Sashe 107
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin rufa rufar da take bashi da amfani sai kawai ta fad'a masa yanda al'amarin ya kasance, takaici yasa shi yayi mata dukan tsiya da blet kuma ya daina kulata, ashe duk hukuncin da yayi mata bai hakura ba mota ya cika da sojoji ya sata a gaba suka nufi gidan *'Yar sa'adu me kayan mata*.....'Yar sa'adu na tare da baki kawai sukaji ihun yara ga unguwar ta cika da kururuwar motar sojoji ai babu shiri ita da matan da take a gidan suka fito waje, ganin zaratan sojoji sun durfafo kofar gidanta yasa ta kusa sakin fitsari a wando! a tsaroce tayi nufin komawa cikin gidan gabanta na wani irin faduwa ganin matar sojan data zo ta hada mata magani makwanni biyu da suka wuce babu shakka akwai abunda ke faruwa, takalmin kafarta ne ya gurde ta tsaya zata gyara matar soja da sojojin dake bayanta suka karaso gurin ba tare da jin tsoron komai ba matar ta nuna 'Yar Sa'adu da fad'in "Gata nan itace matar da siyar da magunguna kan kudi masu yawa."
'Yar sa'adu ta diririce ta hau inda inda, Sojan dake kusa da ita ya taska mata mari da fad'in "Kece kike cutar mata ko kin zama 'yar damfara ki tara mata ki dinga kar'be musu kudi kina siyar musu da abunda zai cutar dasu ko to yau sai kin gane kuranki." doguwar bundigar dake hannunsa ya dora mata a wuya a tsawace! yace."Wuce muje yau kin fad'a komar mu sai kin gane baki da wayo." Yar Sa'adu kuka ne ya kufce mata jikinta ya shiga kyarma! sai ta shiga d'aga hannunta sama tana basu hakuri....Kafin kice kwabo gurin ya cika da jama'a, su kuwa matan da suke tare da ita ganin an shigar da ita mota yasa da sauri kowacce ta fece! tsoro da tashin hankali duk ya cika musu zuciya.
****
Watannin Naja'atu biyu da dawowa gida inda ya kama wattanin cikinta shida kenan yanzu cikin nata ya fito ana d'an ganinsa amma ba sosai ba kasancewarta doguwa yasa cikin bai bayyana kansa ba sai dai amma ita kadai ta san abinda take ji a jikinta, kusan kullum sai ta 'buya a daki taci kukanta ta koshi haka kawai Bash ya had'ata da wahala ya gudu ya bar mutane da jigilar d'ansa duk sanda ta tuno wannan al'amari takan kwana ta yini cikin kunci da damuwa, mussaman idan taga yanda Abbah Abbas ke hidima da ita da cikin jikinta duk sai hankalinta ya tashi ta shiga nadamar abinda tayi masa a baya, itace ta zama sanadiya gurin lalacewarsa cikinsa gashi ita taje ta dauko ciki ta kawo masa wahala, yanzu saboda ita kullum da safe kafin ya tafi harkokinsa sai yazo ya kofar na'isan sannan bayan ya dawo daga kasuwa ya sake dawowa gabad'aya jama'ar gidan sun fahimci saboda ita yake wannan sintirin dukkaninsu su gane ya damu da yarinyar da cikin jikinta, sai hankalinsu ya kwanta mussaman hajia da Alhaji burinsu kawai yarinyar ta haihu lafiya sai ai maganar kome domin su a ganinsu yanda yake nuna damuwarsa a kan yarinyar suna ganin kamar yana so ya mayar da ita gidansa ne. wanda shi kuma kwata kwata ba haka bane a cikin zuciyarsa haka kawai take bashi tausayi da ita da abinda ke cikinta shiyasa ya mayar da hankalinsa a kanta duk da bashi ne keda alhakin kula da itaba , a yanzu dai cikin zuciyarsa bai dauki Naja'atu a matsayin komai ba face 'Yarsa.
Yau asabar yana zuwa da wuri dalili kenan daya sa takasa komawa baccinta na safe ta fito palo ta zauna tana jiran zuwan nasa, lokacin daya shigo hajia na sama ita kadai ya samu a zaune tana kallon tashar sunna tv Malam Aminu Daurawa na gabatar da shirin tambaya mabudin ilimi, a nutse ta amsa masa sallamarsa ta dan gyara zamanta a hankali tana gaishe shi....Ganin yanda take ya mutsa fuska ne yasa ya mayar da hankalinsa kanta a nutse yace."Ina fatan kina lafiya ya jikinki."?
Kamar za tayi kuka tace"Da sauki inasu Mussadiq." Yace."Suna gida lafiya lau ina hajia."?
Tana sama." Tafada tana kallon kasan kafafunsa, kai tsaye saman ya nufa sai ta bishi da kallo tana girgiza kanta ita kam a duniya akwai mutumin dake sonta irinsa kuwa? gaskiya babu.
Ya kai mintina goma sha biyar a saman ya sakko da sauri yana duba agogon hannunsa, dan kallon gefan da take zaune yayi ba tare da yace wani abu ba ya kama hanyar fita.....Da kyar ta kira sunanshi, tsayawa yayi yana kallonta....Murya na rawa tace."Ina so mu gaisa dasu Mmn Sajida matar nan data taimaka min."
Jim! yayi kafin yace."Yanzu dai sauri nakeyi ana jirana idan nazo da yamma sai ayi yanda kikace." tace."To Abbah Allah ya bada sa'a."Ya amsa yana kokarin futa daga falon.
Sai bayan futarsa ne ta shiga tunanin yanda za'ayi ma tayi magana dasu Mmn Sajidan tunda lokacin data barsu daga ita har Mmn Ladin babu me waya a cikinsu , wannan dalilin ya sanya jikinta yay sanyi taso da hanyar da zata sadata dasu da sun gaisa da juna ta 'kara yi musu godiyar abinda sukayi mata.
