Sashe 52
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Ramlatu da Halisa ne sukayi sallama suka shigo palon a tare, gabadaya yaran suka yi tsamo-tsamo jiki a sanyaye suka amsa sallamar.....Halisa ta dinga bin palon da kallo tana ta'be bakinta, ita kuwa Yaya ramlatu zama tayi kan kujera tana amsa gaisuwar yaran...Halisa ta bude bakinta kenan za tayi magana ya fito daga dakinsa.
Kauda kansa yayi daga inda take dan har yanzu bai daina jin haushinta ba.
Ita kuwa Ramlatu na ganinsa sai yasa ta janyo Saddiqa tana duba hannunta tare da yi mata sannu da jiki!
Yarinyar ta dinga amsawa a tsorace, itama Halisan a sanyaye taje tana duba hannun yarinyar sai wani marairaicewa take kamar mutuniyar arziki
.....Shi kuwa ko kallonta baiyi ba yaje ya zauna suna sake gaisawa da yar uwarsa.
Halisa ta wani risinar da kai kamar mutuniyar kirki ta gaishe shi, amsawa yayi hankalinsa nakan mussadiq inda ya umarce shi da yaje ya kira Naja'atu tazo su gaisa da Yaya Ramlatun
Halisa kuwa ganin yana dauke mata kai duk sai jikinta yayi sanyi tana ganin anya kuwa aikin bokanta zaiyi tasiri a kansa ta lura yana da taurin kai da kuma dafa'i a jikinsa tayi yaji a maimakon ya tarairayeta ko kallo bata isheshi ba.
Koda Mussadiq ya gaya mata sa'kon Abban nasu cewa yaron yaje yace tayi bacci, yaron yayi jim yana tunanin maganar ta buga masa tsawa da fad'in 'Ka wuce daga kaina kaje kace nayi bacci." Yace."Yaya Naja'atu karya fa babu kyau dan Allah kizo ku gaisa kamar yanda Abbah yace.
Mikewa zaune tayi tana hararsa tace"Naji jeka gani nan zuwa." Da sauri yaron ya fita daga dakin.....Sai da tagama zamanta sannan ta mike ta fita.
lokacin ma yaya ramlatun ta mike da niyar tafiya.
Ta dan risina murya a kasa tace" Yaya sannu Ina wuni." Ta'be bakinta tayi tace"Na wuni kalau ai da kin sani kinyi zamanki ma ba sai kinzo mun gaisa ba." Shuru palon yayi dan yanda ta fadi maganar kowa ya fahimci a hasale take da abinda Naja'atun tayi...Hanyar futa ta kama Abban da Halisa suka bi bayanta. ita kuwa juyawa tayi ta koma daki babu wata damuwa a cikin ranta dan tun ranar da matar ta zagi iyayenta ta daina jin tsoronta ba za tayi mata rashin kunya ba amma kuma ba zata lamunci a dinga tozarta mata iyayenta ba Daki ta koma ta kwanta tana cigaba da tunanin mafita a gareta.....'Kawarta Munira dake can jos itace ta fad'o mata, tabbas da tana da waya to data kira Munira tunda tana da numbar ta tasan zata bata shawarwarin da zasu taimake ta amma ta daina zuwa ta kaiwa anty Maryam shawara sabida ta lura itama tana goyon bayan zamanta a gidan Abbah Abbas din...shuru tayi tana sake nazarin yanda za'ayi ta sadu da Munira, tana ganin za tayi dubarar daukar wayar Abba Abbas din ta kira ta tunda tana da numbar ta. wannan tunanin da tayi sai yasa ta samu sassauci a cikin zuciyarta.
