Sashe 3
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakuri take bashi tana share hawaye, ransa ya a 'bace! ya futa daga soron ya barta a tsaye hannunta ri'ke da tabarma.......To tun daga ranar Sakina ta samu lafiya a gidan Yanzu Ramlatu ta daina yi mata gori da kallon banza amma dai duk da haka idan 'yan wulakancin na kusa tana ta'bawa sai dai kawai ta kau da kanta domin dai a zauna lafiya.
****
Irin kulawar da Abbas keyi kan Halimatu ya sanya iyayensu suka ga kamar sonta yake yi, shi kuma ba haka bane a zuciyarsa kawai yana tausaya mata ne a matsayinta na mace kuma mai nakasa, Halima bata da lafiyar k'afa sosai kafarta ta dama ta samu tawaya tun tana yarinya anyi magani na hausa dana Asibiti tafiyarta bata dai-dai ta ba, sai kawai suka hakura suka bar mata hallitarta da alama haka Ubangiji ya hallice ta, kafarta ta dama itace take da nakasa ta inda in tana tafiya take jefata, Amma a fuska Halima bata da muni kyakkyawa ce sosai mai madaidaicin tsayi! komai nata cikin nutsuwa take gudanar dashi.
Magaji ya fitar da matar aure A lokacin da iyayensu suka bukata, shi kuma Abbas din har yanzu ya rasa wacce zai tsayar a matsayin uwar 'yayansa!
Mutum ne mai ruwan idon tsiya ko wace mace ba tayi masa ba!
Da kyar da ya tsayar da Halisa a matsayin matar da zai aura gidansu na bayan layi! kuma Halisa kawar Halima ce tare ma suke tafiya makaranta, Allah sarki Halima tunda Taji labarin Abbas zai auri kawarta sai ta rasa nutsuwa komai nata ya tsaya cak! bata san tana sonsa ba sai da taji zaiyi aure! damuwa ta shiga sosai ta rage walwala har sai da iyayenta suka gane!
Da yake Baba Talatu macece mai saurin fahimtar abu nan da nan ta fahimci abinda ke damun 'yar tata!
Ta sameta tayi mata fada da nasiha sosai tace"Kada ta janyowa kanta lalura mutum baya ta'ba auran mijin da bana sa ba, dan haka ta cigaba da addua Allah itama ya za'ba mata miji nagari." Duk da wannan nasihar da mahaifiyar ta tayi ma bai sanya ta daina damuwa ba, ita gani take waye zai aureta tana da nakasa (gurguwa) tana ganin watakila ma haka zata 'kare rayuwarta ba tayi aure ba.
Ita kuwa Halisa tunda ta fahimci Halima na shiga damuwa a duk sanda taje mata da maganar Abbas sai ta dauki d'amarar muzguna mata kullum kan hanyarsu ta zuwa isilamiyya sai tayi mata zancensa da irin soyayyar da sukeyi, Halima tayi shuru bata tanka mata, ita kuwa Halisa tai tayi mata dariya...........Akwai lokacin da Abbas yaje zance gurin Halisa ta tsare shi wai dole sai ya fad'a mata tsakaninsa da Halimatu! mamaki sosai ya kamashi Yace."Halimatu kanwata ce amma babu wata soyayya a tsakanina da ita." Halisa tace"To idan kai baka sonta ita tana sonka dan ba kaga halin damuwar da ta shiga ba lokacin da ta samu labarin abinda yake tsakanina da kai, dan haka gaskiya gwara kayi wa tufkar hanci tun kafin tafiyar tayi nisa duk da take kawata bana tunanin zan iya zaman kishi da ita."
Mamaki ya rufe shi da yake mutum ne mai tsare gida sai yace."Okey yanzu kina so ki nuna min ga yanda zanyi kenan?
Idan na fahimce ki kina so kice ke ba zaki zauna da Halimatu ba a matsayin kishiya ko me."?
