Sashe 123
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah Abbas ma da yazo dubashi sai da hankalinsa ya tashi, a take yasa hannu ya kuma biya zunzurutun kud'aden da asibitin ke bukata yace maza a shiga dashi teater , Allah sarki Yaya Ramlatu kuka kawai take dan gani take tamkar gawarsa za'a fito mata da ita, sai dai kuma ba a nan take ita cuta ba mutuwa bace mai lafiya ma yana iya mutuwa ya bar wanda yake da shekara goma yana jinya.......Lafiya lau aka fito da Salim anyi aiki cikin nasara yanzu abinda yay saura kula da shan magani akan 'ka'ida.
*****
Alhaji Aminu Dan jarida da kyar ya samu gurin zama bayan fitowarsu daga prison sai kowa ya gudunsu dalilin daya sa kenan ya harhada 'yan kudaden da suka rage masa ya gudu k'yauyen zaria shida iyalinsa ya samu ya siyi wani lalataccen gida, sauran kudin suka siyi kayan abinci....Mommy ta fara sanar sai da gwanjo a cikin kyauyen sai ta shiga cikin gari ta siyo tazo ta baza a kofar gidan jama'ar garin na siya da wannan sanaa suke rufawa kansu asiri.
A lokacin
Munira ta dade da haihuwa inda ta haifi Da namiji a hannun kanwar Momynta Laila.......'Kaskanci da wulakanci babu irin wanda Munira bata gani ba, taci wuya sosai wanda sai da ta kai ta kawo ta daina fitowa waje dan da ta fito za'a soma yi mata waka mai cikin shega babanta karto d'an uwanta 'barawo wasu yaran ma har jifanta suke wannan dalilin yasa take zama a gida taci kukanta ta koshi Lailah ta ta cigaba da azabtar da ita....Tunda ta samu labarin dawowar iyayenta ta gudu ta koma gurinsu, dan gwara tayi rayuwa a cikin kyauyen da suke a kan azabar da Laila take gana mata.
*RANAR JUMA'A*
Ranar aka daura auran Abbah Abbas da Najaatu a karo na biyu daurin auran yayi albarka sosai dan ya samu halartar manya manyan mutane
daga bangaran Alhaji Abbas mai girma governor dashi da mukarrabansa ma sun samu hallatar daurin auran Abbah Abbas ranar kasa rufe bakinsa yay sai murmushi yake yana gaisawa da jamaa cikin walwala da farin ciki.........Najaatu ta sake zama matarsa a karo na biyu ai dole ya nunawa Ubangiji farin cikinsa..
*'Kawata kada kiyi wasa da wanke bakin ki domun ana saurin gane tsabtar mutum ta ha'koransa.....Akwai damuwa ace wai idan kikayi brush da safe ba zaki sakeyin wani ba sai wata safiyar
to idan kuna marking lov da oga yana muradin ya sha bakinki yaji wari ko datti abinci kina tunanin zai sake marmarin kusantar bakin ki
tsotsar bakin juna gurin mu'amula ta aure na qarawa ma'aurata amarshi da son kasantuwa da junansu, duk wata macen da mijinta baya had'a baki da ita ta bunkici kanta,
rashin gyara da kula da kanki zai janyo miki babbar matsala k'awata.......Idan kinyi bursh da asubah da safe kafin ki karya ki sake yin wani, da daddare kafin ki kwanta kiyi wani ki dauki kaninfari guda biyu kisa a bakinki kina tsotsa, kaninfari yana da mutukar sirri a tare dake kada kiyi wasa dayin amfanin dashi, dan Allah kada kiyi saken da zai sanya mijinki ya dinga gudun had'a baki dake
*BINTA UMAR ABBALE*
*07084653262*
80*******A tsakanin gidan Baba malam da gidan Alhaji ban san wanda yafi wani murna da farin cikin zuwan wannan rana ba, ta ko wane b'angare hidima akeyi sosai 'yan uwa da abokanan arziki nata shige da fice a tsakanin gidajan, duk dai da yawa daga cikin wasu mutanan unguwar gulma ce take kawo su ba abun arziki ba, amma haka hajia da Baba Talatu suka dinga kar'bar jamaa har dai taro ya watse lafiya kowa ya koma muhallinsa......Bayan sallar isha'i Baba malam yasa aka kira masa amaryar domin ya zauna da ita...Najaatu a sanyaye ta nufi gidan Malam din tana boye fuskarta cikin hijabi dan gabadaya a daki ta yini saboda Dangin Hajia da alhaji da suka cika gidan, kunya tasa ta zauna a daki ita kadai haka jamaa suka dinga shigowa d'akin wai zasu ganta, ta dinga data sanin zama a gidan tana ganin da gidan Malam ta gudu daya yafi, to yanzu ma data fito akwai sauran jamaar da basu tafi ba sai kallonta sukeyi ita kuma kallon ne bata so tabbas ba zata dawo gidan ba ta fita kenan dan yanzu ita kanta hajiar kunyarta takeji.
Tana zaune gaban mahaifin nata yana mata nasiha mai ratsa jiki nasiha yake mata kan biyayyar aure gami da riqeshi a hannu biyu baba malam ya nuna mata cewar mijinta a yanzu shi yake da iko akanta saboda haka duk wani abu da zai umarce ta dashi tayi kokarin bin umarninsa mutukar bai sa'bawa sharia ba, sannan ya sake jadadda mata cewar sai tabi mijinta sau da qaba san zata samu aljanna dan haka sai ta zage dantse tayi koyi da Nana Fadima d'iyar manzon Allah (slw) bayan haka kuma tayi koyi da 'yar uwarta Halimatu wanda har Allah ya dauki rayuwarta mijinta na shi mata albarka gami dayi mata kyakkyawar addua.
