Sashe 141
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hankalinsa ne ya tashi shifa baya tayar da maganar bane dan rai ya 'baci yana so su fahimci juna da 'yar uwarsa dan baya son irin bambamcin da take nunawa a tsakanin matansa amma ba dan ya 'bata mata rai ya tayar da maganar ba, Najaatu ganin Yaya Ramlatu na kuka sai itama ta fara, Halisa ta fito daga toilet ta tarar dasu suna kuka shi kuma sai magana yake musu.....Tace"Yanzu ashe Abbah Mufida maganar nan bata mutu ba nifa tashin hankalin nan ya tayar min da nakuda wallahi." Yace."Halisa magana ta mutu tuntuni tambayarta nake akan abinda ya faru shine take kuka sabida rashin fahinta."
Halisa ta samu guri ta zauna tare da fad'in "Yaya dan Allah ki daina kuka Zainab fa karya take ta shiga tsakaninki da Dan uwanki kome za tayi kuwa ki daina damuwa."
Yaya Ramlatu ta goge hawaye tare da kallonsa tace"Kace kana so kaji abinda yasa matarka kasa zama a gidan biki ta dawo gida ko." Yace."Eh." Tace"To Najaatu tayi sha'awar 'yarta sai ta nuna ta bata aro tayi mata kwana biyu kai tsaye tace ba zata bayar ba, haushin haka yasa nayi mata fad'a saboda raina ya 'baci sosai da yanda ta nuna rashin kwaicinta a kan 'yar uwarta amma babu wanda ya zage ta ko yaci mutuncin iyayenta duk wata magana da tazo ta fad'a maka karya take."
Shuru yay yana nazarin maganar.......Abinda yasa yay saurin yarda da maganar Zainab din sabida yasan akwai rashin jituwa a tsakaninsu sannan Halisa da Najaatu sun nuna masa kansu a had'e yake ma'ana sun cire Zainab daga cikin su shiyasa ya yarda da cewar za'a iya had'a baki dasu aci mutuncinta tunda kishiyarsu, sai kuma yanzu da yaji farkon al'amarin ya fahimci furucin Zainab din ya janyo duk hatsaniyar shima yaji rashin dad'in abinda tayi ina laifin wanda ya nuna yana son naka, a zamansa da Zainab ya fahimci halinta na rashin iya magana da rashin kawaici da hakuri mutukar akan hakkinta ne bata iya yin shuru shiyasa yake tsoron wani abu na sa'bani ya shiga tsakaninsa da ita sabida hanashi bacci take da daddare, ya lura su kuma su Halisan suna ganin kamar tsoro ne yasa yake biyewa Zainab din da duk abinda tazo masa dashi wanda kwata kwata ba haka bane a gurinsa kawai yana jin tsoron rashin hakurin ta da mitar ta dan kwata kwata abu naya wucewa a gurinta ta dinga nanata magana kenan............Ya jima a tsaye a dakin yana nazarin al'amarin kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Halisa dake kokarin sawa babynta nono yace."Ina fata babu wata matsala ko."?
Tace"Babu matsala." Yace."To sai kiyi kokari kici abinci kamar yanda Dr Saadatu ta fad'a miki kisha magani kafin ki kwanta." Tace."Insha Allahu." Sallama yayi musu ya juya da niyyar fita daga dakin....'Yar uwarsa ce kawai tayi masa magana Halisa da Najaatu shuru sukayi suka bishi da kallo har ya fice daga dakin.
Bayan ya dawo daga sallar asubahi ya sameta ta idar da sallah zama yay gefan gado had'e da kiran sunanta" Zainab'' amsawa tayi tare da juyowa tana kallonsa, yace." zo nan." Jiki a sanyaye ta miqe taje ta zauna kusa dashi." kallonta yayi a nutse yace."Jiya Yaya Ramlatu dik ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku wanda har yanjo ta kasa hakuri tayi miki fad'a kan abinda kikayi wanda ke kika daukeshi da wata manufa, banji dadin abinda kikayiwa Najaatu ba ina laifin wanda ya nuna yana son naka." Shuru tayi tana zumbura bakinta ita yama za'ayi ta dauki 'yarta ta bawa ma'kiyarta ai ba zai yiwu ba."
Yace."Koda ba zaki bata ba ai bai kamata ki fito ki fad'a mata gaban jamaa ba kin nuna mata iyakarta akan abinda take da iko dashi koda bana auranta zan iya bata d'ana ta ri'ke sabida cancantarta to ballanata a matsayin uwa take a gurin Ummi tabbas nasan kamar yanda zata kula da d'an cikinta haka zata kula da Ummi amma meye na nuna mata iyakarta."
"Abbah Mufida nifa koda ba ita taba ba zan iya bada d'ana yaje wani guri ya kwana bs kuma ni ban fad'i maganar da wata manufa ba dan da nasan zasu dauki zafi to da nayi shuru da bakina yarinya dai 'yata ce sai nayi niyya zan bayar."
