Sashe 8
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*PEGEN YAU NAKU NE*
*My Son Najib Sa'id*
*Abue Sale alqurami*
*Bashir Saleh*
*Umar Abbas Yusif*
*Muhammad Karim*
Ina mutukar godiya da kulawarku a kaina da 'kokarin yi min sharing ina rokon Allah ya sadaku da alkairin duniya dana lahira Allah ya za'ba muku abinda yafi alkairi a rayuwarku
~~~~~~~~~~~~~~~
A takaice dai duk wannan fad'in tashin dasu Halisa sukeyi a kan Halimatu ba suyi tasiri a kanta ba, saboda halimatu ta kasance mace mai ibada kuma dukkaninsu bata nufe su da sharri ba shiyasa kullum Ubangiji ke kara kareta daga sharrin su da makircin su, duk wani asiri da sukeyi baya tasiri idan ma yayi baya dadewa yake karyewa, ta inda Halisa take samun galaba akan Abbas din shine ta gurin shaye-shayen magungunan mata to tana d'an janye hankalinsa watarana dan gaskiya irin magungunan da Halisa take sha suna da tsada har dana turawa sha take ita dai burinta ta janye hankalin Abbas din ya wulakanta matarsa uwar 'yayansa, abinda Halisa bata sani ba kuwa shine irinsu Abbas asiri baya saurin kama su idan ma ya kama su to baya wani tasiri a jikinsu zai karye! saboda Abbas mutum ne me yawan azkar da karatun al'akurani mai girma gashi sallahr asubah bata wuce shi, shiyasa duk wani asirin da suke masa baya zama a jikinsa.
Halisa tun haihuwarta ta farko take samun matsala daga zarar ta samu ciki baya yin kwari zai zube, ta shiga tsananin damuwa da tashin hankali! ganin 'Ya'yan Halimatu sunyi wayo har sun soma zuwa makaranta gashi mahaifinsu naji dasu yana yi musu hidima kamar hauka, ai babu shiri ta bazama yawon gidajen masu magani har gurin 'Yan bori zuwa take su bata magani tazo ta jika tasha, ta yini tana amai, da murkukusu, amma taki ta gane hanya madaidaiciya ta fawwalawa Allah domin shine mai bayarwa da hanawa, Kullum kokarinta ya za'ayi ta haihu ko ta halin 'kaka.
Abbas ganin ta tashi hankalinta dan har ramewa tayi sai yayi musu viza domin zuwa 'kasa mai tsarki su roki ubangiji hakan be mata dadi ba taso ita ya kaita kasar waje likitoci su dubata idan ma dashe za'ayi mata zata amince ita gani take idan sukaje saudian ba zata sanja zani ba!
Gabadayan su dashi da iyalinsa suka nufi kasa mai tsarki, Halisa ta dinga wani iyayi tana shige masa gani takeyi ai saboda ita aka zo kasar!
Halima dai sai dai tayi mata dariya kawai dan ita wataran idan Halisa na wani abu har dariya take bata, tana kallonsu zasu shirya su fita ita da Abbas wai zasuje asibiti sai dai tayi musu fatan dawowa lafiya, ta lura shima mijin nasu na biyewa Halisan ne dan kawai a zauna lafiya.
Ita kuwa Naja'atu mugun haushin Halisan take ji dan ta soma hankali a lokacin, idan taga tanayi wa mamanta wani abu ranta 'baci yake sai tayi yun'kurin magana sai Halimatun ta hanata, sai dai tayi 'kwafa kawai! ita hakurin mamanta ta har mamaki yake bata, kuma a duk sanda za taga Abban nasu yana magana da Halisa sai taji haushinsa, tashi ma take ta bar gurin, wani lokacin kuma idan taga sun shiga daki da Halisan sun dade kuka take zuwa taci ta koshi! ta fito tana kumbura fuska, Halimatu ta gane yarinyar na kishinta shiyasa takejin ciwon abinda ake mata, ta kuma fahimci yarinyar za tayi kishi sosai dalilin da ya sanya take yi mata 'yar nasiha a fakaice!
Naja'atu kam jinta kawai take yi tana ganin kamar wani abun ma itace take bada goyon bayan Halisan nayi mata, 'kiri-kiri sai suna zaune a guri daya Halisa zata tsiri wasu abubuwa wanda suke sawa ta janye hankalin Abban nasu! duk sanda haka ta faru taga ya tashi yabi bayan halinsa ji take kamar zuciyarta zata babbake! ko ya fito bata kulashi idan yazo yana musu magana banza take dashi sai dai yai ta tambayar Halimatu ko wani abun ne yake damunta Halimatu tasan abinda take fad'a masa maganar ta wuce!
Naja'atu gabadaya daina walwala tayi ta daina sakin fuskarta, rashin kunya takeyi wa Halisa a duk sanda tasa mata baki a cikin maganarta dan Halisa akwai katsalandan daga zarar tazo taga suna hira da wasa da 'yan uwanta su Saddiqa da Mussadiq sai tazo ta dinga buga musu tsawa tana hantararsu, aikuwa dama a ciki take da ita, tace watarana suna wasa tazo tana yi musu tsawa!
Tace"Mu dan Allah ki daina zuwa kina takura mana muna maganarmu ke waye ya takura miki eye? ina cewa abinda kike so shi kikeyi saboda haka ki daina zuwa kina mana tsawa mtwsss!." Takarasa maganar tana jan tsaki.
Halisa ta fusata sosai hannu ta fitar ta tsinka mata mari tana d'ura mata ashar! sai ambato sunanan Baba malam take tana zagi!
Naja'atu ta dinga kuka tana fad'in "Allah ya isa ba kakana kike zagi ba naki kike zagi!
