← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 143

Sashe 135

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abbah ganin irin uban kyawun da Zainab din tayi yasa duk ya wani susuce ya dinga kallonta yana murmushi, Zainab farin ciki duk ya isheta dan ganin kwaliyarta ta samu shiga ta jere masa gabansa da kayan abinci nau'i nau'i, iyayi kawai take masa tana wani fari da idonta, Abbah abinci yaci sosai suna hira kamar babu wata matsala data ta'ba shiga tsakaninsu a baya......Bayan ya kammala cin abincin ya dauki Ummi yana mata wasa Zainab tazo ta shige jikinsa tana shafa fuskarsa tace"Habibi jiya da daddare na kira wayarka kamar yanda na saba kawai Najaatu ta dauka ta farfad'a min maganar da ranta yake so harda cewa wai duk abinda kakeyi da izininta kakeyi saboda haka yau bata baka izinin daukar waya ta ba.....Al'amarin sai ya bani mamaki saboda ni dai nasan mijina jajurtaccan namiji ne babu wata mace da zata iya juyashi a gida da waje, sannan kuma ni dai banga laifi ba dan na kira ka a waya a matsayinka na mijina ai ina da hakkin a kanka to ita kuma sai naga ta dauki abin da wata manufa."
Abbah sanja fuska yayi ranshi ya 'baci jin abinda zainab ke fad'a masa ashe akwai wata mace da zata iya bashi umarni mutukar ba uwar data haifeshi ba, lallai Najaatu ta rainashi, shin wai ina ruwanta da abinda yake tsakaninsa da matarsa ne ? ya lura duk wata fitina daga gurinta take tasowa tunda gashi a gaban idonsa ta dauki sar'ka guda biyu ta kuma fada masa ita da Halisa wannan na nuna masa cewar zata kawo masa rashin zaman lafiya a gidansa.

Yace" Kiyi hakuri ki bar maganar kinji ko amma inaso na sheda miki cewar ni wata mace bata isa tace ga abinda zanyi ba nafi karfin gidana gabad'ayanku a karkashina kuke babu wacce tafi wata a cikinku sai wacce tafi kyautata min Najaatu bata isa ta hanani na kula dake ba.

Zainab tayi murmushin samun nasara tare dayin wani irin fari da ido tace"Nagode Habibina dama nasan kawai ta fad'i hakane dan ta tunzura min zuciya muzo muyi abinda be dace ba ni kam yanxu zaman lafiya nake so muyi da junanmu kai ma sai kafi samun nutsuwa mutukar iyalanka kansu a had'e yake.

Da sauri yace."Yawwa ashe kin gane shiyasa kullum nake cewa daku ku zauna lafiya da juna dan wannan kishi da rikicin da kuke ba zai barni na samu nutsuwar da nake bukata ba." tace"Nidai insha Allahu ta bangarena ba zaka sake samun wata matsala ba." Cike da jin dadi yace."To nagode sosai kayan ki na mota sai kisa yara su dauko miki.

Rungumeshi tayi tana murna da farin ciki tace "Habibi saura mota dan Allah ka siya min." Yace."Kada ki damu zan siya muku keda Najaatu insha Allah." Jin ya ambaci sunan Najaatu yasa ta rage walwalar da take, tace"To mungode sosai Allah y kara budi.............Zainab ri'ke wuta tayi da kyar ta barshi ya tafi gurin Halisa .

Cikin rashin walwala ya samu Halisa a zaune a falo ita da yaran duk sunyi ado da kwalliya sunata zaman jiransa yana can gurin Zainab ta ri'keshi sama da awa biyu, shi kansa sai da yaji nauyin hada ido da Halisa saboda ya lura ranta a bace yake beyi tsammanin sun san ya shigo gidan ba shiyasa ya shantake a gurin Zainab.......Yaransa suka rungumeshi suna murna gami da yi masa sannu da zuwa, Cike da farin ciki ya rike hannun Mussadiq ya zauna kusa da Halisan tare da fad'in "Mussadiq ina fatan na sameku lafiya."?

Gabayansu suka amsa da lafiya lau Abbah." Yace."To Alhamdullhi.

Idonsa ya d'ora kan Halisa da taci kunu kamar bata ta'ba dariya ba.

Ya kalli yaran a nutse yace."Kuje dakinku kafin nasa a kawo muku abinda nazo muku dashi." Da sauri suka miqe suka bar falon..........A nutse Yace."Ranki ya dad'e ina fata na sameku lafiya."
Halisa ta ta'be baki tace"Lafiya lau gashinan idonka ya nuna maka ai." Yace."To masha Allah haka nake so dama nima ai ban jima da shigowa ba wallahi sa..........Katseshi tayi da sauri tace"Abban mufida kada kace min komai dan Allah!

Ka shigo gidan nan tun misalin uku baka shigo gurina ba sai yanzu dubi agogo biyar da rabi kana can gurin 'yar gwal wallahi kada ka zama daya daga cikin mazajen da basa adalci a cikin gidajensu.

