← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 143

Sashe 7

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naja'atu ta mike a guje taje ta d'ane jikinsa tana fad'in "Oyoyo Abbana."!

Dariya yasa ya mi'ka mata kumatunsa kamar yanda suka saba! aikuwa ta manna masa kiss a gurin! shima yayi mata sannan ya sauketa kasa, yana d'an ya mutsa fuska ya kalli Halimatu dake ta faman yi musu dariya! hannunsa ya mi'ka mata da fad'in " Ranki ya dad'e zo muje daki ina da magana." Halimatu ta tsira masa ido tana kallonsa da mamaki a tare da ita!

Gira ya daga mata yana yi mata wani irin kallo.

Girgiza kanta tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa, lallai wato sai yau take da amfani a gurinsa kenan! duk sanda yake cikin halin sha'awa tana ganewa.

Ji tayi ya kamo hannunta ya mikar da ita tsaye, gudun kada yayi abun kunya a gaban Yarinya yasa tayi saurin cire hannunta tace"Kaje ganin nan zan shigo." Babu kunya ya nufi bedroom dinta yana wata irin tafiya.

Zama tayi kan kujera tana kallon Naja'atu na rubutunta sai da ta tabbatar abinda take ya dauke mata hankali sannan ta mike a nutse ta bishi dakin.

Wannan had'uwar tasu ta firgita Halimatu gabad'aya mijin nata ya sanja mata hallitarsa ma kamar ta sauya, ya zage karfi a kanta yana bugunta babu tausayi da jin 'kai irin wanda yake mata, sosai yake sarrafata salo-salo duk ya fice daga hayyacinsa itama sai wuya yake bata, kukan wahala take masa tana bashi hakuri ya saurara mata haka, sam ba haka ya saba yin mu'amula da ita ba, da kyar ya saurara mata ya kwanta gefanta yana maida numfashi........To tun daga wannan had'uwar Ubangiji ya zartar da ikonsa ciki ya shiga ya zauna daram a mahaifar Halimatu, cikin kuma da bai bayyana kansa ba sai da yayi wata hudu tukkuna sannan Allah ya bayyana shi, saboda ita kanta Halimatu bata san da ciki a jikinta ba kasancewar ba ko wane wata take al'ada ba shiyasa duk ta rikirkice, ta dinga kokwanto a kan ciki.......Kai tsaye asibiti ya dauketa sukaje, likita ta dubata sosai dan har scanning akayi mata ciki wata hudu kuma yana cikin koshin lafiya.

Abbas ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki, tun a mota ya kira wayar mahaifiyarsa ya sheda mata abinda ke faruwa, Hajiya Abu tayi murna da farin ciki sosai ta kuma yi addua kan Allah ya sauke ta lafiya........Halisa kwanan kuka tayi da taji labari wai Halimatu nada ciki, ya akayi haka ta faru? wai dama mijin nata ashe yana lallabawa gurin Haliman yana biya bukatarsa bata sani ba, lallai zai shigo ya sameta.......Shi kuwa da farin ciki a tare dashi yake sake jaddada mata k'aruwar da ya samu! ta hasala! sosai ta dinga zazzaga masa rashin kunya kamar zata zage shi! aikuwa ta fuskanci 'bacin rai! dan lafiyayyun marika tasha wanda hakan bai ta'ba faruwa ba tsayin shekarun auransu, Yayi mata gargadi sosai kan tsaurin idon da take masa kana kuma ya dauke mata wuta gabadaya ya daina kulata, ya tare sashen Halimatu!!

