← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 143

Sashe 62

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da taci kukanta ta koshi sannan ta lalla'ba ta shiga wanka ta fito da wata iriyar masifaffiyar yunwa da kyar ta shirya jikinta ta zauna a zaune a kan dadduma tayi sallah saboda tsabar rashin tsoron Allah haka ta hada sallahr azuhur da la'asar a zaune ba tare da tayi addua ba ta cire hijabin ta fita palo
Larai tana zaune ita kadai tana kallon tv tana so hudu da rabi tayi ta shiga kicin...Tana ganin Halisa ta fito tace"Hajiya sannu da jiki kin fito kenan."
Da kyar ta amsa tana kokarin zama kan kujera tace"Ki kawo min abinci yunwa nakeji." Larai ta mike da sauri ta nufi kicin domin kawo mata abincin.

Larai na ajiye mata abincin tace."Ina Naja'atu take."?

Larai tace"Eh to tun dai da suka fita da maigidan bata dawo gidan ba." Halisa tayi shuru tana tsakurar abincin mamaki take sosai akan ya akayi yarinyar ta iya samun galaba a kanta har ta iya janye hankalin mijinta ya rufe kofa da ita a cikin kwananta a gaskiya al'amarin yayi masifar girgizata wai yau ita yarinyar k'ankanuwa tayi wa satar kwana humm!!

Da kyar take cusa abincin tana tunanin irin mugun abun da za tayi wa yarinyar ta huce bakin cikinta.
*Halisa in banda abinki meye abin damuwa bayan kinsan ko ya kulle kofa da yarinyar ba iya tsinana komai zaiyi ba to meye abin d'aga hankali kuma*
Naja'atu na can tare da aunty maryam tana ta fad'a mata karya da gaskiya aunty maryam kuwa ta hau kai ta zauna dan saboda ta riga tasan halin halisa babu irin abinda ba zata iya aikatawa ba shiyasa taji gabadaya ba tayiwa yarinyar sha'awar zaman aure a gidan domin Halisa duk macen da zata zauna da ita sai ta shirya.

Sai bayan magariba suka dawo gidan shida Abbah Magaji sukayi sallama kowa ya nufi gidanshi, yayi mamaki da baiga Naja'atu a gidan ba...Tabbas yarinyar naso ta d'ora masa ciwo mai tsanani duk da cewar yana da tabbacin tana gidan abokinsa hakan bai masa dadi ba saboda shi a rayuwarsa ya tsani ya dawo gida ya tarar da babu daya daga cikin iyalinsa....Halisa ta daure ta kula dashi gurin cin abinci ya tambaye jikinta a sanyaye tace da sauki Yace."Kin san abinda yake damunki kuwa." Kamar wata shashasha tace"Ban sani ba wallahi." Yace."Kina tare da ba'ka'ken aljanu wanda ni tunda nake tsayin shekarun da nayi dake ban ta'ba sanin kina dasu ba sai da kikaji labarin aurena da yarinyar nan sannan kika fara tayar dasu shin kodai ke kika janyowa kanki su dan saboda ni nasan lafiya lau na aureki baki da wata matsala."
Murya na rawa tace"Kawai sai na janyowa kaina aljanu a ina zan gansu na janyosu dan Allah ka daina wannan maganar kada ka 'bata min rai.

Shin kai baka tunanin iyayen matar taka zasu iya had'ani dasu ai wannan tsohon mai zama akan buzu kullum babu abinda ba zai iya ba, kullum yana nunawa duniya shi na Allah ne nan kuwa zuciyarsa tafi ta fir'auna."
Abbah Abbas 'bata rai yayi yace."Bana son rashin kunya da zargi Baba malam bazai cutar dake ba malami ne shi ba boka ba kuma yana d'aya daga cikin malaman da zan kawo domin suzo suyi miki ru'kiya."
Jin maganar ru'kiya yasa ta fashe da kuka tace"Ashe har an kai wannan matakin da zaka dauko malamai su rufu a kaina suyi min ru'kiya ni kuwa wace iriyar iska ce dani da za kayi min haka."
Cike da mamaki yake kallonta yace"Okey wannan yana nuna min cewar kinfi so a rabu dake kiyi abinda kike so ko kuma suyi abinda suke so a kaina da iyalina kina dauko wuka da makami domin cutar dani da wanda ya shafe ni to idan kina sane kikeyi zanyi maganinki idan kuma su aljanun ne suke saki ki fad'a musu nafi karfinsu." Halisa ta dinga kuka tana fad'in "A ina zan gansu na fad'a musu sa'konka dan Allah ka bar maganar rukiyar nan." Yace."Baki da gaskiya tunda kike maganar a bar maganar rukiya hakan na nufin abubuwa da dama ana so a rabaki da wahala kina cewa a bari to bazan bari ba sai anyi idan kece kika siye su da kudinki zasu fad'a kowa yaji
Halisa gabanta ya dinga dukan uku uku shikkenan asirinta ya kusa tonowa Allah yasa aljanunta su rufa mata asiri kada su tona mata asiri a idon duniya, adduar da takeyi kenan a cikin zuciyarta tana kuka.

Naja'atu kuwa tana can suna fafatawa da Abbah Magaji dan cewa tayi ba zata dawo gidan ba, Abbah magaji tun yana mata masifa har ya dawo rarrashi dan sabida yasan halinta da taurin kan tsiya da kyar ta hakura zata koma gidan, Abbah magaji yasa Aunty maryam ta rakota.

