Sashe 15
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa tayi kici-kici da fuska kamar gaske tace ita sai ya bata zata cika masa hannu idan kuma bai bata ba sai ta cire masa kayan jikinsa a bakacin kudinta......Saddiqa sai dariya take musu, Mussadiq na ganin Naja'atu ta shigo yace."Yawwa Yaya Naja'atu kizo ki cece ni a gurin tsohuwar nan tana so ta karya min hannu." Hjy Abu tace'' Kina zuwa nan sai na murd'e miki hannunki dan dukkanin ku zan iya daku."
Naja'atu tasa dariya tana k'arasawa gurin tace"Lallai Hajiya 'karfi ne dake haka duba kin murd'ewa yaro hannu ki fad'i nawa ne kudin sai a biya ki." Tace."Ai ba zaku iya biya na ba." Tace"To dan Allah sakar masa hannu ya tuba." Tana dariya ta sake shi tace"Ja'iri ashe ba wani karfi ne dashi ba." Yace."Hajiya aike tsohon 'kashi ne dake ni kuwa sabo ne shiyasa da kika ri'ke ni na kasa kwacewa." Gabadayan su suka sa dariya har da ita.
Naja'atu ta zauna a nutse tana gaisheta!
Ta amsa cikin kulawa tana kallonta tace"Dama kuwa ina neman ki amma ki fara zuwa ku gaisa da Alhaji yana sama sai kizo mu tattuna magana kinji 'kawata." Naja'atu ji tayi gabanta ya fad'i !!! to wace magana zasu tattauna da hajiyan? tabbas ta tsuniyar gizo bata wuce ta 'koki! sai
Tayi kokarin kauda damuwar fuskarta tana kokarin mikewa tace to shikkenan bari naje mu gaisa da Alhjin."
Sama ta hau inda dakin Alhaji Sama'ila yake, nan ta tarar da Hajiya Rabi a dakin tana gyare-gyare suka gaisa cikin mutunci kafin ta shiga dakin da yake ciki............Tayi kusan minti goma a ciki kafin ta sauko 'kasa suna zaune a inda suke suna hira koda ganin zuwanta gurin sai sukayi shuru Saddiqa ta dinga bin fuskarta da kallo ganin kamar ta sauko da damuwa a tare da ita............zama tayi kusa da Hajiyan cikin tunanin mafita tace"Hajiya gani to na dawo." Hajiya Abu ta gyara zamanta sosai ta bude bakinta kenan za tayi magana, Yaya Ramlatu ta shigo bakinta dauke da sallama.
Amsawa sukayi gabadayan su, Ramlatu na ganin Naja'atu kusa da Hajiya sai ta 'bata rai! tayi kici-kici da fuska dan koda Naja'atun ma ta gaisheta bata amsa ba sai gaisuwar su Mussadiq ta amsa!
Naja'atu jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa tana jinta tana tambayar su Saddiqa ina Abbansu suka ce ya tafi kasuwa!
Yaya Ramlatu ta kalli Mahaifiyar ta tace"Hajiya wata magana naji daga bakin Salim dazu da safe yake fada min shine nace to bari nazo naji shin da gaske ne abinda ya fad'a wai Abbas zai auri waccan yarinyar ta zaune." Tana nuna Naja'atu da hannu tayi maganar.
Hajiya Abu a nutse tace"Eh kwarai kuwa hakane Salim bai miki karya ba!
Abbas zai auri Naja'atu insha Allah sai ta zama *Madadin* 'Yar uwarta ko babu komai wad'annan yaran zasu samu walwala da farin ciki."tafada tana nuna su Saddiqa.
Yaya Ramlatu ta zabga salati tana tafa hannu tace"Haba Hajiya da hankalinku da komai zaku bari wannan al'amarin ya faru?
Yanzu shi Abbas din ko kunya baiji ba zai auri yarinyar da ya ri'ke ta a matsayin 'yar sa, yarinyar da kuma ya san Salim ne ke neman auranta shine kuma zai had'a takara dashi! a gaskiya wannan abu bai tsarantu ba! gwara tun wuri yayi wa kansa fad'a dan wallahi idan ya sake ya auri wannan yarinyar to duniya sai ta zage shi saboda ya aikata abun kunya, kuma baiyi wa Salim adalci ba."
