaman aure a tsakaninsu shiyasa Ubangiji ya yanke alaqar auranta da Bashir bayan ya saukar da ikonsa na samuwar cikin jikinta."
Baba Talatu tace"To Allah yasa dan wallahi nafi mata sha'awa ta koma dakinta akan ta sake wani auran." murmushi hajia Rabi tayi a zuciyarta tace akwai yiwuwar hakan dan ganin irin kulawar da Abbas keyi wa yarinyar alamu sun nuna har yanzu yana muradinta.