Da sauri tace"Kwarai kuwa ai naga kusancin dake tsakanin gidanku da gidansu ne ina tunanin idan iyayenta suka fahimci halin da take ciki a kanka zasu ce ka aure ni kuma bana so gaskiya shiyasa nake so tun kafin tafiya tayi nisa kayi wa tufkar hanci." Ya girgiza kansa yana kallonta yace."Bari kiji Halisa ni ba irin mazan da mata zasu zauna suna tsarawa magana bane! abinda nasa kaina shi nake yi ke baki isa kice ga yanda zanyi ba, bani da ra'ayin zama da mace d'aya ki rubuta wannan ki ajiye bayan na aureki zan sake auran uku mutukar Allah ya bani iko saboda haka sai ki daura d'amarar zama da kishiya Halimatu kuma da kike magana na jawa kunne a kan tana sona to kin sanya ma naji sha'awar auranta zan aureku rana d'aya tunda dama 'kawayen juna ne." Da jin abinda ya fada sai ta mike a fusace! tace"Wallahi sai dai ka za'ba ko ni ko ita dan na rantse da girman Allah ba zanyi kishi da gurguwa ba."!!!
Ya bude bakinsa yana kallonta cikin tsananin mamaki! lallai Halisa muguwar jahila ce yanxu me bambamcin muskini da mai lafiya? saboda jahilci da hauka kishi ma sai ta za'bi da wanda za tayi!
Ya mike tsaye fuskarsa a murtuke yace." Tunda kin rantse ba zakiyi kishi da Halimatu ba to nima kuma ba zan janye 'kudirin dana dauka a kan auranta ba, saboda haka sai kije ki r'ike duk wani abu da nasa aka kawo miki da niyyar auranki na bar miki, ki samu wani mijin ki aura ni kuma zanje na auri muskiniya sai naga abinda zai cinye ni." Yana 'kare maganarsa ya futa daga soron gidan nasu. durkushewa tayi kasan soron ta fashe da kuka tana data sanin abinda ta aikata, tun farko ta lura Abbas din ba irin lusaran mazan da mace ke tursasawa bane yana da wani irin baud'addan hali tabbas kamar yanda ya fad'a din babu me sashi yayi abinda baiyi niyya ba mutukar ba iyayansa ba.
Tofa al'amarin yayi tsanani dan Abbas yaja tunga ya tsaya kan maganarsa kan cewar ya janye maganar auransa da Halisa saboda wasu dalilai saboda haka Halimatu itace matar da ya za'ba a matsayin uwar 'yayansa, Baba malam da Alhajinsa suka dinga bashi hakuri suna rarrashinsa, kan yayi hakuri ya auresu gabadaya, nan ya futo ya fada musu abunda ke faruwa!
Yace."Halisa tayi mummunan furuci ga Halima kuma tayi izgili ga hallitar da Ubangiji yayi mata, dan haka to shi ba zai auri macan da zata dinga kokarin nuna masa yanda zaiyi ba, saboda haka shi ya janye maganar auranta Halimatu yake so.
Baba Malam da Alhaji Sama'ila ba suji dadin faruwar al'amarin ba kasancewar mahaifin Halisa din mutumin kirki ne duk tare suke zama bakin titi ranar juma'a da yamma, dan haka sai suka yanke shawarar fada masa halin da ake ciki, suna kuma fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi.
Koda mahaifin Halisa yaji yanda al'amarun suka kasance sai hankalinsa ya tashi sosai! babu shakka yarinyarsa tayi wa kanta wauta ba kad'an ba ta cutar da kanta kuma shi sam baiga laifin Abbas ba, da irin hukuncin da ya yanke yana bala'in son yaga jajurtaccen namiji mai tsayuwa kan magana daya.............Halisa tasha fada sosai gurin mahaifinta yace."Tunda ba zata auri mai mata ba to taje ta nemo wanda bashi da mata wanda kuma yayi mata alkawarin da ita kadai zai zauna, mutukar ta kawo masa komai illarsa da rashin nagartarsa to shi kuma zai daura mata aure dashi tunda itace taji ta gani.
