← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 143

Sashe 102

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai sa naji tana fad'in "Ya kyauta mata hakan da yayi dama saboda dukiya Abbas ke wulakantata har da dauko mata police yazo har gida yaci mutuncinta saboda haka idan ma da akwai wata hanyar da yaron zai sake bi yaga ya kassara dan uwanta to ta bashi goyon baya yaje yayi ya kuma cigaba da nuna masa cewa shi mai kaunarsa har dai bukatarsu ta biya suga sun kai Abbas d'in k'asa! wannan al'amari ya d'aga min hankali mutuka dan ban san sanda na fad'a dakin ba, suna ganina duk sai suka diririce alamun rashin gaskiya ya bayyana a idonsu.

Cikin takaicin da tsananin bacin rai da damuwa nace musu duk naji abinda suka aikata ashe dama sune silar faruwar gobarar data cinye dukiyar Alhaji Abbas? sai dukkaninsu suka shiga rantse rantse cewa basu bane gabadaya ma ba maganar suke ba.....Alhaji ku yafe min a lokacin ji nayi ina nadamar auran Ramlatu ina kuma nadamar hada zuria da ita! hakika tunda na auri wannan baiwar Allah na kasa samu nutsuwar zuciyata kasancewa ta matafiyi duk sanda zan dawo sai jama'ar unguwa makusantana sun kawo min magana a kanta, cewar kullum a kan hanya take bata zama gida itace shiga can fita can! tun a wancan lokacin zargi ya shiga tsakanina da ita sabida kowa akwai maganar da zai kawo min a kanta......Allah ya had'ani da mace tagari Sakina kullum itace ke hanani na aikata abinda nayi niyya akan Ramaltu Sakina mutuniyar arziki ce kuma tana kaunar zama da Ramlatu da shiriyarta shiyasa ta juri cin mutuncin da take mata.....Ban ta'ba jin tsanar Ramlatu ba irin yau! jin mummunan aikin data tunzura d'anta yaje ya aikatawa d'an uwanta wannan dalilin yasa naji kamar naje na dauko musu hukuma a tafi dasu dan gabadaya zama dasu annoba ne tunda sun zama 'yan ta'addah gwara suje su fuskanci hukunci sai kuma nayi tunanin cewar ai bani da hurumi yin hakan, wannan dalilin yasa ni na yanke shawarar rabuwa da ita dan gaskiya dama can zama hakuri kawai nake da ita, idan ina gurin sana'ata hankali kwata kwata ba a kwance yake ba saboda ina tunanin abubuwan da suke faruwa a gidana, jama'ar gari da abokaina gabadayansu babu wanda yake wa Ramlatu kallon mutuniyar kirki harda masu kiranta karuwa! wannan kalmar na daga min hankali mutuka! shiyasa na gaza samun nutsuwar zuciyata da ita gurin mu'amular aure..........Ina rokon ku afuwa kan hukuncin dana yanke a kanta kamar yanda na rubuta mata saki daya jikin takarda hakane na sake ta saki daya idan ta samu miji tayi aurenta kai kuma Salim babu ni babu kai na yafe ka a duniya tunda ka zama butulu maci amana." Ayuba ya kare maganar muryasa na wani irin rawa.

