Sashe 76
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya dan sauke ajiyar zuciya yana sake jin wani irin tsanarta na d'arsuwa a zuciyarsa yace."Kada ki damu tun ranar da kika tura min text na datse igiyar aurena guda daya dake kanki ina fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi kiyi hakuri ki dawo gida saboda samun kwanciyar hankalin iyayenki." Jin abinda yace yasa taji wani sanyi na saukar mata a zuciya shima bash dake kusa da ita murmushi yayi kawai ya cire wayar daga kunnanta ya kashe ya mikawa me ita...Abbah magaji rasa bakin magana yayi ya dinga binsu da kallon takaici.....Bash ya mike da fadin "Bari nayi wanka ina tsammanin tare zamu tafi inaso naje na nuna kaina a matsayin wanda zai auri Naja'atu." Abbah magaji uffan bai ce masa ba har ya shiga toilet dinsa.....Naja'atu ita da Munira suka fita daga dakin cike da farin ciki bukatarsu ta biya, shi kuwa bayan fitarsu daga dakin guri guda ya tsirawa ido kawai yana kallo babu shakka hukuncin da abokin nasa ya yanke baiyi masa dadi ba ko kadan! to amma yana adduar Allah yasa haka shine yafi alkairi Naja'atu kuwa ya tabbata da cewar sai ta girbi abinda ta shuka da hannunta yanzu shi dai zaiyi kokarin sadata da iyayenta shikkenan sai ya zare hannunsa daga kanta idan Allah ya kaddara auranta da Bash to shi kam dan kallo ne babu abinda ya shafe shi duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka.
Abbah magaji yana zaune Bash ya kintsa jikinsa cikin sabuwar shadda galila mai kalar sararin samaniya (sky blue) dinki tazarce da dogon hannu mai link yasa hula irin ta kanawa sai kace wani mutumin arziki yayi wani irin kwarjini da kamala, Abbah magaji na zaune yana ta mamakinsa babu shakka yaron ya shirya tsaf domin zuwa ya yaudari su baba malam to idan ba hakaba meye nasa manyan kaya harda hula, Bash na daura agogo ya kalli Abbah Da murmushi a fuskarsa yace."Nasan duk wanda ya gan ni cikin famliy naku zai yaba dani da cancanta ta a matsayin wanda zai auri Naja'atu ina fatan kai ma a matsayinka na makusancinta ka sanya mana albarka a cikin al'amarin."
Abbah Magaji na kallon rashin kunya da tsabar jahilci shikkenan daga anyi saki kuma sai a shiga neman aure ai ya bari yarinyar tayi iddah tukkuna....Yace."Bashir da alama baka da ilimin addini waye yace maka ana neman aure cikin iddah ai ka bari yarinyar tayi iddah tukkuna in yaso sai kayi wata magana....Bash yace"A'a da zafi zafi akan bugi karfe alhaji gwara naje na gabatar da kaina in yaso koma meye sai ya biyo baya." Abba magaji ya bishi da ido cike da tsantsar mamakin maganarsa gaskiya jahilci bai yi ba.
Abbah Magaji motarsa ya shiga a maimakon Naja'atu tayi masa kara ta shiga motarsa sai ta nuna jin tsoransa yana kallo ta zauna gaban motar Bash ko kallonsa ta'kiyi takaicin haka yasa yaja motarsa da karfi... ya bar gurin..
Bash na murmushin samun nasara yaja tasa motar suka dauki hanya......sai da sukayi nisa so
sai ya kalleta yace."Baby wannan dan uwan naki fa na fahimci baya k'aunar alaqa ta dake ko kad'an!." murmushin takaici tayi tace."Bash bana tsammanin Abbah magaji zai kaunace ka dan shine babban abokin Abbah Abbas to kaga kuwa dole ya tsaneka." Cike da rashin damuwa yace."Hakan bai dame ni ba mutukar kina sona iyayenki sun amince dani ai bukata ta biya." Jin abinda yace yasa gabanta ya fadi addua ta shigayi kan Allah yasa su baba malam su amince mata da auran Bash dan yanxu gabadaya shine babban burinta.
Alhaji Sama'ila da Baba Malam dashi uban gayyar ne a zaune a guri daya suna tattaunawa kan al'amarin da yake faruwa.
Alhaji Sama'ila yana ta nuna rashin jin dadinsa dangane da hukuncin da d'ansa ya yanke a kan naja'atu shi kuma Baba malam yana nuna masa hakan ba laifi bane dan Abbas ya saki naja'atu domin samun maslaha ga junansu ya kuma nuna masa shi bai ji takaicin faruwar hakan ba dan dama ya riga ya barwa Allah al'amarin yana ganin tunda hakan ya kasance to shine alkairin..........Dukaninsu suna zaune suna jiran tsammanin dawowar Abbah magaji tare da Naja'atun.........To Sai daf da magariba suka iso, Abbah magaji bai saurare su ba ya gyara parking na motarsa ya fito ya nufi massalacin dake jikin gidan Alhaji.....Naja'atu da kyar ta iya fitowa tana ta 'boye kanta a cikin mayafi gabanta kuwa sai faduwa yake...Bash ganin Abbah magaji na alwala a cikin massalaci sai shima kamar gaske ya nufi inda yake Naja'atu kuwa tsayuwa tayi ta rasa ina zata shiga gidan Alhaji ko idan baba malam...Munira tace"Wai tsayuwar me mukeyi ne? haba duk kinbi kin damu kanki dan Allah ki daina jin tsoron abinda zai faru babu fa wanda ya isa yayi miki abinda Allah be miki ba ki saki jikinki dan Allah."
