← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 143

Sashe 70

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka fita da Mmn Sajidan ta zauna kusa da ita tana d'an taimaka mata da wasu abubuwan....Mazan da sukayi yawa ne a gurin yasa taji zaman gurin ya fita daga ranta, ta tsani kallon k'urrula ko kadan ta fahimci mazan garin su kuma dabi'arsu ce..Da har tayi niyyar shiga gidan kodan ta huta da kallon da ake mata sai kuma ta hakura ta daure ta zauna ta cigaba da taimakawa Mmn Sajida dan ta lura abin yayi mata yawa kowa idan yazo da kalar abinda yake so.......Naja'atu na kallon wani magidancin mutum wanda tunda ya tsaya a gurin yake kallonta yana mata murmushi, har sanda Mmn Sajida tazo kansa tana masa magana hankalinsa gabadaya na kan Naja'atu sai kace zai cinyeta...Mmn Sajida tace"Haba d'anTalle tun dazu nake magana kayi shuru yanzu idan wani na sallama kace na tsayar da kai."
Mutumin da ta kira da 'DanTalle ya shafa gemunsa a sanyaye yace"Mmn Sajida yaushe kika samu yarinyar nan lallai na kwana biyu banzo gurin nan ba." Mmn Sajida sanin halin Dantalle yasa tasha kunnu sosai tace" Bakuwa ce wannan kuma ba irin taku bace kai dai ka fad'i me kake so na zuba na had'a maka."
Yace."Ki zuba min shinkafa da wake da miya." Mmn Sajida na kokarin zuba masa tace" 'Kashi ko nama wane zan sa maka." ?

Hankalinsa na kan Naja'atu yace"Ki samin 'kashi." Mmn Sajida ta had'a masa komai ta mika masa ya dauki jarkar zu'bo guda d'aya a sanyaye ya nufi cikin 'yan uwansa dake cikin rumfar kwanon da Mmn Sajida ta tanadar musu.

Yana barin gurin Mmn Sajida taja tsaki tace"Narasa wane irin hali ne da Dantalle wallahi ko wace mace ya 'kyalla idonsa a kai yace yana so.

Ta kalli Naja'atu da fad'in "Nasan shi da mugun bin diddigin tsiya saboda haka kiyi taka tsantsan dashi koda wasa kada ki sakar masa fuska har Allah yasa ki bar garin nan."
Naja'atu a sanyaye tace"Nagode Mmn Sajida nima wlh mutumin gabadaya beyi min ba tunda ya tsaya a gurin nan yake kallona kamar maye." Mmn Sajida tace"Kad'an kika gani ai haka yake mugun son mata ne dashi ga shegen aure auren tsiya hanzu haka matansa hud'u amma baya cin abinci a gidansa kullum yana nan yaci mai dadi ya barsu da garau garau shike nan yawon bariki da kashewa matan bariki kudi."
Naja'atu tace"Allah ya shiryeshi idan zai shiryu.....Koda DanTalle ya kammala cin abincinsa sai yazo ya tsaya yana gyara bakin aljihunsa domun fito da kudi Mmn Sajida taga ya dauko dubu hudu ya mika mata tace"A'a Ai dari shida ne kudin abincinka." Yace."Eh na sani nayi niyyar yi miki kyauta ne ki dauki dubu biyu sai ki bawa yarinyarki dubu biyu.'' Mmn Sajida tace"Anya za'ayi haka kuwa na fad'a maka komai kuma kasan ni bana cikin wannan shirman da kuke yi."
Yace."Haba Me yasa kike wannan maganar Mmn Sajida ni bada wata manufa na baku kudi ba nayi niyya ne kuma idan inason yarinyar nan da aure zan so ta bada wata manufa ba.

Mmn Sajida tace"To godiya mukeyi Allah ya 'kara budi." Ya amsa da amin yana kallon Naja'atu da wani shegen murmushi a fuskarsa..Girgixa kanta kawai take tana mamakinsa lallai kam ya ci sunansa 'DanTalle ita wannan ko a 'kafa a daura mata shi a ta kwance da gudu, daka ganinsa idanunsa a bude suke kar!! dasu irin na mayaudara!