Halisa ta zama tamkar mahaukaciya gashi *'Yar Sa'adu* bata gari ta tafi Nijar dama 'Yar can ce kullum ita kenan a tafe gurin zuwa gidan Yaya Ramlatu, suna tattauna yanda zasu 'bulluwa al'amarin, Ramlatu tsoron zuwa gidan takeyi saboda tasan halin 'Kanin nata zai iya kunyatata shiyasa ta zauna a gida, Halisan na zuwa inda take................Sau uku yana dawowa gida ya tarar bata nan a'lamarin da ya fusata shi sosai, ya tsaya harabar gidan nashi yana kai kawo kana ganinsa kasan ransa a 'bace yake, Tana shigowa ya buga mata tsawa da fad'in "Ta koma inda ta fito! gabanta ne ya fad'i baki na rawa tace''Wallahi naj.......Hannu ya daga mata yace." Bana bukatar naji komai daga bakinki sau uku ina dawowa gida bakya nan ina kike zuwa ba tare da na sani ba? saboda haka ki fuce min daga gida sai nazo gidanku inaso kafin nazo ki fada musu inda kike zuwa."
Halisa ganin yayi fushin mai tsanani yasa ta juya jiki a sanyaye ta futa daga gidan, kai tsaye gidansu ta nufa tana kuka.

A takaice dai sai da Halisa tayi sati biyu a gidansu sannan Yaje yayi bikon ta iyayenta ran su ya 'baci sosai jin irin abinda take aikatawa na fita yawo ba tare da izinin mijinta ba mahaifinta yace da Abbas duk sanda ta sake futa bata fada masa ba to ya sanar masa sai ranta ya 'baci sosai!

Halisa ta tsorata sosai d'a zaman da tayi a gidansu har jikinta ya soma sanyi tsayin sati biyu da tayi a gidan nasu ji take tamkar shekara biyu tayi, ganin ya shere ta da ita al'amarinta yasa jikinta yayi sanyi tana addua kada Allah yasa yace zai saketa.....To tunda ta samu yanzu ya mayar da ita sai ta dauki aniyar gyara kuskuranta a gurinsa amma dai duk da haka ba zata fasa yiwa Halima zagon 'kasa ba.

Koda ta dawo gidan d kafin ya sakar mata fuska sai da ta dade tukkuna sannan ya warware gabadaya, tun daga sannan ta kiyaye abinda zai dugunzuma masa zuciya wanda zai haifar da sa'bani tsakaninsu har ta kaishi ga korata gidansu.

Cikin Halimatu nada wata bakwai Allah ya bawa Halisa nata, Halisa aka dinga murna da zumudi ana iyayi! shi kuwa maigidan ya dinga biye mata da duk abinda take so burinsa kawai yaga matayen nasa sun haihu lafiya shima ya shiga sahun mutanan da ake kira da Abbah, duk da sunan da Naja'atu ke kiransa dashi kenan Abbana, ko Abban Naja, a duk lokacin da zata kirashi da sunan yakan ji wani iri dan saboda yasan ba shine ya haifeta shi dai yafi bukatar 'yayansa na cikinsa su kirashi da wannan suna.
*****
Lafiya lau Halimatu ta haihu inda ta haifi 'yar ta mace ta d'an d'ebo kammanin mahaifinta gurin hasken fata gami da siririn hanci, Abbas mai kyau ne sosai irin namijin da mata keso yana da haske da cikin zati dogo ne amma ba sosai ba, yana da manya ido da dogon hanci wanda ya kyata masa fuskarsa, amma kuma bashi da fara'a da saurin sabo!

Mutum daya ya amince dashi cikin abokansa shine Magaji Yayan matarsa kenan Abba magaji yasan sirrinsa kamar yanda shima yasan nasa...........Halisa ganin Halima ta haifi mace sai ta dinga addua Allah yasa ita ta haifi namiji dan tasan farin cikin da mijin nasu zaiyi sai yafi wanda yake yi a yanzu, hankalinta na masifar tashi a dik sanda taga ya shiga gurin Haliman ya jima bai fito takan shiga tashin hankali da damuwa saboda tasan yana can yana shiriritar da ya saba da shegiyar yarinyar nan Naja'atu da Babynsa wacce ya sanyawa suna Fatima amma sai suke kiranta da *Saddiqa* dalili kenan da ya sanya take Allah Allah itama ta haihu itama taga yana nuna kulawarsa a kan d'anta.

