← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 143

Sashe 96

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dr." Muryarta ta katse musu hanzari daga shi har Mmn Sajidan da take kokarin bin yansa domun tafiya.....Duk suka juyo suna kallonta, tace"Idan babu damuwa ina bukatar ka bani aron wayarka zan kira mahaifina da ita insha Allah za'a tura maka kudinka."
Dr yayi kasaqe! yana kallonta kafin ya d'an d'age kafad'arsa ya dauko wayarsa dake gaban aljihun rigarsa ta likitoci ya karasa har bakin gadon da take zaune ya miqa mata....Ta kar'ba a sanyaye, tana dubawa dama kafin ya bata wayar sai da ya cire mata sucurity da yake kai.....Tana tararrabi da fargaba ta sanya numbar Abbah Abbas din a wayar ta shiga gurin kira gabanta na wani irin fad'uwa ta shiga kiran wayar.....Daf da zata katse aka d'aga! ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya tana jiran taji muryarsa sai kawai taji murya mace mai tafe da iyayi da feleqe! tana fad'in "Waye yake magana."?

Gabanta ya dinga dukan uku uku! wacece wannan?

Take tambayar kanta, tasan muryar Halisa kuma tasan muryar Saddiqa Mussadiq Mufida! muryar wannan me maganar ce bata tantance ba, Zuciyarta tayi saurin fad'a mata cewar amaryarsa ce! ji tayi idanunta na neman rufewa! tsabar fargaba!

Tayi gum! da bakinta takasa magantuwa tana jin muryar Zainab sai magana takeyi amma uffan ta kasa cewa....Zainab tace" To ikon Allah waye wannan anata magana yana ji yayi shuru tsaki taja ta kashe wayar......Naja'atu ta shiga rarraba idonta a dakin gumi! na tsatstsafo mata!

Dr yace."Ke nake saurare naji kamar an d'aga wayar ana magana kuma baki ce komai ba.

Da sauri ta dawo hankalinta tace"Yi hakuri Dr bari na sake kiran wayar bana ji sosai shiyasa na kasa magana." Okey kawai yace ya zuba mata ido yana kallonta tamkar zai lasheta.......Zainab hannunta r'ike da wayar ta kama hanyar fita palo inda Abbah Abbas din ke zaune yana hutawa.. tana daf da karasawa inda yake wani kiran ya sake shigowa, a maimakon ta kai masa wayar sai kawai ta d'aga tare da kara wayar a kunnanta da fad'in "Waye yake magana." Naja'atu ta daure da kyar tace."Nice."?

Zainab jin miryar mace yasa gabanta faduwa tace"Kece wa."?

Abbah Abbas yayi saurin juyowa yana kallonta jin yanda tayi maganar cikin izzah! da gadara!

'Bangaran Naja'atu kuwa ji tayi tamkar yarinyar ta soka mata wuqa a kirjinta jin yanda take wani daka mata tsawa kamar uwarta! har ta hasala! sai kuma ta sassauta zuciyarta tace."Naja'atu." Zainab tayi shuru tana mamaki!

Naja'atu Naja'atu? tasan sunan rad'au! a bakin yaran gidan kuma ta samu cikakken bayani a bakinsu da sauran jama'ar gari tunda dama hausawa nacewa ko haqa rami kayi ka bunne abu to wata rana sai ya fito an ganshi, duk labarin Naja'atu tasan shi daga farko har'karshe sai dai duk yanda take zungurar maigidan kan maganar koda wasa bai ta'ba bata wani labarin da ya dangace shi dashi da Naja'atun ba........"Oh! nagane to wa kike nema."?

Naja'atu murmushin takaici tayi Kai tsaye tace"Ina neman mijinki ne idan yana kusa ki basa wayar zanyi magana dashi." Zainab tace"Okey kada ki damu." Sai kitt! ta kashe wayar ta nufi inda yake tana wata karairaya ga wani tsadaddan murmushi a fuskarta, zama tayi a kusa dashi tasa hannu a fuskarsa tana shafa gemunsa tare da wasa da karan hancinsa tace"Masoyinta sannu da hutawa." Kafad'arta ya r'ike hankinsa na kan wayarsa dake hannunta ya kar'ba yana fad'in "Waye ya kira ne."?

