Sashe 13
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To shin wai ko ya manta abinda yake tsakanina dake ne da har zai bijiro da wannan tatsuniyar."
Tace"Oho! ni gani nake kawai san zuciya ne yama za'ayi yace haka bayan shi da bakinsa ne yace."Mu daidaita kanmu zai daura mana aure kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai yace a mayar masa dani a *MADADINTA."*
Salim yayi wani murmushi na takaici yace."Ke nifa na daina mamaki! wallahi zai aikata dama yanda yake wani kula dake da wani takatsantsan a kanki akwai alamun tambaya dama so yake matarsa ta mutu ya aure ki! saboda haka ni kuma wallahi bazan bar masa ba, to in banda ma rigima ina ke ina shi! shekara hamsin har yake tunanin auran yarinya 'yar 'karama kamar ki 16years fa to idan ya aure ki yayi yaya dake? mtwwss."!!
"Humm! ni wallahi Salim mamaki ma ya hana ni nace komai ba kaga yanda su Baba malam suke murna ba, wannan ai tauyewa mutum hakki ne.
Ni duk na rasa ma yanda zanyi."
Yace."Kece kuwa kike da yanda za kayi, tun kafin yafiya tayi nisa ki kokarin ganin kin rusa maganar ni kuma gobe idan Allah ya kaimu idan naje daukarshi domin zuwa kasuwa zanyi masa magana akan inaso yazo gurin Baba malam kan maganar auramu sai naji me zaice."
Tace"To yauwa kayi masa hakan nasan dole kunya tasa ya kasa magana ni wallahi duk mutuncin sa ma ya zube a idona mtssssw!!!
Takarashe maganar tana jan tsaki!
Yace."Baby ki daina wani damuwa ki kwanta kiyi bacci bazan bari wannan al'amari ya tabbata ba, duk yanda zanyi to zanyi na rusa al'amarin.
A sanyaye tace"Tom shikkenan my Prince kayi bacci mai dad'i kaji ko." Yace."Ke ina wani maganar bacci mai dadi a gurina Wannan dattijon na nema yasa zuciyata ta buga."!!
"Hummm! kawai tace dan ta rasa ma abin cewa, kashe wayar tayi ta zurfafa cikin tunani da nazari! gabad'aya bata so tayi masa rashin kunya saboda shi mutum ne mai muhimanci a gurinta to amma tunda ya 'bullo da wannan maganar kashi hamsin na 'kima da mutuncinsa suka zube a gurinta.
Numbarsa ta laluba ta dinga kallon numbar kamar shi take kallo, shawara take da zuciyarta shin ta tura masa text ko kuwa, wata zuciyar tace" Idan kika tsaya lako-lako kan wannan al'amarin to za kiyi kuka da idonki.......Da sauri ta shiga rubuta masa text kamar haka.
_Assalamu alaikum Abba nmu barka da dare ina tafan kana nan lafiya?
Abbah wata magana naji daga bakinsu Baba malam kuma sun ce kaine kazo musu da maganar shine nake so naji daga bakin ka._
Tana tura masa text din ta kashe wayar! kwanciya tayi tana takure jikinta hawaye ne ke kokarin 'kwace mata tana kokarin hana shi fita.
Sai bayan da ya dawo daga sallahr asubahi ne ya kunna wayar tasa, aikuwa text din ne ya shigo yayi saurin bud'ewa yana dubawa............Ya karanta ya kai sau biyar ya girgiza kanshi! lallai To bata yarda ba kenan tana so taji daga bakinsa, shi kam bai san abinda zaice mata ba, kawai sai ya share bai mayar mata da amsa ba, ya cire jallabiyar jikinsa, ya kwanta rigingine kan bed din yana tunanin rayuwa, Halisa ce ta shigo dakin jikinta sanye da hijab kamar wata mutuniyar arziki, tun bayan mutuwar Halimatu wata shiriya tazo mata takeyi komai cikin rashin kuzari.
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*8*
Tana tashi da asubah ko sallah ba tayi ba ta dauki wayarta ta kunna ta shiga dubawa wai ko ya turo mata da amsa, wayar ta kai minti goma a hannunta tana jiran shigowar replay dinshi bai shigo ba, a sanyaye ta mike ta fita domun daura alwala, tana shigowa dakin ta sake daukar wayar tana dubawa, ganin alamun shigowar sa'ko yasa hannu na rawa ta bud'e! tsaki! mai 'karfi taja ganin messege din daga *Mtn* ne, jefar da wayar tayi kan katifa, idanunta na kokarin kawo ruwa ta shiga tayar dasu Saddiqa daga baccin da suke.........Suna bude ido tace"Ku tashi kuyi alwala kuyi sallah." Saddiqa ta sauko da sauri ta bude akwatin kayansu makilin da brush ta dauka ta fita domin daura alwala.....Cikin tsawa ta kalli Mussadiq kamar shi yayi mata laifin tace"Kai ba zaka tashi ba sai na gaggaura maka mari ko."!
Yaron ya tashi a furgice yana kallonta! da hannu ta nuna masa 'kofar fita tace"Kaje kayi alwala gari ya waye." sakkowa yayi daga katifar shima ya dauki abun wanke baki ya fita.
Hijab ta zura ta gyara dadduma ta tayar da sallah, Tana idarwa ba tayi wata adduar kirki ba ta sake daukar wayar tana dubawa, har yanzu dai babu amsa!
Tsaki ta dinga ja zuciyarta na wani irin tafarfasa! babu shakka Abbah Abbas da gaske yake! tasan yaga text d'inta kunya ta hana shi bata amsa shiyasa ya shareta.
