← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 143

Sashe 136

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab ta bashi wahala jiya gashi duk wasu dabaru bata iya ba sai shirmen kwalliya da iyayi amma daga an hau kanta zata fara ihu ita ta gaji shiyasa Najaatu take burgeshi ta kowane fanni
To Ita kanta Zainab din sai da ta fahimci wani abu daga gurinsa, jikinta yay sanyi data zauna tayi nazari da tunanin akan abinda yake b'acin rai! ita dai tasan daidai gwargwado tayi gyaran jiki kuma a jikinta tana jin ni'ima to me yanyo yake jin haushinta, jiki a mace ta miqe ta nufi bandaki ko kafin ta fito ma yay ficewarsa daga dakin, ta zauna gefan gado tare da zabga tagumi da tunanin neman mafita( Wasu lokotan maza sune suke sanyawa matansu na haukan shaye shayen maganin mata idan namiji ya kusanci matarsa yaji ba daidai ba na rana daya kacal sai ya hau fushi da muzurai! shi dai kullum idan ya hau yaji daidai! kuma wasu mazan fa babu ruwansu da kula da matayensu babu abinci mai kyau ballantana azo ga maganar kayan marmarin da zasu saukar da ni'ima, wasu matan na kokari sosai da kudinsu zasu siyi magani duk domin kaji dad'i ka gamsu amma saboda rashin adalci rana d'aya idan kaji sauyi sai ka sanja fuska, dan Allah a dinga adalci idan kana so kullum kaji matarka zam-zam to kana kawo mata kayan ciye ciye irin su *Nama 'kwai kayan marmarni kwakwa dabino mazarkwaila cikwi zuma da dai sauransu
...........Team din Najaatu nifa yau ina gurin Zainab dan wallahi ta bani tausayi
Gurin Halisa ya shiga suka gaisa ya jima tare da ita kafin ya nufi gidan Alhaji.........Lokacin da ya isa gidan Hajia na sama dakin Alhaji Ya Ramlatu da Najaatu na zaune a falo suna hira, zama yay suka gaisa kafin ya haura sama gurin iyayen nasa.........Lokacin daya sauko kasan Yaya Ramlatu kawai ya tambayeta ina Najaatu tace yanzu ta shiga d'aki...Kai tsaye dakin ya nufa, lokacin tana kokarin shiga wanka dan bata dauka zaizo gidan da wuri ba shiyasa ba tayi wanka ba, Ganinta daure da towel yasa hankalinsa ya tashi dama ba wata cikakkiyar gamsuwa ya samu a gurin Zainab, ido a lumshe yake kallonta, Tace" Dama yanzu nake so na kiraka a waya akwai maganar da zamuyi."
Ya zauna gefan gado tare da fad'in "To gani ai zonan ki fad'a min ko menene."
Tace"To bari nayi wanka na fito." Shuru yay yana binta da ido har ta shiga toilet din....Mikewa yay yaje yasa key a dakin, ya cire rigar shaddar jikinsa da wandon ya ajiye gefan.......Da gajeran wando ta sameshi a kwance a gado.gabanta ya fadi da sauri tace"Abbah meye haka."?

Ya miqe zaune yana kallonta da jan ido yace."Abinda idonki ya gane miki."
Girgiza kanta ta shigayi tare da fadin"Ta'bdijam! dan ita al'amarin ma mugun mamaki ya bata a gidansu ya cire riga da wando tsaf ta gane abinda yake nufi.....Shan kunu tayi ta nufi gurin jakar kayanta tana kokarin dauko riga da zani na atampa yazo gurin ya tsaya, ta dago a tsorace tana kallonsa, "Dan Allah ka mayar da tufafinka jikinka beda ce ba, kai da ka baro gidanka be kamata ace kana da wata bukata ba.

Yace." Ni dai ba surutu nace kiyi min ba kaya kuma ba zan mayar ba sai na samu gamsuwa.

