Sashe 4
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halisa hankalinta yayi masifar tashi ganin irin uban gidan da'a kai Halimatu ga uban lefen da Abbas yayi mata atampopi da lesuka masu tsada kuka ta yini tana yi ta rasa nutsuwarta, mahaifiyar ma ba'kin ciki ne fal a cikinta zuciyarta tana aikace-aikacen ta na yau da kullum ta nayi wa 'yar tata fad'an wautar da tayi, in banda rashin tunani da kuma jahilci ina kai ina kushe hallitar Allah alhalin kaima baka wuce Allah ya mayar da kai wata hallitar ba, gashinan lokaci guda Allah ya juya al'amarinsa, tayi kuka tayi nadama gami da dana sani wanda hausawa suke kira da 'keya ce.
Zama mai tsafta ne yake wanzuwa a tsakanin Abbas da Halimatu! tawayarta bata hanata sauke hak'kokin mijinta dake kanta ba, Tana kula dashi sosai dan wani sa'in idan yaga tana hidima dashi har tausayi take bashi dalili yanayin tafiyarta da rashin kuzarinta ma abin tausayi ne, amma abin na bashi mamaki sosai! kafin ya dawo daga kasuwa ta gama komai na gida tayi masa kwalliya mai burgewa. duk sanda ya shigo gidan yayi tozali da ita wani farin ciki ne yake rufeshi, wai shin meye aibunta ne?
Halimatu bata da wani abu ko nakasu a gurinsa tinda duk wasu hakkokinsa tana saukewa kwata-kwata nakasarta bata dameshi ba zahirinta yake so ba wani abu na jikinta ba, zaman lafiyar da suke da juna ya sanya yake ji a cikin ransa zai iya zama da ita har'karshen rayuwarsa.
*****
Wata goma cif da auransu Maryam matar Yayanta magaji ta haifi d'a namiji, murna da farin ciki a gurinta tamkar ita ta haihu kullum tana gidan tare da mai jego tayi ta hidima da ita da jinjirin 'Yan uwan Maryam suyi ta tausaya mata idan sunga ta wani abun na wahala sai suce ta zauna, murmushi kawai take musu ta rabu dasu idan kuma sun matsa mata takan ce dasu itafa babu abunda ba zata iya ba saboda haka su daina yi mata kallon mara lafiya da rashin kuzari!
To suma ganin ranta ya 'baci yasa suka daina cewa da ita komai! kafin ma suzo ta shiga gidan ta gyara tsaf ta gyara yaron sannan ta had'awa maijego abun kari, sannan ta dawo gidanta tayi wanka ta shirya ta sake komawa, haka ta dinga zurga zurga har sai da akayi suna inda yaron yaci sunan Maigidanta Abbas sai take kiransa da Amir...................KullumAmir a hannunta yake wuni sai dare take mayar dashi ko kuma idan ya bukaci nono sannan, gabadaya dai ita Maryam haihuwar yaron tayi amma raino yana gurin Halimatu, idan ta dauki yaron tun safe to sai dare ita dashi.
Abbas bashi da matsala ta 'bangaran wannan dan shima mutum ne mai son yara duk sanda ya dawo ya tarar da ita tana fama da takwaransa yakan ji dadi yayi ta addua Allah suma ya basu nasu mai albarka.
Shakaru uku da auransu Halima bata ta'ba 'batan wata ba, gashi har anyiwa Amiri 'kanwa Ilham, Abbas tun yana daurewa dai har ya kasa hakuri yace ta shirya suje asibiti a dubasu, koda sukaje likita ya dubaso gabadayansu babu abunda ke damunsu kawai dai lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, likita ya rubutu musu magani mai kyau yace suje suyi amfani dashi insha Allahu za'a dace.....Dukkaninsu a sanyaye suka koma gida, kuma ba suyi 'kasa a gwiwa ba suna amfani da maganin kuma suna sake kula da kansu.
Ramlatu kuwa a duk sanda suka had'u da Halimatu a taro sai ta zage ta tayi mata gorin rashin haihuwa, duk taro na family dinsu sai ta tara mata mutane tayi ta nuna ta tana fad'in mugwayen kalamai a kanta, wata irin tsana Ramlatu keyi wa Halima ko ta mece oho! dan akwai ranar da tazo har gida taci mata zarafi da fad'in sun gaji da jiran gawon shanu dan su duk irinsu babu mara haihuwa saboda haka sun gaji da daci da ita idan ba zata haihu ba to zasu kawo wacce zata cika musu gida da 'ya'ya.'
Wannan cin zarafin ya 'bata marai rai sosai ta yini tana kuka dan ki girki ba tayi ba ballanta tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba, koda maigidan ya dawo rasa gane kanta yayi, tambayar duniya tayi masa shuru sai kuka take yi, tsayin shekaru uku da auransu bai ta'ba fuskantar irin wannan matsalar daga gurinta ba, da kyar ya samu yayi wanka ya futo palon tana dai zaune a inda take tana kukan da take, zama yayi kusa da ita yana sake rarrashinta kan ta fada masa abinda ke faruwa, da kyar tayi masa magana tana hawaye gwanin tausayi ta
ce ita taga ji tunda bata haihuwa ya 'kara aure ko kuma ya saketa dan cin zarafin da Yayarsa take mata ya isheta.
Ransa idan yayi dubu ya 'baci! shin wai me yake damun Ramlatu ne? ina ruwanta da matarsa ina kuma ruwanta da rashin haihuwarsa, idan zai mutu bai haihu ba bai dameta ba shine yaga zai iya zama da matarsa a haka, shi kam ya rasa wace irin 'kiyayya Ramla keyi wa Halimatu, hakuri ya bata sosai yace zai same ta yaja mata kunne kan kada ta sake zuwar masa gida.
