← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 143

Sashe 118

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi tace"Idan miliyan kikace kina bukata yana da ikon da zai baki mijinki fa yana da kudi ne wanda be san a dadinsu ba meye a ciki dan ya baki dubu dari biyar 'ya guda fa kika haifar masa darajar dan mutum yafi komai." Zainab tace"To zan gwada nagani anty bana so yaga rashin hankalina wallahi.

Tace"Baki da wayo zainab na fada miki fa yanzu ne lokacin ki amma tunda kina ganin kamar wani abu shikkenn kanki zaki cuta ba wani ba, yanzu idan ya baki kudin nan sun isa ki siyi komai na qawa da kece raini ke har sai sunyi miki saura sai ki ajiye a account dinki kyayi wata bukatar dasu
Zainab tace"To shikkenan bari ya shigo da daddare zan fada masa."
Zainab tayi mamaki lokacin data fada masa a dadin kudin da take bukata yace babu matsala zai saka mata a account dinta in yaso duk abunda take bukata baby ke bukata sai tasa 'yan uwanta su cire kudin su siya mata.......Zainab yana fita ta dinga murna da farin ciki kanta na sake girma tana tunkaho da cewar ita din 'yar gaban goshi ce wannan zunzurutun kudin da ya bata tayi hidimar haihuwarta yasa ta daina jin haushin abubuwan da yayi wa Najaatu a lokacin data haihu, ta tabbata kyauta da hannun bayarwa a jinin jikinsa yake......koda yan uwanta suka zo ta nuna musu shedar kudin a wayarta sai suka dinga mamaki! wasu daga cikinsu har sai da hassadar su ta fito fili, babbar yarsu aunty Hauwa tace"To sai ki bani Atm din ki naje da kaina zan had'o miki kaya na alfarma wanda zaki fita kunya dashi ranar suna." haka kuwa akayi aunty Hauwa yayar Zainab itace duk ta had'o kayan barka saboda tsabar rashin hankali duk ta qarar da kudin gurin siyawa 'yar uwarta
kayan banza da wofi amma baby ta tashi da akwati daya itama ba wasu kayan kirki ne a ciki ba.

Ita kanta Halisa da aka kai kayan ta shiga ta gansu sai da tayi mamaki! daurewa kawai tayi ta dudduba tasa albarka ta nufi gurinta, aikuwa tana fita 'yan uwan Zainab suka shiga dariya kowa na fadin albarkacin bakinsa akanta wai 'yar bakin ciki ce hassada tasa ta kasa zama ta duba kayan a tsanake, ita kuwa zainab sai wani figala take tana fad'in ita waye yasan abunda akayi mata a baya saboda haka taje tayi ta hassadarta idan ma mutuwa za tayi ta mutu babu ruwanta.'' Babu wanda yay mata fadan arziki sai ma qara zugata da suke idan tayi arbain tace ya siya mata mota. kai tsaye tace"Dama ai yanzu abinda yake gabana kenan naga ina hawa babbar mota wacce tafi ta Halisan kudi da girma."
Halisa kuwa sa masa ido kawai tayi taga iya gudun ruwansa, shin ita da yara me ya tanadar musu na fitar suna ai ko turaman atamfofi ya kawo musu suma su sanya, tun ranar da sukayi cacar baki akan Najaatu suke sama sama da juna dan haka ana ya gobe suna ta same shi yana shiryawa zai fita tace"Naga kayan barka na Zainab sai nace to mu ina namu kayan fitar suna ni da yara."
Ba tare da ya kalleta ba yace."Kinyi magana kina bukata ne?

Tace"Sai nayi magana zaka san abinda ya dace a qallah dai ai muma ka kawo mana namu ba sai nayi magana ba tunda muna da hakki.

Yace."Itama bani naje nayi mata siyayya ba dan bani da lokaci kudi na bata kuma kin san dole ayi mata hidima tunda haihuwa tayi." Tace"Ina ruwana da haihuwa tayi ni ina maka maganar akan hakkina da yara na." Afusace! yace."Ke!

Halisa ba zanyi ba! uwata ce ke zaki sani a gaba kina nuna min abunda ya dace to ba zanyi ba nace! kusa wanda kuke dashi." Yana gama maganarsa ya buge rigarsa tare da daukar wayoyinsa ya qara gaba....Halisa ta jima tana mamakin wannan al'amarin ta dinga tunanin hukuncin da zata dauka a kansa, miqewa tayi a guruguje tayi wanka ta fito ta shirya key din motarta ta dauka ta kama hanyar fita
Daidai kofar gate din Zainab ta dinga jiyo hayaniyarsu sai shewa sukeyi da fad'in gobe har d'an asharrale zasu dauko su cashe!

Motar ta kawai ta shiga ta fita daga gidan, kai tsaye kofar na'isa ta nufa.

Lokacin data isa gidan Hajia da Ramlatu na zaune a palo suna hira Najaatu na daki tana bacci....Halisa ta samu guri ta zauna fuskarta a ba'ce!