Tace.'' To wai ina aunty Halisa da Zainab din." kai tsaye yace."Suna nan kalau jiya nayi da Zainab yanzu kuma naki nake so.''
Taji kamar ta kwada masa mari saboda takaici wato baya bambamce mai girki da mara girki a duk lokacin daya bukaci mace kawai ya afka mata, murya na rawa tace"To ai ba girki na bane sai ka bari girki ya zagayo kaina." Towel din dake jikinta ya fizge yace"Bana bukatar wasting time ki bani abinda nake bukata domun tun jiya bana cikin hayyacina.

A tsorace ta dinga kallonsa tana ja da baya yana kara kusantota tamkar wani zaki! sai huci yake! hawaye ne suka soma zubo mata tasa hannuwanta tana kare kirjinta, daukarta yay ya kwantar da ita kan bed din ya danneta..........Ya saba idan ya hau kanta baya sauka sai ya kawo sau uku sannan , tayi ta kuka da magiya akan ya hakura idan ya kawo sau daya ya sauka saboda kada su hajia su fahimci wani abu amma ko a jikinsa bai sauka ba sai da yay release sau uku ya d'agata!

Takaici yasa ta takure jikinta gu guda tana kuka
Tsaf yay wanka ya fito yana jin annushuwa a cikin ransa, haba jamaa sai yanzu yaji daidai amma jiya Zainab haukane kawai bata sa yayi ba, yana daura agogonsa yace"Wace magana zamuyi." Juya masa baya tayi ta kyaleshi yana ta magana, da ya gaji ya fita daga dakin ya kyaleta.

Tun daga ranar take ci masa kunu ko zuwa yay bata sakar masa fuska shi kuwa ko ajikinsa al'amuransa yake yi kai tsaye kuma da bukata zata ciyoshi haka zai zo ya danneta babu abinda ya dameshi.......Ranar da girki ya zagayo kanta ya sameta a daki yanda take shan kunu shima haka yasha, yace"To zaman ya isa haka tunda girki ya zagayo kanki anjima Dan Azimi ya kaiki gida.

Kai tsaye tace"Ai mun gama magana da Hajia zan tafi jos nayi sati biyu.

Ya bude baki yana kallonta da fad'in.''Ashe baki da hankali Hajia ce ke auranki ko ni? da har zaku gama magana ban sani ba." Tace"Ranar naso na fada maka ka fita.

Yace."To babu inda zakije gida kuma ki tafi kafin yamma dan wallahi nazo gidan nan da yamma na ganki sai na 'bata miki rai."
Yana gama maganarsa yasa kai ya fita daga dakin.....Najaatu na kuka ta shedawa hajia yanda sukayi Hajia tace daina kuka ki koma gidanki kamar yanda ya bukata insha Allah zan zauna dashi akan zuwanki jos ai ya dace ka gaishe da mai gaisheka Wa'yannan mutanan sun cancani ayi musu komai.....Wannan maganar da hajia tayi yasa taji sassuaci a cikin zuciyarta tana cin abincin rana Dan Azimi ya dauketa a mota ya kaita gidanta bayan tayi sallama da iyayenta
*BAYAN SATI BIYU*
Tana zaune a falon gidanta taji sallama da sauri ta daga kai tana kallon kofar shigowa ido suka had'a da Munira wanda da badan tayi mata kyakkyawan sani ba ba zata ganeta ba saboda ramar da tayi.........Najaatu ta miqe da sauri tana kallonta hade da kiran sunanta!

Munira tun kafin ta karaso falon kuka ya subce mata, tana isowa ta dauki Daddy ta rungumeshi kam a kirjinta kan kujera ta zube ta dinga rizgar kuka tana sake 'kam'kame Yaron a kirjinta.........
*MADADI!*
******89 Najaatu zubawa Munira ido kawai tayi tana kallonta sai kuka takeyi ta kasa cewa komai gashi ta matse yaro a jikinta yana ta kuka gami da son zuwa gurin uwarsa ta ri'keshi tsam a jikinta taki sakinsa.