Bayan Baba malam ya gama Baba talatu ta d'ora nata, Najaatu na kuka tace"Insha Allah ba zan baku kunya ba nayi al'kawarin zan zauna da mijina har karshen rayuwata sannan zanyi masa biyayya kamar yanda Allah ya umarce ni da nayi sannan ina kara rokon ku da ku yafe min abinda nayi muku a baya da yardar Allah wannan karon ba zan baku kunya ba.
Baba Talatu da baba malam sun ji mutukar dadi da maganarta, Baba malam yace."Allah yay miki albarka ya baki zuria mai albarka." Miqewa yay yasa takalmansa ya fita, Baba Talatu tace" Ki shiga dakina wajan gado zaki ga wasu kaya a cikin leda viva Hafsa 'yar gidan Yakumbo ce tace idan kin shigo a baki ban dai bud'a naga ko menene a ciki ba.
A sanyaye ta miqe ta nufi dakin....Kayan ta d'auko a nutse ta shiga fito dasu kayan mata ne zuma cikin wata jarka sai tsumi shima a jarka sai kuma garin magani irin wanda akesha da nono ko madara roba kusan biyar ko wanne da nau'insa, Hasken wayarta ta kunna tana dudduba maganin gami da bayanin dake jikinsa, Murmushi tayi a hankali tace lallai akwai dirama bari na fara da wannan biyun.
Zuma ta dauka kawai ta bud'e bakin abin ta kafa kai tana kwankwad'a! sai da tasha da yawa tukkuna ta dauki jarkar tsumi din a maimakon ta samo kofi ta tsiyaya shima bude murfi kawai tayi ta kafa kai tasha yanda take so ta rufe....Tana kokarin mayar da kayan cikin ledarsu taji sallamar aunty Maryam, tace ashe bata tafi ba, tana jin sanda take tambaya baba ina take, tace mata tana cikin daki....Kafin ma ta gama mayar da kayan cikin ledarsu ta shigo dakin.
"Aunty Maryam baki tafi ba dama."?
Aunty maryam ta samu guri ta zauna tare da ajiye fulas din dake hannunta, Tace" saboda ke na dawo ai, ga kazar amarci nan ba zan tashi daga gurin nan ba sai kin cinye tas kin tsotse kashin.
Dariya tasa tace"Lallai aunty Maryam kema gudumawar da zaki bani kenan kinga fa wasu maganin da Aunty Hafsa ta Yakumbo ta kawo min."
aunty maryam ta shiga duba maganin tana murmushi tace"Lallai ta gwangwaje ki sosai sai ki mayar da hankali kina sha a kai a kai! zasu taimaka miki sosai."
'Yar dariya tayi tace"Ni wallahi aunty maryam da kun barni haka sai yafi meye duk sai kun tashi hankalin ku nifa ina da ni'ima daidai gwargwago ba sai nasha wani magani ba.
Aunty maryam ta harareta tare da fadin "Mara wayo kawai to ko kina da ni'ima sai akace ba zaki 'kara wata ba, okey da haka kike so kije masa babu gyara yaji ki lami! humm to wallahi ba kunyar ki zaiji ba zai iya barinki ya tafi inda zai samu gamsuwa saboda haka kiyi hattara da gyara kanki har wani cewa kike kina da ni'ima a'ina kikayi ni'imar mtwws!
Najaatu ban san sanda zakiyi wayo ba wallahi, zaki zauna tsakanin kishiyoyi idan suka fiki kula da kansu kin shiga uku gwara ki san yanda al'amarin yake tun yanzu....Duk wata mace mutukar tana da kishiya to burinta ta fita a gurin miji kiyi kokarin ganin kin zama tauraruwa akan kishiyoyinki idan kuma kin zauna sakarci shikkenan
Najaatu jikinta yay sanyi Zainab ce kawai ta fad'o mata ta lura yarinyar nada wayo sosai dole ne ma ta zage damtse a kanta dan ta fahimci shima yana ji da ita ko ga yanayin yanda yake kula da ita da sauransu.....Fulas din gaban aunty maryam din ta janyo gabanta ta bude kamshi ya bigi hancinta kamshin tattasai dana magani amma dai maganin yafi yawa a ciki....Hannu tasa tayi bisimillah a nutse ta soma ci tana had'awa da ruwan roman
Najaatu tas ta cinye kazar ta shanye roman aunty Maryam ta rufe fulas dinta ta miqe tare da fadin"to ni zan tafi sai gobe idan munzo rakiyar amarya.
Najaatu mikewa tayi tana sud'e hannunta tace"Wai dan Allah da gaske gobe zan tare aunty Maryam wallahi bana so na tare gobe nafi so adan kwana biyu tukkuna." Aunty maryam harararta tayi tace "Sai kiyi ai ni har gidan da zaki zauna ma na gani a waya....Gidanki daban mai kyau da burgewa babu abinda babu a ciki gaskiya yay kyau sosai wallahi." Gabanta na faduwa tace"Wane unguwa ne ni wallahi daya sani ya had'ani dasu Aunty Halisan zaifi.....Aunty Maryam tace"Aa gwara ki zauna ke kadai yafi mutumci watakila shima yana da manufarsa akan hakan saboda haka ki kwantar da hankalin ki gidanki na rijiyar zaki wajejan massalacin jumaa na d'an sarari." Najaatu shuru kawai tayi tana addua Allah yasa haka shi yafi alkairi amma dai da za'a bi son ranta to da tafi so ta zauna gida daya dasu Halisa......Aunty maryam na kokarin fita daga gidan Yaya Ramlatu ta shigo da Daddy a hannunta yana kukan a mutunce suka gaisa da juna kafin ta shige cikin gidan da sauri....