← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 143

Sashe 58

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halisa da kyar ta iya binsa dakinsa ta taimaka masa yayi wanka ya shirya jikinsa suka zauna suna mayar da maganar abinda ya faru ita dole sai ta wanke kanta ta d'ora laifin abinda ya faru a kan Naja'atu shi kuma ya kasa fahimtar ta shifa ba zai fahimci komai ba mutukar magana ta kasance a kan yaransa to yakan iya daukar mataki mai tsauri a kan koma waye (Lallai Abbah Abbas kana da son 'ya'ya da yawa) Halisa da taga ya kasa fahintarta sai ta kawai ta bar maganar ta shiga fada masa zuwan mai'aikin da hajiya ta turo...Yace."To alhmdullhi naji dadin zuwanta kowa sai ya huta dama dake da Naja'atun dukkaninku kuna ganin kyashin kulawa da yaran wannan kuwa kudi zan biya ta nasan zata kula min dasu.

Halisa ta rike bakinta tana kallonsa da mamaki a tare da ita tace"To me kuma yayi zafi da fadin wannan maganar." ?

Yace."Duk maganar dana fada a kanku ai ba karya nayi ba, ke 'yar da kika haifa ma baki nuna kulawarki a kanta to akan wa zaki nuna." Halisa ganin yana nema ya mayar da abin rigima sai ta shiga bashi hakuri wai ya bar maganar kada tayi tsayi ita dai tasan tana iyakacin bakin kokarinta a kan yaran, kuma tasan Allah yasan zuciyarta.....Jinta kawai yake saboda halinta sai da ya fadawa wani
Idanunta ne ya sauka kan ledojin kayan lefen Naja'atu da suke ajiye a gefe guda, tace"Wai wannan yarinyar ba zata dauki kayanta ta kai d'inki ba."
Yace."Tace bata so ki kwashe ki bawa wanda ya dace! kafin mu tafi umara zamuje da ita ta duba duk abinda take so..Halisa zugum! tayi tana kallonsa cike da mamaki tace"Yanzu meye laifin kayan nan da zate ce bata so kai kuma zaka biye m
ata wallahi ka dinga amfani da kudinka a inda suka dace." Cike da kishi ta fadi maganar
Yace."Duk da ban san kayan mata ba na duba naga kayan na gane basu da kyau da quality saboda haka tunda tace ba suyi mata dole a sanja mata wasu tunda hakkinta wannan kuma ni nace ki bayawa mabukata ko a cikin danginki ne."
Halisa sai taji maganar tasa kamar da akwai cin fuska a cikinta Ikon Allah!

Lallai yau ya shigo gidan da son yaci zarafinta dan haka sawunta a likkafa ta fita tabar masa dakin.
*( To dama waye ya fad'a miki kullum ake kwana a gado Halin namiji ai yafi dubu yau zuma gobe mad'aci! haka suke Komai asirinki idan wani namijin ya burkice miki sai kin rasa yanda za kiyi gwara ma ki daina asirin shi zai fi miki alkairi*)
Daure da alwala ya fito ya samesu a zaune a palon Naja'atu ta sake sai dariya take ita da yaran ya kallesu yana jin dadi a ransa a duniya yana so ya gansu suna walwala yace."Ku tashi kuje kuyi sallah!

Da sauri suka kashe tv din shi kuma ya kama hanya ya fita da niyyar shiga massalaci
Sai da ya sallaci isha'i ya shigo, kai tsaye gurin cin abincin ya nufa, Naja'atu da yaran suka bi bayansa, sukayi zaune suna jiran Halisa tana daki ta'ki fitowa sai haushi take ji...Ya kalli Mufida da fadin taje ta kira ta.

Yarinyar ta fito ta zauna tana kallonsa tace"Wai gata nan zuwa." Suka cigaba da zaman jiran fitowarta bata fito ba, Ya kalli Naja'atu da fad'in "Zubawa kowa abincinsa." Ta kuwa mike da sauri ta shiga had'awa kowa nasa, dadi take ji itama yau ta samu galaba kan Halisa.......Tun kafin ya fara cin towon ya bashi sha'awa kuma gabadaya girkin baiyi kama dana Halisa ba yace"Da alama wannan abincin na bakuwar da mukayi ne." ?

Tace"Eh nima bayan na dawo daga gidan aunty maryam na tarar da matar tace sunanta Larai daga gidan Hajiya." Ba tare da yace komai ba yayi bisimillah a nutse ya fara cin abincin gaskiya yaji dadin abincin matar sosai ashe Halisa ba ta iya komai ba hakuri kawai yake amma yanzu tunda ya samu mai aiki dattijuwa wacce ta iya girke-girken zamani dana gargajiya to yasan matsalarsa ta kare....
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina so ki biya kudin karatu ga yanda abin yake.

