← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 143

Sashe 72

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har yanzu ina tare da Abbah
ina kuma taya shi alhini da jimamin faruwar wannan al'amari*
*Tofa gwanar taku ta tsinci dami a kala duk ta rud'e ta samu saurayi mai jini a jika wanda zai iya da jarabarta anata ganin Bash ne zai iya dauke mata dukkanin laluranta akwai dramar
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake
Vip gruop #600
Normal gruop#300
accont: 0542382124..Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn45
*Bash* ya sake tausasa muryarsa kamar wani mutumin kirki yace."Idan kin amince min da wuri nake so ayi komai a gama dan akwai tafiyar da take tunkaro ni aiki zai kaini kasar Ghana inaso in tafi dake can sai muyi amarcinmu hankali kwance."
Lumshe idonta tayi tana jin wani irin feelings na taso mata jin maganar amarci yasa ta sake kwadaituwa da auran *Bash* domin tana ganin a yanzu za tayi irin auran da take muradi.......Cikin wani irin yanayi Tace"Zaka iya auran bazawara."? *Bash* yayi sak yana kallonta, da wani irin yanayi na alhini gami da damuwa tace"Ina da aure yanzu haka dalilin auran dolen da akayi min da mijin 'yar uwata data mutu yasa nazo nan garin.....Tiryan tiryan ta bashi labarin rayuwarta...
*Bash* ya shiga murza fatar goshinsa cikin damuwa yace."Amma banji dadin wannan labarin naki ba wallahi wannan dattijon yayi min shigar sauri amma babu damuwa tunda ina sonki zan iya auranki a haka yanzu babban burina ya sake ki dan yanda kika bani labarinsa na fahimci mai taurin kai ne watakila dik wannan abun da kikayi masa sai iya 'kin rabuwa dake amma idan yasa gardama da taurin kai sai kawai muyi maganinsa." Tace"Kada ka damu a jikina ina jin zamana dashi yazo karshe zai iya sakina idan yaji na zubar masa da ciki domin yana da bala'in son yara bana tsammanin zai iya hakura ya kyaleni.....Kuma zan tura masa text domin na tabbatar masa da cewar cikinsa ya lalace nasan hakan sai sake tunzurashi...
*Bash* yace."Okey ina ganin yanzu ma zaki iya tura masa text din ayi ta ta 'kare dan wani irin kishinsa nake ji a cikin zuciyata." Murmushi tayi tare da mika hannunta domin kar'bar tsadaddiyar wayar tasa.......Daidai lokacin Munira ta shigo palon hannunta rike da wasu ledoji sha'ke da kyan ciye ciye..Ganinsu zaune guri guda yasa tace" Kai gaskiya kunyi bala'in dacewa da juna kada dai har soyayya ta shiga tsakaninku gaskiya idan haka ta kasance zanfi kowa jin dadi wallahi... *Bash* na shegen murmushinsa yace."Munira kina da wannan Friend din baki ta'ba nuna min hotonta ba ai da tuni nine zan aureta amma kika bari wani tsoho yayi min shigar sauri." Munira ta 'karaso gurin tana wata irin dariya ta farin ciki ta bawa Naja'atu hannu suka tafa suna dariya..Munira ta zauna kan kujera tana fad'in"Wallahi Broth Allah ne kawai yayi ba kai zaka fara auran Naja'atu ba amma tuntuni na dade dayi maka sha'awar auranta kawai sabida nasan baka so ayi maka maganar aure yasa banta'ba nuna maka hotonta ba amma yanzu naji dadi sosai daka ganta da idonka kace kana so."
Cike da sha'awa yace."Munira Friend dinki tayi sosai dan lokaci guda ta tafi da zuciyata matsalata guda auran da yake kanta shin wace shawara kuka yanke akansa."
Munira tace"Haba broth kada ka damu wannan auran ai dashi da babu duk daya suke insha Allahu sai ya saketa komai nacin sa."
*Bash* ya mi'ke tsaye idanunsa kan Naja'atu yana mata wani irin kallo wanda kana ganinsa kasan na sha'awa ne yace"Ki rike wayar a hannuki zuwa gobe da safe zan 'karba amma ki tabbatar da cewa kinyi masa text din da kika fad'a."
Tace"Insha Allah zan masa kada ka damu." Hannunsa ya zura a aljihun jins din dake jikinta ya wani tsira mata shu'uman idonsa gabad'aya jikinsa ya mutu ai dole ne ya fita ya nemi biyan bukatarsa...Munira ta dinga dariya tana fad'in "Lallai yau ina kallon soyyaya mai zafi!

Had'uwar farko Naja'atu kin rikita min dan uwa gaskiya naji dadin wannan al'amarin." *Bash* Yayi saki murmushi had'e da sosa kanshi ya kama hanyar fita yana wata shegiyar tafiya irin ta marasa kunya.

Naja'atu murmushi kawai take dadi na ziyartar zuciyarta salon kallon soyayyar da *Bash* ke mata shine yake sake rikita ta tana jin sonsa na sake karuwa a cikin zuciyarta..