Jin abinda ya fad'a yasa hankalinta ya tashi sai ta dinga bashi hakuri tana nuna masa illar abinda zai aikata, mutukar ya tunkari Ramlatu da wannan maganar to babu shakka ya sake rura wutar gaba mai zafi a tsakaninsu, kuma ita ba zata so su samu matsala da 'yar uwarsa ba, Nuna mata yayi ya hakura ba zaije gidan Ramlatun ba........Washe garin ranar kafin ya tafi kasuwa sai da ya tsaya gidan Ramlatun sukayi ta babu kyau babu dad'i a tsakaninsu, dan ya nuna mata mahimanci da matsayin Halima a gurinsa kuma ya nuna mata cewar itama ta tsaya a matsayinta na 'yar uwarsa mutukar tasan wata fitina ce zata kaita gidansa to kada ta sake zuwar masa gida, dan tuntuni shi ya riga yasan Allah ne ke bada haihuwa ba wani mahaluki ba!
Ramlatu kuka taci ta 'koshi 'dan uwanta da take alfahari dashi shine yazo ya ci kata mutumci a gaban kishiryata lallai babu shakka dole sai ta tashi tsaye kan Halima dan da alama Iyayenta suna tsaye a kanta gurin ganin ta mallake mata d'an uwa.
*Kaji rigima ta Ramlatu ke ba uwar Abbas ba komai ba amma kina kishi da matarsa, Uwar miji aka sani da kishi da matar d'anta Uwar mijin ma irin wacce bata san abinda take ba.*
Abbas zuciyarsa wasai yaje kasuwa yayi harkokinsa......koda suka tashi daga kasuwar kai tsaya 'Kofar Na'isa suka nufa dan ji yake idan bai fad'awa mahaifiyarsu abunda Ramla ke masa ba za'a iya samun matsala nan gana gwara ya fada mata ta kira ta ta ja mata kunne.
Hajiya Abu ranta ya 'baci sosai tace"Ni dik abinda ke faruwa a tsakaninsu ban sani ba wallahi amma Wannan yarinya anyi babbar kwabo wallahi dan taga matar taka mai saukin hali ce shiyasa take mata cin kashi a ko'ina amma kayi hakuri ka kuma bawa Halimatun hakuri insha Allah zan aika yara har gidanta su kira min ita zan mata tsakani da matarka duk sanda ta sake zuwa gidanka domin ta kuntatawa matarka to babu shakka na samu labari da Alhaji maihifinku zan had'ata....
To tun daga wannan rana Halimatu ta samu lafiya Ramlatu ta saurara mata da gorin haihuwa ammafa sa'i da lokaci suka had'u a wata sabgar sai ta yar mata da habaici al'amarin Ramlatu sai addua.
*****
Halisa ce ta shiga kara kaina a gidan, mussaman ranaku guda biyu Juma'a da Lahadi ranakun da ta tabbatar da cewar maigidan nan bai futa sai taci uwar kwalliya ta sanyo turare mai 'kamshi tazo ta yini a gidan! idan sun had'u dashi tana nuna masa kamar babu wani abu a ranta, ta hakura dashi kawai ta zuwa ziyara ne gurin 'kawarta!
Sai dai ya girgixa kansa kawai ya shareta dan shi ba yaro bane ballanta ta raina masa hankali.........Ita kuwa Halima zuciyarta ce ta shiga sa'ka mata wani abu! tana ganin tunda dai har yanzu Halisan bata da tsayayye mai zai hana ya aureta ya had'asu tunda ta lura da Halinsa tayi hankali kuma duk wasu alamu da take nunawa a kan mijin nata ta gane sabida shi take zuwa gidan........Koda ta sameshi da maganar cewa yayi zaiyi shawara zai fada mata kome ya yanke!
Kwana biyu ta sake tuntu'barsa da maganar ya dinga kallonta yana mamakinta yace."Ke kina ganin idan na auri Halisa na had'aku babu matsala kuma zaki iya zama da ita."?
Cikin farin ciki tace"Zan zauna da ita tsakani da Allah nasan ko ta nufe ni da sharri zai koma kanta tunda ban cuce ta ba, sannan kuma ina so ka aureta kaga tanan za'a tabbatar da rashin haihuwar mu shin waye yake da matsala tsakanina da kai."!
Wannan magana da tayi sai ta sake sa masa 'kwarin gwiwa shima yana so ya tantance waye mara lafiya a cikinsu, kai tsaye ya tunkari Halisa sa maganar, ranar kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki! ta dinga murna da godewa Allah!
Yace."Ina so ki zauna lafiya da Halimatu dan da yawun bakinta nazo nan neman auraki kada ki shiga gidana ki tayar mana da hankali mun gina rayuwarmu cikin mai kyau da inganci" Halisa taji wani irin d'aci a ma'kogwaronta! wato ma ba'a karan kansa yazo neman auranta ba sai da izinin matarsa!
'kwafa tayi a cikin ranta! a zahiri kuwa cewa tayi" Haba Alhajina kada ka damu zan zauna lafiya da ita ai ko lokacin baya ma kuruciya ce ta janyo nayi wannan furucin amma ka daina kokwanto da shakku a kaina."
Yaji farin ciki ya kamashi dama can yana son Halisa halinta ne baya si to tunda dai yanzu tayi hankali zai aureta su zauna tare cikin inuwa daya.
Ba'a wani ja dogon lokaci ba aka d'aura aure Halisa ta tare a dakinta, da yake gidane mai dauke da bangare uku sai kowa ya dauki d'aya, kasancewar babu yara a gidan yasa maigidan ke bin 'Dakunan matayen nasa bai tare a nasa part ba din sai ranar da ya tara iyali tukkuna.