← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 143

Sashe 131

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya d'aga mata bai bari ta karasa ba ya miqe ya fita daga dakin, kai tsaye gurin Zainab ya nufa, Hayaniyarsu da shewarsu yaji a daya dakin can kunnuwansa suka jiyo masa kukan Ummi dake dakin Zainab da sauri ya nufi dakin yaga yarinyar saboda kuka da mutso mutso har ta fito daga cikin net dinta ga bargon dake jikinta ya toshe mata hanci! da mugun sauri ya ka'rasa inda take bargon yayi gaggawar daukewa yarinyar ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya! gumi hawaye majina duk sun 'bata mata fuska!

Abbah hannusa yasa ya dauki yarinyar jikinsa sai kyarma yake ya shiga jijjigata inaa! kamar sake tunzurata yake ta dinga kuka tana yakushin fuskarsa, cikin tsantsar tashin hankali gami da nadamar kar'bar auran Zainab ya fita da yarinyar a kafadarsa
Cin karo yayi dasu sun fito daga dakin dik su ukun a sakamakon jin kukan yarinyar daya cika falon......Zainab a tsorace! ta karasa kusa dashi ta miqa hannu zata kar'bi yarinyar ya wanke fuskarta da wani gigitaccan mari!

Gefe guda ta matsa tare da dafe kumatun ta da hannunta jikinta in banda rawa babu abunda yake.....Ya kalli su Aunty Balaraba yace."Wallahi kunji kunya kun zama annoba a guri yanzu da girmanku da komai kuke aikata abu irin na marasa imani! me yarinyar nan tayi muku kuke azabtar da ita!

Kuna manya masu shekaru wanda suke sama da nata ba zaku d'orata a hanya mai kyau ba sai ku d'orata hanya mara kyau! hanyar da zata cutar da kanta da abinda ta haifa, hakika zamanku a gidan nan be amfaneni da komai ba sai sharri! ya kalli Zainab dake wani irin kuka na tsoro yace."Zainab ban ta'ba tunanin kishi zai rufe miki ido ki nemi hanyar halakar da abinda kika haifa ba, ashe dama karya kike Ummi lafiyarta lau amma kika dora mata lalura duk dan ki hanani samun nutsuwa shin yanzu meye ribarki nayin hakan?

Jiya Dr sai da ya fad'a miki matsalar yarinyar nan ashe kamar 'kara tunzuraki yay kin barta ita kadai a daki tana ta kuka ke kina ta tare da wad'anda zasu kaiki su baro, wallahi in banda darajar mahaifinku da dukkaninku sai na baku mamaki ni ba shashashan namiji bane da zaku dinga wasa da hankalinsa, sabida haka ko wacce ta fita ta bar min gidana zaman ya isa haka, kuma ku sani sai na sanar da Ya sheik abunda ke faruwa." Yana gama maganarsa ya shige ya barsu a gurin....Zainab na wani irin kuka na nadama tabi bayansa....Zubewa tayi k'asan kafafunsa tana kuka hade da bashi hakuri, Abbah ya dinga jin tamkar yayi ta boll da ita gurin, hakuri ya bawa zuciyarsa ya buga mata tsawa tare da fadin"Kar'beta ki bata nono muguwa kawai." Zainab jiki na rawa ta kar'bi yarinyar a hannunsa ta fito da nono tasa mata a baki.........Girgiza kafafaunsa yake yana tunanin irin hukuncin da zai dauka akanta, ba zai saketa ba amma sai ta gane kuranta harshi zata yiwa wasa da hankali lallai sai ya wulakantata dan baya iya had'a kowa da 'ya'yansa.....Zainab kuka take tana masa magajiya gami da kokarin wanke kanta yaki sauraranta data isheshi ma cewa yay ta rufe masa baki ko ranta yay mummunan 'baci!