Gabad'aya palon shuru yayi kowa na mamaki da Tu'ajibun wannan al'amarin....Hajia Kuka take tana Kallon Ramlatu tana so tayi magana amma tsabar damuwa da 'bacin rai ya hana ta iya cewa komai.........Wani sabon kukan suka ji da sauri suka kalli inda kukan ke tashi...Halisa dake tsaye a bakin kofar daki ta karaso cikin palon tana hawaye cikin tsananin damuwa gami da nadamar abinda suka aikata a baya, ta kalli Ramaltu tace"Nima babu abinda zance dake sai dai na had'aki da Allah ya saka min kin cuce ni kin cutar da d'an uwanki sannan kin cutar da baiwar Allah Halimatu wacce ba taji ba bata gani ba! wallahi tunda uwata ta haifeni ban ta'ba zuwa gurin wani boka ko malami ba wai dan yayi min duba ko yayi wa wani asiri sai da kika shigo rayuwata kika lalatani da zuwa gurin bokaye! wane gari ne baki jani kin kaini ba, har tsutsa sai da kika kaini gurin bokan da ya bani naci! a matsayinki na 'yar uwar mijina bai kamata kiyi mana hakaba kin cutar damu Allah zai saka min gashi garin biye biyen bokaye gami da shaye shayen maganin mata kinsa na had'u da lalura mai wahalar magani ni kuwa me zance miki a rayuwata wallahi Yaya Ramlatu kinci amanar zumunci."!

Yaya Ramlatu ta dinga kuka tana had'a hannuwanta guri da fad'in "Ku gafarce ni nima ba laifina bane sharrin shedan ne wallahi kuyi min addua Allah ya gafarta min laifukana."
Gabad'aya palon suka zuba mata ido jin maganganun da takeyi tana kuka....Naja'atu murya na rawa tace"Salim idan ban manta ba ka ta'ba fad'a min wata magana a kan Abbah cewar a kwai lokacin da kake so ka rabu dashi bayan bukatarka ta biya a kansa! ashe wannan ne lokacin kana so ka cutar dashi ko? yanzu meye ribar abinda ka aikata masa? kada fa ka manta Abbah yayi maka abinda iyayenka da suka haifeka ba suyi maka ba me yasa kake cin dunduniyarsa? kana nufin dan kasa masa wuta a kan dukiyarsa ya gama arziki kenan? lallai ashe baka da hankali kuma baka san waye Ubangiji ba! a lokacin da hassada da ganin kyashi sukayi yawa a kan mutum a lokacin shi kuma Ubangiji ke qara daukaka darajarsa! wallahi wannan abun da ka aikata a banza domin duk zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi, daga karshe nake so in sake jaddada maka cewar ka samu nasarar raba tsakanina da Abbah ta hanyar zuga ni da nuna min aibunsa tare da tunzurani nayi masa rashin kunya to bukatarka ta biya amma ka sani duk abinda kayi mana mutukar muna da hakki sai Allah ya saka mana sannan kuma insha Allahu sai na koma dakina sai dai ka mutu da bakin ciki." Cikin kuka mai wahala take maganar.

Wannan tone tone da akeyi yayi masifar sanya shi cikin d'imuwa da tashin hankali......
*Ke duniya!!!* ina zaki damu? wai shin me mutane suka dauki duniya ne? duk yanda fa ka tafi da ita haka zata tafi da kai!

