← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 143

Sashe 92

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Vip gruop#600 normal group#300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Barkamu da Juma'a My Fans
Ina rokon Allah ya sadamu da alkairan dake cikinta
58 Hajia Abu ta qaraso inda aunty Maryam take hankali a tashe take tambayarta abinda ke faruwa.

Aunty Maryam jiki a sanyaye tace"Naja'atu bari zan kira ki anjima."Sai kawai ta kashe wayar tana kallon hajian bakinta sai rawa yake yi tsabar fargaba da tashin hankali ya hanata magana, ita ma Hajian jin ta ambaci sunan Naja'atu sai gabanta ya tsananta faduwa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta tace"Maryam me yake faruwa da Naja'atu? jikina yana bani akwai mumman abinda ke faruwa da rayuwarta."Aunty Maryam tayi qasa da kanta tana tunanin yanda zata fad'a mata maganar....Aure wata uku kacal har anyi angama kuma saki har uku dan tsabar wulakanci a ganinta ko wane irin laifi naja'atu tayi bai cancani a wulakantata irin haka ba(Hausawa nacewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne) hakika aunty maryam ta tausayawa Naja'atu sosai yarinya da quruciyar ta da komai maza sai katantawa suke da ita, koda yake na farko itace taqi to amma wannan a tunaninta ba daga gurinta bane kawai ta had'u da sharrin d'a namiji....Sai da ta dan samu nutsuwa tukkuna ta d'ago kanta cikin tararrabi da alhini tace"Hajia al'amarin ne babu dadin ji wallahi shiyasa kikaga duk jikina yayi sanyi Naja'atu ce ta kira ni take tabbatar min da cewar wai mijinta ya saketa saki har uku kwana uku da suka wuce."
Hajia tayi salati tana sanar da Ubangiji tace "A kan me? me tayi masa yayi mata wannan wulakancin saki Uku!!? innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ai kafin kice kwabo palon ya cika da jama'ar da suke waje mafi akasari 'yan uwan Alhaji ne da hajian sai kuma Yaya Ramlatu! dukkanisu suka dinga tambayar ba'asin abinda yake faruwa, Aunty Maryam da hajia sukayi shuru domin sirrinta al'amarin, irin wannan maganar ba mai dadin fada bace shiyasa sukayi shuru.....Yaya Ramlatu tayi murmushi tana girgiza kanta tace" Hajia meye abun 'boye magana nifa dama nasan sai haka ta faru shuru kawai nayi muku ban sanar miki da halin da ake ciki ba, kwana uku da suka wuce na samu labarin abinda ya faru da mijin data aura ashe d'an fashi ne 'barawo d'an shaye-shaye d'an Luwadi ne manemin mata! ke mutumin daj mugun mai laifi ne jam'ian tsaro sun jima suna nemansa sai a ranar dubunsu ta cika shida abokanan harkarsa sun shiga wani bank sunyi sata sun fito asirinsu ya tuno yanzu dai 'yan sanda sun samu nasarar kama abokan harkar tasa shi kuma ya tsere amma sun damqe mahaifiyarsa jiya na sake samun labarin cewar sunje har inda mahaifinsa yake sun damqe shi, yanzu dai sun baza binkice sosai dan gano inda yake shima su damqe shi! ai wallahi naso harda ita shegiyar suka damqe dama ai duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka! makwadaita kawai gashi nan sun dauki 'yarsu saboda tsabar kwadayi sun aurawa 'barawo."
Palon yayi tsit! kowa yana mamaki da salati a cikin zuciyarsa!

Yaya Ramlatu ta cigaba tsinewa Baba malam dashi da zuriarsa tana kwashe musu albarka!

Hajia da taga abun nata na nema ya wuce gona da iri sai ta tsawatar mata Yaya Ramlatu ta fita daga palon tana cigaba da surutai....Hajia ta sallami kowa tace kowa ya koma ya cigaba da aikinsa.

Shuru palon yayi bayan fitar jama'ar hajia ta kalli anty maryam dake zaune da waya a hannu tace"Sake kiran number data kira ki da ita.'' Aunty Maryam ta duba numbar da sauri ta shiga kira... swich up wayar a kashe take! tayi ta kira ana ce mata a kashe take, cike da mamaki tace"Yanzu fa mukayi waya amma duba suna cewa a kashe wayar take."
A sanyaye hajia tace"To watakila babu chaji a wayar anjima kadan kafin ki tafi sai ki sake gwadawa mugani." Aunty maryam tace"To shikkenan.

Naja'atu bayan gama wayarsu da aunty maryam kwanciya kawai tayi tana kukan bakin ciki! gami da nadama da dana sani!

Hakika tasan duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta, gashi yanzu tazo tana dana sani wanda hausawa ke cewa qeya ce! da tasan auran Bash ba zai tsinana mata komai ba data hakura ta zauna a dakin mijinta data san Bash amanarta zai ci to da babu abinda zai sanyata ta fujirewa auran *MADADI* da iyayenta sukayi mata, hakika da tasan Bash ba mutumin kwarai bane to da babu abinda zai saka ta za'be shi a matsayin abokin rayuwarta...Data san ! data san!

Data san! (babu wanda yasan gaibu sai Allah kuma komai ya faru da rayuwarki qaddara ce amma kuma akwai son zuciya da qin jin maganar magabata mafi akasari iyaye zasu za'bawa d'ansu abunda yake alkairi ga rayuwarsu sai su kuma 'Ya'yan fujire su nuna ga abinda suke so, hausawa nacewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba)
Mmn Sajida data gaji da rarrashinta sai kawai ta fita gurin sana'arta ta qyaleta dan al'amarin Naja'atun tana gani kamar yafi karfinta......Mmn Sajida da wayarta ta fita tana so ta bayar a kai mata chaji kasancewar kwana biyu wutar unguwar ta lalace sai ta ajiyeta a kusa da ita ta cigaba da hada hada da jama'a! kawai wani d'an bana bakwai yazo siyan abinci ya dauketa yasa a aljihu a gurguje ya cinye abincinsa ya bar gurun.....Sim card din ya cire ya yar ya qara gaba abinsa.