Halimatu tazo tana doke bakinta cikin 'bacin rai tace" Ashe baki da kunya Naja'atu." Tana kuka tace"Mamma kina ji fa tana zagin Baba Malam me yayi mata? wallahi sai na fad'awa Abbanmu." Kai tsaye ta nufi dakin da yake kwance yana bacci!
Halisa da Halimat suka bita da kallo cike da mamaki!
Halisa mamakin yarinyar take na mayar da uban wasu nata komai akayi sai tace Abbanta ko a gidan ubanwa ya zama Ubanta oho.
Yana tsaka da bacci yaji kukanta a kansa, ya bude idonsa da sauri! yana kallonta a tsaye a kansa tana goge fuska hawaye wani na sake zubowa, mikewa yayi zaune ya kamo hannunta ya zaunar kusa dashi.
Cikin tausasawa yace."Waye ya saki kuka." ?
Cikin shashsheka tace"Gata can Anti Halisa muna wasa da dariyarmu tazo tana hantarar mu wai sai mun tashi mu bata guri zatayi kallo, shine dan nayi magana ta mareni har da zagin Baba Malam."
Ransa ya 'baci!
Yace." Kan wane dalili zata tashe ku a guri kuna wasa? saboda za tayi kallo sai ta hantareku! hannunta ya ri'ke suka mike a tare suka fita palon
Halisa da Halima na tsaye sai musayar yawu suke Halisa na fad'in "Wannan iskancin da 'kanwar taki take yayi yawa haka kawai saboda samun guri ta mayar da uban wasu nata to tun wuri ki fada mata ba ubanta bane kada ma ta dauka tanada gadonsa."
Halimatu ta bude baki kenan za tayi magana ta hango fitowarsu yana rike da hannunta, Halisa ta kallesu ranta idan yayi dubu ya 'baci!
Hura hanci ta shigayi tace"Au! zuwa tayi ta taso ka daga baccin."?
Ya 'bata fuska sosai yace."Koda bata tasheni ba dama dai-dai wannan lokacin nayi niyyar tashi, shin me yaran nan suke miki kullum kike matsa musu bakya barin su su huta."!
Halisa ta rik'e bakinta cikin mamaki take dubansa!
Yace."Magana nake miki." Ganin yanda yasha kunu ne yasa ta sassauta murya saboda tasan halinsa sai tace"Kawai dan nace su tashi su bani guri zanyi kallo shine fa yarinyar nan ta hau yi min rashin kunya harda zagina."
Da sauri tace"Ni wallahi sharri tayi min ban zageta ba." Halisa tace"To nayi miki karya ko." Zumbura mata baki tayi ta murguda mata shi!
Halisa ta shiga jijjiga kanta tana mamakin saken da yarinyar ta samu a gurin maigidan, kauna da son da yakewa yarinyar ta lura ko 'yayansa bayayi wa."
Yace."Kawai saboda zaki zauna kiyi kallo sai ki tashesu mai suka tsare miki! bana so ki sake hantarar min 'yaya duk wani abu da nake nema a duniya saboda su nake nemansa, kafin Allah ya bani sai da na cire tsammani dan haka dole ne na kyautata musu dan bana son abinda zai 'bata musu rai! duk abinda suke su zasuyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar yanda kema kikeyin abinda kike so."
Halisa takaici kamar ya kasheta, har ta bud'e bakinta zata ce "Ai ita wannan d'in da kake magana a kanta ba 'yar ka bace.......Sai kuma ta sanja shawara, tace" Shikkenan me 'yaya nima Allah ya bani." Tana 'kare maganarta sai ta fashe da kuka ta nufi daki....Jikinsa ne yayi sanyi kuma, Halimatu ta kalleshi murya na rawa tace"Haba Abban Naja'atu ba haka ya kamata ka yanke hukunci ba! kasan kowaye akayi wa haka dole yaji rashin dadi, yarinyar nan Naja'atu itace tayi mata rashin kunya kamata yayi ka fara hukuntata tukkuna."
'Dan ya mutsa fuskarsa yayi kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa, hannun Naja'atu dake cikin nasa ya saki ya juya ya nufi dakin da Halisan ta nufa
Ita kuwa Naja'atu bata so hakan da yayi ba taso ya kyaleta taje tayi kuka taji ciwon a ranta kamar yanda take yini tana 'kuntatawa mamanta rai to itama yau ta d'and'ana taji.
Halima ta rufeta da fad'a kan abinda tayi tace"Wallahi duk sanda na sake ganin Kinyi mata tsaki sai ranki ya 'baci ko an fada miki sa'arki ce." ?
Kuka tasa ta nemi guri ta zauna tana fad'in "Mama kina ji fa tana zagin mahaifinki Baba malam Kinyi shuru dan nayi magana sai kice nayi laifi ."
Jikinta a sanyaye tace"Dan ta zage shi sai me? ni nasan ba Ubana ta zaga ba nata take zagi saboda haka na fada miki babu ruwanki da ita har mu bar 'kasar nan." Shiru tayi kawai ba tace komai dan gaskiya ita ba zata dauki cin kashi da wulakancin da Halisan keyi mata ba
haka suka cigaba da zaman doya da manja tsakanin Halisa da Naja'atu babu sassauci kowa najin haushin dan uwansa, Naja'atu taci alwashi kan cewar duk sanda Halisa ta sake kuntatawa mamanta rai to itama sai ta 'kir'kiri abinda zai janyo musu fad'a a tsakaninta da Abbansu, Halisa tunda taga take-taken Naja'atu da irin iskancin da take mata sai ta shiga taitayinta ta rage yiwa Halima wasu abubuwan na rashin arziki badan komai ba sai dan sanin matsayin Naja'atu da tayi a zuciyar maigidan nasu, tasan idan ta tsananta ranta ne kawai zai 'baci a banza.