Haihuwar *Saddiqa* ta janyo masa bud'i da alkairai da yawa, harkokin kasuwancinsa suka bude sosai yake harkar gwangila na gina gidaje da ma'aikatu da sauransu........Wani 'katon gida yake ginawa a cikin unguwar *Danbare* sabuwar unguwa ce da masu kudi suka siyeta suke ta gasar gidana gida a gurin, gaskiya gidan da yake idan aka gama aikinsa babu shakka zai zama abun kallo a gurin jama'a.

Halisa ta haihu lafiya lau ta haifi namiji kamar yanda Scanning ya nuna mata, sai dai kuma cikin ikon Allah kwanan yaron d'aya a duniya ya koma.....Ihu! ta dinga zabgawa tana kuka dan rashin tawakkali cewa take wallahi Halima ce tayi mata asiri d'anta ya mutu saboda tana bakin cikin ita bata haifi d'a namiji ba.

Abba Abbas tun yana rarrashinta har ta si'ke shi haushinta ya rufeshi, ya shiga nuna mata illar abinda takeyi, Allah ne ya bata kuma ya kar'bi abinsa dan me zata d'orawa wani! sai da yayi mata kaca-kaca! sannan ta daina ikirarin cewar Halima ce tayi mata asiri.

Bayan shekaru uku Halimatu ta sake haihuwa inda ta haifi 'Da namiji!

Wanda wannan haihuwar ta janyo tashin hankali sosai a gidan dan iskokai Halisa ta dinga tayarwa na 'karya dana gaskiya tana yun'kurin kashe maijego da jaririnta......Babu arziki ya tarkata ta ya kaita gidansu dan al'amarin yafi karfinsa haka kawai yana ji yana gani ta illata masa d'ansa.

Ashe iskanci ne Halisa na ganinta a gidansu, sai ta dawo hayyacinta mussaman da mahaifinta ya samo malamai, masu ru'kiya suka dinga jibgarta, babu arziki ta dai-dai ta nutsuwarta ta dinga kiransa a waya yazo ya dauketa taji sauki!

Shi kuwa dama tuntuni ya yanke shawara kan cewar zai raba musu gurin zama, dan gudun aikata mummanan aiki idan baya nan shima ya fahimci duk wani abu da Halinsan keyi sharri ne da ba'kin kishi da ganin kyashi!

Gidansa dake *'Dan bare* suka tare shida Halimatu da 'yayansa kana yasa aka gyarawa Halisan wanda suka bari ta zauna a ciki yana ganin hakan shine yafi alkairi a tare dasu baki daya...

Wannan al'amari ya sanya zuciyar Halisa kusan bugawa, gidan da take kulafucin zama a cikinsa shine zai ce ba zai je da itaba, kuka taci ta koshi tana tunanin mafita babu shakka ta ko'ina Halima tayi mata zarra! ta haihu har sau biyu kuma ta tare a sabon gida. tabbas dole ne ta nemawa kanta mafita yanzu ne ta sake gazgata maganar Yaya Ramlatu inda take cewa mugun sihiri iyayen Halimatu sukayi akan Mijin nata, itama idan hakane to tabbas zama bai kama ta ba.

To da yake yanzu bata da matsalar kudi yasa ta d'auki d'amarar shiga malamai domin bukatarta ta biya, duk ranar da ya kasance ba a gidanta yake ba to id
an ta fita tun safe sai yamma zata dawo gida tare suke yawace yawacen malamansu da Yayar mijin nata.....Yaya Ramlatu bata da matsala saboda mijinta matafiyi ne shiyasa takeyin abinda take so a gidan, haka zata fuce ta watsar da 'yayanta a tsakar gida, kishiyarta Sakina mutuniyar kirki ita ke mata dawainiya da 'yayanta tayi da nata, tabbas albasa ba tayi halin ruwa ba, dan da Ramlatu ta gado halin iyayen nata to ba zata aikata abinda take ba.
Chapter 7 · 0% Book details