Sashe 18
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Allah yasa ya taulace ya zama wanda bashi da cin yau bare na gobe insha Allahu kuma Naja'atu sai ta zame masa masifa a rayuwarsa, tana kuka take wannan surutan tamkar wata mahaukaciya, Cikin wannan yanayi suka shigo gidan shi da yaran gabad'aya dan dubara yayi wa Baba malam yace zai tafi dasu Mussadiq saboda zasu koma makaranta, baba malam baiji dadin haka ba dashi da Abba Magaji sun fahimci cewar abinda Naja'atu tayi musu ne yasa yaji sha'awar dauke yaransa.......Kai tsaye Dakinsa ya nufa yana so ya samu nutsuwa sosai kafin ya tunkari Halisan dan ya fahimci dole sai ya karyar da kansa mussaman yanzu da ya dauko nauyi 'yayansa ya d'ora mata.........Mufida da Saddiqa Mussadiq suka nufi bedroom din Halisan nan suka tarar da ita ba yanda take sai sambatun surutai take da alama dai har yanzu mutanan nata basu gusa daga jikinta ba, Mufida taje ta zauna kusa da ita tare da dafata tana kiran sunanta.........Saddiqa da Mussadiq a bakin kofa suka tsaya saboda dama can sun san halin masifar Halisan ba kaunarsu take ba sai taga Abbansu take yi musu magana da wasa da dariya, shiyasa suka kasa 'karasawa, Halisa ta juyo tana kallon 'Yarta Mufida ganin su Saddiqa a tsaye a bakin kofa yasa ta mike tsaye a furgice tace"Ku dan Ubanku waye ya kawo ki gidana maza ku fuce mun daga d'aki shegu tsinannu 'yayan asara."!
Saddiqa da Mussadiq suka zabura! a tsorace suka fita daga d'akin sukaje suka nemi kujerar palo suka zauna jikinsu sai rawa yake dama can Saddiqa da Mussadiq suna masifar tsoron Halisa Naja'atu ce take musu maganinta.......Mufida na goge hawaye tace."Mommy ya kike zaginsu su Yaya Saddiqa ne fa 'yan uwana." Wani irin bahagon mari ta kifawa yarinyar tana huci! tace"Zanci Kutumar ubanki wallahi shegiya munafuka ni zaki fad'awa su d'in 'Yan uwanki ne?
Wallahi duk ranar da kika 'kara kiransu da sunan 'yan uwanki sai naci ubanki." Mufida tana kuka tace"To mommy me yasa kika tsanesu bayan mamansu ta mutu dan Allah ki daina yi musu abinda kike musu babu kyau."!
A fusace! ta sake gaura mata wani mari tana wata irin fuffuka tace"Tashi dan babanki mara mutunci ki bar min dakina ko kuma yanzu na sumar dake." A gigice! yarinyar ta mike hannunta dafe da kuncinta ta fita daga dakin tana kuka, wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga daki yana sanye da jallabiya ruwan toka, Ganinsu Saddiqa sunyi muzu-muzu a zaune yasa jikinsa yayi sanyi ya kalli Mufida dake dafe da kunci tana kuka, yace."Menene?
Cikin rawar murya tace"Mommy ce ta mare ni tace na fito mata daga d'aki.
Ba tare da yace."Komai ba ya kama hanyar dakin Halisan, Har yanzu tana zaune gefan gado ta had'a tagumi babu maganar sallah a tare da ita, cikin nutsuwa ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama, Kallonsa ma ba tayi ba ballanta ta amsa masa sallamarsa, gefanta ya zauna yana kokarin ri'ke hannunta ta fizge a fusace! ta mike tsaye tana nunashi da hannu tace"Kaga dan girman Allah ka fita ka bani guri naji da abinda ke damuna baka da abinda zaka ce dani." Yaji zafin maganarta amma sai ya danne ya mike ya iske inda take, Rungumeta yayi a jikinsa yayi amfani da wata murya wacce ya tanade ta dan rarrashinta, yace."Haba Halisa wai duk me yayi zafi ne kike nema ki zautar da kanki akan abinda bai kai ya kawo ba!
Menene abin damuwa dan nace zan auri Yarinyar nan Naja'atu? idan kin kwantar da hankalinki kin ri'ke girmanki sai kinfi daraja da kima da martaba a idona!
