← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 143

Sashe 41

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya tace"Ai zamanta a gidan baida amfani tunda ka kasa ri'ke amanarta, sannan ka bawa matarka da 'yar uwarka lasisin dukanta da zaginta gami da hanata sakat! a cikin gidan."
Sai ya kasa gane inda maganar mahaifiyar tasa ta dosa." Yace."Hajiya bangane ina maganarki ta dosa ba." Tace"Ai dama ba zaka gane ba sai na ganar da kai, to wannan yarinyar dai 'karar ka ta kawo min kancewar kuna azabtar da ita kai da matarka sannan kuma yau Ramlatu taje har gidan ta doketa."
Maganar ta bashi mugun mamaki! kamar shi da girmansa da shekarunsa a kawo shi 'kara gaban iyayensa, Ya dago kansa yana kallonta sai yaga kanta na kallon wani guri sai faman zum'bura bakinta take, tunda yake da Halimatu da Halisa tsayin shekarun da sukayi a tare babu wacce ta ta'ba kawo 'kararsa gaban iyayensa sai wannan yarinyar gaskiya ya jinjina al'amarin sosai! amma babu komai idan ma raini ne ya soma shiga tsakaninsu to dama ya dauki alkawarin yau yake so ya fitar da raini a tsakaninsa da ita.
......Hajiya ta cigaba da cewa"Wannan dalilin ne yasa nace ba zata koma gidan ba sai kazo naji ta bakin ki, shin me yasa a duk sanda Halisa zata kawo magana baka tsayawa kayi bunkice zaka hau kai ka zauna kazo kana yin abinda ya dace."
Rashin abinda zaice ne yasa yace."Ayi hakuri Hajiya."
Tace"To Dan Allah daga yau ka zama mai adalci a tsakanin matanka idan wani abu ya faru a tsakaninsu ka daina dora laifi a kan mutum daya ka dinga yin binkice tukkuna."
Tace."Insha Allah Hajiya to amma ni abinda ke bani mamaki anan shine har yaushe akayi auran da har za'a fara kawo 'kara duka fa yau kwananta hud'u a gidan kuma iya bakin kokari inayi a tsakaninsu.'' Hajiya tace" To nidai ga abinda tazo ta fada min kuma nasan wannan matar taka babu abinda ba zata aikata ba dan haka kaja mata kunne ita in banda abinta ai kamata yayi ta dauki naja'atu a matsayin kanwarta ba kishiyarta ba kuma itama Ramlatu zata zo ta sameni har gida, idan ta dinga zuwa gidanka tana lalata maka zamantakewar matanka to tun wuri ka taka mata burki tunda har yanzu taki tayi hankali." Yace."Ba zan hanata zuwa gidana ba domin suna zumunci da Halisa amma zanyi bunkice sosai kan maganar da ita Naja'atun tazo ta fad'a miki idan na tabbatar da gaske ta doke ta to ni kuma zan nuna mata rashin jin dadi na."
Hajiya tace"To Allah ya sa'ba halaye dama nace idan tayi sallah taci abinci sai ku tafi.'' Agogon dake daure a hannunsa ya duba ya mike da fad'in "Bari na hau sama mu gaisa da Alhaji." Kafin ma ya rufe bakinsa ya hango shi yana sakkowa daga benansa, Alhaji Sama'ila ya sauko ne d'aure da alwala da nufin zuwa massalaci, gaisawa sukayi da Abba Abbas d'in dama ita Naja'atu har dakinsa taje ta gaisheshi, ita kuwa Hajiya 'kin fada masa abinda ke faruwa tayi saboda ba wata cikakkiyar lafiya ce dashi ba......Abbah Abbas da mahaifinsa a tare suka nufi massalaci domin gabatar da sallar magariba...
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu to ga yanda abin yake.

