Sashe 26
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To shima dai da ya fad'i maganar yasan abune da ba zai ta'ba yiwu ba dan ya riga yasan yanda Halisa take da masifar kishi ai da wuya ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ko *'Yar uwa*......Hankalinsa ya mayar kan Naja'atu ya dan tsira mata ido na minti biyu kafin ya kira sunanta.
Da sauri ta d'aga kanta tana kallonsa da idanunta da suka soma kawo ruwa.
Ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa!
Yace."Ke ma d'azu kafin na kawo ki cikin gidan nan mun gama magana dake kuma ina fatan dukkanin abinda na fad'a miki sun shiga kunnan ki kiji ki kuma shiga hankalin ki, zaman aure kika shigo kiyi a gidana ba shirme da shashanci ba, wannan da take zaune tafi kar'fin raini a gurinki." Yafada yana nuna mata Halisa, bata kalleta ba sai sake sunkuyar da kanta 'kasa da tayi
Ya cigaba da cewa"Duk ina sane da rashin kunyar da kike mata a lokotan baya! bakya ganin girmanta duk irin maganar da tazo bakin ki fad'a mata kike bakya gaisheta a duk inda zaku had'u! tsaki! harara duk babu wanda bakyayi mata, to duk nasan da hakan nake kyale'ki koda ita Halisan zata kawo 'karar ki ina bata hakuri saboda a samu zaman lafiya ina kuma nuna mata ke yarinya ce idan kika kara hankali zaki daina.......Halisa tayi hakuri da halayen ki a baya, dan haka a yanzu kada naji kada na gani kin zageta ko kin fad'a mata bakar magana ko kuma kinyi mata tsaki! tsakaninku mutunci da mutunta juna inaso ki dauki Halisa a matsayin Uwa abokiyar shawararki wannan kad'ai zakiyi min nasan cewar ke d'in tarbiyar Halimatu ce."...............Tsit dakin yayi bayan gama maganarsa Halisa tamkar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki taji dadi sosai yau da ya nunawa yarinyar matsayinta a gurinsa, ashe duk yana sane da iskancin da yarinyar ke mata a baya amma bai ta'ba magana ba, ji tayi duk wani haushinsa da take ji ta daina, sai wani murmushi take tana jijjiga 'kafa.......Ita kuwa Naja'atu kanta a kasa ta kasa dagowa dan tasan idan ta dago 'kwallar dake kokarin zubowa daga idananunta zata tona asirin zuciyarta...........'Dan kashingid'a yayi kan bed din yana kallon Halisa babu alamun wasa a fuskarsa yace."Yarinyar nan zata cigaba da zama anan dakin! tunda ya kasance d'akuna uku ne to bai kamata ta kwana cikin yara ba idan yaso ni nabi da'ki-d'aki! kafin komai ya daidaita." Halisa ba haka taso ba amma sai tayi kokarin danne kishinta tace"To shikkenan hakan ma yayi dai-dai ai." Yace."To tunda kece uwargida sai ki shirya yanda al'amarin zai kasance."
Cikin ya'ke! da danne wani mugun kishi tace"Kwana biyu zaka dinga yi kamar dai yanda kake yi lokacin Halimatu." Gemunsa ya shafa yana d'an murmushi yace."Ai na dauka ko zaki sanja tsari ne shiyasa na tambaye ki."?
'Yar dariya tayi tana ta'be baki tace"Kwana bibbiyu shine tsari mai ma'ana idan kuma kafi son kwana d'ai-d'ai to." Ya kalli Naja'atu had'e da kiran Sunanta!
A firgice! ta kalleshi dan ita bata san wainar da suke toya ba tana can tunanin ya za'ayi ta fece daga gidan.
Yace."Ke a ganinki kwana nawa-nawa zan dinga yi a tsakaninku."?