Halisa kam bayan sun raka Yaya Ramlatu sai tabi bayansa dakinsa ta shiga tana wani salo-salo ta rike hannunsa kawai sai ta fashe da kukan kissa tana bashi hakuri wai wallahi ranta ne ya 'baci shiyasa ta yanke hukuncin bar masa gida amma insha Allahu ba zata sake kwatantawa ba." Yace."Idan kina ganin yin hakan shine mafita a gareki to sai ki cigaba da daukar mayafi kina tafiya ni dai ko yau na rabu dake idan nayi ra'ayi zan maye gurbinki da wata sabida haka wallahi duk sanda na nuna miki kuskuranki akan wani abu kika dauki mayafi kika fita to ki tabbatar da cewar kin fita daga gidana har abada." Murya na rawa tace"Dan Allah ka daina wannan maganar insha Allah ba zan sake ba raina ne kawai ya baci shiyasa na tafi amma ka daina cewa zaka rabu dani har abada.
Yace."Ai na lura hakan kike so shiyasa nake sake jadadda miki." Tace" Kayi hakuri na daina magana ta wuce insha Allahu.
Halisa sai da tasan yanda tayi ta wanke kanta a gurinsa sannan hankalinta ya kwanta.
Abbah Abbas shi kadai yayi kwanciyarsa dan da Halisan da ita Naja'atun babu wacce ya tunkara ya rabu dasu su samu nutsuwa tukkuna...Bangaran Naja'atu ma tayi mamaki sosai da ba taji yayi mata wata magana ba koda asubah da ya shigo tashinsu lafiyar Allah suka gaisa babu wani abu a tare dashi ya fita daga dakin, sosai hakan yayi mata dad'i dama bata so ya dinga ta'ba ta yana tayar mata da sha'awa tafi so suyi nesa da juna har Allah yasa su rabu ....Yini tayi cikin walwala dan har palo ta fito ta zauna tana kallo ita kuma halisa taci kwalliya kamar itace amaryar sai shige da fice take tsakanin kicin da dainng an shiryawa maigida girki iri-iri kuma sai jan Naja'atu take da hira, to itama ganin Halisan ta dawo da sigar son a zauna lafiya sai ta saki jikinta tana amsa mata jefi-jefi!
Koda maigidan ya dawo ya gansu suna hira ga yaran suna zaune a kusa dasu, sai ya shiga mamaki sosai ikon Allah yau Halisa da Naja'atu ne a zaune a guri guda suna hira harda dariya! kyataccen murmushi ne a fuskarsa ya shiga kallonsu yana jin dadi...Halisa da sauri ta iske inda yake ta kar'bi abubuwan dake hannunsa tana masa barka da zuwa, ita kam naja'atu sunkuyar da kanta tayi ba tare da wata cikakkiyar kulawa ba tayi masa barka da zuwa.
Ya amsa babu yabo babu fallasa ya kama hanyar dakinsa...Yau kwalliyar da Halisa tayi ta tafi da imaninsa sosai Halisa 'yar gayu ce gashi ta iya ado da d'inkunan banza atamfa ce a jikinta riga da sket amma anyi mata dinki banza dan gabadaya saman rigar net ne brest dinta duk a waje ga wani masifaffan kamshin turare da takeyi...Halisa duk da ta san da cewar ba a cikin kwanakinta take ba hakan bai hanata bashi kulawa ba saboda tana so ta sake wanke kanta a gurinsa ta gane ba da asiri kad'ai zata tsaya ba dole sai ta had'a kissa da siyasa sannan bukatarta zata biya.
A
Nasa 'bangaran kuwa shima bai hanata tattalinsa ba dan sabida ganin wacce alhakin hakan ke kanta bata wani nuna yana da muhimanci ba a gurinta shiyasa ya kyale Halisan take cin karanta babu babbaka
Naja'atu ganin sun kwashe sama da rabin awa a daki basu fito ba sai taji zuciyarta nayi mata sake'sake! dan sabida tasan baya dogon zango a daki yake fitowa yaci abinci amma yanzu sun kai minti talatin basu fito ba.
Ranta ne ya 'baci! tayi d'if! a gurin yaran sai hayaniya suke mata akam..Koda suka fito kin kallonsu tayi tana dai kallonsu ta gefan idonta suka nufi gurin cin abinci yaran ma suka mike suka nufi gurin suka zauna.....Ita kuwa ko motsi ba tayi ba a gurin ta tsirawa tv ido kamar kallo take nan kuwa mugun haushin halisa ne ya cika mata zuciyarta....Halisa cikin kissa tace"Naja'atu ki taso muci abinci mana.