Tace" Wata ce aka samu akasi ta kira number ka." Abbah Abbas bai gamsu da maganarta ba ya 'kurawa number ido, wayarsa babba ce sosai shiyasa daga ko wane gari ko wace qasa aka kirashi sai ta nuna masa, ganin number daga garin jos ne yasa ya d'an shiga mamaki!

Sai kawai ya tsinci kansa da kiran wayar...Lokacin Dr har ya kar'bi wayarsa zai fita kiran ya shigo, da sauri ya dawo da baya ya miqa mata wayar.....Rai a 'bace! ta daga wayar ta kara a kunnanta tace"Ke! dallah malama! ki bawa mai wayar abarsa mana wai ke amarya sai hauka kikewa mutane mtssw! ki bawa mai waya wayarsa zanyi magana dashi."
Muryarta ta dinga dukan kunnansa yayi shuru yana sauraranta har sai da ta gama hayaniyar sannan yayi gyaran murya a nutse ya kira sunanta. *"Naja'atu!!!*
Wani irin yarrr! taji tun daga saman kanta har i zuwa tafin 'kafarta a sanyaye tace"Na'am Abbah Ina wuni."?

Ajiyar zuciya ya sauke da fad'in "Lafiya lau ya kike ya maigidanki." ?

Ya nuna kamar bai san abinda ke faruwa ba.

Kuka tasa masa tace"Abbah bani da lafiya gani a kwance a gadon asibiti likita na bukatar kudi bani dashi bani da wanda zai biya min shine na kira ka ko zaka taimaka min kamar yanda Allah yake taimaka maka." Jin maganar rashin lafiya yasa ya mayar da abin serious yace."Baki da lafiya Baki da wanda zai biya miki kudin magani ina mijinki yake."?

Tana kuka tace"Ya sake ni ai."?

Shuru yayi dama abinda yake so kenan yaji daga gareta...Yace."Yanzu kina ina."?

Cikin shashshekar kuka tace"Ina tare da wata mata mai kirki tana taimakona." Girgiza kansa yayi yace"To Allah ya sawwaqe!

Bani Likitan zamuyi magana dashi." Tayi saurin miqawa Dr din wayar........Tana jinsu suna magana da Dr din yana tambayarsa abinda ke damunta Dr yayi masa cikakken bayani sannan ya fad'a masa kudin da ake buqata....Yace Yanzu ya tura masa account number nasa zai sa masa kudin...Sallama sukayi da juna Dr ya kallesu a nutse yace."To alhmdullhi zaku iya tafiya yanzu." Mmn Sajida da Mmn Ladi sukace "To mungode." Da sauri Dr ya fita daga dakin su kuma suka shiga shirye shiryen tafiya gida......
*_Allah yasa cikin ya zube Aunty Binta ci kuma!!!
dan Allah kada ta haihu da Bash Aunty Binta wannan pege d'in ya bani haushi
......Wato kuna so rabo ya kashe ni ko?

To Yanda Allah ya saukar da ikonsa a kan Naja'atu nima 'yar kallo da addua ce........Alhamdullhi saqona na cikin littafin nan ya soma isa, ha'kika wani baya ta'ba haihuwar d'an wani Allah ya qaddarta akwai rabo mai zafi a tsakanin Bash da Naja'atu shiyasa suka rabu da Abbah Abbas cikin 'kan'kani lokaci ta auri Bash shima suka rabu cin 'kan'kanin lokaci bayan ya saukar da ikonsa a kansu, babu wani wanda yasan gaibu sai Allah
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account....0542382124....Binta umar gtbank.....Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
****61 Abbah Abbas shuru yayi da wayar a hannunsa yana tunanin maganar da dr ya fad'a masa, Naja'atu na dauke da cikin wannan lalataccen yaron! hakika wannan al'amarin ya tsaya masa a rai mutuka, ba wai yana kishi ne da faruwar hakan ba yasan Allah ba yanda baya tsara al'amarinsa, yarinyar kawai yake tausayawa had'uwar jininsu da yaron da duniya tasan mutumin banza ne, koda yake Ubangiji kan saukar da shiriya akan bayinsa a lokacin da yaso, wannan dalilin ya sanya yaji zuciyarsa tayi sanyi sai kawai yayi addua a kam Allah ya shiryi Bash din ita kuma Naja'atun Allah ya sauketa lafiya ya sanya rabuwar auranta da Bash din shine alkairi......Zainab kuwa kunya ce ta isheta tana jin tsoron kada ya tuhumeta a kan me yasa tayi masa karya bayan ta gane Naja'atu ce ta kira wayarsa, sai taga gabad'aya ma hankalinsa da tunaninsa bayan kanta yana can wani tunani na daban.

