← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 143

Sashe 17

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mussadiq ya 'karaci maganarsa ko kallonsa ba tayi ba haka ya fita daga dakin jikinsa duk a sanyaye! haka suke shiga damuwa koda can idan sun ganta tana kuka ko rashin lafiya daga su har mamansu da Abbansu duk su damu duk da bashi da wayo sosai shima ya fahimci cewar Antin tasu bata 'kaunar zaman aure da babansu........Zama yayi kusa da Saddiqa tana gyarawa Baba Talatu wake suna hira jefi-jefi ya kalli Baba talatu da fad'in "Baba me akayiwa Yaya Naja'atu take kuka."?

Baba Talatu tace." Kyaleta Mussadiq ka fita daga sabgarta kaji ko." Mussadiq yayi shuru jikinsa duk yayi sanyi.........To Har aka idar da sallahar azuhur Naja'atu na kwance a daki tana juye-juye zazza'bi me zafi ne ya rufe ta wanda ya hanata mikewa taje tayi alwala tai sallah.

Saddiqa ta shiga dakin domin yin sallah ta kalleta itama ta kalleta babu wanda yace komai a tsakaninsu, Saddiqa ta gyara dadduma ta tayar da sallaharta, koda ta idar mikewa tayi ta fita daga dakin ba tare da tace komai ba, to sai hakan da tayi ya bata mamaki sosai! kuma ya nuna mata cewar yarinyar fushi take da ita, jikinta ne yayi sanyi sosai ta rinste idonta murya na rawa tace"Ba laifi na bane laifin zuciyata ne Saddiqa bana 'kin mahaifinku sai dan zuciyata ta riga ta gama makancewa da kaunar Salim, a dai-dai lokacin da muke sanya rai da bukatarmu zata biya a dai-dai lokacin kuma za'a kawo mana cikas a rayuwarmu ha'kika rayuwarmu nida Salim na cikin kalubale mai girma mutukar akace baza'a daura mana aure da juna ba."
Muryar Mussadiq taji a kanta, tayi saurin bude idonta tana kallonsa......Mussadiq duk yaji abinda take fad'a ya fahimci wata maganar wata maganar bai fahimce ta ba, Yace."Yaya Naja'atu ki tashi kiyi sallah kici abinci mu tuntuni munyi sallah munci abincinmu.

Hannunsa ta ri'ke ya zauna kusa da ita murya na rawa tace"Mussadiq bani da lafiya zuciyata na daf da tarwatsewa."!!

Da sauri yaron ya d'ora hannunsa saman goshinta yana fad'in "Yaya Naja'atu kanki ne yake ciwo ? sannu bari na kira Abbanmu a waya ya kawo miki magani." Girgiza kanta tayi tana kokarin mikewa zaune tace"Mussadiq wannan ciwon nawa Abbanmu shine ya haddasa mun shi dan Allah kace dashi yayi hakuri ya k'yaleni." Mussadiq ya dinga kallonta cikin mamaki yace."Yaya Naja'atu Abbanmu ba zai cutar dake ba kiyi hakuri ki aureshi ki zauna dashi."!

Taji wasu hawaye na kokarin kufce mata, wai kowa sai yace tayi hakuri ta zauna dashi to wai ta yaya zata iya zama dashi alhalin bata sonsa kuma a matsayin Uba take kallonsa, abunfa da wahala wai (gurguwa da auran nesa) mikewa tsaye tayi a hankali ta fita daga dakin, Shi kuma Mussadiq din ya dauki wayarta ya nemi numbar Abban nasu ya shiga kira.

Koda yaga Numbar Naja'atu na kiransa bai 'ki dauka ba, sai dai babu walwala a tare dashi yayi sallama! sai kawai yaji muryar Mussadiq yana fad'in "Abbanmu nine Mussadiq na kira ka da wayar Yaya Naja'atu." Murmushi yayi yana jin wani farin ciki yace."Na gane ka Magajin Abbah Ina fatan lafiya ina Naja'atun take."?

Mussadiq yace."Yanzu taje yin sallah bama ta da lafiya sai kuka takeyi tana cewa wai dan Allah ka 'kyaleta."!!

Shuru yayi yana nazarin maganar yaron daga bisani yace."To shikkenan kace mata na kyaleta tunda bata son Allura ba zan kawo likita yayi mata ba." Mussadiq yace."Ba wannan ba Abba naji tana cewa kada ka aure ta ita tafi so ta auri ancle Salim Abbanmu tunda bata so ta zauna tare da kai ka kyaleta ta auri wanda take so."!!

Abbah Abbas ya jima yana mamakin maganar yaron, kuma yana mamakin abinda yarinyar take yi na rashin kyautawa! wato yaran take zaunawa dasu tana nuna musu a zahiri bata kaunar Ubansu har tana bawa 'Dansa sa'ko ya bashi! ranshi ya 'baci sosai da sosai! sai kawai yayi 'kokarin bagarar da maganar ta hanyar fad'in "Ina Saddiqa take kace mata nace ku shirya gobe zan aiko Salim ya dauke ku xaku koma makaranta ranar Monday." Yace."Tom zan fad'a mata Abbah." Yace." Yawwa ka gaishe min da Baba Talatu da kyau." Yace." Za taji Abbah." Kashe wayar yayi ya shiga nazarin irin iskanci da wulakancin da yarinyar ke masa, zai iya hakura da duk irin cin fuskar da za tayi masa amma kuma ba zai lamunci ta dinga cin fuskar 'yayansa ba, hakan da take yi zai sanya ransu ya 'baci! su shiga halin damuwa da maraicin mahaifiyarsu.