Murya na rawa tace"Ban gane maganar ba." Mikewa zaune yayi yana kallonta yace."Muna maganar raba kwanan girki ne a tsakaninku shine nake tambayar ra'ayin ki." Shuru tayi wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska wai yau itace Abbah Abbas ke tambayarta maganar kwanan girki.
Ganin tayi shuru yasa ya kalli Halisa yace."Kwana bibbiyu din shi zamu dauka kamar yanda kika ce."Mikewa tayi tana fad'in "Hakan yayi! to ni dai sai dai nace Allah ya bamu alkairi." Hanyar fita ta nufa zuciyarta kamar ta babbake!
Kallo ya bita dashi kafin yace."To Allah ya tashe mu lafiya idan kin fita kisa yara su tashi daga kallon da suke suje su kwanta haka." Ai fad'ar wannan magana da yayi sai ya 'kara tunzura ta a fusace! ta bud'e kofar dakin ta fita tare da doko kofar da karfin gaske........Tana fita palon ta raraka yaran d'akinsu sai masifa take tana zaginsu kamar sune sukayi mata laifi......Mussadiq da Saddiqa a tsorace suka bar gurin.
Innalilihi wa'ina ilaiji raji'un! kawai take ta ambata bayan fitar Halisa daga dakin gabadaya Jinin jikinta ya daskare hatta da kafafunta jinsu take sunyi mata nauyi da sanyi tana ji kamar ba a jikinta suke ba.........Gyaran muryarsa taji kafin taji ya kira sunanta, amsawa tayi tana kallonsa ya iya kiran sunanta tamkar a bakinsa a ka rad'ashi.
''Kinci abinci ko."?
Yafada yana mata wani kallo na 'kasan ido!
'Daga kanta tayi tana mai dauke idonta daga kansa, Yace." To shiga toilet ki dauro alwala kizo muyi nafila ta godiya ga Allah." Mi'kewa tayi salo-salo ta nufi toilet d'in.........Minti biyar ta fito daure da alwala ya mike ya shiga toilet din shima ya dauro alwala ya fito.
Nafila sukayi raka'a biyu kamar yanda Annabi ya koyar da sababbin ma'aurata!
Abba Abbas ya jima hannunsa a saman kanta yana addua kafin ya cire ya d'aga hannunsa sama nan ya jima yanayi wa Allah kirari, daga bisani ya rufe adduarsa da fatihatulkitabi suka shafa ita dashi, mikewa yayi daga kan abun sallahr ya dauki key motarsa dake kan drowar taga ya bude dakin ya fita.
Zukud'un!! tayi bayan fitarsa daga d'akin, ita yanzu abun ma mamaki yake bata gami da tsoro! da gaske dai sai tayi zaman aure dashi, tunda gashin nan har ya zaunar dasu tare da matarsa yana kawo mata tsare-tsarensa harda kashedi da gargadi kada ta zagi matarsa, lallai Abbah Abbas yayi masifar bata mamaki! to ita yanzu ba wannan ne ma yake sake furgitata ba sai kawo ta dakinsa da yayi, to me zaiyi mata? bata da mai bata amsa! mikewa tayi da saurin gaske ta nufi kofar fita, cikin ikon Allah kuwa tana jan kofar ta bude! palon ta fita tana zazzare ido! tv a kashe yaran duk sunje sun kwanta.
Kujerar data zauna a dazu nan ta nufa ta duba wayarta zama tayi kan kujerar ta shiga lalubar numbar Salim.......Lokacin shi yana ma can gidan kallo hayaniya ta hanashi ya daga wayar sai ihu suke shida abokansa sunci 'kwallo.
Text ta tura masa tana hawaye tace.
