← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 143

Sashe 66

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naja'atu tace"Wallahi Munira banga laifinki ba....Nima bani da ra'ayin haihuwa da yawa a duniya sabida gudun wulakancin namiji....wannan cikin da ace ina son ubansa zan iya bari na haife shi to gabadaya na tsani wanda yayi sanadiyarsa shiyasa kawai na yanke shawarar zuwa garinku inaso ki bani cikakken address insha Allahu gobe ko jibi zaki ganni a gidanku idan yaso idan nazo sai muyi sha'awar yanda za'ayi kinga cikin ma baiyi wani kwari ba ba zamu sha wahala ba...Munira tace"Eh gaskiya kinyi dubara kada ki damu zan baki cikakken addrees din gidanmu idan kinzo zamuje Chamis akwai tablet din da zasu baki ki sha d'aya kisa d'aya a 'kasan harshenki sannan kisa d'aya a gabanki! insha Allah cikin sai yabi rariya.''
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Nagode sosai k'awata! ina jiran address din ta whasap." Munira tace"To ki kunna data zan turo miki.'' Da sauri tace to tare da kashe wayar......Abbah Abbas kuwa al'amarin ne ya daure masa kai sosai dan ya sake kiran wayar ya kai sau hudu sai suce masa line is busy mamaki yake to wace irin waya yarinyar take mai tsayi haka kuma da waye take wayar.? da yaga bashi da mai bashi amsa sai ya dauki wayar ya sake neman line! sanyi yaji a zuciyarsa jin wayar tana shiga sai dai har ta katse bata dauka ba!

Takaici kamar ya kasheshi shin wai me yarinyar nan take nufi! mikewa yayi ya fita daga dakin Harabar gidan ya fita ya zauna kan wasu kujeru kasa hakuri yayi ya sake kiran wayar a karo mara adadi!

Naja'atu ta bawa banza ajiyarsa dan kin dauka tayi ta kyale wayar nata ringing! wannan al'amarin yayi masifar dugunzuma masa zuciya sai yaji gabadaya zaman garin ya isheshi hankalinsa yayi gida wannan iskancin da yarinyar takeyi ba na lafiya bane! ya kira waya sama da sau goma saboda tsabar raini da wulakanci ta'ki dauka...Halisa ita kanta sai da ta fahimci baya cikin hayyacinsa to da yake itama ba'a cikin hayyacinta take ba sai aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu.

Washe gari da sassafe Aunty maryam tazo ta dubata, Naja'at gaisuwar arziki ba tayi mata ba, aunty maryam cikin zuciyarta take fad'in "Albasa ba tayi halin ruwa ba..Aunt maryam na tafiya da kamar mintina ashirin saiga Alhaji Sama'ila da Hajiya Rabi Abbah Alhassan ya kawo su su dubata....Daurewa tayi ta fito ta zauna tana sinne kanta kamar mutuniyar arziki suka gaisa da juna! suna tambayar yanayin jinta tace musu da sauki!

Ta lura kowa da kowa na farin ciki da samuwar cikin jikinta ita kadai ce take cikin bakin ciki saboda son zuciya kowa ya kasa gane halin da take ciki..........Bayan tafiyarsu Alhaji Aunty Rakiya ce tazo matar Abbah Alhassan kenan itama wai tazo dubata!

Naja'atu cikin zuciyarta tace duk zaku gama gulmarku ku daina........

Tashi tayi ta bar musu palon aunty Rakiya ta zauna tare da Larai suna hira gefe guda kuma tana mamakin wulakacin da yarinyar tayi mata.

Abbah Abbas koda dare yayi bai sake yunkurin kiranta a waya ba, sai kawai ya kira wayar abokinsa ya tambaye shi yanayin jikin nata, Abbah magaji yace masa jiki yayi sauki sosai dan maryam ma bata jima da fitowa daga gidan ba.

Hankalinsa ne ya kwanta sukayi sallama da juna yana d'an jin sassauci a cikin ransa, amma idan ya tuno wulakancin da yarinyar tayi masa yana ji tamkar yayi tsuntsuwa yaje yaci mata mutunci ko ya huce.

Washe garin ranar Naja'atu da niyar guduwa ta tashi sai kuma su Baba malam suka dira a gidan!

Ganinsu yasa duk jikinta ya mutu ta dinga share hawaye a fakaice tana nadamar abinda zata a kaita musu na bacin rai....Nasihohin da malam yayi mata sunyi masifar kassara mata jiki taji kamar ta hakura kawai ta cigaba da zama a gidan tunda haka Allah ya tsara mata rayuwarta, sai dai suna tafiya ko gida basu je shed'aniyar 'kawarta Munira ta kirata a waya tana sake zugata kan abinda suka kudurta.

Washe gari ta kuma tashi da yunkurin guduwa garin Jos garinsu Munira sai kuma Allah ya saukar mata da ciwon ciki. ta yini a kwance tana murkususu! duk da tasha maganin ciwon bai lafa mata ba sai dare lokaci guda ta rame saboda tsananin axabar da taci
A daran ta sake kwanciya da kudurin garin Allah na waye wa zakara zai bata sa'a! aikuwa hakane ya kasance yara na tafiya makaranta lokacin Larai na kicin tana aike aike ita kuma ta fito, cikin rashin kwarin jiki da karfin hali taja k'aramar akwatin kayanta ta fita daga cikin gidan...
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a groups to na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake.

