Sashe 113
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halisa jiki a sanyaye ta dawo gida tana ta mamakin yanda al'amura suke kasancewa, mijinta ya siyawa mejego raguna biyu manya manya sannan ya siyi wanda akayi miyar suna duk a bakin Ramlatu take jin maganar, hakikanin gaskiya jikinta yayi sanyi da irin qaunar da yakewa yarinyar tana ganin dawo da ita gidansa shine yafi masa alkairi sai kawai ta yanke shawarar watsar da makamanta za ta kuma tunkareshi da maganar Naja'atun taji mai zai sake cewa.
Ranar dama itace take da girki ta fito falo ta sameshi yana abunda ya saba, da kyar ya saurareta dan har yanzu haushin abinda sukai masa yake ji......Yace."Ai kin bani mamaki Halisa ina tunanin kece ta farkon wacce zata fadawa wani halina, meye a cikin abubuwan da nakewa Najaatu da duk zaku tayar da hankalin ku akai har kuna had'e min kai saboda baku da hankali! to inaso na tuna miki abunda kika manta, Naja'atu bata da wanda ya fini tunda tun tana shekara hudu take a hannuna nine na rainata tana riqe ta tamkar 'yar dana haifa a cikina ni ta sani duk wani nauyi nata yana kaina, koda iyayenta nada halin daukar d:awainiyarta to bazan bari ba saboda tun farko sun dauke ta sun bani ita, wannan dalilin ya sanya nake kokarin ganin na sauke nauyin amanarta dake kaina, duk ki ture ta wasu abubuwan da suka faru a tsakanina da ita, ni ba mutum ne me riqe abu a cikin ransa ba, da ina da wannan d'abiar to na tabbata ba zan kalli inda take ba, ballantana na 'batar da kwabona a kanta, sannan idan banda abunku ai Najaatu abar ku tausaya mata ne duba da halin da take ciki menene abin ganin k'yashi da kishi dan na taimaka mata."?
Halisa tace"Duk naji bayanan ka amma dai kasan kishi halak ne ko.?
Shuru yay yana kallonta ta cigaba da cewa"Nifa wallahi idan zaka dafa al'kur'ani ba zan yarda cewar baka son yarinyar nan ba." 'Bata fuska yay yana dan harararta Tace"Ai gaskiya ce abunda kakeyi yay yawa haba kowa ya d'ora zarginsa akanka nasan ita kanta yarinyar tana ji a jikinta ko zaka mayar da ita gidanka ne, dan haka nima wallahi nafi sha'awar ka dawo da ita dani da kai da ita Zainab din dukkaninmu sai hankalinmu yafi kwanciya
Ya jima kafin yay magana yace"Na fad'a muku ni ba zan dawo da Najaatu gidana ba amma kun'ki yarda da maganata, magana ce mukeyi a kan cikinta da haihuwarta to tinda Allah yasa ta haihu lafiya ai abunda ake bukata kenan daga haka kuma me zai sake shiga tsakanina da ita idan ba gaisuwa ba, amma tunda na lura zama ku biyu ne bakwaso zan fara neman aure shikkenan sai hankalinku ya kwanta.
Murmushin takaici tayi tace"Ba sabon aure ya kamata kayi ba Najaatu ya kamata ka dawo da ita dan wallahi ko sabon auran kayi ba zaka samun nutsuwar da kake bukata."
Yace."Haka dai kike gani ni Najaatu bata gabana wallahi kune dai kawai kuke zargina akanta zaku wahalar da kanku ne a banza." Yana gama maganarsa ya cigaba da duba laptop din gabansa.....Halisa takaici yasa ta bar gurin, kwanciya taje tayi tana tunanin maganganunsa itafa ba yarinya bace ballantana ya raina mata hankali.
Tunda akayi suna ya daina zuwa gidan da safe, ya dawo zuwa da yamma kamar yanda ya saba kuma babu ruwansa da shiga sabgar Najaatu gaisuwa ce kawai take had'ashi da ita yay abunda ya kawoshi ya tafi, ba Najaatun ba su kansu su hajia sai da suka fuskanci sauyawarsa sai duk jikinsu yayi sanyi kada fa yay musu bazata ya nuna musu abunda suke zargi ba haka bane a gurinsa.
*BASH!*
Abunda sukeyi dashi da abokansa ya wuce tunanin masu tunani, yanzu harkar siyar da hodar ibilis suke da turawan america, Bash ya had'a kansa da manya manya yahudawa suna ta aikin sa'bo!