Ya juya baya da niyyar barin gurin tabi shi da kallo!

'Tab! gabad'aya bashi da tsarin mazan da take so wani siriri dashi kamar zai karye sai dogon wuya kamar mari'kin lema a ganinta ma ina yaga kuzarin da zai tunkareta..ita duk wani siririn mutum raina shi takeyi tana ganin kamar basu da wani karfi da kuzari( Kaji wauta irin tana Naja'atu 'kananun maza ma sunfi jaraba kuma babu abinda za'a nuna musu)....Sai kusan sha daya da rabi na dare Mmn Sajida ta siyar da abincinta suka harhada kayan suka shiga cikin gidan.

Karfe takwas na safe sun shirya Naja'atu tayi wanka ta shirya tsaf Mmn Sajida ta bata sabuwar atampa da mayafi tasa a jikinta sannan kuma ta hada mata wasu atampopin kala uku tasa mata a leda viva Naja'atu ta dinga yi mata godiya tana mamakin karamcin matar gaskiya samun Mai hali irin nata sai an tona.

Suna kokarin karyawa Mmn Ladi ta shigo gidan, ganin naja'atu cikin sabuwar atampa sai tayi kici kici da fuska ta wani dogare a bakin kofa tsabar bakin ciki da hassada yasa ta kasa shiga.

Mmn Sajida tace" Ki shigo mana ki zauna dama yanzu nake cewa zan aika Walid ya fada miki ko zaki zo muje tare."
Mmn Ladi ta ta'be bakinta tana girgiza kanta da fad'in "Babu inda zani aikin gidana ma ya isheni."
Mmn Sajida tace"To shikkenan ki shigo kisha tea gashi muna hadawa.

Babu kunya Mmn Ladi ta shigo tana ya'ke da fadin "Kamar kuwa kin san ban karya ba har yanzu dan yau mutsiyacin mutumin nan ko 'kwandala bai bani ba ya futa.

Mmn Sajida tace" Ke Mmn Ladi kiji tsoron Allah ki daina tsinewa mijinki wallahi ki dinga hakuri da yau da gobe idan kina ganin ba zaki iya jurewa ba to ki nemi sana'ar yi amma zagin miji da tsine masa bashi da amfani."
Mmn Ladi na had'a tea tace"Ke rabu dani dan Allah wallahi jiya da kyar nayi bacci saboda tsabar takaicin da mutumin nan ya 'kunsa min haba me za'ayi da talauci ace kullum a gidanka baka da sakakken abinci sai shinkafa da wake da mai da yaji haba jama'a wannan wace irin masifa ce ace kudin cefane dari biyu mtsssw!" takare maganar tare da jan dogon tsaki
Mmn Sajida tace"To ina laifi da kika samu shinkafa da waken ni na samu mana! kina kallo fa ni nake ciyar da kaina da 'ya'yana ke kin samu kina rainawa wallahi ki dinga godewa kad'an sai kiga Allah ya wadataki.'' Mmn Ladi kur'bar tea take tana dangwalar bread da miya tace"Duk yanda zanso ki fahimta ba zaki fahimta ba mu bar maganar kawai."
Mmn Sajida tace"To ai dole na bari tunda bakya so a fada miki gaskiya." Dariya kawai tayi ta cigaba da cinye musu naman dake cikin miyar gabansu.

Naja'atu tun abun na matar na bata mamaki har ya dawo bata dariya ikon Allah kenan wannan shi ake kira Allah daya gari bambam!

Mmn Ladi sai da ta cika cikinta tsaf sannan ta karkad'e zaninta mike tare da kad'a kan yaran ta tafi kaisu makaranta...Naja'atu sai so takeyi suyi gulmar Mmn Ladi ita kuma Mmn Sajidan ta'ki yarda, ta lura da Mmn Sajida tana da kyakkyawar zuciya akan matar.

