Sashe 115
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mmn Sajida tace." Ni kuma sai nake ganin kamar yana jira yaron ki yay wayo ya bijiro da maganar kome din kin san fa koda zai mayar dake gidansa ba zai mayar dake kina da d'anyan jego ba, wallahi ko kaffara ba zanyi ba yana sonki dan da baya sonki ba zai dinga yi miki wahala ba, haba ki duba fa ki gani shine yazo ya daukar ki anan sannan lokacin da kika kwanta a asibiti kina kiran wayarsa ko minti ashirin ba'ayi ba ya turo da kudiin da'a ka bukata..........Duk da kin kasance mai laifi a gurinsa hakan bai hanashi kula dake ba, ki kwantar da hankali da kansa zaiyi miki maganar ki koma gidansa amma kema dole ki dan yawaita kwalliya da gyaran jikinki da kowane lokaci ya dinga ganinki tsaf tsaf zaki janyo hankalinsa sannan kina kiransa a waya kina gaisheshi."
Najaatu murmushin takaici tayi tace"Mmn Sajida sau nawa zan kira wayarsa yasa matarsa ta dauka! a gabanki ma fa hakan ya ta'ba faruwa Abbah wani irin mutum ne wanda baka gane gabansa da bayansa."
Mmn Ladi tace"Kome baud'ewar halinsa mace na
iya sanja shi saboda haka idan kika mayar da hankali akan shawarwarin da muke baki zasu taimake ki."
Najaartu shuru kawai tayi tana sauraran maganganunsu, tana daukar na dauka tana watsar dana watsarwa bata tunanin zata tunkareshi da maganar ya mayar da ita gidansa idan ya tausaya mata da yaronta ya mayar da ita haka take so idan kuma yana ganin bashi da ra'ayi sai ta hakura ta barwa Allah.
Sai bayan taci abinci ta nutsu tukkuna ta shiga fito musu da tsarabar data kawo musu , kowacce turmin atamfa biyu da mayafi da takalmi sai sabulai na wanka dana wanki da kayan kwalliya irin na mata.
Sosai suka shiga yi mata godiyar hidimar da tayi musu, ashe da sauran godiya, dan kudinta na haihuwa data samu kimanin dubu saba'in da wani abu a ciki ta dauko dubu hamsin ta kawo musu
Mmn Sajida ta miqawa tace su raba....Mmn Sajida ta riqe kudin a hannunta tana kallonta cikin d'umbun mamaki!
Murmushi tayi ta kalli Mmn Ladi tace"Mmn Ladi naki kudin sai kiyi kokarin ki fara sanaa dasu kafin naga abunda Allah zaiyi anan gaba insha Allahu idan na samu yanda nake so zan qara miki wasu.
Mmn Ladi fashewa tayi da kuka ta rungumeta tana fad'in "Wallahi Najaatu na rasa bakin da zan gode miki ashe ke din alkairi ce a tare damu muna mutukar alfahari da sanin da mukayi miki wallahi Kinyi min abunda d'an uwa na jini baiyi min ba, a cikin 'yan uwana akwai masu hali amma babu wanda yay tunanin dauko kwabonsa ya bani da sunan naja jari nayi sana'a sai ke da Allah ya had'ani dake kin gyara min aurena kuma kin dauki kudi kin bamu, kin kawo min babban zani irin wanda banta'ba daurawa ba, babu abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da alkairi ya biya miki dukkanin bukatunki.
Naja'atu tace"Haba Mmn Ladi meye abun kuka wallahi wannan ba komai bane a gurina idan ina da abunda yafi haka zan baku domin kuma kun taimakawa rayuwata a lokacin da nake bukatar taimako saboda haka ki daina kuka kina gode min Allah ne ya had'amu ina fatan zumuncin mu ya d'ore har 'ya'ya da jikoki." Mmn Sajida tace"Insha Allahu Najaatu Allah zai cika mana burin mu kuma kamar yanda muke zumunci insha Allah 'ya'yanmu suma za suyi."
Da wannan addua ta Mmn Sajida suka rufe maganar suka shiga hirar Bash da hukuncin da'a ka yanke masa.
Laifin Najaatu ya shafi su Halisa a tunzure ya shiga gidan, girkin Halisa ne ganin yanda ya shigo yana shan qamshi yasa bata tunkari inda yake ba gudun wulakanci yasa taje tayi kwanciyar a dakinta tana kallo, har ya gama abinda yake a falo ya shigo yay shirin kwanciya, zama yay gefan gado da wayarsa a hannunsa.
Number Najaatu ya nema
Lokacin dare yayi dan goma da rabi ta wuce duk sunyi shirin kwanciya Mmn Sajida dalilin zuwan Najaatun yasa bata fita sana'arta ba, suna hira sama sama kiran wayarsa tasa ya shigo.
Ta dauka tana dan tunani to me ya kirata yace mata?
Shawarar dasu Mmn Sajida suka bata ta tuna, sai kawai ta daga wayar tana wani maqale murya tace"Hello Abbah! barka da dare." Wani irin yarrr! yaji a jikinsa sakamakon jin yanda muryarta ta ratsa jikinsa, tamaza yay yayi gyaran murya as'usul yace."Barka dai ina fatan kin suturta yaron nan da kayan sanyi saboda kin san dai yanda ake sanyi gashi na lura gurin da kike bashi da tsaro da sauransu."
Dan murmushi tayi tana kallon Mmn Sajida, ta sake kashe murya tace" Abbah ni baka damu dani ba kenan kana tambayar na suturta Mai sunanka nima ai ina jin sanyi sosai a jikina."!
Cikin shagwaba ta k'arasa maganar.
