Sashe 129
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Najaatu ta dinga bashi mamaki ganin yanda take sarrafa shi sai kace wata babbar mace ko Halisa da taga jiya da yau ba zata nunawa Najaatu komai ba, a daidai lokacin da suke daf da biyawa junansu bukata, kiran waya ya katse musu hanzari......Abbah gabansa ya fad'i! sai ya shiga tunanin wayar jiya zuciyarsa tace masa watakila jikin Ummi ne ya tashi, sai kawai ya fara kokarin sauka!
Najaatu ta kamoshi ta qamqame shi tsam! ta hanashi sauka tana masa magana qasa-qasa! sam bai ma ji abinda take cewa ba yace."Ki bari na duba wayar nan na gani ina tunanin Zainab ce." Ranta ya sake 'baci! a sarqe tace"Umum! kawai ka cigaba idan komai yayi kammala sai ka kirata kaji komeye."
Kallonta yay duk da da akwai duhu a dakin sai da ya fahimci cewa tana cikin yanayi.
Yace."Bana jin zan iya samun wani kuzari a yanzu hankalina ba'a jikina yake ba dan ina tunanin jikin ummi ne ta tashi."
Sai kawai ya zare jikinsa ta zura kafafunsa kasa wayar ya laluba kan bedside ya d'auka daidai lokacin wani kiran ya sake shigowa ganin sunan Zainab kan screen din wayar yasa da sauri ya daga wayar.....Yau ma da innalilhi ta fara kuma kukan da take har yaci uwar na jiya tace "Abban Mufada Ummi tun misalin sha daya da rabi numfashinta ya dauke gashi yanzu sha biyu da rabi bata farfado ba."!
Cikin damuwa gami da tashin hankali yace." Me yasa tun lokacin baki kirani ba sai yanzu.."?
Haba Abban Mufida tun yaushe nake kiran wayar taka kaqi dauka ni dai har na fitar da rai da yarinyar nan wallahi." Cikin gursheken kuka ta karashe maganar......"Kashe wayar yay ya mike ciki tashin hankali ya lalubi jallabiyarsa da gajeran wanda yasa gabadaya ma baiyi tunanin wanke najasar dake jikinsa ba ya kama hanyar fita......Najaatu miqewa zaune tayi rai a bace ta kira sunansa"Abbah."!
Juyowa yay yana kallonta da fad'in "Najaatu kiyi hakuri kinji ko bari naje na duba yarinyar nan naga halin da take ciki......." Karya ne fa wallahi Ummi lafiyarta lau kawai tana so ta hanaka nutsuwa ne bayan haka kuma tana so ta kuntatawa zuciyata shiyasa ta d'orawa 'yarta ciwo.
A fusace!
Yace"Saboda rashin hankali haka kawai sai ta d'orawa 'yarta ciwo ashe kenan abinda Dr ya fad'a karya ne ko? kada ki sake wannan maganar kawai kiyi addua Allah ya bata lafiya." Najaatu sakin baki kawai tayi tana kallonsa ya kama handile zai bude kofa tace"To kada ka fita da najasa yana da kyau ka wanke ta." karamin tsaki yaja ya dawo da sauri ya shiga toilet din, yayi wanka ya fito ya sanja jallabiya da gajeran wando duk tana zaune tana kallonsa yasa kai ya fice daga dakin ba tare da ya tanka mata ba, lallai kawai saboda tace ciwon Ummi karya ne yake jin haushi, lallai babu shakka Zainab tana so ta sanyawa mijinsu rashin nutsuwa, a gida da waje al'amarin gabadaya sai ya tsaya mata a rai ta dinga jin wani irin tausayinsa na ratsa mata zuciya...
*Afuwa Mommy naga Comment d'inki......Tunda Halisa ta ha'kura ta sakarwa Najaatu to ina ganin abinda Zainab take 'karamin alhaki ne, Najaatu ta riga tayi mata illah tunda har ta fahimci cewa itace tauraruwa a zuciyar mijinta to duk wani makircin ta gami da sharin ta ba za suyi tasiri ba dole za tayi ta gaji ta daina*
*Littafin na kudi ne ....*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip group #600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbabk idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
******84 Abbah cikin damuwa gami da mayar da al'amuransa ga Allah ya isa gidan, yanayin yanda yake horn da karfi yasa maigadi ya tashi a firgice!! ya fito da daga dakinsa da toch a hannunsa, k'aramar kofa ya bud'e tare da leka kansa, ganin motar maigidan yasa da sauri ya nufi bakin gate ya fara kokarin bud'ewa, ko 'karasa budewa baiyi ba yasa hancin motar a gidan, maigadin yay saurin ya matsa gefe, nan bakin gate din ya faka motar ya bude ya fito, maigadin ne ya karasa da sauri yana gaishe tare da fad'in "Alhaji ina fata dai lafiya nagan ka cikin dare." Yace."Malam Halliru babu lafiya wallahi yarinya ce bata da lafiya." Malam Halliru yace."Ayya nima dama ganinka a cikin wannan daren yasa na zargi akwai wani to Ubangiji Allah ya bata lafiya." Abbah na kokarin shiga gurin Zainab ya amsa da ameen.......Zainab dasu aunty Balaraba suna zaune suna magana kasa _kasa jin sallamarsa yasa Zainab ta shiga sheshshekar kuka had'e da fad'in "Aunty Balaraba ki cigaba da shafa mata ruwa a fuskarta ko Allah zai sanya numfashinta ya dawo ni kam na fitar da raina da yarinyar nan." Cikin kuka ta'karashe maganar, Aunty Balaraba dake rungume da baby ummi wacce take bacci sai kawai ta shiga shafa mata ruwa a fuskarta da jikinta tana fad'in "Haba Zainab cuta ai ba mutuwa bace yarinyar nan dogon suma tayi zata farfad'o insha Allah."
Zainab na sha'kar hanci tace"Ai abun ne ya tsorata ni wallahi kina ganin fa ko motsi ba tayi." Aunty Balaraba na kokarin magana ya shigo dakin
Zainab a guje taje ta rungumeshi tana kuka na fitar hankali take fadin shikkenan Abban mufida na rasa 'yata gatanan a hannun aunty Balaraba tun dazu ake shafa mat
a ruwa numfashinta yaki ya dawo."
Cikin sanyi jiki gami da miqa al'amuransa ga Allah ya cireta daga jikinsa ya nufi inda aunt Balaraba ke zaune....Hannu yasa ya kar'bi yarinyar aunty Balaraba na share hawaye tace"Gata nan dai mun rasa abinda ke damunta numfashinta ya dauke ya dawo haka yake gashinan dai yanzu ya dawo saboda ruwan da nake shafa mata a fuska da jikinta."
Ba tare da yace komai ba ya nemi gefan gado ya zauna da yarinyar a hannunsa, aunty Balaraba ita da yar uwarta suka mi'ke simi simi suka fita daga dakin.