Hankalinta a tashe ta nufi gidan Ramlatu, tana kuka ta zayyane mata abinda ke faruwa, a ganinta tinda Itace take gaba da Abbas din zata fada masa yaji tace dan Allah ta bashi hakuri yanzu ta yarda zata zauna da Halimatun a matsayin kishiyarta.......Ramlatu ta fusata ta dinga surutai tana aibata Halimatu da iyayenta a cewarta sam Abbas bai dace da auran muskiniya ba, saurayi dashi mai kyau da kudi da Ilimi yama za'ayi ya auri nakashshiya wacce take ci take sha a 'karkashin alfarmarsa dan haka sai ta shiga bawa Halisa hakuri tace ta kwantar da hankalinta za taje ta same shi, insha Allahu zai aure ta.........Da safe da wurwuri ta sauka a gidan kowa yayi mamakin zuwanta, ko gaisawa ba suyi da mutanan gidan ba ta nufi dakinsa, lokacin yana kokarin fitowa da shirin fita kasuwa!
Yace."A'a barka da safiya kece a gidan." Tace."Eh gurinka nazo." Cike da mamaki yace."Gurina."?
Tace"Eh yace."To Kinga ni yanzu sauri nake zan fita ki bari na dawo ko kuma ki koma gida da yamma idan na dawo zan shigo gidan naki sai naji abinda yake faruwa.
Cikin d'aga murya kamar wata uwarsa tace"Yanzu kai Abbas ka rasa wacce zaka aura sai Halima muskiniya nakashshiya ashe dama anan ruwan idonka zai 'kare gaskiya ka bani mamaki wallahi!
Ga Yarinya mai hankali da nutsuwa 'yar gidan mutunci mai kaunarka amma kace ka fasa auranta ka koma gurin wata banza wacce take ci da sha a 'karkashin mahaifin.......'Daga mata hannunsa yayi fuskarsa a murtuke yace."Wallahi ban san sanda zakiyi hankali ba! kullum kina girma kina cin 'kasa!
Yanzu ke ko kunya baki ji ba ki shigo har dakina kina daka min tsawa da nuna min yanda zanyi, haifata kikayi da zaki dinga yi min haka? ina ruwanki da aurena da Halimatu idan ba zaki saka albarka ba to kiyi shuru da bakin ki dan ni wallahi duk abin nan da kuke yi 'kara mun 'karfin gwiwa kukeyi babu gudu babu ja da baya sai na auri Halimatu in yaso ku kasheta saboda 'kiyayyya." Fashewa tayi da kuka tana nuna shi da hannu tace"Ni kake zagi ko Abbas dama ai baka da mutunci baka dauke ni a bakin komai ba kuma kai dama ba'a fada maka magana kaji." Yace."Da kinzo min da lisilama zan fahimce ki amma kinzo kina yi mun hayagaga! a kunne ai kin san halina ni ba'a haka dani." ratse ta yayi ya futa dada dakin, kallo ta bishi dashi tana jijjiga kanta, dama tun yana yaro bata iya lankwasa shi gwara Alhasan shi tana fada masa magana yaji amma banda Abbas futo na futo yake da ita girgiza kanta tayi ta futa daga dakin.
To haka al'amura sukayi ta kasancewa kowa na fadar albarkacin bakinsa kan wannan auran yayin da Abbas ya shafawa idonsa toka ya tsaya kai da fata sai da yaga auransa da Halimatu ya tabbata sannan hankalinsa ya kwanta.
Gida gudu biyu iri d'aya Alhaji Sama'ila ya mallakawa Abbas da Magaji Gidajen nasu na cikin unguwar *Gwangwazo* wajejen gidan Sarki.
kowanne ya tare da matarsa a ciki, Maryam matar Magaji 'yar cikin gari ce dai-dai gwargwado tana da hankali da nutsuwa shiyasa tasu tazo d'aya da Halimatu suke zamansu lafiya, kamar yanda mazajensu ke zaune da juna lafiya suma haka suke mutunta junanmu.