Yayi masifar kudi irin wanda yake b'ukata gabad'aya idan kun ka ganshi ba zaku ganeshi ba saboda dukkanin kammaninsa sun sanja ya samu duniya sosai duniya tasan da zamansa kuma abokanansa sunaji dashi saboda yana brain sosai yana kawo musu cigaba a cikin harkokin da sukeyi a 'boye............... to hausawa sukace rana dubu ta barawo rana guda ta me kaya Ranar Asabar Allah yay nufi tona musu asiri sun shirya shida abokanasa suka nufi Cameroon domin shigar da musu da kayan sana'ar tasu, lafiya lau suka sauka a filin jirgin garin suka soma saukowa kowa na goye da wata katuwar jaka a bayansa, wani ma'aikaci ya dakatar dasu, yace su ajiye jakkunan dake bayansu, cikin turanci Bash yace idan zaiyi bunkice a kansu yayi su ba zasu ajiye jakarsu ba, mutumin sabon ma'aikaci ne mai aiki domin kishin qasarsa, kawai yace azo a tafi dasu tunda sun sa gaddama sunqi suyi abunda ake bukata suyi......Jin haka da sukayi kawai sai Bash yayi dubarar dauko k'aramar bundiga dake cikin jakar bayansa ya harbi ma'aikacin nan a gwiwa kafin kice kwabo guri ya hautsine! ganin haka yasa da saurin gaske shima ya saita kafafun Bash din ya harbi daya Bash ya zube a gurin yana ihu hade da riqe kafarsa data jiqe da jini,
abokansa suka nemi hanyar tserewa Jami'an tsaron da suka iso gurin suka damqe su.........sai da sojoji sukayi bunkice sosai a gurin kafin su bari kowa ya fita daga airport din, tashin hankali su Bash suka raina kansu lokacin da jamian tsaro suka ga abubuwan dake cikin jakkunansu, tun a airport din suka fara jibgarsu kafin su sasu a mota su tafi dasu.......tsayin sati guda suna binkice a kansu kafin su san kasar da kowanne daga cikin su ya fito, jamian tsaro na kasar Cameroon sun samu cikakken bayani akansu Bash cewar mugwayen 'Yan taaddah! ne wanda suka addabi mutane da gomnati dama kullum cikin bukince ake a kansu da abubuwan da suke aikatawa tunda Allah yasa yanzu suna hannu sai a yanke musu hukuncin daya dace.........Koto aka shiga dasu, alqali yaji ya kuma tabbatar da dukkanin abunda ake zarginsu dashi tsabar wahala yasa dukkaninsu basu karyata ba sabida sun riga sun saddaqar da cewa karshensu ne yazo.....A take mai girma mai sharia ya yanke musu hukuncin kisa domin barinsu a doron duniya had'ari ne hukuncin da aka yankewa su Bash babu wanda bai sa farin ciki ba lokacin ne 'yan jarida suka samu aikin yi......suka dinga daukar hotonan su da muryoyinsu Allah Sarki Bash sunkuyar da kansa kawai yake yana hawayen nadama, dan da wani dan Jarida yazo yana masa tambayoyi kasa magana yay ya dago kansa kawai hawaye na zuba a kumatunsa magana biyu kacal ya iya fad'a...."Iyayane sune silar lalacewata babu abunda zance musu sai dai nace zamu hadu a gaban Allah.
Magana ta karshe da zanyi a kan wata yarinya ne dana yaudara sunanta Najaatu Ina fatan maganar nan da na keyi tana ji kuma tana kallonta, Najaatu ina rokon ki daki yafe min abunda nayi miki ba ke kadai bama da duk wanda na zalinta ina rokonsa ya yafe min ni tawa takare a duniya." Sai kawai yayi qasa da kansa hawaye na cigaba da zubowa daga idansa
Lokacin da labarin abunda ya faru ya isa kunnan iyayen Bash sun shiga tsananin tashin hankali da nadamar abunda suka aikata, dan jin bayanin da Bash yayi yasa jamaar gari sun sake gazgata maganar dama kowa yana tunanin sune suka dorashi a kan hanyar banza gashi yanzu sunzo suna nadama, 'Yan jarida kuwa ai kewaye Alhaji Aminu sukayi wai lallai sai yayi musu qarin bayani dangane da jawabin da Bash din yayi kafin mutuwarsa.
Najaatu kuwa al'amarin yayi masifar d'aga mata hankali tayi kuka sosai tayi nadamar rayuwa hajia kasa gane kanta tayi a gidan, sai da ta dinga yi mata nasiha gami da kawo mata misalai sannan ta daina kukan da takeyi ammafa kullum da daddare sai ta rungume 'Danta taci kukanta ta koshi!! sannan take jin sassauci bata ta'ba tunanin zata auri Mutum mai miyagun halaye ba sai gashi ta auri bash wanda ya tara munanan halaye harda albarka haihuwa a tsakaninsu hakika ta tabbata wannan al'amarin da ya faru da rayuwarta qaddarace dan da tasan abinda zai faru kenan da bata bujirewa auran da iyayenta sukayi mata ba, A duk sanda zata kalli fuskar d'anta ji take zuciyarta na karaya ta dinga tunanin halin da zai shiga idan ya girma yaji labarin ta'addacin da ubansa ya aikata kafin a kashe shi, wannan tunanin yasa ta dinga wata iriyar rama kafin tayi ar'bain duk ta fige kullum cikin tunani da nazarin yaya rayuwar d'anta zata tashi take. tunda wanda take tunanin zai tallafeta shima ya daina sakar mata fuska ya nunawa duniya cewa ba zai mayar da ita ba dan yanda yake nuna mata halin ko'in kula yasa kowa ya fahimci munufarsa ita dashi gaisuwa ce kawai ke had'a su watarana har yazo gidan ya tafi bata sani ba, dan zaman daki ta aura yanzu tafi so ta kadaice ita kadai tayi tunanin abinda zai fishsheta.............Allah Sarki Ramlatu itace ke hidima da (Daddy) sunan da suke kiran yaron dashi kenan, Tayi masa wanka ta shiryashi ta goya shi a bayanta mutukar kinga yaron a hannun uwarsa to nono zai sha, Najaatu tana jin dadin yanda Ya Ramlatu da sauran mutan gidan ke nuna kulawarsu a kan yaronta
To haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau fari gobe baki Najaatu nata hakuri da halin ko'in kulan da Abbah Abbas ke nuna mata, ita abun sai ya dinga bata mamaki ya damu da d'anta amma ita kallo bata isheshi ba ko gaishe shi tayi baya kallonta yake amsawa amma wani sa'in idan yazo za taji shi suna maganar Daddy da Yaya Ramlatu wani lokacin ma har daukar yaron yake yay masa wasa kafin ya tafi. sai tayi ta mamakin al'amarin wallahi ita ta dauka dukkanin irin kulawar da yake nuna mata a baya yana so ta haihu ne ya mayar da ita sai gashi ya juya mata baya lokaci guda ko kallonta ma baya yi.