Sashe 57
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama tayi a kusa da ita ta dafa kafadarta a sanyaye ta kira sunanta, ta juyo tana kallonta idonta na kokarin kawo ruwa.
Anty maryam tace"Ki daina kuka kinji ko! jikina kuma yayi sanyi yanzu dana ganki cikin damuwa, tabbas hakan tana iya kasancewa gaskiya ne insha Allah idan Abbah Magaji ya dawo zan fad'a masa abinda yake faruwa sai muji abinda zai ce a kan matsalar abokin nasa ke kuma dan Allah ki daina wannan kukan da kikeyi ita mace da kawaici da hakuri a kasanta.
Dan ta 'kara tunzura Anty maryam din tace"Ni wallahi anty bazan iya hakuri na jure ba ni bani da hakuri ta wannan bangaran kawai a san yanda za'ayi."
Aunty Maryam tace"Ni abinda yake bani mamaki anan kince bakya sonsa to ya akayi kike sakin jikinki dashi har wata mu'amula take shiga tsakaninku kike jin dadi wanda har kike ganin kamar yana cutarki."
Tace"Aunty shine kullum sai yazo yayi wasu abubuwa wanda suke sawa hankali na ya tashi ni wallahi da baya ta'ba min jikina bazan damu ba amma kullum sai yayi ta damuna ni kuma na kasa hakuri."
Aunty Maryam tace"Tom magana dai ta wuce kija bakinki kiyi shuru kada ki fadawa kowa kuma kada ki sake Halisa ta sani dan za tayi farin cikin hakan ki cigaba da bashi kulawa insha Allah idan bashi da lafiya to zai samu sauki ai kowace cuta nada maganinta."
Shuru tayi kawai Aunty maryam ta cigaba dayi mata nasiha gami da koya mata dabarun zama da miji da kishiya Naja'atu jinta kawai takeyi domin ita ta riga ta gama yankewa kanta hukunci.
Sai bayan la'asar ta koma gidan, nan tarar da wata dattijuwa a zaune a palo ita dasu Saddiqa, ta zauna kan kujera tana fuskantar matar suka gaisa a nutse, matar tace"Sunana Larai daga gidan Hajiya nake tasa aka kawo ni nan gidan domin na dinga taimakawa matan gidan da aikace-akaice."
Sai da matar tayi mata bayani sannan ta gane cewar mai'aiki aka kawo musu, tace"To sannu da zuwa Allah ya bamu hakurin zama da juna." Matar tace"Ameen ya Allah.
Tace"Ina kayanki suke." Larai tace"Suna can wani daki a harabar gidan Hajiya tasa an kai mun can tace can ne masaukina."
Tace"To hakan yayi Allah ya taimaka."
Larai tace"Ameen" Halisa ce ta fito daga dakinta ganin Naja'atu da larai suna hira sai ranta ya 'baci!
Ta kalli Larai fuska a 'bace! dama can halisa akwai girman kai tace"Yana da kyau ki shiga kicin ki fara aikin ko."
Larai ta mike da sauri tana fadin "To Hajiya a nuna min kicin din." Tace"Muje na nuna miki yanda ake amfani da komai." Larai tace"To." kicin din suka nufa Naja'atu ta bisu da kallo tana girgiza kanta, Halisa ba 'yar gidan uban kowa ba amma dan kawai tana auran mai kudi sai shegen girman kan tsiya, tsaki taja ta kalli Mussadiq dake mata magana
Tace"Ba gidan Alhaji naje ba gidan Aunty Maryam naje." Yaron yace"Da kin sani kinje dani Yaya Naja'atu.
Tace''Wani weakend din sai ku tambayi Abbanku kuje ku yini a can."