Vip Group #600
Normal gruop#300
account.. 0542382124..Binta Umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Sai da ta ganta a cikin tasha tukkuna hankalinta ya kwanta ta samu wani ke'bantaccen guri ta zauna tana mayar da numfashin wahala, gabadaya jikinta a rikice yake sam ba tajin dadinsa daurewa kawai takeyi, a hankali ta zuge zif din jakarta ta dauko wayarta ta bude numbar Salim ta nemo ta shiga kiransa.

Salim na kasuwa a lokacin cike da zumudi ya daga wayar tare da ambatar sunanta.....Kuka tasa mai shashsheka tace"Salim ina cikin tashin hankali mai girma dan Allah kayi hakuri da abinda zakaji daga bakina wallahi duk abinda ya faru tsautsayi da kaddara ne amma nayi al'kawarin sai na salwantar da cikin da yake kokarin ruguza mana farin cikinmu." Cike da so yasan abinda ke faruwa yace."Naja'atu wai meke faruwa ne? naji kina wata magana wacce na kasa fahintarta." Hawaye tagoge tace"Salim ciki ne dani."?

Yaji gabansa ya fad'i! sai yayi d'if takaicin kamar ya kashe shi...Ta cigaba da cewa"Dan Allah kayi hakuri salim kada kace na yaudareka ba laifina bane wallahi karfi ya gwada min har hakan ta faru gashi yayi min ciki ba tare dana fargaba wannan dalilin yasa na yanke shawarar zubar dashi dan wallahi ni bazan haihu dashi ba tunda bana sonsa." Salim yayi murmushin mugunta da fadin"Yanzu kina ina."? kai tsaye tace"Gani a cikin tasha zan bar garin gabad'aya dan nagaji da zama cikin wannan masifa.

Yace."Kiyi hakuri kada ki tafi ki dawo gida sai mu san yanda za'ayi." Tace"Salim nifa wallahi sai na zubar da cikin nan hankalina zai kwanta." Yace."To yanzu wane gari kika nufa haba Naja'atu kiyi hakuri ki kar'bi qaddara mana." a fusace tace"au abinda zakace kenan Salim? ashe dama ni kadai nake wahalar da kaina a kanka ko." Yace."Ai dama na fada miki tuntuni kinfi karfina ni yanzu ke auntyna ce dan haka hakuri shi yafi alkairi a tsakaninmu." Cike da bacin rai tace"Shikkenan salim nagode da butulci dama ai idan ba kayi min haka ba to baka cika namiji ba idan baka aureni ba akwai maza a duniya wanda suka fika komai da komai kuma ba zan fasa abinda na kudurta ba." Tana gama maganarta ta kashe wayarta....Salim yayi sauri yayi serving din rocouding din da yasa ya sake kiran wayartata, kin dauka tayi ta hada kanta da gwiwa sai kuka take...Salim ganin taki daga wayar sai yayi murmushi a fili yace."Alhmdullhi bukatata ta biya. numbar Kawun nasa ya shiga kira...Abbah Abbs ya daga wayar kafin ma yayi magana yaji muryar Salim din cikin tashin hankali yana fad'in "Kawu gida babu lafiya Naja'atu ta gudu ka bude whasap na turo maka muryarta yanzu muka gama waya da ita tana sheda min hukuncin data yankewa kanta.

Abba Abbas kasa gane maganar yayi yace." Kai ka nutsu kayi min bayani ina zata nufa bayan yanzu mukayi waya da abokina magaji yace tana gida lafiya lau...Salim yace."Wallahi kawu babu wasa a cikin maganata idan kana so ka gazgata ka bude audion dana turo maka ta whasap..Abbah Abbs hannunsa na rawa ya kashe wayar ya shiga whasap kawai sai yaga yayi exipire tsaki yaja yayi saurin shiga playstore domin dauko wani.

Can gida kuwa Baba Larai ta gama aikace-akaicen ta ta shiga dakin da naja'atun take domin ta dubata, taga bata dakin sai tayi tunanin kota tana toilet sai ta zauna gefan gadon Mufida tana jiran fitowarta.....Zaman minti ashirin tayi a dakin ba taji motsinta ba, sai ta mike da sauri ta isa bakin bandakin tana kiran sunanta. shurun da taji ne yasa da sauri ta tura kofar bandakin, tana rarraba idonta a ciki babu naja'atu babu dalilinta...Cikin faduwar gaba ta fito palon tana dubata hade da kiran sunanta. shuru taji babu alamunta a gidan, sai ta bude kofar palon ta fita da sauri ta nufi bakin gate.

Malam Ayuba maigadi na zaune shida Yunusa suna hira Larai ta karasa tace"Malam Ayuba kana zaune anan ko kaga fitowar Naja'atu." Malam Ayuba yace."Eh kwarai kuwa kimanin awa d'aya data wuce ta fito da akwati a hannunta nine ma na bude mata karamar kofa ta fita.

Baba Larai jin maganar akwati sai taji wani irin fargaba ya rufe ta, da sauri ta juya ta koma cikin gidan ta dauko mayafinta kai tsaye gidan aunty maryam ta nufa tana adduar Allah yasa kada yarinyar nan tace zataje wani gurin
Aunty maryam ta shiga rud'ani mutuka jin maganar da Larai ke tafe da ita, Gaskiya naja'atu bata da hankali kuma taurin kanta ne zai kaita ya baro.

Waya ta dauka ta kira mijinta a sanyaye ta fada masa halin da ake ciki...Abbah magaji bai nuna alhini ba dan shi a tunaninsa ina naja'atu ta sani da xata je?
Chapter 66 · 0% Book details