To koda ya dawo gidan da Yamma batai masa maganar ba shima al'amuran dake gabansa sun mantar dashi, sai kawai ya ajiye mata abubuwan da ya saba siyo mata ako wace rana yay tafiyarsa gurun iyalinsa.
Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan.....Yana tsaka da shiryawa domin tafiya kasuwa kira ya shigo wayarsa, Zainab yasa ta miqa masa wayar ya daga tare da karawa a kunnansa.......Mmn Sajida dake d'aya bangaran ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da sauri tace"Sannu ina kwana sunana Mmn Sajida daga jos." Sai yayi saurin duba number yana so ya tabbatar, ya mayar da wayar kunnansa yace." Lafiya kalau Mmn Sajida na gane ina fatan kuna lafiya."?
Ta amsa da lafiya lau Alhaji muna fatan kunje gida lafiya." Yace."Lafiya lau alhmdullhi." Tace."Dama na kira ne idan da dama inaso a bani Naja'atu mu gaisa wallahi har yanzu alhinin rabuwa da ita bai sakemu ba." Yace."Ayya! kada ki damu insha Allahu anjima kad'an idan naje Inda take zan bata wayar ku gaisa." Tace."To Alhaji mungode sai anjima." Yace."To masha Allah." Kashe wayar yayi ya ajiye kan drowar dake gefansa, Zainab tunda taji ya ambaci sunan Naja'atu ta sanja fuska dan har sai da ya fahimci sauyawarta alhalin labari take bashi amma lokaci guda yaga ta 'bata rai! kwanciya ma tayi ta juya bayanta kishin Naja'atu naso ya dargagaza mata zuciya.
Sai da ya gama shiryawa tsaf ya juyo yana kallonta a nutse yace."Zainab lafiya dai ko.? ba tare data jiyo ba tace."Lafiya lau bacci zanyi shiyasa na kwanta." Yace."Okey ni zan fita." Tace"A dawo lafiya." ya amsa a nutse ya bude kofar dakin ya fita, mikewa zaune tayi tana jan tsaki! kai gaskiya ta gaji da wasiwahsi gami da takurawa zuciyarta dole yau idan ya dawo ta tambayeshi tsakaninsa da Naja'atun nan da ya damu da ita idan mayar da ita zaiyi gwara ya fad'a musu su ya daina wani 'boye-'boye...........
*Littafin na kudi ne.....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karanta littafin ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
69*******Lokacin daya isa gidan Alhajin Naja'atu na daki tana baccinta na qa'ida dama idan tayi sallar asubahi komawa take ta kwanta tayi ta bacci watarana hajia da kanta take shiga dakin ta tashe ta sannan fa tayi break fast.... tunda cikinta yayi kwari take wannan bacci mara qa'ida daddare ma tana idar da sallar isha'i take kwanciya, hajia da taga abun yayi yawa cewa tayi aje asibiti a dubata, Yaya Ramlatu tace" Lafiyarta lau kawai yanayin cikin nata ne yazo a haka dama ana samun ciki mai sanya baccin tsiya ta ce ta kwantar da hankalinta bacci lafiya ne. bana cuta ba to wannan maganar da Yaya Ramlatu tayi itace tasa hajian ta kwantar da hankalinta amma dai duk rintsi da daddare bata barinta ta kwanta sai ta tabbatar ds taci abinci ta koshi tukkuna.
Koda ya shigo gidan bai samu kowa ba, wai ashe sun tafi jana'izar 'yar 'kanin Hajia Rabi dake mandawari, da yake mutuwar ta dare ce shiyasa bashi da labari sai daya ya shigo gidan tukkuna maigadi ke fad'a masa..........
Juyawa yayi da niyyar fita daga gidan sai kuma yayi wani nazari, yana tunanin ko zasuje gidan mutuwar bai zama lallai suje da ita ba shima yasan a daidai lokacin take baccin data saba, dan wani lokacin idan yazo baya samun ganinta sai dai kawai ya tambayi hajia lafiyarta.
Shuru falon lokacin daya shiga, bai jira
komai ba ya nufi dakin da take..........Kallon sharia yayi mata yayi saurin kauda kansa, yanayin kwanciyar da tayi taso ta saka shi cikin wani yanayi yayi saurin kawar da abun daga cikin ranshi...Ya karasa bakin gado tare da tsayawa saitin kafafunta yana kallon fuskarta dake kallon rufin dakin, da yake irin kwanciyar da ba'a masu ciki suyi ita tayi (rigingine) ta tayar da kafafunta sun taka gadon kana ta d'ora dukkanin hannayenta a saman cikin nata......Sunanta ya shiga kira yana korar shad'en d'in da yake ra'barshi....idan da baiyi wa Mmn Sajida al'kawari ba da yana ganin tafiyarsa zaiyi dan tsayuwarsa a dakin na nema ta haifar masa da matsala.
Kamar a mafarki taji muryarsa na kiran sunanta! ta bud'e idonta da sauri! shi take gani dishi dishi a idonta, shi kuwa yanayin yanda yaga idanunta sun sauya yasa ya dauke kansa yana kallon gefe guda, yace."Tashi ku gaisa da Uwar dakin ki ta jos dazu ta kira waya tana so ta dubaki."
Da sauri ta miqe zaune jin cewar Mmn Sajida ta kira waya...Wannan gaggawar miqewar da tayi yasa yaron dake cikinta ya kai mata wani irin naushi! yayi fushi! ya samu guri guda ya dunkule mata!
Rintse! idonta tayi murya na rawa tace"Wayyo cikina."!
Kafin kice me zufa ta tsatstsafo mata a saman goshi!