Vip gruop#600
Normal #300
Account:0542382124...Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Mddbhrmbn37
Har suka kammala cin abincinsu Halisa bata fito ba tana dakinta a kwance abun duniya ya isheta, gabad'aya ba tayi tsammanin al'amarin zai kasance haka ba ita abinda taso shine yana dawowa yaci mutuncin yarinyar ko kuma yace ta koma inda ta fito kamar yanda ya saba yi mata a duk lokacin da ta fita ba tare da izininsa ba to tana dawowa ko zama baya bari tayi zai ce ta koma inda ta fito, sai tayi kuka ta bashi hakuri sosai tukkuna yake barinta ta shiga gidan......Abunda kuma ya sake hassala mata zuciyarta shine ganin kwata-kwata daya shigo gidan baiyi maganar ba ballantana yayi wa yarinyar fad'an fitar da tayi ba tare da izininsa ba, bayan kuma d'azu data kirashi a waya ya nuna fushinsa harda cewa idan ya dawo sai ya hukunta yarinyar sai gashi ya kasa aikata komai a kanta ta tabbata idan itace ta futa ba tare daya sani ba sai yayi mata cin mutunci amma da yake Naja'atu ce ya kasa cewa komai, gaskiya alamarin yayi masifar bata mata rai! bayan haka kuma yana maganar zai dauki yarinyar suje siyayya ita kam ta rasa yanda zata kamo bakin zaren daga aiki ya fara kyau sai ya lalace! ta rasa wane irin sirri da asararai Baba malam yake dashi wanda da yakewa 'ya'yansa, lokacin Halimatu ma haka tasha wuya da jikinta da aljihunta, daga ta fara ganin daidai sai aiki ya wargaje! to yanzu ma ga Naja'atu tazo tana lalata mata aiki wai shin ya za tayi ne!? *(Hum Halisa kenan Baba malam babu wani abu da yakewa 'ya'yansa face addua itace maganin kowa ce irin masifa! kuma dama waye yace miki asiri na tabbata? asiri gaskiya ne tunda ya kama fiyayyan hallita annabi Muhammad slw! amma karfin addua bai sa yayi tasiri a jikinsa ba, karkarin asiri kwana bakwai zuwa ar'ba'in ya lalace shiyasa zaku ga masuyi kullum suna tafe kamar mahaukata! sannan kuma Wani lokacin asirin da Halisa keyiwa Abbah Abbas yana tasiri a kansa amma kuma akwai lokacin da asirin ba zaiyi tasiri ba a tare dashi ba tunda dai shi ya kasance mai yawan azkar da addua domin kare kansa da iyalinsa, idan hakane kuwa yana da kyau Halisa ta gane cewar aikin banza takeyi domin akuwa asiri ba zai ta'ba sanja mata Abbah Abbas ba ya koma lusarin namiji kamar yanda take b'ukata.....Mata masu biye-biyen malam wallahi ku daina kuyi wa kanku fad'a! babu wani abu da boka ko dan bori zai muku a duniyar nan face abinda Allah yayi muku suma bokayen Allah ne ya basu wannan ilimin domin sun kauce masa sunbi shaid'an to dama shi shaid'an kullum tunaninsa yaya za'ayi ya janyo wani jikinsa domin ya cutar dashi kamar yanda yayi wa Allah al'kawari!

Duk mutumin daya had'a Allah da waninsa to ya ta'be!

Kuma Ubangiji ya lan'ance shi, Allah na yafe wa bayinsa lafuka da yawa amma kuma baya yafewa bawansa idan ya had'ashi da abokin tarayya ba........Allah bashi da kishiya shi kad'ai ne tal sabida haka ka/ki nemi biyan bukata a gurinsa ba'a gurin wani ko wata ba.*
Naja'atu na kokarin barin daning din ya kalleta cikin kulawa yace." ta koma ta zauna yana so za suyi magana." a sanyaye ta koma ta zauna tana dan kallonsa....Yace." Ina fatan baki mance cewar yau kwanaki bakwai din da musulunci ya tanadar miki suka 'kare ba." Ta kalleshi tana dan nazari, ita ta manta dan ba lissafawa take ba.

Yace."Yau zan koma dakin Halisa insha Allah zaku cigaba dayin kwana bibbiyu kamar yanda muka tsara ranar da kika zo gidan nan da sunan matata.

Shuru yayi wai ko za tayi magana, tayi shuru bata ce komai ba, sai ya cigaba da cewa''Sabida yawan sa'bani da kuke samu da Halisa yasa na yanke shawarar cewa zaki koma d'aya 'bangaran da zam...katse shi tayi tun kafin ya karasa tace"Umum!

Abbah ni tsoro nake ji wallahi nafi so in cigaba da zamana anan." Yace."Ni kuma bana son tarayyarki da yara dan sabida watarana kada su gane wani abun.....ki koma gurinki yafi alkairi.

Murya na rawa tace"Dan Allah ka barni anan d'in Abbah." Yace." ba zai yiwu ba Naja'atu a duk ranar girki zaki dinga yi min yawo da hankali a gaban yara na sabida haka na yanke wannan shawarar."
Had'ashi da Allah ta shiga yi kan yayi hakuri ya barta anan din tayi al'kawarin zata zauna da Halisa lafiya.

Ganin tana kuka yasa jikinsa yayi sanyi yace"To shikkenan na kyaleki tunda kinfi kaunar ki takura kanki har yanzu kin kasa zama cikakkiyar mace a gidanta ke kenan ra'be-ra'be daga wannan d'akin zuwa wannan." Shuru tayi ba tace masa komai ba.

Yace."Insha Allahu sati mai kamawa zamuje umara nida Halisa da Hajiyarmu kafin mu tafi zamuje dake sahad store ki had'o lefanki sannan kema tuntuni na siya miki mota inaso ne naga kin 'kara hankali da nutsuwa sai na baki key din.

A sanyaye tace"Abbah daka bar maganar lefan nan dan ni basu ne a gabana ba."!

Tsira mata ido yayi cikin sigar tuhuma yace."Menene a gabanki."!?

Ganin yana mata kallon zargi yasa ta sunkuyar da kanta tace"babu komai." Yace"Karya kike kina so kice abinda ke gabanki rabuwa da aurena ko."?
Chapter 58 · 0% Book details