Hawaye ta d'an goge tace"Mu shiga gidan Alhaji munira ba zan iya shiga gidanmu ba ina jin tsoron Baba Talatu da Abbah Magaji kada ya shigo ya doke ni." Munira tace"To muje gidan Alhajin tunda kinfi amincewa da nan." Kai tsaye suka nufi gate gidan tana tafiya tana hard'ewa saboda matsatstsen siket d'in Munira dake jikinta gashi ba hijab bane mayafi ne a jikinta shiyasa duk ta tsargi kanta!
Abbah Abbas da Alhaji sune suke kokarin fitowa daga gidan Naja'atu jin 'kamshin turaransa yasa ta zabura! da sauri ta matsa gefe tana kauda kanta!
Abbah Abbas karaf! idanunsa ya sauka a kanta duk da ta 'boye fuskarta hakan bai hanashi ganeta ba kallon zatin jikinta kawai ya fahimtar dashi itace! cike da mamaki yake kallonta kwana uku kacal a jos ya mayar da ita watsatstsiya wane irin suttura ne wannan a jikinta sun fito mata da jikinta! da sauri ya kauda kansa ya wuce domin shiga massalaci.....Tana ganin wucewarsa ta zube 'kasan gurin tana gaishe da Alhaji dake kokarin wucewa dan shi sam be ganeta ba, Jin muryarta yasa yayi saurin juyuwa yana amsawa da fad'in "Naja'atu kece."? murya na rawa tace" Eh." yace."To masha Allah ku shiga cikin gidan mu zamu shiga massalaci domun gabatar da sallah." A sanyaye tace "To" tana kokarin mikewa Alhaji kasa barin gurin yayi har sai da yaga sun shiga gidan tukkuna ya nufi massalaci zuciyarsa sam babu dadi dangane da faruwar al'amarin.
*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu toga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account 0542382124...Binta umar gtbank..idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
Mddbhrmbn49
Halisa da Yaya Ramlatu ne a zaune a palon Hajiya sai hira suke cikin nishadi sunayi suna ciye ciye kana kallonsu zaka fahimci cewar suna cikin walwala da farin ciki...Hajia Abu lokacin ta hau sama domin daura alwala su kuma bayan barinta gurin ne suka tsiri gulmar abinda ya faru inda Yaya Ramlatu ke fad'in"Ai wallahi Halisa na sake gazgata al'amarin mutumin nan da 'yar shagamu ta kai mu gurinsa kinga ni dai duk abinda ya fad'a zai faru gashi ya kasance gaskiya kiyi kokarin siyawa 'Yar shagamu turaman atampopi muje tare dake gidanta mu kai mata domin mu sake nuna mata jin dadi da farin cikinmu sabida kin san hausawa nacewa dan towon gobe ake wanke tukunya nan gaba zamu iya zuwa mu sake neman wata alfarmar gurinta shiyasa nake so ki kyautata mata sosai dan itama taji dadi."
Halisa na shirin yin magana su Naja'atu suka shigo palon..Naja'atu ganin Halisa da Yaya Ramlatu a zaune yasa jikinta yayi sanyi da kyar suka shiga palon suka zauna cikin kokarin aro jarumta tace"Anty Halisa sannunku Yaya Ramlatu Ina wuni."? babu wanda ya amsa mata a cikinsu Halisa sai binta da ido take tana ta'be bakinta, ita kuwa Munira ganin Naja'atu tayi musu magana basu amsa ba yasa ta kama kanta 'kafarta ta d'ora kan d'aya tana taunar cingum had'e da duba tamfatsetsiyar wayarta....Yaya Ramlatu ta ri'ke bakinta tace"Oh! ikon Allah ke kuma Naja'atu garin yawon karuwancin naki kika samo wannan mara kunyar yarinyar daka ganinta 'yar isaka ce da wasu idanunta a tsaye irin na marasa kunya."!Munira ta zubawa Yaya Ramltu idonta ranta a 'bace da jin irin mugwayen kalaman da take jifanta dasu.
Za tayi magana Naja'atu ta rufe mata bakinta tace"Dan Allah kada ki kulata ki kyaleta duk wanda ya wulakanta wani kansa ya wulakanta." Halisa tace"Ke Naja'atu Yaya Ramlatu kike kokarin gayawa magana? ai gaskiya ta fad'a a kanki dake da kawarki idan ba yawon karuwanci kika tafi ba to me ya had'a ki da wannan me wankakken idon." Munira ta nuna Halisa da hannu tace"Wallahi kika sake kirana da wannan kalmar sai na wanke ki da mari zan nuna miki tsageranci na yanzu." Halisa ta ri'ke bakinta tana kallonta tace"Sai ki mareni mara kunya kawai.
Naja'atu tace"Kinga Halisa mu ba tashin hankali ne ya shigo damu gidan nan ba saboda haka dan Allah ki fita daga sabga ta kada ki sakeyi min magana tunda dai yanzu bani da al'aka dake." Da sauri Ramlatu tace"To dan ubanki tashi ku fice mana daga gida tunda da bakin ki kin fad'a baki da al'aka damu ubanki kika shigo kiyi mana a gida." Naja'atu jin zagin yayi yawa yasa ta fashe da kuka da fad'in "Ki daina zagina dan banga abin zagi ba anan." Ai kamar 'kara tunzura ta take ta dinga zabga mata zagi tana ambato sunanan Baba Malam tana cusa masa ashar!