Sashe 11
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Talatu dashi Magajin suka amsa da "ameen" Mikewa yayi yai musu sallama da niyar tafiya gida dan lokacin goma na dare ma ta wuce!
Fatan sauka lafiya sukayi masa ya dauki hularsa da key dinsa ya fita daga gidan.
Cikin tausawa ya kalleta da fad'in"Ki tashi kije ki kwanta komai yayi tsanani maganinsa Allah kuma ina so ki zauna kiyi tunani kan wannan hukuncin da muka yanke a kanki, mune muka haife ki ba zamu cutar dake ba, da mutumin nan da ba nagartacce bane to da baza mu amince da bukatarsa ba to mun tabbatar da cewar idan muka dauke ki muka bashi muna da tabbacin zai kula dake kamar yanda ya kula dake a lokacin da baki san kanki ba."
Mikewa yayi ya shiga da'ki bayan ya gama maganarsa, Baba Talatu ta jima tana rarrashinta kafin ta mike itama tabi bayan Malam din suka barta ita kadai a tsakar gidan tana kukan zucci.
Mamaki take sosai! wai ashe dama Abban Abbas din ne ya bukaci auranta ita duk a tunaninta su Baba malam ne, girgiza kanta kurrum take tana mamakinsa, to ta aureshi tayi yaya dashi? ta yaya za ta iya rayuwar aure dashi? lallai ma! ita abun ma mamaki yake bata ko kunya bai ji ba yace zai aureta bayan yana amsa sunan Uba a gurinta, gashi kuma yasan da maganar Salim hummm! aikam ba zata yarda ba duk yanda za tayi sai ta rushe wannan auran, sam ba zata auri tsoho dan shekara hamsin ba haka kawai sun gina soyayyarsu da masoyinta yazo yayi musu kutse a rayuwarsu ko kunya baya ji zai zo da wannan maganar!
'Kwafa tayi ta mike ta shiga d'aki!
Tana shiga dakin taji shashshekar kukan Saddiqa suna kwance ita da Mussadiq a katifa ta rungume shi sai kuka take!
A gigice ta kunna haske wayarta, tana haske su!
Saddiqa ta rufe idonta tana sake takure jikinta guri guda......"Ke Saddiqa menene? dama ba kiyi bacci ba."?
Saddiqa ta mike zaune tana goge fuskarta, 'Karasawa tayi ta zauna gefan katifar tana kallonta, a sanyaye tace"Meye kika kuka? nafada miki ki dainawa Mamma kuka idan kina so ta dinga samun rahamar ubangiji."
Saddiqa ta goge fuskarta tana kallonta tace"Ni ba Mamma nakewa kuka ba, nasan abinda nake yi a halin yanzu Mamma babu abinda take da bukata a gurinmu sai addua ba kuka ba."
A d'an sanyaye tace"To me kikewa kuka."?
Saddiqa ta kalleta wasu hawayen na sake zubo mata tace"Yaya Naja'atu me yasa kike nuna 'kiyayyar ki 'karara a kan Abbanmu."!?
Gabanta ne ya fad'i! sai tasha kunu! tace"Wace irin magana ce wannan Saddiqa? kada kice min kema kina goyon bayan na aureshi."
Saddiqa taja majina tana goge hancinta tace"To menene aibu a ciki? dan kin auri Abbanmu ai ba wani abun bane kuma ba ke kad'ai ce kika ta'ba auran *MADADI* ba Yaya Naja'atu idan kika maye gurbin mahaifiyarmu zamu ji dad'i sosai dan Allah kiyi mana wannan alfarmar ki daina nuna 'kiyayyar ki a fili."
Shuru tayi tana nazarin maganar yarinyar!
Wai shin da suke ta wannan maganar ta yaya zata fara ne? wane matsayi zata ajiye shi miji ko mahaifi? bafa zai yiwu ba.!