Kawai sai taji itama zuciyarta ta karye hawaye suka shiga zubowa daga idonta......Sun jima cikin wannan yanayi kafin Munira ta sassauta kukan da takeyi tasa hannu ta goge hawayen fuskarta ta d'ago fuskar Daddy ta tsira masa ido sai kawai wasu hawayen suka sake kwace mata.....Najaatu a sanyaye tace"Haba Munira wannan kukan da kikeyi ya isa haka dan Allah ki daina komai kikaga ya faru dama can rubutaccene daga Allah.

Munira murya na rawa tace"Najaatu dole nayi kuka domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda zuciyata hakika nayi nadamar rayuwa nayi dana sanin abinda na aikata hakika na cutar dake gashi da yake baki da hakki Allah ya musanya miki da alkairi Najaatu rayuwata data iyayena ta zama abin tausayi da kyama kowa gudunmu yake dalili kenan da yasa muka tarkata kayanmu muka koma kauyen zaria da zama, yanzu haka acan muke rayuwarmu, Mommy itace ta bani umarnin zuwa na sameki domin neman afuwarki abisa abubuwan da suka faru a baya, kai tsaye gidan Alhaji na sauka Hajia tayi min kar'bar mutunci tasa aka kawo min abinci naci na koshi, Itace take sheda min haihuwar wannan yaron nayi mamaki sosai kuma alokacin naji sake jin tsoron Allah ya kama ni hakika Ubangiji babu yanda baya tsara lamarinsa tsorona Allah da Annabi yaron nan ya girma ya mallaki hankalin kansa ya samu labarin abunda ya faru a baya dole yayi mana kallon lalatattun iyaye marasa nagarta domin mun cutar da rayuwarsa tun kafin yazo duniya mun ruguza farin ciki gami jin dad'in rayuwarsa saboda son zuciyarmu wannan dalilin ne yasa ki kaga tunda na shigo nayi tozali dashi nake kuka saboda nasan mun riga munyiwa rayuwarsa illah."
Najaatu shuru tayi tana tunanin abubuwan da suka wuce, ta goge k'wallar dake kokarin zubowa daga idonta tace"Munira a lokotan baya na dauki abunda ya faru da rayuwata na d'ora a matsayin kece sanadi sai daga baya kuma nagane cewa bake kadai keda laifi ba har dani dan da nabi umarnin iyayena ban kuma bi son zuciyata ba to na tabbata haka ba zata faruwa ba, to dukkaninmu muna aikata abune a duhu domin bamu san abinda Allah ya lullu'be ba, hakika aurana da 'Dan uwanki kaddara ce da kuma tsananin rabo gashi nan a hannuki rabon Wannan yaron ne yasa duk abubuwan da suka faru a baya suka kasance saboda haka ki daina kuka da damuwa wallahi tuntuni na yafe miki kuma na tausayawa rayuwar da kuke ciki keda iyayenki ina rokon Ubangiji Allah ya sassauta muku......Munira a sanyaye ta amsa da ameen ameen Najaatu nagode sosai da karamcin ki kema inayi miki fatan alkairi a rayuwarki Allah kuma ya tabbatar da zaman lafiya a tsakaninki da mijinta.'' Najaatu ta amsa da ameen ameen nagode kwarai da adduarki." Falon yay shuru na minti uku kafin tace"Ina Muktar ina fata kunyi aure."?

Munira tayi wani irin murmushi kai kana ganinsa kasan na takaici ne tace"Najaatu Muktar ya yaudare ni ko kuma nace na cuci kaina na amince masa yana mu'amulanta ta kamar matar auransa sai da yayi min ciki tukkuna yayi min korar kare tare dayi min gargadi da cewar naje na nemi uban d'ana sannan kuma idan na sake na sake zuwa nace cikina nasa ne sai ya d'aure ni, a takaice dai yanzu
haka yaron dana haifa yana nan yay wayo shekaransa daya da wata hud'u.

Najaatu ta dinga girgiza kanta cikin alhini da damuwa tace" Munira kinga irin abinda nake fad'a miki ko?
Chapter 136 · 0% Book details