Numbar Salim ta laluba ta shiga kira. sai dai wayar a kashe take dan bai tashi ba ballanta ya kunna wayar......Mi'kewa tayi ta koma bakin katifar ta zauna had'e da cire hijab din jikinta, Numbar Abbah Abbas din ta sake nema ta 'kara tura masa wani text in kamar haka.
_Abba ina jiran amsa nasan dai kaga text d'ina dan Allah ka bani amsa shin kaine ka nemi aure na? ko kuma su Baba malam ne suka baka ni."?_
Tura masa tayi ta tsirawa wayar ido tana adduar Allah yasa yayi mata magana.............Shi kuwa Abbah Abbas yana kwance Halisa na matsa masa a jikinsa yana lumshe ido baccin da ya tara kwana da kwanaki ne yake damunsa, tinda Halimatu ta rasu bacci da nutsuwa suka 'kaurace masa, mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa, gani yake ma ba zai ta'ba samun mace tagari kamar ta ba, Yayi yun'kurin auran Naja'atu ne ba dan komai ba sai dan yasan ita d'in tarbiyyar Halimatu ce yana kwadayin ta zama matarsa domin hausawa suna cewa gida bai 'koshi ba to ba za'a bawa dawa ba, bayan haka kuma yana tausayawa 'yan 'ya'yansa sosai saboda yanxu suna bukatar mai kula dasu sun saba da mamansu sosai dole idan suka dawo gidan suka ga babu ita su shiga damuwa, amma duk rintsi idan suna kallon Naja'atu a gidan kuma a matsayin matarsa to zasu samu sassauci a tare dasu.
Babban abinda yake d'aga masa hankali acikin al'amarin shine! yanda zai tunkare su da maganar!
Salim da Naja'atu gabadayan su bai san abinda zai ce musu ba, Salim bashi da Uban da yafi shi, hakan nan itama Naja'atu bata da uban da yafi shi, tabbas da zai iya hakura da ya hakura ya kyalesu sunyi auransu, amma ba yajin zai iya janye kudirinsa ba dan komai ba sai dan samun walwala da farin cikin 'yayansa guda biyu, saboda ya riga ya sani cewar babu wata mace da zai aura ta ri'ke masa su tsakani da Allah! shiyasa yake ganin auran Naja'atun shine yafi alkairi a garesu baki daya.
'Dan juyawa yayi ya d'auki wayarsa ya bud'e text din ya sake bud'awa domin ya sake karanta sai yaga wani ya sake shigowa, Ya bude idonsa sosai yana karantawa!
Murmushi yayi wanda yasa Halisa kallonsa da sauri tace"Allah yasa alkairi ne naga kana murmushi." Kallonta yayi yana kokarin rufe wayar dan ganin tana le'ko da kanta tana so ta ga abinda yakewa murmushin, a hankali yace."Alkairi ne insha Allahu." Tace"To Allah ya tabbatar mana dashi, mikewa tayi ta fita daga dakin tana fad'in "Bari na shiga kicin na shirya abin karin kummalo." Ya bita da kallo Ba tare da yace mata komai ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta daga d'akin, tabbas idan Halisa taji wannan babban al'amarin akwai tashin hankali! ya riga yasan halinta da mugun kishin tsiya! uwa uba kuma tsakaninta da Yarinyar basa jituwa ko kadan yanzu yanda zai tunkareta da maganar yake tunani.......Kira ya shigo wayar dake hannunsa, koda ya duba numbar Naja'atun ce yayi serving da My doghtar! kamar kada ya daga sai kawai yayi 'kundumbala ya d'aga wayar yana d'an gyaran murya, kafin ma yace wani abu yaji shashshekar kunanta a kunnasa.
Jikinsa ne yayi sanyi ya sassauta murya irin yanda yake mata idan tana irin wannan kukan yace."Dota ya akayi kuka da sassafe kiyi shuru muyi magana ko."!! hanci ta sha'ka! zuciyarta sai tafarfasa take tace"Abba tun jiya na turo maka da text baka bani amsa ba kuma nasan ka gani dan girman Allah ka bani amsar abinda na tambayeka ko na samu zuciyata tayi sanyi."""" Jim yayi kafin yace."Kinga ni ban ga text d'inki ba ballanta na baki amsa amma kome kika rubuta min a text din ina sauraranki yanzu ki fad'a min."
Cikin rawar baki tace"Jiya bayan kasa Salim ya kawo mu gidan Baba Malam shine naji suna wata magana wacce tasa raina ya kusa futa daga jikina, ashe wai kai ba kaine ka haifeni ba , sannan babban abinda ya furgita ni yasa na shiga cikin halin damuwa da tashin hankali wai kaine da bakin ka kace musu su baka ni na zama *MADADIN* matarka da ta rasu, shine nake ganin kamar sune suke so suyi wannan had'in da bai dace ba! ai abun kunya ne ace wanda nake amfani da sunansa ako ina a matsayin mahaifina aji shine kuma zai aureni ina zan saka raina idan hakan ya tabbata."!!
Cikin sar'kewar murya ta 'karasa maganar........Shuru yayi kawai yana jin saukar numfashinta a kunnansa bakinsa yayi masa nauyi gabad'aya ma ya rasa me zai ce mata.
Murya na rawa tace"Abbah wannan shurun da kayi yana nuna min cewar da gaske ne maganar daga bakin ka ta fito!!!
Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! kaico da wannan furucin naka!
Abbah! dan girman Allah ka janye wannan maganar da kayi, na rantse da Allah ba zan iya zaman aure da kai ba ni a matsayin Uba na dauke ka."
Tana wani irin kuka take masa maganar, Yaji jikinsa duk ya mutu!