Gum tayi da bakinta ta cigaba da shayar da 'yarta nono.............
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
85*******'Bangaransu aunty Balaraba kuwa hankali a mugun tashe suka had'a kayansu suka bar gidan cikin nadama gami da dana sanin abinda sukayi dan sunyi masifar tsorata da yanayin 'bacin ran da suka ga maigidan a ciki tabbas daba dan darajar mahaifinsu ba to da babu shakka sun san sai ya dauki mataki a kansu kamar yanda ya fad'a musu fargabarsu daya kada ya sami mahaifinsu ya fada masa abunda ke faruwa babu shakka idan mahaifinsu yaji wannan al'amarin to sai sun fuskacin bacin rai mai tsanani.

Abbah da babbar murya ya gargadin Zainab gami da kafa mata dokoki akan 'Yarsa duk da yasan rai da rayuwa na Allah ne haka kuma cuta da lafiya shima na Allah amma dan ya tsoratar da ita yasa yace mutukar wani abu ya samu 'yarsa tofa ba zai kyaleta ba sai ya dauki mataki a kanta tunda ya gane inda ta dosa wato yarinyar bata itace a gabanta ba kishin jahilci ne yake damunta to kome za tayi taje tayi akan kishinta amma kada ta kuskura ta sake yi masa yawo da hankali ko kuma ta dauki ciwon karya ta d'orawa 'yarsa wannan itace damarta ta karshe idan ta sake ta kuskura ta sake maimaita masa abu makamancin haka to zasuje gaban mahaifinta ya sheda masa abubuwan da faruwa.........Sosai take kuka ta kuma raina kanta da wayonta bata ta'ba tsammani al'amarin zaiyi zafi hakaba hakuri take bashi ya'ki sauraranta sai da ya 'kare mata tanadi tukkuna yayi ficewarsa daga dakin ya barta cikin nadama mara amfani.

Rai a bace ya isa gidan Najaatu a maimakon ya samu sassauci sai ya tarar da wani 'bacin ran dan kicin -kicin ya sameta tunda ta gaishe shi ta tambayi jikin Ummi bata sake masa magana ba fitowa ma falo tayi ta kyaleshi a dakin shi kadai......Takaicin sa ya sake nunnkuwa a gaskiya al'amarin mata yana da wuyar sha'ani tabbas lusarin namiji ba zai iya had'a mata biyu ko uku ba.

Wanka yayi ya kintsa jikinsa ya fito falo ya sameta a zaune tana wasa da d'anta tana murmushi kamar yayi mata magana sai ya rabu da ita, gurin cin abinci ya nufa, a tunaninsa zata zo ta had'a masa abin kari, sai yaga ta kara gyara zamanta, girgiza kansa yay da kansa ya hada tea ya zuba soyayyar doya da kwai a plate a nutse ya gama karyawa ya miqe daga gurun, inda take ya nufa ya tsaya a kanta tare da tsira mata idonsa.

Kasa d'ago kanta tayi ta kalleshi tana dai ganin Inuwarsa tsaye a kanta, yatsun hannuwanta ta shiga wasa dasu kwallah na kokarin zubowa daga idonta tana kokarin mayar da ita.

Gyaran murya yay ya kira sunanta"Najaatu." A hankali ta kalleshi tare da amsawa ciki ciki ta mayar da kanta kasa, Yace."Gaisawa kawai mukayi da juna babu wata mu'amular arziki koda akwai wani dake damunki ne."?

Girgiza kanta tayi tace"Babu abinda ke damuna." Yace."Karya kike ai ba haka fuskarki take ba tunda na shigo gidan nan na lura da canzawarki ko dan na kwana gidan Zainab ne kike fushi! kada ki manta fa na nemi alfarmarki kuma lalura ta wuce komai.

Tace"Haba dai saboda ka kwana a gidanka gurin iyalinka sai naji haushi nifa na baka damar haka wallahi babu komai yau ma kaje can kayi kwanciyarka sai yafi maka akan a kira ka da tsakar dare ace kazo..