Shuru yay na minti biyu kafin yace."Ke ai kin girma sanyi ba zai miki lahani ba kamar shi so sabida shi na kira wayarki sannan kuma na sake tunasar miki da abinda na fad'a miki d'azu! gobe da wurwuri Dan Azimi zai zo ya daukeki."
Kamar za tayi kuka tace"Allah ni bazan dawo gobe ba, Abbah wa na'ajiye a garin kano da zan takurawa kaina dawowa ni dai dan Allah ka bari na kwana biyu a gari jos dan ina jin dadin garin sosai da sosai.''
A hasale yace."Ke! ashe baki da hankali wannan garin duk babu mutunin arziki a cikinsa ashe kina so ki sake haduwa da wani mara tarbiya kenan( Afuwa mazauna wannan garin banyi da niyyar naci muku fuska ba labari ne yazo a haka a gafarce ni garin jos akwai masu tarbiya sosai ga misalin irinsu Mmn Sajida nan nayi)......Tace"Haba dai Abbah ba duka a ka zama d'aya ba Wallahi su Mmn Sajida suna da kirki da tarbiya kuma ni da naje ziyara mai zai had'a ni da wani saurayi ko bazawari babu ruwana dasu.
Yace."Ni dai na fad'a miki gobe ki zauna cikin shiri domin hankalina bai yarda da zamanki a wannan gari ba." Kashe wayar yay bai saurari ta bakinta ba.......Halisa ta miqe zaune tana hararar bayansa ji take kamar ta makeshi! saboda haushi yana yaudarar kansa yana yaudararsu to meye nasa na damuwa dan ta tafi jos da har zai ce zai tura a daukota. tsaki taja a zuciyarta kafin tace"To wai kai meye na damuwa dan ta tafi wannan gari? babu fa nauyin kowa a kanta da kake cewa ta dawo haba ai ka kyaleta ta huta su gaisa sosai da wannan mutanan da sukayi mata hallaci."
Yana jinta yay shuru sai ma ya fara kokarin kwanciya yana kokarin rufe kafafunsa, Halisa bata san sanda taja tsaki ba tace"Abban Mufida kenan ka tsaya wasa wallahi sai dai kaji anayi dan Najaatu a yanzu allura cikin ruwa ce da d'anyan jegon da take dashi ba zata rasa me auranta ba......Fad'in wannan magana da Halisa tayi sai ya fusata! ya miqe zaune ya dinga zazzaga mata masifa da fad'in "mahaukacin Namiji ne zai auri mace da d'anyan jego saboda haka kada ta kuskura ta sake yi masa irin wannan magana.
Halisa itama ta fusata tace" To itama kada ya sake zuwa gabanta yayi waya da Najaatu tunda abun nasa ya zama rainin hankali, haka suka dinga cacar baki tana fad'a yana fad'a dan gabanyansu a tunzure suke kowa yana ganin ba'ayi masa daidai ba.......Gabad'ayansu Haka suka kwanta suna jin haushin juna.....
*Infaction*
_Ko wace mace kaji tace miki tana fama da infaction wai shin ya zamuyi mu kare kanmu daga wannan laluran mai wahalar magani?
Idan kina da sanyi koda mijinki bai dashi sai ya samu....Ko kuma ke baki dashi mijinki nada shi to sai kin samu, idan ya kasance duk kuna dauke da lalurar sai ku durfafi shan magani a tare! dan idan daya yasha daya bai shaba to akin banza kukayi ciwon yana nan babu inda zaije..........Kina budurwa kina kyaikayin gaba da zubar da farin ruwa gashi an kusa bikin ki kinja bakinki kinyi shuru baki fadawa mamanki ba, to zaki haifarwa da kanki matsala babba dan idan kikaje gidan mijinki da wannan ciwo kika shafa masa zai miki mummunar fahinta ya dunga yi miki wani irin kallo na daban......... saboda haka mutukar kina da matsala irin wannan maza ki sanar da mahaifiyarki kafin ki sanar dani mahaifiyarki itace mafi kusa dake kuma ita ta haifeki babu kunya a tsakaninku!
Ki fada mata komai zata kaiki gurin mai magani....Ni shawara ce kawai a tsakaninmu._
*Idan da tsumma kike using a lokacin da kike jin al'ada to ya kasance kullum kina sanjawa sau uku ko sau hudu, sannan idan kin wanke tsumman ki dinga sashi a rana ya bushe kwayoyin cutar zasu mutu.......mutukar kina barin matuncin ki da danshin ruwa to ba zaki rabu da kyaikyayin gaba ba, wannan guri an fiso kullum ya kasance a bushe.......Idan da pad kike using lokacin haila yana da kyau kina sanjawa a kai kai kada kisa tun safe ki barshi sai dare dole gabanki yayi miki kyaikyayi daga haka kuma kwayoyin cuta su shiga jikinki, wannan kyakiyayin masifa ne, saboda haka dan Allah muyi hattara
Vip group #600 normal group #300 accont...0542382124....Binta umat gtbank...WhatsApp number... 07084653262
_Yau mura ta hana ni nayi muku post akan lokaci duk naga adduoin ku dana pravite dana group
Nagode sosai Binta tana tare daku insha Allah
*BHRMBN 74_75*
Da maganar Halisa ya kwanta bacci ya kuma tashi da maganar a cikin ransa, ya jima yana nazarin maganar da tunanin abinda zai biyo baya a jos din mutukar an san ita din bazawara ce to tabbas maganar Halisa na iya kasacancewa a samu wanda zai ce yana sonta duk da jegon da take dashi, dan haka yana dawowa daga masallaci ya nemi number wayar Dan Azimi suka gaisa da juna yace."Ina fatan dai ka shirya ka tafi da wuri bana so kuyi shigowar dare.