Sai goma shaura na dare suka isa gida, Mmn Ladi kai tsaye gidanta ta wuce saboda tasan mijinta ya dawo kuma bata fad'a masa zata fita ba tunda bata da waya, yanzu babu laifi sun shirya sun daina fada sosai duk a sakamakon nasihar da Naja'atu tayi mata......Mmn Sajida ganin mutane sun cika rumfar kwanon siyar da abincinta yasa ta sallamesu da fadin yau babu abinci sai gobe idan Allah ya nufa......Dantalle ya nufo inda suke ya sha shaddarsa 'yar rini hannunsa rike da mukkulin lifan d'insa, yana washe baki yace."Mmn Sajida dama wannan qanwar taki tana nan."?

Mmn Sajida tace"Eh tana nan Dantalle ya gida ya iyali."?

Ya amsa idanunsa a tsaye a kan Naja'atu." Yace." 'Yan mata ya kike ya gari ya jin dadi."?

Naja'atu duk da halin ciwon da take ciki sai da ya bata dariya, wai shi dole sai ya burgeta ta lura mutumin yana so ya wuce gona da iri....Tace"Lafiya lau jin dadi na gurinku."' Dantalle dadi ya isheshi ya kalli Mmn Sajida yace yau babu abinci naga alamar ma kamar daga unguwa kuka dawo ko."?

Mmn sajida tace wallahi kuwa munje wani guri ne." Yace."To bbu laifi bari naje na dawo kada ku rufe gida da wuri." Mmn Sajida tace"To shikkenan." Ya juya da sauri ya nufi inda lifan dinsa yake.....Su kuma suka shiga gidan Mmn Sajida na fad'in "Wahalalle kawai ya fito ya bar iyalinsa yana biye biyen gidajen abinci gabad'aya Dantalle baiyi ba wallahi." Naja'atu murmushi tayi tace."Ni kam gani nayi ma kamar sonki yake." Mmn Sajida na kokarin bude dakinta tace"Ai ko maza sun kare a duniya ba zan auri dantalle ba Gwara nayi ta zama a haka."
Walid da Sajida tuntuni sunyi bacci da yake Walid nada wayo shine yayi musu shimfida ya daura musu net suka kwanta, ita kuma Mmn Sajida kicin ta nufa da sauri da yake tana da karamin gas sai ta fara kokarin d'ora ruwa ta dafa musu indomee sai kawai sukaji sallamar Dantalle daga waje....Mmn Sajida tace"Naja'atu gashi can ya dawo ko zaki 'kokarta kije kiji dame yazo.'' Naja'atu tace"Rabani da wannan guy Mmn Sajida ki daure dai kije kada yace an masa wulakanci." Mmn Sajida ta dauki mayafinta ta fita....Minti biyar sai gata ta shigo hannunta rike da manya manyan ledoji Dantalle yaje ya kashe musu kudi gurin siyayyar kayan ciye ciye gami da kayan masarufi." Sosai Naja'atu ta dinga mamakin siyayyar tafi ta dubu biyar haka kawai bai ka gidansa ba yazo yana bawa duniya kai Allah ya shiryi mazan dakewa iyalinsu mugunta suna bayarwa a waje....Mmn Sajida tace"Kadan kika gani in dai Dantalle ne kuma wannan hidimar da yake yi da biyu yake wallahi ko shakka bana yi saboda dake yake yi.
Chapter 96 · 0% Book details