Tare suka shiga dakin ita da Munira ta zauna gefan gado tana ta duba wayar Bash din Hotonansa ne kala kala yawancin pictures din bana Najeria bane yayi su a kasashe daban daban! ganinshi rungume da turawa black americas bai dameta ba tana ganin ai wayersa da kudinsa ya cancanta yayi mu'amula da kowane irin jinsin mutum..Munira ta fito daga wanka tana kintsa jikinta tace"Gaskiya Naja'atu kinsha wuya na tausaya miki kuma wannan matar data taimake ki yana da kyau naje nayi mata godiya." Tace"Gaskiya kam yana da kyau idan an kwana biyu muje na rakaki gidanta...Munira ta zauna kusa da ita tare da fad'in "To alhamdullhi Yanzu mun samu ciki ya zube ba tare da munsha doguwar wahala ba yanzu babban abunda yake gabanmu shine rabuwa da wannan tsohon.

Hankalinta nakan wani had'ad'dan hoton *Bash* wanda ya dauke shi yana sanye da kayan wanka a bakin swimming hoton yayi masifar dauke mata hankali ganin zahirin *Bash din* ya sake firgitata sai ta sake kwadaituwa da auransa hakika ta samu nasarar auransa to ta kere sa'a kuma zata iya shiga koina dashi ta nuna shi da sunan mijinta ba kamar Abbah Abbas ba da take jin kunya a dangatata dashi a matsayin miji...

Munira ganin Naja'atu bata fuskantar maganar da take yasa ta le'ka cikin wayar tana dubawa!

Dariya tayi tace" Naja'atu kenan naga alama kema kin mutu akan Brother d'ina Humm! na taya ki farin cikin samun zuciyar *Bash* 'Yan mata da yawa suna sonsa baya ta'ba sauraransu amma ke gani daya yayi miki ya haukace harda maganar aure duk da kasancewarki bazawara yana da kyau kiyi gaggawar nemawa kanki mafita tun kafin damar da kika samu ta kufce miki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Yanzu wace shaw
ara kike ganin ta dace?

Ni da cewa nayi zan tura masa da text na fada masa cikinsa ya zube kuma ina nan ina jiran takardarta." Munira tace"Wannan shawarar tayi.....Kawo wayar na rubuta masa text din...Naja'atu tasa numbarsa da yake amfani da ita a saudia, Munira babu sallama ta shiga rubuta text din kamar haka.
_Ni ce Naja'atu ina so in tabbatar maka da cewar wannan cikin daka yi min yabi rariya dama tun kafin haka ta faru sai da na fad'a maka bani da ra'ayin zama da kai ballantana har na haihu dakai komai ya faru son zuciyarka ne ya janyo maka....Abbah banso muyi irin wannan rabuwar da kai ba amma ina ganin hakan shine daidai Ni ce dai Naja'atu ina nan cikin koshin lafiya bayan samun nasarar rabuwa da masifar daka 'kunsa mun a cikina ina nan ina jiran saki daga gareka idan baka sakeni ba to kuwa zanyi ta zama a inda nake har'karshen rayuwata_
Kafin a tura text din Naja'atu sai da ta karanta kusan sau biyar tana ganin kamar maganganun sunyi tsauri da yawa! amma kamar wacce aka sawa lemon tsami a baki ta kasa cewa komai tana kallo Munira ta tura text din ya tafi gabanta sai ya tsananta fad'uwa cikin zuciyarta tana ji kamar bata kyauta ba...Munira tace"Yana da kyau ma a tura masa ta whasap dan naga kamar yanayi ko."?

A sanyaye tace"Duba ki gani." Munira ta shiga dubawa taga numbarsa tana whasap amma kuma kwanansa biyu bai hau ba, dan tun ranar daya bude ya saurari audion da Salim ya turo masa bai sake kunna data ba dan dama ba kasafai yake shiga whasap din ba.....Tace" Ya kwana biyu baya kai amma Bari a tura masa domin ya dauki abin da muhimanci."
Naja'atu dai shuru tayi Munira sai zartar da hukunci takeyi ita kuma gabanta sai faduwa yake tana adduar Allah yasa ya mayo da martanin saki.

Munira kayan ciye ciyen data shigo dashi ta baje musu suka dinga ci suna hira Naja'atu dai daurewa kawai take bini bini sai ta duba wayar dake hannunta wai ko ya turo amsa.....Jiki a sanyaye ta ajiye wayar ta nufi toilet din dake cikin dakin tayi wanka ta kimtsa jikinta tare da sanja pad ta fito Munira ta bata sababbin kayan bacci tasa tasa turare ta zauna tare da daukar wayar tana sake dubawa...Ita kuwa Munira tana kwance a bad daga ita sai 'karamar vest da gajeran wando wanda ya matseta sosai pictures take dauka kala kala tana turawa Muktar ta whasap.....
*Allah ya shiryaki Munira*
'Bangaran Abbah Abbas kuwa bai samu damar duba wayarsa ba sai lokacin da yazo kwanciya dan basu dade da shiga masaukin nasu ba sun fita duk gabadayansu sun dan shiga kasuwa dalilin barin 'kasar da za suyi jibi idan Allah ya nufa dama kwana goma sukeyi ko sati biyu suke dawowa........Halisa na kokarin kwanciya a kusa dashi taga ya mi'ke zumbur!

Gabanta ne ya fad'i! tayi saurin matsawa dan ta dauka marinta zai yi! sai dai kuma ganin ya tsirawa fuskar wayarsa ido yasa da sauri ta 'leka kanta tana dubawa!
Chapter 72 · 0% Book details