Ya dinga kallonta yana nazarin maganarta dik maganganun da take fad'a tana fad'arsu ne iyakacin bakinta amma ba har zuciyarta ba.........."Wannan maganar da kike fada kina fadarta ne iyakacin baki ba har zuciyarki ba na kuma fahimci cewar al'amarin beyi miki dadi ba kiyi hakuri kinji ko Ummi ta samu lafiya insha Allah yau tare dake zan kwana.

Shuru tayi tana dauke kanta, Ya kalli agogo hannunsa ya mayar da hankalinsa kanta da fadin"Zanje kasuwa tunda na fahimci kamar bakya bukatata a gidan....Ba tare da damuwa ba tace"To Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa tare da kama hanyar fita, bayansa tabi da kallo tana jin tausayinsa da haushinsa duk wani abun da Zainab takeyi a ganinta duk shine yake bata dama ita kuwa duk tausayinsa da take ba zata yarda ya dinga daukar kwananta yana kaiwa wata ba, da dai da gaske ne yarinyar bata da lafiya sai ta iya hakura amma ko shakka ba tayi Zainab ta shirya mata ma'karkashiya ne......

Abbah cikin rashin walwala ya isa kasuwa gabad'aya rashin walwalar Najaatu ta sanyayyar masa da jiki ya dinga jin shigar zazzabi zazzabi a jikinsa, sai da ya kira wayarta sau biyar kafin a tashi daga kasuwar........Abbah Abbas gudun tsegumi da surutai irin na Yaya Ramlatu yasa bai shedawa mahaifiyarsa abinda zainab da yan uwanta sukayi ba, lokacin dai da ya isa gidan Hajian ke sheda masa cewar basu dade da dawowa daga gidan nasa ba sunje sun duba yarinyar sun sameta taji sauki sosai..............Godiya yayi dan jin cewa sunje duba yarinyar sannan yayi mata sallama ya nufi can babban gidan nasa.

Gurin Zainab ya fara shiga domin ya tabbar da cewa ta dauki maganarsa da muhimanci ko kuwa, a zaune ya sameta a falo da yarinyar a hannunta, yaci kunu sosai kamar bai ta'ba dariya ba, koda ta gaisheshi kin amsawa yayi ya kar'bi yarinyar ya dubata sosai kafin yace."Ina fata dai kin bata magani." Da sauri tace"Eh na bata. anjima zan kara bata na dare." Shuru yay na minti biyu kafin ya miqa mata yarinyar ya kama hanyar fita ba tare da ya sake yi mata magana ba.

A sanayaye ta kira sunansa ya juyo tare da fadin"Menene kuma."?

Dan darajar Allah kayi hakuri ka yafe min wallahi bazan 'kara ba nima na gane nayi wauta da ganganci kishi ya rufe min ido ina nema na kashe 'yata." Tsaki yaja mai kar'fin gaske yasa kai ya fice daga falon.....ta rushe da kuka tare da rungume 'yarta hakika wannan fuskar gizagon da yake mata na masifar bata tsoro gashi kullum sonsa da kaunarsa kara karuwa yake a zuciyarta..

Ya jima a gurin Halisa suna hira da ita da yaransa sosai ya samu nutsuwa ganin yaransa na cikin walwala da farin ciki yasa shima yaji duk k'uncin da yake ciki ya dauke ya zauna yana ta saurarar shirmen su yana tambayarsu yanayin karatunsu, gefe guda kuma yana fargabar tunkarar Najaatu dan tsoron shiga gidanta yake saboda ya fahimci acikin fushi take......Halisa ta fito daga daki ta sameshi beda niyyar tafiya tace"Abbahn mufida baka duba lokaci ne tara saura fa." Yay saurin kallon agogon hannusa yace"Kinga wa'inda suka tsayar dani nan kin san fa ni sune sanyin idanuna na gane a gurinsu kawai zan iya samun nutsuwa da farin ciki.
Chapter 131 · 0% Book details