Hajiya Abu tace"Kece kike ganin kamar hakan bai dace ba amma *MADADI BA HARAM BANE* Dan ya ta mutu a mayar da kanwa d'akinta ba laifi bane!
Kuma naji kina cewa duniya zata zagi Abbas a kan me? duniya zata zageshi? naga ke da kanki kika nuna bakye so 'Danki ya auri yarinyar to me yasa kuma yanzu zaki zo da wata magana, idan Salim mai hankali da tunani ne ya dace yayi wa Kawunsa adalci ya hakura da yarinyar ya bar masa kodan marayun 'yayan dake gabansa."
Yaya Ramlatu tace"A'ah!! ni ban hana Salim auran yarinyar nan ba wallahi a duk lokacin da zamuyi maganar auransa yakan ce dani Abbas din ne yake cewa ya dakata tukkuna zaiyi magana da iyayenta, sai kuma yanzu kawai daga ya rasa matarsa ya 'kwace masa budurwa ai hakan sam bai dace ba."
Hajiya Abu tace"To ai sai kiyi tayi dan tuntuni an riga an gama magana insha Allahu kafin nan kafin sati uku za'a daura auran Abbas da Naja'atu insha Allah."
Wani irin kuka ne ya kufcewa Naja'atu! da sauri duk suka juya suna kallonta! had'a kanta tayi da gwiwa tana kuka sosai da sosai!
Yaya Ramlatu tace"To hajiya gashi nan dai kin gani zahiri yarinyar nan bata son wannan al'amari dan dai ba zata iya fitowa ta fada muku bane! a wannan zamanin ba'a yiwa yaran yanzu auran dole kada ku tauyewa yara hakkinsu, ni a ganina Abbas ya hakura kawai ya barwa Salim shine maslaha."
Hajiya jikinta ne yayi sanyi ganin irin gursheken kukan da Naja'atu keyi tana kokarin tayi magana Alhaji Sama'ila ya sauko daga sama!
Ganin Naja'atu na kuka sai hankalinsa ya tashi ya zauna kan kujera yana tambayar abinda ke faruwa, Yaya Ramlatu ta shiga warware masa duk abinda yake tsakin Salim da Naja'atun da irin soyayyar da suke.
Alhaji Sama'ila yayi shuru yana nazarin maganar, shi duk abinda akeyi bai san da maganar Salim a ciki ba, to gaskiya idan hakane shi Abbas din shine ya dace ya hakura da yarinyar duba da cewar maganar Salim din ta dad'e kuma shi ya san da ita bai fad'a ba saboda biyan bukatarsa, wannan ba adalci bane, a matsayin sa na wanda suka dauka a matsayin uba a garesu to bai dace yayi musu haka ba, dole ya janye maganar auran yarinyar ya kyale yara suyi auransu.
Ya kalli Naja'atu a nutse yace."Daina kuka Naja'atu ki kwantar da hankalin ki insha Allah ba zaki auri Abbas ba tunda bakya sonsa zamu baki wanda kike so insha Allahu."
Jin abinda Alhajin yace yasa Saddiqa ta fashe da kuka!! ta had'a kanta da gwiwa tana shashsheka! tofa gida ya zama na makoki mutuwa ta dawo sabuwa dan Saddiqa rungume Mussadiq tayi tana fad'in "Mussadiq mutuwa tayi mana tonan silili kowa sai gudun mu yake ana neman kai damu! meye laifin Ubanmu da ba'a sonsa!
Ubangiji Allah ya zama gatanmu." Hajiya Abu ta rikice da kuka ta kama yaran ta rungume a jikinta tana fad'in "Babu wanda ya isa yayi neman kai daku!
Kuma insha Allahu Naja'atu zata tare a gidan ubanku."
Yaya Ramlatu jikinta ne yayi sanyi ganin mahaifiyar tata na kuka.........Bayan alhajin ya fita Hajiya Abu ta goge fuskarta tana kallon Ramlatu tace"Kin kyauta kan abinda kikeyi kullum burin ki ki tayar min da hankali bakya kaunar na zauna lafiya yanzu meye amfanin wannan abun da kika zo kikayi ashe kinfi kaunar d'anki a kan d'an uwanki? meye Abbas beyiwa d'anki ba amma da abunda zaki saka masa kenan! kinzo kin saka marayu kuka da damuwa suna cikin damuwa a maimakon ki taya su alhini sai kizo ki sake saka musu wata damuwar to sun gode da abunda kikai musu."