Jama'a su sakankance a duniya suyi ta shirya mugun abu kamar sun samu madawwama! me yayi wa mutane da dama da suke cin dunduniyarsa ba'a gida ba ba'a waje ba, Yanzu ashe dama da sanya hannun Salim gurin fujirewar Naja'atu gurin rashin so zama dashi, meye ribar abinda Salim yayi masa gashi nan da yake bashi da hakkin kowa tun ba'aje ko ina ba daga shi har uwar tasa asirinsu ya tuno shi kam me zaice da wad'annan bayin Allah."
Alhaji ya kalli Ayuba da fad'in "Banji ciwo da takaicin sakin da kayiwa Ramlatu ba, shi aure anayin sa ne bisa amana da yarda da juna, kayi kokarin ma tsayin shekaru kana zaune da ita bayan kana zarginta! nima yanzu zargin nata nake saboda dukkanin abinda ka fad'a jama'ar gari suke a fad'a a kanta zata iya aikatawa saboda ba tsoron Allah take ba saboda haka kada ka sanya a ranka cewar ni Sama'ila zan qullace ka dan ka saki Ramlatu nayi maka farin cikin rabuwa da ita."
Ramlatu na kuka ta rarrafo gaban Alhajin tana kuka tace"Alhaji ka gafarce ni dan darajar annabi ka ro'ki Ayuba ya mayar dani wallahi duk abinda na aikata kuskurene da son zuciya hakika nasan nima ban kyautaba zuciyata ta tunzurani na cutar da dan uwana, sannan wallahi zargin da jama'ar gari suke min ba haka bane! ban ta'ba zina ba nasan dai kullum bana zama a gidana ina yawace yawace amma ba bin maza nake ba
*( qalubale gareku matan dake yawace yawacen banza da wofi haka kurrum ki kulle gidanki kiyi ta shige da fice a unguwa to wallahi yanzu kiwon mutum ake ba dabbah ba, shashahar mace itake yawon bid'id'i! fakal fakal ko wane namiji na qarewa tafiyarki kallo ke idan aka samu 'yan iska ma kiji wani yay miki magana idan kince ke matar aure yace ya raina miki hankali yace ai ya dauka bazawara ce! hattara mata mu mutunta kanku sai Allah ya mutuntamu)*
Alhaji miqewa yayi ya kama hanya zai hau samansa dan zamansa a gurin yana kallon fuskar Ramlatu zai iya sanyawa jininsa ya hau dama ba lafiya gareshi ba......Ramlatu ta rarrafa gurin Dan uwan nata ta rike masa kafafu tana kuka tace"Abbas ka gafarce ni wallahi sharrin zuciya ne ni kaina na rasa me yasa nake maka hassada duk da cewar babu abinda zan nema a gurinka ba kayi min ba, ka dauki d'ana ka ri'ke tamkar kai ka haifeshi kayi masa komai na rayuwa amma na kasa kyautata maka zuciya na ingixani akan na cutar da kai nima yanzu na gane zuciyata bata da kyau! kayi hakuri ka gafarce ni ka yafe min ka yafewa Salim abunda mukayi maka."
Abbah ya ciro hankici a aljihunsa ya goge zufar goshinsa hularsa ya dauka yasa cikin wani irin yanayi na damuwa da alhini yace."Na yafe miki sai ki cigaba da neman gafara gurin Allah ina rokon Ubangiji yasa wannan tuban da kikayi na gaskiya ne." yana gama maganarsa ya miqe!

Salim cikin borin kunya gami da nadama Yace."Kawu ka duba darajar Annabi Muhammad ka gafarce ni wallahi shedan ne! ya tunzurani cutar da kai yanzu na gane qarya da yawancin wasu abubuwa na mugunta basa lasting Idan mutum naso ya zauna lafiya a wannan duniyar to ya kad'aita Allah shi kad'ai kuma ya ri'ke gaskiya d'aya mutukar yayi haka to zai zauna lafiya kuma koda mutum ya nufe shi da mugun abu to Allah zai kareshi."
Abbah Abbas ya jima a tsaye yana kallon Salim din dake hawaye kansa a kasa kunya ta hanashi ya dago kai ya kalleshi, yace."Salim kaima na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya." Ya kalli Hajia cikin wata iriyar murya da bata fita sosai yace ''Zamu tafi." Hajia ta goge hawayen idonta cikin tausayi da jin kai irin na uwa da d'anta tace" Ina rokon Ubangiji Allah ya ji'banci al'amuranka Abbas Allah ya kare ka ga miyagun mutane da aljanu, duk wanda ke nufinka da sharri Allah ya maida masa kansa, Allah ya daukaka darajarka daukaka mai amfani Ubangiji Allah ya shi maka albarka Abbas hakika ina alfaharin haihuwarka Allah ya albarkaci zuriarka." Wannan adduar da mahaifiyarsa tayi masa itace ta wanke masa zuciyarsa tayi wasai gabadaya ma yaji ya daina jin takaicin abinda akayi masa........sai ya kasa 'boye farin cikinsa ya dinga amsa adduar mahaifiyarta sa yana jin wani irin dadi yana ratsa shi.
Chapter 102 · 0% Book details