VIP #600
normal#300
Account: 0542382124..Binta Umar gtbank...Idan katin waya zaki turo kiyi min mgn ta whsap da wannan numbar.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
BHRBN
*28*
Sai bayan ishai ya shigo gidan, a lokacin itama tayi sallah taci abinci tana zaune suna hira da Hajiyan, ba tare da ya zauna ba ya kalli hajiyan da fad'in "To hajiya sai da safe." Hajiya ta kalli Naja'atu da fad'in "Tashi kuje ki kara hakuri insha Allahu zakici ribar hakurinki."ta kalli Abba Abbas din da fad'in " Kai kuma ina fatan kaji abunda na fada maka ko." Yace."Naji hajajju Allah ya shige mana gaba." Ta amsa da ameen." ya juya ya fita, ita kuma ta mike a sanyaye tasa takalmanta hajiya tace"To Allah ya tsare insha Allah zansa a kawo ni gidan naku." Tace." Tom Hajiya sai kinzo." Kafin ta fita sai da ta shiga dakin hajia Rabi kishiyar Hajiyar tayi mata sallama Hajiya Rabi ta bata kayan islamic irin na mata masu kyau. ta kar'ba tana godiya tayi mata sallama tabi bayansa.

Tare ta gansu da Abba Magaji a jikin mota suna magana, gabanta ya fadi ganin Abba magaji duk sai ta tsorata kai a sunkuye tana kokarin bude mota tace"Abba Magaji ina wuni." Ya amsa fuskarsa a sake, dan shi gabadaya bai san wai yaji tayi ba tunda shi Abbah Abbas din bai fada masa komai ba....Bude mota tayi ta shiga tana zazzare ido addua take Allah yasa Abbah Abbas din ya shigo su tafi dan gabadaya jikinta yayi sanyi tasan da Abba magajin yasan abinda ta aikata sai ya 'bata mata rai.

Motsin bude motarsa taji sai ta nutsu tayi kasa da kanta gabanta na fad'uwa.

Ya shiga motar ya zauna ba tare da kalleta ba a nutse yaja motar suka bar gurin.......gabadaya hankalinsa nakan draving din da yake bai ko kalli inda take zaune ba. ita kuma ganin yanda ya sha kunu ne yasa duk tsoro ya cika mata zuciya. kire ne ya shigo Wayarsa dake gaban aljihunsa, ya dauka yana dubawa yaga Halisa ce, ya kara wayar a kannunsa tare da amsa sallamarta, tace"Abbah Mufida yau shuru baka shigo gida da wuri ba nace Allah yasa dai lafiya sannan kuma ina so na fada maka cewar yarinyar nan Naja'atu tun safe bata gidan nan."
Yace."Kada ki damu gani nan tare da ita taje gidan Alhaji ne." Halisa tace"Au! to ai da da zata tafi sai ta fad'a mana nida yara duk hankalinmu ya tashi wallahi."
Yace."Nima bata fad'a min saboda tana da iko da kanta na dawo daga kasuwa na sameta a can." Halisa tace"Ikon Allah." Yace."Ganinan shigowa yanzu." Cikin kissa tace"Allah ya kawo ka lafiya." Kashe wayarsa yayi a mayar aljihu ya cigaba da draving dinsa .....Naja'atu taji ciwon yanda ya banzatar da ita tana ganin ai kamata yayi ya rarrasheta tunda ita akayiwa laifi amma saboda bata da wata daraja a gurinsa laifinta ma yake gani....Itama sai ta dinga kauda kanta tana kallon hanya, tana kuma kokarin mayar da hawayen dake so ya zubo mata.

Dai dai asibitin Hasiya bayaro yayi parking ya fito ya tsallaka titi naga ya nufi wani ke'bantaccen gurin gasa kaji da sauransu ya jima a ciki kafin ya fito hannunsa rike da ledoji masu dauke da sunan gurin, tana ganin zuwansa ta juyar da kanta ya bude motar ya shiga ya zaune, 'kin juyowa tayi har ya tayar da motar suka bar gurin fuskarta na kallon hanya sai zumbura baki takeyi, a haka sukaje gidan babu wanda ya kula dan uwansa.