Shuru tayi kamar ba taji ba.Halisa ta daure ta sake yi mata magana, kai tsaye tace"Kin san bana cin sakwara wallahi naga kamar ita kikayi ko" Halisa tace"Ayya wallahi na manta amma ai ba ita kadai nayi ba akwai jollop din taliya tare da dankali nasan za tayi miki.
Murmushi tayi kamar gaske tace"Wai gaskiya anty Halisa jollop din taliya bata dame ni ba dama dai da miya ce to da sauki."
Mugun takaici ya turnuke Halisa sai kawai taja bakinta tayi shuru ta cigaba da zubawa yaran abincinsu.
Shi kuwa Abba duk yana jinsu baice musu komai ba, ya ajiye wayar da yake dubawa yayi bisimillah tare da fara cin abincinsa........Naja'atu mikewa tayi daga inda take zaune ta nufi d'akinsu Saddiqa, ta wutsiyar idonsa ya bita da kallo yana mamakin halinta sai ana zaune kalau da ita lokaci guda ta burkice jiya dai lafiya lau suka yini amma tunda aka wayi gari ya rasa gane kanta, abinci ma tayi masa k'aura saboda wani dalili nata.
Bayan sun kammala cin abincin Halisa da yaran palo suka koma suka cigaba da kallon tv shi kuwa Abbah Abbas dakinsa ya nufa, ko minti biyar baiyi ba a ciki ya fito, Halisa na kallonsa ya nufi dakin da take... girgixa kanta tayi cikin zuciyarta tace"Duk wannan kulafucin naka sai yarinyar nan ta zama haramiyarka.
Samunta yayi tana kuka yayi tsaye a kanta tare da kiran sunanta, hannu tasa tana goge fuskarta ta kasa dagowa ta kalleshi...Yace"Kin 'ki cin abincin Halisa duk da kokarin da take miki kin watsa mata 'kasa a ido to inaso yanzu ki fada min abinda kike so kici tunda dai nine bakya so na huta sai na fita na siyo miki.
Zumbura bakinta tayi tace"Bana bukatar komai sai abu daya kuma nasan ba zakayi min shi ta dadin rai ba." Yace."Ki fada min kome kike bukata insha Allahu idan ina da iko dashi zanyi miki."
Tace"Abbah tunda ka samu biyan bukatarka a kaina me zai hana ka rabu dani naje na auri dai-dai dani."
Yace."Okey dama abinda yake damunki kenan kike ta nukufurci.?
Dauke kanta tayi tana shakar hanci.
Yace."Ki rubuta ki ajiye cewar ni Abbas banga abinda zai sanya ni na rabu dake ba ni dan halak ne!
Ki sani abu daya zakiyi min a duniya na iya rabuwa dake kuma bana fatan kiyi min abun har abada dan haka idan zaki samu nutsuwa ki samu idan kina ganin zaki cigaba da tayar hankalinki gami da yiwa kanki horon yunwa to sai ki mayar da hankali ni dai nasan ko a lahira Allah ba zai tuhume da hakkinki ba tunda nasan ina iyakacin bakin kokarina."
Yana kare maganarsa ya kama hanya ya fita daga dakin ranshi a tsananin bace!
Halisa ganin ya fito ransa a 'bace! sai wani farin ciki ya saukar mata a zuciya ta girgiza kanta cikin ranta tace"Insha Allahu kun dinga samun sa'bani kenan har mai afkuwa ta afku..Hanyar fita ya nufa ta bishi da kallo tare da dora kafarta kan daya tana girgizawa.
Naja'atu kuwa yana fita daga dakin kwanciya tayi ta cigaba da share hawaye ta rasa wane irin mayen mutum Allah ya hadata dashi, ance ba'a sonsa ba'a son zama dashi ya nace sai kace kaska aikuwa zata shuka masa rashin mutunci wallahi.