Yaya Ramlatu ta share guntin hawayen fuskarta a sanyaye tace"Hajiya ban san al'amarin zaiyi miki zafi haka ba dan Allah kiyi hakuri idan ranki ya 'baci kuma insha Allahu zan umarci Salim ya janye maganar auransa da yarinyar Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Jin abinda tace ne yasa Naja saurin kallonta hawaye na tsere a fuskarta shikkenan magana ta 'kare! jiki a sanyaye ta mike ta fita daga palon.
Salim na driving maganar dake damusa nata cin zuciyarsa, ya dan kalli Kawun nasa dake bayan mota shi da 'Kaninsa suna magana, Yace."Kawu ina da magana da kai."!
Babu walwala a tare dashi yace."Ina sauraranka." Da kyar iya cewa "Dama kan maganarmu ta kwanaki ce." Kamar be san komai ba yace."Wace irin magana kenan."?
Salim cikin dakewar zuciya yace."Maganar Naja'atu mana a cikin 'yan kwanakin nan gabadaya zuciyata ta kasa daurewa sai nake ganin kamar akwai wani abu da zai faru dan Allah ina so kaje ka nema min auranta kamar yanda kayi min al'kawari a kwanakin baya."
Shiru motar tayi babu wanda yayi magana, Abbah Alhassan mamakin maganar da Salim din yayi yake ashe dama soyayya ce a tsakanin Salim da Yarinyar? to me yasa dan uwan nasa yasan da soyayyar dake tsakaninsu ya bijiro da bukatarsa.
Shuru Abba Abbas yayi ba wai dan bashi da abin cewa ba, sai dan ganin cewar shi a gurinsa a bin kunya ne ace yana maganar aurensa da Salim d'in, yafi so yaron yaji maganar a bakin wani idan yaso ya gane ruwa ba'a sa'an kwando bane....
Shurun da yayi tasa jikin Salim yin sanyi, tabbas yanzu ya gazgata maganar Naja'atu cewa Abba Abbas din da gaske yake ba gudu babu ja da baya.
Yaji wani irin d'aci! a ma'kogwaronsa! dishi-dishi! yake gani a idonsa tsabar bakin ciki da 'bacin rai!
Ga wani masifar kishin Kawun nasa dake sasakar zuciyarsa!
Wai yau an wayi gari wanda yake tunanin shi zaiyi masa wakilcin aure shine yake kassaya dashi.........Shi kuwa Abbah Alhassan ganin 'Dan uwan nasa bai ce komai ba yasa yaja bakinsa yayi shuru haka suka isa kasuwar kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa mussaman Salim da yake jin shigar zazzafan zazzabi a jikinsa.
Yaya Ramlatu na fita daga gidan Alhaji Kai tsaye unguwar gwangwazo ta nufa gidan d'an uwan nata........Halisa na zaune a palo tana kallo Yaya Ramlatu ta shiga da sallama a bakinta......Halisa ta mike tana mata barka da zuwa taje ta kawo mata abinci da ruwa da lemo kana ta zauna suna gaisawa.
Yaya Ramlatu sai da ta cika cikinta ta 'koshi tukkuna, ta kalli Halisan tace"Kin san gagarimar maganar da nake tafe da ita kuwa."
Halisa taji gabanta ya fadi! a sanyaye tace"Ban sani ba Yaya sai kin fad'a."
Murmushin takaici Yaya Ramlatu tayi kafin tace"Kina zaune da baki a bud'e har kin samu damar zama kiyi kallo ana can ana shirya miki kasassa'ba."!!
Halisa miyau ya dauke daga bakinta tace"Yaya Ramlatu dan Allah fad'a min abinda ke faruwa."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace"Mijinki Abbas nacan yana neman auran budurwa 'yar cikinsa, auran cuta da ha'inci Auran da duniya za tayi turr! dashi."!