Ta kalli Saddiqan data kura mata ido tana jiran amsarta tace"Saddiqa nayi wa Abbanku 'kan'kanta kuma shima yayi mun girma bayan nan kuma ni matsayin mahaifi yake a gurina bazan iya rayuwar aure dashi ba, kuma ki daina tunanin ina 'kinsa wallahi bana 'kinsa saboda Abba Abbas yayi min abinda ba zan ta'ba mancewa dashi ba, kawai dai bana tunanin zan iya rayuwar aure dashi."
Saddiqa tace"To idan baki aureshi ba kin san dole yayi aure kuma gabadayan mu bamu san matar da zai aura ba, kinga zamu shiga halin 'kaka na kayi tunda dai kin san ba 'kaunar mu Anti Halisa take ba, kinga rayuwarmu na cikin 'kalubale nida Mussadiq."
"Eh gaskiya ne duk maganar da kika fad'a to ai ba dole sai kun zauna tare da matansa ba, sai ku dawo gidan Alhaji da zama ko kuma ku dawo gidanan nan nasan Baba Talatu zata ri'ke ku to meye abun tashin hankali.
Saddiqa ta shiga girgiza kanta zuciyarta na wani irin d'aci! tace" Yaya Naja'atu kin manta maganar Abbanmu kenan kin san fa yasha fad'a cewar mutuwa ce kawai zata rabashi da 'yayansa bana tun
anin zai amince ya kawo mu nan mu zauna ke ko gidan Alhajin da kike magana ba zai barmu muje ba duk da cewa gidansu ne."
Naja'atu shuru tayi tana tunanin al'amarin Babu shakka zaman Saddiqa da Mussadiq hannun Halisa gagarimun had'ari ne zata iya cutar dasu ta ko wace siga!
Itace zata rike su tamkar uwarsu, to ita kuwa ko a mafarki bata tunanin zata koma gidansu a matsayin matar mahaifinsu, insha Allahu ta bar gidan har abada.
Ganin Saddiqan ta tsura mata ido yasa tace"To ki kwanta kiyi bacci zanyi tunani kan maganar ki." Saddiqa taji farin ciki ya rufe ta tace"To shikkenan Yaya Naja'atu nagode Yaushe zaki gama tunanin."?
Kallonta tayi na minti biyu tace"Ke dai tunda nace zanyi to zanyi duk hukuncin dana yanke zan fada miki."
Saddiqa tace"To Ubangiji Allah yasa naji alkairi." Amin tace a takaice, Saddiqa ta juya ta kwanta tana adduar Allah yasa ta amince da maganar ta.........
Tsuru tayi ta tsirawa guri guda ido tana tunanin yanda za tayi ta rusa wannan gagarimin al'amarin daya tunkaro ta, kira ne ya shigo Wayarta dake gefanta, ta dauka hannu na rawa, a kunne tasa wayar, ta fashe da kuka 'kasa-'kasa tace"My prince kaji abunda Abbah Abbas ya 'bullo dashi ko.''
Salim dake kwance kan katifar sa yace." Menene ya faru ni banji komai ba." Juyawa tayi tana kallon bayanta, dan bata so tayi wata magana ya kasance Saddiqa taji, sai da ta tabbatar da bacci takeyi sannan ta sake sassauta murya ta shiga fada masa abinda ke faruwa.......Mi'kewa zaune yayi da sauri! lokaci guda gumi ya tsatstsafo masa, yace."Da gaske kike wannan maganar ko kuma dai tsokanata kikeyi."?
"Humm! wane irin tsokana wallahi tallahi da gaske nake wai Abba Abbas shine ya bude bakinsa yake fadawa su Baba malam yana so ayi masa *MADADI* dani!!!
Katifar da yake kai ya doka! da hannunsa da 'karfi!
Yace." Kai kaji wata tatsuniya! shi yanzu dan girman Allah baiji kunyar fad'ar wannan maganar ba!!?
To shin wai ko ya manta abinda yake tsakanina dake ne da har zai bijiro da wannan tatsuniyar."