Yana parking ta bude motar tayi gaba, ya girgiza kansa tare da fitowa daga motar yabi bayanta da ledojin a hannunsa.

Halisa da yaran suna zaune a palo suna kallo kamar dai koda yaushe yaran suka iske inda yake suna masa sannu da zuwa, mussadiq ya kar'bi ledojin hannunsa yana kokarin kai masa daki, yace."Bani guda d'aya sauran naku ne kowa ya dauki daya." Mussadiq yace."Mungode Abbah." Mussadiq Ya mikawa kowa nasa, Halisa kuwa mi'kewa tabi bayansa dakin.

Naja'atu kuwa dama data shigo gidan babu wanda ta kula kai tsaye daki ta nufa..tana jin wani irin kunci na dawowarta gidan a duniya ta tsani ta budi ido ta ganta a gidan ji take tamkar tana kurkuku!

Mussadiq ya shiga dakin da ledarta a hannunsa a sanyaye yace."Yaya Naja'atu ga naki." Girgixa kai tayi tace''Jeka hada ka cinye naci abinci gidan hajiya." Yace."Yaya Naja'atu gidan Hajiya kikaje me yasa bakije dani ba."?

Murya na rawa tace"Ka bari idan zan sake zuwa zai je da kai." Yace."To nagode amma dan Allah ki kar'ba kici ni ba zan iya cinyewa duka ba." Tace."To ka ajiye gobe sai ka tafi dashi skull." Yace." Uhum!uhm ni dai nafi so kici hankalina zaifi kwanciya." Kar'bar ledar tayi ta bude tana dubawa, taga gashashiyar kaza da sauran kayan ciye ciye....Tace"To zauna muci tare." Yace."To bari na dauko nawa." Da sauri ya fita daga dakin.

Halisa kuwa cikin kissa da kisisina ta dinga bugun cikin Abbah Abbas din, saboda tana so tasan dalilin da yasa yarinyar tafiya gidan Hajiya, shi kuwa ba tare da tunanin komai ba ya fada mata dalili.....Ta ri'ke bakinta tana jimantawa tace"Amma gaskiya yarinyar nan bata kyauta ba, yanzu kamarka zata kai 'kara gurin hajiya! hummm! gaskiya ta bani mamaki kuma a yanda kake kauntarta da nuna kulawarka a kanta bai kamata tayi maka hakaba, kuma wallahi karya take Yaya Ramlatu bata doketa ba sharri kawai tayi mata! dan haka kada ma kace zaka tunkari Yaya Ramlatu da wannan maganar idan haka ta kasance Yaya Ramlatu zataga kamar kafi kaunar matarka a kanta kuma kasan karfin zumunci yafi gaban a hadashi da komai. ni a ganina yarinyar zaka hukunta ba wai ita Yaya Ramlatun ba."
Yace."Koma dai menene insha Allahu ya kusa zuwa karshe, sannan bana daukar wasu abubuwan da yarinyar nan take da zafi dan saboda nasan akwai karanci shekaru a tare da ita gaba kadan idan ta kara hankali ba zatayi ba.....Ta'be baki tayi tace"Babu wani kuruciya tsabar iskanci ne wallahi.' Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta da fad'in "ki duba cikin rigar dana cire ki dauki key din motarki." Halisa ta ru'kun'kume shi tana dariya." Shima dariyar yake yana mamakin murnar da take, Halisa ta dauko key din tana ta washe bakinta, mikewa yayi yace."Gobe zan kaiki ki d'auko motar a inda na siya miki." Tace"To nagode sosai Allah ya saka da alkairi." tare suka fito daga dakin, ya zauna a gurin cin abinci Halisa ta had'a masa abincin data girka wanda ta barbade shi da maganin mallaka, shi kuwa kamar koda yaushe yayi bisimillh sannan ya soma cin abincin ba tare da ya kawo komai a cikin ranshi ba.
Chapter 41 · 0% Book details