Cikin 'bacin rai yace."Kiyi min shuru nace! wato har wani fuffuka kike kina maganar yarinya yarki ce bayan kin gama azabtar da ita ashe akwai ranar da zata zo kiyi wannan maganar to ki daina cika baki idan nayi niyya wallahi zan dauke yarinyar daga hannuki na kaita duk inda raina yake so sai naga k'aryar so." Shuru tayi gabanta na bugawa jin abinda yake fada.
Yace"Anjima ki shiga gurin Halisa Yaya Ramlatun nan ki bata hakuri kan abinda ya faru kinji ko." Murya na rawa tace "To."
Kwanciya yay kan bed din tare da tsirawa rufin dakin ido, Zainab hijabin jikinta ta cire taje ta kwanta kusa dashi, itafa tunda taga Najaatu da ciki to itama sai ta samu hankalinta zai kwanta, jikinsa ta shiga tana shashshafa kirjinsa tare da sumbatar fuskarsa, duk da yasan wuya zata bashi hakan be hanashi kar'bar tayin ta ba rungumeta yay a jikinsa yana mayar mata da martanin abinda take masa.
Najaatu da Yaya Ramlatu na zaune suna karyawa suka shigo tare, Tinda tayi musu kallo daya ta dauke kanta, Zainab ta nemi guri ta zauna shi kuma ya tsaya suna gaisawa da 'yar uwarsa, Najaatu ba tare ta kallesa ba ta gaisheshi cikin kulawa ya amsa yana tambayarta Halisa tace"Tana bandaki....
Bakin bed din ya zauna yace "Bani yarinyar." Babyn dake hannuta ta bashi kamar yanda ya bukata ta juya ta cigaba dayin break dinta.
Zainab a sanyaye tace"Yaya Ramlatu dan Allah kiyi hakuri akan abinda ya faru jiya." Yaya Ramlatu tace''Haba ai ni bani da ri'ko 'yar nan magana ta wuce a gurina." Zainab tace"Nagode insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba kema Najaatu ki gafarce ni ban san maganata zata 'bata miki rai ba."
Najaatu murmushin takaici tayi tace"Babu komai magana ta wuce."
Abbah yaji dadi sosai ganin yanda Zainab ta dauki nasihar sa dan baiyi tsammanin zata nemi afuwar Najaatu ba sai gashi tayi masa bazata, sosai yaji dadin abinda tayi.......Sai da halisa ta fito daga toilet suka gaisa sannan yay musu sallama ya tafi kasuwa.
Zainab kuwa zama tayi tana ta kokarin wanke kanta ita lallai sai sun manta abinda ya faru, Halisa dai da Ramlatu suna sata a maganarsu amma Najaatu idan tana magana tasa mata baki shuru takeyi dan bata son abinda zai sake had'asu suyi ta hayaniya sai kace wasu karnuka a ganinta yanzu duk an daina irin wannan kishin jahilcin.
Bayan sallar la'asar ya kirata a waya tare da sheda mata cewar yanzu yay magana da Dan Azimi zai zo ya dauketa ya mayar da ita gida." Tace."Da kabari idan kazo sai mu tafi tare." Yace."Aa ki dai zauna a shirye Dan Azimi zai zo ya dauke ki shawarar dana yanke kenan." shuru tayi bacin rai ya hanata cewa komai dan ma kada ta kashe masa waya yaji haushi da tuni ta kashe, tana jinsa yana magana ta dinga umm eh da ya gaji da abinda take masa sai kawai ya kashe wayarsa ransa a 'bace
Najaatu dauke masa wuta tayi lokacin daya shigo gidan ma tuni ta bar falo ta shige daki tayi kwanciyarta tasan abinda yasa yace ta dawo gida sabida yana so yazo ya haye kanta yay abinda yake so, ita da take biya masa bukatarsa ta kowane fanni itace abar wulakantawa a gurinsa aikuwa zata nuna masa tasan abinda take sai tayi sati bata amincewa bukatarsa ba in yaso yaje can gurun Zainab din ya 'karata
Abbah babu yanda beyi da ita ba akan ta tashi taci abincin daya shigo dashi tace ta koshi alhalin data dawo ba tayi girki ba tunda ta cika cikinta da abincin mejego take jinta a koshe!
A kammala cin abincinsa yaje yayi wanka kamar koda yaushe turare ya shafa a jikinsa sannan ya kwanta kusa da ita...............Matsawa tayi can karshen gado tana takure jikinta, ganin abinda tayi yasa ransa ya 'baci sha'awarsa ya danne ya juya mata baya tare da jan bargo ya rufe kafafunsa.
A haka sukayi bacci ita tana gabas shi yana yamma!
Ta dauka da safe zai sanja mata fuska sai taga bai nuna mata komai ba yace tayi maza ta shirya da wuri zai fita, a gurguje tayi wanka ta shirya ko beak fast ba suyi ba suka fita.........Can babban gidan nasa suka nufa tare.