'Bata rai yay yace." Shikkenan kuma ba zan zauna naji matsalarta ba sai nayi laifi na gama da dakinta nazo gurinki kina nema ki 'bata min rai shin wai ya kuke so nayi ne? kowa akayi abu sai yace ba'ayi masa daidai ba.

Itama a fusace! tace"Aa ni ban ce kada ka zauna da matarka ba, amma ai bai cancanta ka share gindi ka zauna sama da awa biyu ba, ka barmu nida yara muna ta zaman jiranka kome ka shigo dashi gidan ka bari kazo kaga lafiyar yaranka in yaso daga baya bukatarka ta biyo baya ni dama nasan baka sani a lissafin mata tunda ka gama morata kuma ba wata cikakkiyar lafiya ce dani ba kafi kowa sanin hakan.

Jikinsa yay sanyi yace"To naji nayi laifi ayi hakuri dan Allah kada ki kara cewa bana saki a sahun mata wannan maganar sam bata dace ki fad'eta ba kin dai san kafin na nunawa ko wace mace so ke na fara nunawa kuma har yanzu kina da matsayi a zuciya saboda haka ki daina fad'in wannan magana bana so.

Shuru tayi tare da kauda kanta.

Yace"Na samu labarin cikin dake jikinki dik da kina 'boye min kada na sani shin ko zaki iya fad'a min dalilinki."
Halisa ta dinga kallonsa cike da mamaki!

Girarasa ya daga mata yace"A ranar da kikaje asibiti aka tabbatar miki da cikin aranar nima na samu labarin samuwarsa......A sanyaye tace"Dr Sa'adatu ce ta fada maka kenan."?

Yace."Kwarai kuwa ita ta fada min kuma nayi farin ciki sosai na kuma roki Allah ya bar mana shi ya kuma saukeki lafiya."
Halisa murya na rawa tace"Wallahi Abban Mufida ba'kin fada maka nayi ba inaso yayi kwari tukkuna sai na fad'a maka nasanka da sa abu a rai kada sai bayan mun saka rai a samu matsala shiyasa nayi maka shuru..

Tausayi ta bashi yace."Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zaki haife abunda ke cikin lafiya keda ki tsananta addua da rokon Allah." Tace."Inayi sosai wallahi." Yace."Nima zan sanya a yi miki saukar al'akurani mai girma." rungumeshi tayi tana masa godiya tare da rokon Allah ya amshi addua
Duk da yaci cika cikinsa a gurin Zainab hakanan ya daurewa itama Halisan yaci nata duk dan a samu zaman lafiya sabida yasan babban abinda mace ta tsana shine tayi abinci a'ki ci dalili kenan da yasa ya daure yaci abincinta ya kuma zauna tare da ita har misalin goma na dare kafin yay mata sallama ya nufi gurin Zainab.

Zainab Ta shirya cikin kayan bacci ta jik'a jikinta da turaruka masu kamshi! duk inda ta gifta sai kamshi, maigidan nata kawai take jira ya shigo a fara harka dan itama a d'okance take da al'amarin tayi shaye shayen maganin matanta dik domin ta gamsar da bukatarsa.

Abbah ya sake rikicewa jin uban kamshin da dakin Zainab keyi ya kalleta yana lasar baki kayan baccin sun fito mata da tsaraicinta yaji jijiyarsa ta harba! da sauri ya nufi toilet domin ya watsa ruwa.

Koda ya fito daga toilet din gajeran wando kawai yasa ya kashe fitila, Ya nufi bed din, Yana zama ya kamota rungumeta yay a jikinsa yana matsa mazaunanta to anan labari ya sauya...................Da asubah da bacin rai ya tashi ya nufi toilet wanka yake cikin takaici yana kallon joystick d'insa, tun jiya ta'ki ta kwanta masa yanda yake so, duk da ya jima kan Zainab yana suburbudarta hakan besa ya samu cikakken satisfaction din da yake bukata ba, ya dai rage abin da ya rage, Zainab haihuwa daya kacal duk ta sakawarkwace gashi bata da wata cikakkiyar ni'imar da yake bukata shi ya dauka tayi masa tanadi mai kyau shiyasa yake ta zumudi ashe takaici zai kwasa.....Koda ya dawo daga massalaci kasa hakuri yay ya sake haike mata nan ma ba ta canza zani ba, dan zainab da taji wuya kuka ta dinga yi masa yay hakuri ya kyaleta ita ta gaji, shi kuma a yanda mararsa ke k'ullewa baya tsammanin zai kyaleta, da kyar ya samu ya zubar da abinda ke mararsa, ya jima a kwance a kanta kafin ya sauka, toliet ya nufa yana addua Allah yasa jijiyar tasa ta risina, cikin ikon Allah kuwa tayi laushi! yay wanka a gurguje ya fito yana kimtsawa yana jan tsaki! a rayuwarsa ya tsani yaji mace a bushe ko a bud'e!
Chapter 135 · 0% Book details