Tace"Oho! ni gani nake kawai san zuciya ne yama za'ayi yace haka bayan shi da bakinsa ne yace."Mu daidaita kanmu zai daura mana aure kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai yace a mayar masa dani a *MADADINTA."*
Salim yayi wani murmushi na takaici yace."Ke nifa na daina mamaki! wallahi zai aikata dama yanda yake wani kula dake da wani takatsantsan a kanki akwai alamun tambaya dama so yake matarsa ta mutu ya aure ki! saboda haka ni kuma wallahi bazan bar masa ba, to in banda ma rigima ina ke ina shi! shekara hamsin har yake tunanin auran yarinya 'yar 'karama kamar ki 16years fa to idan ya aure ki yayi yaya dake? mtwwss."!!
"Humm! ni wallahi Salim mamaki ma ya hana ni nace komai ba kaga yanda su Baba malam suke murna ba, wannan ai tauyewa mutum hakki ne.
Ni duk na rasa ma yanda zanyi."
Yace."Kece kuwa kike da yanda za kayi, tun kafin yafiya tayi nisa ki kokarin ganin kin rusa maganar ni kuma gobe idan Allah ya kaimu idan naje daukarshi domin zuwa kasuwa zanyi masa magana akan inaso yazo gurin Baba malam kan maganar auramu sai naji me zaice."
Tace"To yauwa kayi masa hakan nasan dole kunya tasa ya kasa magana ni wallahi duk mutuncin sa ma ya zube a idona mtssssw!!!
Takarashe maganar tana jan tsaki!
Yace."Baby ki daina wani damuwa ki kwanta kiyi bacci bazan bari wannan al'amari ya tabbata ba, duk yanda zanyi to zanyi na rusa al'amarin.
A sanyaye tace"Tom shikkenan my Prince kayi bacci mai dad'i kaji ko." Yace."Ke ina wani maganar bacci mai dadi a gurina Wannan dattijon na nema yasa zuciyata ta buga."!!
"Hummm! kawai tace dan ta rasa ma abin cewa, kashe wayar tayi ta zurfafa cikin tunani da nazari! gabad'aya bata so tayi masa rashin kunya saboda shi mutum ne mai muhimanci a gurinta to amma tunda ya 'bullo da wannan maganar kashi hamsin na 'kima da mutuncinsa suka zube a gurinta.
Numbarsa ta laluba ta dinga kallon numbar kamar shi take kallo, shawara take da zuciyarta shin ta tura masa text ko kuwa, wata zuciyar tace" Idan kika tsaya lako-lako kan wannan al'amarin to za kiyi kuka da idonki.......Da sauri ta shiga rubuta masa text kamar haka.
_Assalamu alaikum Abba nmu barka da dare ina tafan kana nan lafiya?
Abbah wata magana naji daga bakinsu Baba malam kuma sun ce kaine kazo musu da maganar shine nake so naji daga bakin ka._
Tana tura masa text din ta kashe wayar! kwanciya tayi tana takure jikinta hawaye ne ke kokarin 'kwace mata tana kokarin hana shi fita.
Sai bayan da ya dawo daga sallahr asubahi ne ya kunna wayar tasa, aikuwa text din ne ya shigo yayi saurin bud'ewa yana dubawa............Ya karanta ya kai sau biyar ya girgiza kanshi! lallai To bata yarda ba kenan tana so taji daga bakinsa, shi kam bai san abinda zaice mata ba, kawai sai ya share bai mayar mata da amsa ba, ya cire jallabiyar jikinsa, ya kwanta rigingine kan bed din yana tunanin rayuwa, Halisa ce ta shigo dakin jikinta sanye da hijab kamar wata mutuniyar arziki, tun bayan mutuwar Halimatu wata shiriya tazo mata takeyi komai cikin rashin kuzari.
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*PEGEN YAU NAKI NE*
*UMMU HANIFA*
Marubuciyar littafin
*ANYA MUTUM CE?
Ina mutukar alfahari dake 'Yar d'akina Allah ya 'kara miki basira da haza'ka, ki cigaba da rubuta littafai masu dadi da ma'ana
Kanta a tsakanin cinyoyinta ta d'ora duka hannuwanta saman kanta ta takure kanta guri guda sai kuka take tana girgiza kanta, Baba Talatu ta dafa bayanta a sanyaye tace"Naja'atu yanzu kinji komai daga bakin malam ko?