Naja'atu tayi mamakin ganin gidansu Munira, ita kam bata dauka zata ganshi haka ba sabida irin karyar da Munira take musu a aji cewar babanta mai kudi ne tsohon dan jarida ne da yake aiki a tashar bbc ta kasar waje! bayan nan kuma yana da company na siyar da motoci da sauransu 'karya iri iri Munira keyi musu su kuma suna yarda sabida ganin irin yanda ake zuwar mata ziyara cikin babbar mota hade da kayan abinci iri iri shiyasa suka amincewa...........Munira bata gidan wai sun tafi shopping ita da Muktar..Mmn Ladi bayan ta huta ta mike da niyyar tafiya, Naja'atu taji kwallah na kokarin zubo mata dan zaman da tayi da matar taji bata son rabuwa da ita...

Mahaifiyar Munnira na hakkince a kan kujera Cikin nuna isa da nuna ita wata me kudi ce ta kalli Mmn Ladi da fadin"Ba zaki bari a kawo abinci kici ba sai kice zaki tafi."
Mmn Ladi tace"Alhamdullhi Hajiya kafin na fito daga gida sai da na karya tukkuna." Mommyn Munira ta dan gyara zamanta cikin isa ta dauki pose dinta dake gefanta ta zuge zif din ta dauko dubu daya sabuwa kar da ita ta mika mata da fadin"Gashi ki shiga napep."
Murmushin takaici Mmn Ladi tayi tace"Nagode hajiya wallahi bazan karbi kudinki ba domun kuwa ina da kudin motar komawa gida ta kalli Naja'atu da fad'in" To Naja'atu saduwar alkairi idan kin koma gida ki gaishe da mutan gidanku.'' Naja'atu tace"Nagode sosai insha Allah zan fada musu." Mmn Ladi sa kai tayi ta fita daga palon tana mamakin izgili da wulakanci irin na matar gidan koda yake dama tun kafin ta tako kafarta cikin gidan take da labarinta sai 'karyar arziki alhalin kowa yasan aikin da babban d'ansu yake yi a gari 'Ri'ka'kken d'an 419 ne (damfara) Laya ta mussaman ce dashi wace yake ma'kalawa a 'kugunsa yana shiga ko ina yayi satarsa ya fito ba tare da an ganshi ba, shiyasa komai na rayuwa baya yanke musu a gidan kuma iyayensa sun sani basu hanashi ba sai ma 'kara masa kwarin gwiwa da suke!.....Duk kuwa d'an kasuwar da ya sake yayi mu'amula da *Bash* to ya zama sorry dan sai yayi masa tas! kuma yasa malamansa sun d'aure masa baki *Bash* mugun hatsabibin mutum ne.......Jama'ar garin kuwa tamkar masu jin tsoro an rasa wanda zai fito yayi magana kowa yaja bakinsa yayi shuru sai dai idan surutu ya tashi ayi a bayan fage.

Naja'atu har duhun dare ya shigo tana zaune a guri guda a rakube dan dama Mommyn Munira bata da sakin fuska tunda suka gaisa wata magana bata sake shiga tsakaninsu ba....Sai bayan magariba ne da taga zaman palon ya isheta ta mike salo salo ta nufi wani daki dake cikin palon taje ta zabga tagumi tana tunanin wannan wane irin shopping ne Munira ta tafi tun safe bata dawo ba gashi dare yayi...Gaskiya sai dai tana tunanin bayan shopping din sunje wani gurin ita da saurayin nata......Abinda naja'atu bata sani ba shine Munira ma kwata kwata bata kwana a gidan ba tana can gidan Muktar din kwananta biyu kawai dai Mommyn tata ce ta tsara cewar sun tafi shopping ne..............

Kwanciya tayi tana share hawaye abin duniya ya isheta gabadaya kuma hankalinta yayi gida tana tunanin yanzu wane hali iyayenta suke ciki sai Musaddiq da yake yawan fad'o mata a rai!

Abbah Abbas kuwa dama tuni ta cireshi daga cikin ranta tana ganin ta ku'buta daga hannunsa har abada.
Chapter 70 · 0% Book details