Hajia tace"Halisa Allah yasa dai lafiya na ganki da tsakar rana ina fata dai ba wata matsala bace.....Halisa kasa magana tayi sabida tunda take bata ta'ba kawo kararsa gurin iyayensa ba ba dan bayayi mata laifi ba kawai tana hakuri ne amma hakika yau ya kaita bangon makura....Ta gaida hajian murya na rawa ta shiga sheda mata abunda yake faruwa, Tace"Saboda nace ya mayar da Najaatu gidansa yake jin haushina kullum babu kalma mai dadi to yau dan nayi masa magana akan hakkina dana yara ya farfad'a min magana iya son ransa Hajia wallahi ina hakuri da halin Abban mufida ina ganin zan tafi gida kawai na bashi guri."
Hajia tayi shuru tana nazarin maganar Ramlatu kuwa hasala tayi tace"Ai wannan yarinya fitinanniya ce wallahi watakila ma ita ta hanashi yay muku komai aini tunda ta zugashi ya dauko min police ta fita daga raina, kuma haka kawai saboda kin bashi shawarar arziki sai ya dinga jin haushinki to meye da Najaatun da yake gudunta."
Najaatu jin hayaniya a falo yasa ta fito daga daki ta samu guri ta zauna tana kallonsu da so ta fahimci inda maganar ta dosa.....Halisa tace"Wallahi kuwa Yaya Ramlatu Abban Mufida wani iri ne yana son abu amma sai ya dinga nunawa baya so saboda nace idan ya tsaya wasa wani zai aureta duk da jegonta shine fa yake Jin haushina." Hajia tace"Duk dai yanzu magana ta kare kiyi hakuri ki koma gida kada ki tafi gidanku idan yazo da yamma zanji dalilinsa na danne miki hakki maganar zuwa asibiti dama munyi dashi kancewar sai bayan suna hankali ya kwanta zai kaiki yace watakila ma dubai zakuje a dubaki sosai."
Jin wannan magana da hajia tayi yasa Halisa taji sassaucin akan bacin ran dake zuciyarta sai ta miqe tana gyara mayafinta da fadin ita zata tafi." Hajia da Yaya Ramlatu suka sake tausarta akan kada tace fa zata je gida ta koma dakinta, nan ta tabbatar musu da cewar gidan zan ta koma insha Allah....Bayan fitar Halisa Najaatu tunani ta shigayi ta fahimci maganganun da
Halisa takeyi a kanta wato saboda tace masa ya mayar da ita yake gaba da ita to ita kuwa wace iriyar kiyayya yake mata da har zai dinga gaba da wani a kanta.....Allah sarki Halisa ashe yanzu tana kaunarta tunda gashi har tana cewa mijinta ya dawo da ita. jin hawaye na kokarin su zubo mata ne yasa ta miqe da sauri ta bar gurin.

Hawaye na sauka a kan kumatun ta ta zaune gefan gado tana tunanin abinda zai taimake ta, gabadaya ji tayi zaman gidan Alhajin ya fita daga ranta, ba dan komai sai dan tayi nesa dashi da duk abinda ya shafe shi tana ganin idan ya daina ganinta sai tafi martaba da daraja a idonsa, me yay zafi da har zai dauki fushi da gaba akanta ashe dama haka kiyayyar ta tayi girma a zuciyarsa........... yanzu idan tace zata koma gidan Malam su hajia hankalinsu zai tashi kuma ba zasuji dadi ba sannan zasu dinga tunanin ko wani abun suke mata na rashin kyautawa yasa take gudun zama dasu, amma da badan hakaba da wallahi barin gidan za tayi domin ba taga amfanin zamanta a ciki ba
Tana wanka tana tunanin maganarsu da Mmn Sajida....Itafa gani take dukkanin wani abu na jan hankali da za tayi masa bai zama lallai ya kalleta da qima da daraja ba , amma dai tana ganin zata kwatanta yin wasu abubuwan ko Allah zai sa a dace.

Shiryawa tayi tsaf! ta fito ta samesu har yanzu suna falon suna tattauna maganar, sai ta nuna tamkar ba taji abinda suke magana a kai ba.....Hajia tace"Ya na ganki da hijabi ko gidan Malam zaki shiga."?

Tace"Eh inaso na shiga mu gaisa bayan na dawo daga gidan Lalle ('Kunshi) inaso nayi kwalliyar suna." Hajia tace"Aikuwa yana da kyau hakan to da akwai kudi a gurinki ne." Tace"Eh akwai wanda zasu ishe ni." Yaya Ramlatu tace"To ko zaki bar Daddy a gida kyafi samun nutsuwa gurin zaman kunshin." kokarin kwanto yaron take daga bayanta tana fadin " Aikuwa kin kawo shawara mai kyau Yaya Ramlatu dan yana iya rikice min da rigima ya hana lalle na yayi kyau.

Yaya Ramlatu ta kar'be shi da zanin goyonsa ta miqe tana kokarin goya shi a baya tace"Ai har kyaje ki dawo yana baya idan ya tashi a bacci sai a dama masa madara." Hajia tace"Duk da haka dai kada ki zauna kada a shiga hakkinsa." Tana kokarin fita tace"Insha Allah bazan jima ba zan dawo.

Gidan Lallen kabuga ne kuma lokacin da taje akwai mutane dan ma mai lallen kawar Salimat ce budurwar Salim wacce a lokacin auranta da Bash yasa ta gane gidan.....Dalilin wannan sanayyar yasa Bilki mai kunshi ta tsallake mutanan dake gabanta ta kama kafafun Najaatu tana yi mata, aikuwa jamaar dake gurin suka dinga surutu kowa na ganin an shiga hakkinsa....Tace" Dan Allah kuyi hakuri na bar karamin yaro ne a gida kuyi min uziri.'' jin haka yasa wasu suka daina magana wasu kuwa fushi sukayi suka tafi.....Bilki ta dauki lalle mai tsayi da ado da yawa, Najaatu tace"Bilki da kinyi min takaitacce tunda kinga akwai jamaa a gabanki." tace"na riga na dauki mai ado dole kema sai kin jure zama.'' shuru kawai tayi ta zubawa kafafunta ido wanda bilki ke zane su da jan lalle.

Kafafuwa da hannuwa akayi mata jan lalle mai kyau da burgewa sosai kunshin ya dauki hankulan jamaar dake gurin suka dinga so ayi musu irinsa.
Chapter 118 · 0% Book details