Sai bayan jama'a sun tsagaita ta qwalawa Walid kira ya fito daga cikin gidan Mmn Ladi yana amsawa, ta laluba kusa da ita zata dauki wayar taji wayam! tashi tayi tana zazzage jikinta tana dubawa babu waya babu dalilinta, ta dudduba bata ganta ba sai tace"Shiga cikin gida ka tambayi Naja'atu ko wayar ta nan watakila dama ban fito da ita ba.

Yaron ya shiga gidan da sauri ita kuma ta cigaba da abinda take....Minti biyar Walid ya fito yace."Mama wai tace baki wayar a cikin gidan ba da ita kika fito kika ce zaki bada chaji ."
Mmn Sajida tace"Shikkenan sun sace yau kuma tsautsayin a kan wayata ya afka ai shikkenan Allah ya mayar min da alkairi." Mutanan dake tsaye a kanta suka shiga jajanta mata, tace"Wallahi ni layina ma nake ji." Da sauri daya yace''Bani numbar na kira muji." Da sauri ta shiga fada masa yasa a wayarsa a take aka ce masa wayar a kashe take, ya dinga kiran yana sake bude hands free domin taji!

Girgiza kanta tayi tace"qyale kawai ai duk wanda ya dauka dama ba zai barta a kunne ba yaje yayi min guzirin kiyama zai biyani a inda bashi dashi." Mutumin yace."Kinyi magana hajia Allah ya mayar miki da alkairi shi kuma daya dauka Allah ya tona asirinsa.

Amma yana da kyau kije ayi miki swapping d'in layin naki saboda jama'arki." Tace"Habu sai na samu lokaci zanje kana ganin dai irin sana'a ta bani da lokacin kaina amma insha Allahu na samu lokaci zanje ayi min.

Naja'atu taji takaicin sace wayar da akayi, haka sukayi ta maganar kafin su hakura, Mmn Sajida ta cigaba da sabgoginta kamar ma 'batan wayar bai dameta ba ita kuwa Naja'atu damuwa ta shiga sosai ta dinga tunanin hanyar da za tabi domin ganin ta taimaki kanta da kanta.

Aunty Maryam dai haka ta gaji da kiran waya ta hakura domun har ta zo tafiya wayar bata shiga ba, Hajiyar tace ta bari kawai tunda taqi shiga....Gabadaya da ita da hajiyan a sanyaye suka rabu da juna
Tun a mota take so tayi wa mijin nata maganar tana jin tsoro dan akwai sanda ta ta'ba yi masa maganar yarinyar ya nuna mata koda wasa kada ta kuskura ta sakeyi mata maganarta, ya nuna mata cewar shi babu ruwansa da yarinyar, a lokacin har sa'bani suka samu sabida hakan, ya daina mata magana tsayin kwana uku, al'amarin ya dinga bata mamaki! mutum da 'yar uwarsa ina laifinta dan ta nuna kulawarta a kanta zai dinga gaba da ita, sai itama ta fusata ta dauke masa wuta! kwana uku dan karan kansa ya sakko ya nemi shiri da ita to tun daga ranar bata sake yi masa maganar yarinyar ba...Sai yanzu da take ganin dole ta fad'a masa abinda ke faruwa tunda dai yarinyar babu wanda ta fara nema da maganar sai ita to tilas ta fad'a masa koda kuwa zai dauki gaba da ita kamar wancan karon....Ta kalleshi a nutse tace"Wai kasan abinda yake faruwa da Naja'atu kuwa.?

Abbah Magaji na driving yace."Maryam ashe ban hanaki yi min maganar yarinyar nan ba."?

Tace" Kamar yaya? wannan wai wace irin magana kakeyi Naja'atu fa kanwarka ce uwa daya uba daya duk abinda zanyi a kanta saboda kai zanyi amma sai ka dinga nuna wani abu daban.

Yace."To bana so na fad'a miki babu ruwana da yarinyar nan, kada ki sake ki tunzura min zuciyata duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta." Murmushin takaici tayi tace"Au! ashe kasan abinda yake faruwa tsayin kwana uku kayi shuru da bakin ka ko."?

Yace." Na sani asirin mijinta ya tuno wanda nasan dama komai daran dadewa dole sai haka ta faru dashi wannan yaron mugun mai laifi ne ni ganau ne ba jiyau ba shiyasa lokacin auran naqi saka kaina a ciki saboda nasan karshe ba zaiyi kyau ba."
Tace"To dai yanzu duk wata magana ta qare tashin ma maganar bacin rai ne dan Allah kayi hakuri ka yafe mata kuma ku duba halin da take ciki!

Dazu ta kirani a waya tana kuka take sheda min cewar ya saketa saki uku!

Tsabar tashin hankalin dana shiga a lokacin yasa na kasa tambayarta inda take, na kashe wayar, to kuma dana sake kira sai wayar taqi shiga nida hajia mun shiga damuwa sosai da sosai A nan ne nima nasan abinda ke faruwa a bakin Ramaltu.....Yace."Maryam ki rabu da yarinyar nan dan Allah! ai tasan hanyar gida, tunda ya saketa to zaman me takeyi sai ta tattaro ta dawo gida.
Chapter 92 · 0% Book details