Shin wai baki ga yanda Halimatu ta sadaukar da rayuwata a kaina ba, bana shakka ko tantama Halimatu yanzu tana gidan aljanna saboda ta rabu dani da iyayenta lafiya, kuma ta mutu hanyar haihuwa, har na gama rayuwata ta duniya bazan ta'ba mantawa da Halimatu ba, a kwanakin baya kin soma kwaiwayon hali da d'abi'unta amma tashi guda zaki watsar da abin da kika fara na alkairi, wallahi auran Naja'atu da zanyi ba zai sanya ni na daina kaunarki ba, kin san dai kece macen dana fara furtawa kalmar so, ko Halimatu ma kece kika jawo na aureta, to itama Naja'atun ina so ki sani bani ne nace inaso ta zama *Madadin 'Yar uwa
rta ba* Iyayenta ne suka nemi haka dan ko yanzu sai da na fada musu cewar maganar auran su barta suka nuna sai anyi So inaso ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa ki kula dani da yarana gasu nan na kawo miki su ni kuma insha Allahu zan baki mamaki zan nuna miki ni d'an halak ne auran Naja'atu ba zai sa na juya miki baya ba." Shuru tayi jikinta duk yayi sanyi da kalamansa tace"Nifa ban hanaka aure ba wallahi ko budurwar zaka aura to kaje ka aura amma banda yarinyar nan bana kaunarta saboda bata ganin girmana." Yace."Na fad'a miki fa cewa kece uwargidana duk ragamar mu tana hannuki har ita Naja"atun idan tazo a 'karkashin ki take sai abinda kika tsara a gidan shi za'ayi." Jin wannan maganar tasa yasa ta sauke ajiyar zuciya tace"Nifa wallahi nasan dadin baki ne kake mun yarinyar nan na zuwa zaka manta dani, dan haka gwara tun kafin tazo na san inda dare yayi min dan bana tunanin zan zauna da ita a karkashin inuwa guda." Yace."In banda abinki ba gidanku daya ba to me zai dame ki da ita ko wacce na gidanta idan wannan da kike ciki bai miki ba sai na sauya miki wani." Tsaki taja tace." bazan yarda ba wallahi sai dai ka had'amu gida daya dan bazan amince a cutar dani ba." Yace."To shikkenan duk abinda kike so shi za'ayi, Zan sa a gyara miki side d'inki dake gidana na *'Danbare* ina fata hakan yayi miki." shuru tayi tana zum'bura baki, Ya saketa yaja hannunta suka zauna a nutse yace."Ki fad'a mun duk abinda kike so na siya miki na fad'ar kishiya komai tsadarsa zan siya miki." Tace"Sai nayi shawara tukkuna." Dariya ta bashi amma beyi ba yace."To shikkenan inaso na baki kudi kije ki had'o mata lefe kuma kema ki had'a naki hakan yayi miki." Dadi ne ya rufe ta tace"To Hakan yayi amma inaso ka sanja min mota." Yace."An gama ranki ya d'ade! amma dan Allah daga yau sai yau kada ki sake aikata abinda kika aikata a d'azu! rashin hankali ne kawai kije ki dauko wu'ka kina so ki kashe ni! kina tare da shed'an a lokacin idan da tsautsayi sai ki aikata aikin dana sani ki 'kare rayuwarki cikin uku'ba kuma ki mayar min da yara marayu." Hanci ta sha'ka! cikin takaici tace"Haba ai wallahi idan ma nayi maka rauni ban huce bacin raina ba, kana kallonta ina magana ka tsalleke ni ka tafi ai dole zuciya ta ta tunzurani a kanka." Yace."Tom yanzu dai duk magana ta wuce Gobe insha Allahu bayan sakkowar sallahr juma'a za'a daura auran amma ina tunanin ba zata tare ba sai nan da sati biyu." Halisa gabanta ya fad'i tace"Da wuri za'a daura auran ashe."?
Yace."Baba Malam ne ya yanke hukuncin haka." Cikin tsabar bakin ciki da takaici tace"Aikin banza aikin hofi 'kwad'ayayyen tsoho mai son abin duniya ai dama dole ya gaggauta yin abun kodan bukatarsa ta biya." 'Bata rai yayi yace."To yanzu zamu 'bata dake kuma bana son wannan d'abi'ar taki ta zage-zage da rashin ganin girman manya." Cikin fusata! ta mike ta nufi toilet tana surutai da 'kananun maganganu, kallo ya bita dashi, Al'amarin Halisa dai sai gyaran Allah, yaji dadi sosai da ya shawo kanta cikin ruwan sanyi *(Tabbas haka maza ya kamata su dinga rarrashin matansu idan zasu 'kara aure, sau tari wasu mazan sune suke ingiza zuciyoyin matansu ga aikata abinda ba shikkenan ba, idan ya kasance zaka 'kara aure to yana da kyau ka dinga nuna kulawarka a kan matarka ta gida, kuma banda kiran wayar amarya a cikin gidan dan hakan ma na iya janyo muku samun sa'bani a tsakaninku*) Mikewa yayi ya fita daga dakin yana dan jin sassauci a cikin zuciyarsa tunda ya gama da matsalar Halisa yana ganin duk abinda zai biyo baya mai sauki ne.