To da wannan 'bacin ran ya shiga gidansa......In da yaje ya tarar da tashin hankalin Halisa dan ko zama bata bari yayi ba tabi shi d'aki! ta shiga zazzaga masa rashin kunya gami da farfad'a masa duk maganar da tazo bakinta kana kuma tace" Sai dai ya za'ba ita ko Naja'atu dan wallahi ba za tayi kishi da Ya tayi da kanwa ba.

Babu Abinda yace mata ya shiga bandaki domin yin wanka zuciyarsa tamkar zata tsaga kirjinsa ta fito dan tsananin 'bacin rai!!!!

Koda ya fito samunta yayi a kwance 'kasan ties tana kuka had'e da wata iriyar fuffuka tana burgima 'kasan ties kamar mai iskokai!

Ya shirya tsaf ya tsallaketa ya fita ya barta a dak'in!

Bin hanyar da yabi tayi da kallo hawaye na sharara ta mi'ke zaune tana cizon tsaya wato Abbas ko gani yayi zata mutu ba zai tanka mata ba kenan ballanta ya fada mata magana mai dad'i! aikuwa a zuciye ta mi'ke tsaye! tana rangaji! da had'a hanya, ta nufi kicin d'inta.

Yana zaune gurin cin abinci yaga fitowarta kallo ya bita dashi yana jan tsaki a fili ya shiga bude kwanonin abincin da ta jera kamar gaske! wayam! babu komai a ciki amma saboda tsabar iskanci da iya shega na Halisa ta shirya tevur kamar ta shirya lafiyayyan abinci......Takaici ne ya kamashi ya tsirawa hanyar data bi ido, kawai sai ya hangota ta fito daga kicin d'in hannunta ri'ke da shar'be'biyar wu'ka sabuwa dal da alama daga cikin kwalinta ta cire, kai tsaye ta durfafo inda yake jikinta na tsuma da rangaji! take fad'in "Wallahi yau koni ko kai a gidan nan Abbas na gaji da wannan abun da kake min ni ka sake ni ma na huta da ganin wannan takaicin auran wannan yarinyar da zakayi masifa ne a gare ni da kai baka sani ba sai sanda nayi maka illah a rayuwarka sannan zaga gazgata maganata." ..........Mufida ta shigo palon tana sanye da uniform na makaranta ta hango abinda ke faruwa, a guje ta jefar da jakarta tayi kan mahaifiyar tata dake dumfarar mahaifinta da dalleliyar wu'ka! tana nema ta caka masa!

" Cikin karaji!! tace" Mommy meye haka? me za kiyi?

Wayyo Abbanmu ka gudu."!!

Tafad'a tare da zuwa ta rungumeshi tana jansa wai ya gudu.

Shi kuwa yana tsaye turmin danya bai razana ba, wato wai-wai d'in da yake ji a gari a na cewar mata na kashe mazajen su idan za'ai musu kishiya abun yazo kansa, jira kawai yake ta 'karaso da wukar yaci ubanta!

Halisa ido a rufe ta 'karasa inda suke Mufida na kuka tana jansa da fadin "Abbah mu gudu kada ta caka maka wu'ka Abba me kayi mata n...........Gani tayi ya kama duka hannuwan Mahaifiyar tata ya murd'e da iyakacin karfinsa Wu'kar ta su'buce ta fad'i 'kasan gurin!

Ya kai mata wani lafiyayyan mari! da bayan hannunsa, wani 'karamin jini ne ya fito daga hancinta, kafin ma ta dawo hayyacinta ya sake kifa mata wani a d'aya gefan, sai kawai yaga ta yanke jiki ta fad'i ta shiga turje turje tana taune harshenta..........Aljanunta ne suke ka da ita a gurin ta dinga turje-turje tana taune harshenta farar kumfa nata fitowa daga bakinta, Halisa na 'karyar aljanu ashe dama tana dasu da gaske! sosai take burgima a gurin tana ta wasu gwalantu wanda ba wanda yake ganewa a cikinsu, Mufida ta nufe ta tana kuka zata ta'ba ta, ya hanata Yace." Je ki cire uniform din'ki idan ta gaji da iskancin da take zata tashi."
Tsakanin Uwa da D'a sai Allah tace"Abbah duba fa kaga abinda take wannan abun ba 'karya bane dan Allah kayi wani abu kai."
Tsayawa yayi tsai yana nazarin Halisan da abinda takeyi Eh kwarai kuwa wannan abun da take yasha bambam dana ko yaushe dan haka sai ya umarci Mufidan ta kawo masa ruwa a kofi, da sauri ta taje ta dauko masa, ya kar'ba ya shiga tofa ayatul'kursiyu da fala'ki da nasi 'kafa bakwai bakwai kana ya iske inda take, ruwan tofin ya guntsa a bakinsa ya shiga fesa mata a jiki, sai da yayi haka sai uku tukkuna sannan ta daina burgimar da take yi ta daina gwalantun surutan da take yi jikinta ya shika sosai tayi lakaf gumi duk ya jika mata jiki, Mufida na kuka taje ta rungumeta tana kiran sunanta................

MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*12* Cikin wani mawuyacin hali Halisa ta tashi duk jikinta yayi mata mugun tsami! ga wani irin ciwo da kanta ke mata, da kayar ta rarrafa ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana ri'ke kanta, a maimakon tayi addua kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in mugwayen kalmomi a kan mijin nata saboda kawai yace zai yi mata kishiya shine take addua Allah yasa ya samu karayar ariki komai nasa ya lalace!
Chapter 17 · 0% Book details