Halisa da kyar ta iya amsawa aunty maryam gaisuwarta dama sun saba 'yar d'auke d'auken kai a tsakaninsu, aunty maryam kasa had'a ido tayi da Abbah Abbas duk kuwa da cewar suna dan wasa a tsakaninsu, abinda yasa ta kasa hada ido dashi kuwa maigidanta ya fad'a mata cewar lokacin da ta kira wayarsa tana fada masa a binda ke faruwa Abbah Abbas din na kusa dashi kuma yaji komai, wannan dalilin yasa ta kasa zama a gidan tayi musu sallama da ta tafi...Naja'atu kuwa dama ko zama ba tayi a palon ba ta shige dakinsu mussadiq tayi kwanciyarta.
********
A tsakanin kwanaki biyu zamantakewar gidan duk ta dawo wani iri Halisa tayi sanyi sosai tunda taji maganar rukiya ta shiga nutsuwarta ta daina rawar kai sai ta yini a dakinta ma bata fito ba Naja'atu da Baba Larai ne kawai suke sha'aninsu.....Yau ya kasance girkin Naja'atu ne, tana ta murna dare yayi su ke'be da maigidan dan gaskiya kwana biyu tayi missing din soyayyarsa ta shirya cikin 'kananun kaya wanda sukayi mata kyau sosai ta zauna a palo cikin yaran suna ta wasa da dariya, taji dadi sosai da taga halisa ta daina power a gidan.....Koda ya shigo gidan ya gansu a palon sai yaji farin ciki ya lullubeshi, amma rashin ganin Halisa a cikinsu ya sosa masa rai! salo salo din da Halisa takeyi bayayi masa dadi ko kadan, dan haka bayan ya amsa gaisuwarsu kai tsaye dakin Halisa ya nufa....Naja'atu tabishi da kallo tana jan tsaki. ta tsani taga yana mu'amular arziki da Halisa( Ikon Allah wai Naja'atu meke damunki ne kullum kina cewa bakya son mutum amma kina kishi a kansa da alama kema kina bukatar ayi miki rukiyar)......Samunta yayi a kwance tayi shuru, ya tsaya a kanta da fad'in "Halisa wai me akayi miki ne kika takura kanki kwana biyu bana jin dadin abinda kikeyi a gidan nan dan Allah ki saki jikinki kamar da ki cigaba da mu'amular ki da kowa.

Kuka tasa tace" Ba dole na ke'be kaina ba tunda ni mai laifi ce a gidan nan yarinyar 'karama na zagina na bangazata nayi min dariya ai dole na takura idan kuma na dauki mataki a kanta a dauki laifi a dora min ai ni kam walwalata da farin cikina ya kare a gidan nan."
Yace."Kiyi hakuri insha Allahu ta kusa ta bar miki gidanki ni nagaji da wannan tashin hankalin naku me yasa lokacin Halimatu kuke zauna lafiya da juna." ?

Tace"Halimatu daban take a cikin mata Naja'atu kuwa annoba ce a cikin mutane wallahi watarana yarinyar nan sai ta wargaza maka gidanka idan ba kayi da gaske ba.

Yace."Magana dai ta wuce insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe ki taso ki bani abinci." Yafada yana me juyawa da niyar fita..Halisa dama irin wannan damar take nema tunda tasan ba girkinta bane to tunda ya nema da kansa bari taje kodan ta cuzgunawa yarinyar
Naja'atu na ganin sun fito daga daki a tare tayi saurin dauke kanta zuciyarta ta sosu amma dai ta share bata nuna komai ba gabadayansu suka zauna gurin cin abincin.....Tana kallon abubuwan da Halisan keyi masa yayi shuru baice komai ba ga yara a zaune sai haushi ya isheta kawai ta mike tana kallon yaran tace"Kowa ya dauko plate dinsa muje palo muci a can." Da sauri suka mike kowa ya dauki nasa, dama can haka suke daga tace musu ga yanda za suyi basa yi mata musu...Halisan dashi kansa suka bisu da kallo domin kuwa sun rasa abin cewa....

To sai bayan goma na dare suka kashe tv kamar dai koda yaushe suka nufi daki domin shirin kwanciya...Naja'atu wanka akaje a kayi tayi bursh ta shirya cikin kayan bacci harda sa turare ta zauna tana jiran shigowar maigidan tasan dole idan ya shigo sai ya nemi data bishi dakinsa aikam zata bishi dan yini tayi cikin sha'awa da tashin tsigar jiki idan ta tuno soyayyarsa har wani lumshe idonta take......Har karfe goma sha daya da rabi idonta biyu tana jiran shigowarsa shuru bai shigo ba, ranta ya baci sosai, a sanyaye ta shiga gyara shimfidarta dake kasan kafet taji ya turo kofar ya shigo da sallama ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke ta amsa masa ya karaso cikin dakin sosai kai tsaye taga ya fara zagaya gadon yaransa yana musu addua kamar yanda ya saba! shuru tayi tana binsa da kallo har ya gama musu ya juya zai fita ba tare da ya tanka mata ba
Takaici kamar ya kasheta kamar wata shashasha tabi bayansa da kallo tana ji kamar taje ta rungumeshi...Kwanciya tayi tana kuka tare da takure jikinta tana jin danshi danshi a pant dinta tsabar sha'awar data yini dashi yasa ta zubar da ruwa sai kace kankana.

Shi kuwa Abbah Abbas bacin ran da yake cike ne yasa yaji gabadaya ma baya sha'awar komai baban burinsa ya kwanta ya huta sannan kuma yayi tunanin yanda zai kawo zaman lafiya a gidansa dan ya lura ba k'aramin gagarimin aiki bane a cikin zaman Halisa da Naja'atu a gidansa.

Washe gari gidan haka kowa ya tashi da rashin walwala dalili ruhikan gidan (Abbah Abbas da Naja'atu) basa cikin walwala sai ya kasance suma yaran basu da walwala Halisa kuwa a cikin yaran babu wanda yake ta tata.
Chapter 62 · 0% Book details