Mufida tace"Aikuwa zamu tambaye shi." Ta kalli Saddiqa da fadin"Saddiqa ya hannunki." Yarinyar tace"Hannu ya warke kinga yanzu ina iya amfani dashi ba tare dana ji zafi ba." Tana kokarin mikewa tace"Allah ya kara sauki." dakin yaran ta nufa, ta shiga wanka ta fito daure da zanin atamfar jikinta jakar kayanta ta bude taga babu duk ta sanye su sai 'kananu irin na kanti sai dogwayen riguna ita kam ba zata sa doguwar riga ana zafi ba riga da sket ta dauka tasa a jikinta ta gyara gashinta tasa masa ribborn ta gaji da rashin kitso tana ganin dole ta tambaye shi zuwa kitso kanta kusan satin sa biyu a tsefe! gashi tubarkalla tana da gashi babu laifi....Dankwali abaya ta daura a kanta ta zauna tana hada kayanta dana yaran wanda da sukayi daud'a! ta fito palon tana kallon Mufida tace"Kije bakin gate kiga idan me muku wanki nan kice yazo ya dauka."
Yarinyar tace"To" Da sauri ta mike zata fita..Halisa ta fito daga kicin tace"Ke ina zakije.''?
Tace"Yaya Naja'atu tace naje na kira Yunusa mai wanki.''
Cikin tsawa tace"Koma ki zauna idan ita ba zata je ba to ta aiki wanda take da iko dasu.
Yarinyar ta kalli Naja'atu dake tsaye tana kallonsu...Jikinta a sanyaye taje ta zauna saboda tana masifar jin tsoron mommyn nata tana kuma tsoron irin dukan da take mata....Saddiqa ta mike ta nufi dakinsu ta sako hijabinta ta nufi kofar fita.
Naja'atu kuwa murmushi tayi ta zauna kan kujera da fad'in "Allah yasa nima na haifa kafin ki haifa ballantana kiyi min gori ina da masu share min hawaye ehe."!!
Halisa na jinta tayi mata banza so take kawai maigidan ya dawo taga irin hukuncin da zaiyi wa yarinyar na fita ba tare da saninsa ba kuma tasan ya tsani yawo komai shirin da kuke dashi kukan iya 'batawa dashi idan yaji maganar zuwa unguwa shiyasa itama bata fiye zuwa sabgogin danginta ba saboda kullen da yake musu.
Larai tuwo tayi musu na farar shinkafa yayi kyau sosai ga lafiyayyar miyar bushashshiyar kubewa da taji nama da daddawa da kayan kamshi, cikin nutsuwa ta shirya musu gurin cin abincin tayi musu sallama ta nufi masaukinta.
Halisa kuwa zuwa akayi ka cancad'o ado da wani uban material mai tsadar gaske sai dai anyi masa banzan dinki riga da siket ne duk an tsaga shi hannun riga mai tsayi da gajere tasa turare mai kamshin gaske, palon ta fito tana shan k'amshi
Naja'atu da yaran suka bita da kallo, Naja'atu Kallo guda tayi mata ta dauke kanta tana kunshe dariya!
Halisa ta lura da ita sai ta shareta ta zauna kan kujera hade da daukar romot tana dannawa!
Yaran kuwa motsin kirki sun kasa yi wanda da kafin fitowar Halisa hayaniya suke akan film din da suke kallo amma zamanta a gurin duk yasa sun shiga taitayinsu......Haka suna ji suna gani ta sanja musu tashar da suke kallo ta mayar dashi Mbc1 tashar larabawa, gabadaya yaran basu ji dadi ba dan yanayin su sai da ya nuna....Naja'atu ta kalleta a da'kire! tace"Kallo fa suke zaki dauke musu dan Allah ki mayar musu su 'karasa.
Halisa ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kallon dramar da akeyi a tashar mbc1 din.
Naja'atu ta mi'ka hannu zata dauki romot din ta wani fizge hannunta ta dauke romat din ta rike a hannunta.
Naja'atu tace"To ikon Allah! kina Iko da abinda ba naki ba?