_Salim anya kuwa kana sona kuwa? tun jiya nake kiran wayarka baka dauka ba ashe dama duk soyayyar da kake min karya kake......Kada fa ka manta kai kad'ai nayi wa alkwarin mallakawa kaina da komai nawa dan Allah kada ka bari Abba Abbas ya samu nasara a kanmu dan gani nan a gidansa a cikin dakinsa ya kulleni kasan hakan da yayi yana nufin abubuwa da yawa, dan haka dan Allah ka daure kayi wani abu akan wannan al'amarin."_
Tura masa tayi tana adduar Allah yasa ya duba ya bata amsa.......Salim shida abokinsa suna cikin mota bayan fitowarsu daga gidan kallo ya dauko wayarsa yana dubawa, ganin Kira da text din Naja'atu yasa yaja tsaki! text din ya shiga dubawa! bayan ya gama karantawa ya nunawa abokinsa, shima ya karanta, dariya yasa ya bashi hannu suka tafa yace."Amma gaskiya yarinyar nan na sonka da yawa, yana da kyau ka fara gudanar da aikinka dan na lura dattijon nan zulamamme ne! ya samu 'karamar yarinya sai 'barin jiki yake kada ka barshi ya lashi zumar nan ta dad'in rai."
Salim yayi wani murmushi yana shafa siririn sajensa yace."Ai wallahi sai na d'and'ana masa d'aci! da bakin cikin daya jefa ni a ciki dan haka bari kaga ni." Sai kawai ya shiga kiran wayar Naja'atun, da sauri ta dauki wayar ta kara a kunnanta.
Salim ya wani narkar da murya cikin sigar yaudara da janye hankali a kasalance yace."My Princess bani da lafiya zuciyata ta kusa ta daina aiki yini nayi ina aman jini! soyayyarki ina tsammanin itace ajalina! na kasa daga wayarki ne saboda ni kadai nasan irin masifar da zan shiga idan naji sautin muryarki, to amma ganin wannan text din naki na yanzu ya firgitani sosai har naji sha'awar na kira ki a waya na gargade ki kan cewar komai rintsi kada ki kuskura ki mallakawa wannan tsohon jikinki kada ki bari ya kusanci inda kike my princess ni kad'ai nasan irin yanda nake jin fleengs a duk sanda na tuno zubin hallitarki hakika na jima ina kwadayin na ganni ina tsotsar bakin ki! sannan babu babban abinda yake d'aga mun hankali kamar breast dinki na jima ina mafarki gasu a hannuna ina wasa dasu ina tsotsa ina lailayasu a hannuna! dan Allah my princess kada ki bari wani yayi amfani da damata duk rintsi duk wuya kiyi min wannan alfarmar."
Tunda yake maganar take 'kan'kame wayar a kunnanta tana sauke ajiyar zuciya tsigar jikinta na tashi, ji tayi gabadaya jikinta ya rikice ta dinga jin sha'awar Salim din na taso mata...........Murya a dushashe tace"My prince kada ka damu zan kula maka da kaina da jikina nayi maka alkawarin babu mai mallakata sai kai kuma insha Allahu zan fito daga gidan Abba Abbas da budurcina muyi auranmu tinda shari'a bata rahamta mana ba."
Salim ya sakeyin 'kasa da murya yace."Yawwa my princess nagode kwarai da soyayyarki gareni nima insha Allahu zan cigaba da yi mana kokarin dan ganin bukatarmu ta biya." Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin magana, taji alamun bude kofar palon..........Da sauri ta mike ta nufi dakinsu Saddiqa da wayar a kunnanta tana magana 'kasa-'kasa tace"Salim gashinan ya dawo zan kashe wayar yanzu." Yace."To shikkenan my Prince.
" Kashe wayar yayi ya kalli abokinsa dake draving sai kawai suka kwashe da dariya kamar wasu shashashai!
Kamalu yace."Gaskiya Salim ka iya tuggu! yarinyar nan fa gabadaya ta mato a kanka duk maganar daka fada mata da sauri take amsawa kamar wani ubanta." Salim ya shafa sajensa yana dariyar mugunta yace."Ai na fada maka dama gangar jikinta kawai ya aura, amma zuciyarta na tafin hannuna." Yafadi maganar yana nuna hannunsa.