Kayan kallon nan fa ba daga gidanku kika zo dashi ba maigidan ne ya siya ya ajiye domun 'ya'yansa kawai kuma sai ki dinga 'kuntatawa yara kina son zuciyarki." Halisa ba tare data kalleta ba tace"Ki cigaba da zagina kina min rashin kunya zaki gane baki da wayo wallahi."
Naja'atu tace"Babu wani zan gane bani da wayo ai gaskiya na fada miki dama ni tuntuni abinda yake had'ani dake son kai aikin banza kawai." A fusace!
Halisa ta juyo ta wanke mata fuskarta da mari ta mike tsaye tana wani irin huci! tace"Ke na gaji da rashin mutuncin da kike miki wai dan uwarki ni sa'arki ce."!
Naja'atu ta dafe fuskarta tana kallonta ta'b!!!
Mikewa tsaye tayi a zafafe! kawai suka ji sallamarsa a palon...Naja'atu ta fashe da kuka tana sake rike fuskarta ta da fadin "Kawai daga na fad'a miki gaskiya shine zaki mareni har da zagin uwata."
Ya k'araso gurin yana tambayar abinda ke faruwa, Halisa dai jikinta ne yayi sanyi dan ta kasa magana data san zai dawo da wuri to da bata aikata abinda ta aikata ba shi kuwa ya dawo da wuri ne domin kawai yaga shin naja'atu ta dawo gidan ko kuma tana waje.
Tana kuka ta kama hanya zata bar gurin.
Hannunta ya rike ya dawo da ita yana tambayarta abunda ke faruwa...Tana kuka tace"Kawai daga na aiki Mufida nace ta kira Mai musu wanki yazo ya dauka shine tace yarinyar ba zataje ba wai naje da kaina ko kuma na aiki wanda nake da iko dashi, sai kawai Saddiqa ta tafi ta kirawo shi yazo ya dauki wankin, to kuma yanzu yara suna kallon film dinsu kawai daga zuwanta tazo ta sanja musu tasha shine dan nace ta mayar musu su karasa gani sai kawai ta hau d'ura min ashar harda zagina." Cikin gawurtaccen kuka ta 'karashe maganar.....Halisa jikinta yayi sanyi lallai yarinyar nan ta gawurta gurin iya sharri yanzu dame zata kare kanta ji tayi giwarta tayi sanyi.....Babu walwala a fuskarsa ya kalli Halisa da fad'in "Wai me yasa kema da girmanki kike mayar da kanki yarinya?
Akwai Tv a dakinki me zai sanya ba zakije can kiyi kallonki ba sai kinzo ki takurawa yara kuma idan nayi magana kice ina fifita yara a kanki ke abinda kikeyi ya dace kenan."?
A sanyaye tace" To ni dai bani da abinda zance anan gurin shuru shi yafi min alkairi amma duk abinda yarinyar nan ta fada maka to karya take yi Tunda ta dawo daga yawonta take zagina dama kuma na fada maka tun kafin ta fita ta fara to ina tunanin inda taje an zugata! shiyasa ta shigo da neman fitina kuma ni ban zauna dan na takurawa yaranka ba kayi hakuri."
Tana kare maganarta ta bar gurin, tana mamakin yanda al'amarin ya juye kanta tana so ya dawo gidan taga irin cin mutuncin da zaiyi wa yarinyar sai gashi al'amarin na nema ya dawo kanta aikuwa dole ta lalla'ba kada ya kunyata a gaban yara shiyasa tayi gaggawar barin gurun.
Halisa na barin gurin Ya shiga bin jikin Naja'atu da kallo drassing din da tayi yayi masa kyau! komai na jikinta ya futo kuma yau bata sanye da hijabi!
Ganin yana kallonta ga yara a zazzaune sai tayi saurin zama kan kujera tana dauke kanta...Shima da sauri ya bar gurin gudun kada yaran su fahimci wani abun.
Mufida ce ta dauki romot din tayi saurin mayar musu da Mbc2 tashar da suke kallo, suka cigaba da kallon film dinsu.