Sashe 25
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri'ke 'kugu tayi tace"Nifa bangane ba meye amfanin kawo ita gidana naga harda jakar kayanta." Yace."Eh kamar yanda na fad'a miki a waya hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci." Murya na rawa tace"To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo min ita gida." Yace."Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba zata samu nutsuwar da ake bukata ba." Tace"To naji a'ina kake shirin ajiyeta." Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace."A duk inda nayi ra'ayi gidana ne ai." Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta tace"Sai dai a gyara mata d'aya sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita." Yace."Ai dama ba'ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can gidan." Girgiza kanta tayi tana 'kas-'kas! da cingum! din bakinta tayi wani murmushi tace"Ba zai yiwu ba! ai na fad'a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan babu inda zanje." Daga mata hannu yayi yace."To magana ta 'kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba zaki koma wallahi." Tace."Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka." Shuru yayi mata ya zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin "Bari na kawo maka kayan break din." Tana fita ta gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take musu.....Halisa taja tsaki cikin tsawa tace"Ke Mufida me kike anan zo nan ki taya ni 'aiki." Yarinyar ta mike da sauri!
Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad'in "Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza." Naja'atu dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana surutai.........Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu, kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq tare da fad'in "Kayi rashin lafiya ne."?
Girgiza kansa yayi yace." Yaya Naja'atu kema kin dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na kai miki dakinmu."?
Kanta ta d'aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa, Naja'atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta zauna tare da dasu.......Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri'ke da tire jere da kayan tea ko kallon inda Naja'atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin maigidan, Naja'atu ita dai binta da kallo kawai take..........
Yana zaune 'kasan kafet ta shiga dakin, ajiye tiren tayi ta zauna tana kokarin had'a masa tea din yace."Ki bawa Naja'atu abinci dan bana tsammanin taci wani abu tun jiya." Kallonsa tayi kamar za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga dakin...........Saddiqa ta kalla tace"Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace."! tana gama maganarta ta shiga dakinta......
Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja'atun tace."Don Allah Yaya Naja'atu kada ki kulata." Murmushin takaici tayi tace."Jeki yi aikin ni ba'a gabana take ba ballanta na tanka mata." Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe dinsu, Tace"Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi." Yace."Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a ciki." Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na 'yan boarding....Mussadiq yace."Yaya Naja'atu zan baki gado na ki kwanta kafin Abbanmu ya kawo miki naki." Tace"To nagode Mussadiq." ya mike da sauri yana fad'in "Bari ma naje na fada masa." Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin....Dakin Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad'in "Me zaka shiga kayi."?
Yace."Zan fad'awa Abbanmu ne cewar Yaya Naja'atu bata da gado." Cikin tsawa! tace"To sarkin iyayi da rawar kai ai ya fika sani." Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta Tace."Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa kana cin abinci sai ka fito tukkuna." Ya kalli Mussadiq din a nutse yace."Menene."?
Mussadiq yace."Abbah Yaya Naja'atu bata da gadon kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d'in mu." Murmushi yayi yace."Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja'atu sosai kada ka damu zansa a kawo mata gadonta itama." Murmushi yaron yayi yace."Nagode Abbah." Cike da farin ciki ya nufi dakin nasu yana so yaje ya fad'a mata abinda Abban nasu yace..........Abbah Abbas fita yayi daga gidan ya tafi sabgoginsa sai yamma likis ya shigo unguwar kuma bai shiga gidan ba sai bayan sallahar isha'i, Halisa yau ma ta cancad'a kwalliya kamar itace amaryar tana zaune a palo ita da yaran suna kallo kamar jiya, ita kuwa Naja'atu ta kasa zama a palon tana d'aki ta takure kanta sai neman Salim take a waya bata shiga.....Hannu bibbiyu Halisa ta kar'be shi, ta bashi abinci yaci kamar koda yaushe ya dawo palon ya zauna nan yaga babu Naja'atu a gurin, Ya kalli Mussadiq da fadin "Ina Yaya Naja'atu." Mussadiq yace."Tana dakinmu nace ta fito muyi kallo ta'ki." Kai tsaye yace."Je ka kirata." Yaron ya tashi da sauri! ita kuwa Halisa shan kunnu tayi ta wani tamke fuskarta....Da hijab a jikinta suka fito ta zauna kan kujera kanta a kasa tace"Abbah Sannu da zuwa." Ya amsa yana nazarinta yace."Me kike a daki ke kad'ai bayan kowa na palo." Shuru tayi, Ta kalli Halisa a nutse yace."Inaso nayi magana daku a dakina." Mikewa yayi ya nufi dakinsa." Halisa ta mike tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu gyara zama tayi dan bata fahimci maganarsa ba, Minti biyar da shigar Halisa dakin nasa Kira ya shigo Wayarta koda taga numbarsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! ta dauki wayar Yace."Ki shigo dakina zanyi magana daku." a raunane tace"To." Kashe wayarsa yayi, Halisa kam sai jijjiga kafa take ta cika ta batse sai wani 'kas-'kas take da cingum din bakinta, Ya kalleta cikin 'bacin rai yace."Malama ki cire wannan cingum din na bakin ki." Ta daina 'kas-'kas din tayi ta dauke kanta......Da 'kyar ta iya mi'kewa ta nufi d'akin nasa yayin da yaran suka bita da kallo, Saddiqa dai duk tafi su hankali ta gane Yanzu Yaya Naja'atu dai-dai take da Anti Halisa a gidan to dan ta shiga dakin Abban nasu ba abun mamaki bane.......
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
MADADI!!
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Aunty Binta wai dan Allah me yasa duk littafin ki kike bawa maza Power akan mata ni dai duk na karanta novls din 'ki ban ta'ba ganin wanda kika bawa mace power ba*
_*MAFI A KASARIN TAMBAYAR DA MUTANE KEYI MIN KENAN WAI ME YASA NAKE BAWA MAZA POWER!
A LITTAFIN NA, TO GA AMSA, BANI NA BAWA MAZA POWER (IKO) BA ALLAH NE YA BASU, NAMIJI IN DAI SUNANSA NAMIJI TO KOMAI 'KAN'KANTARSA SAI YA JAGORANCE KI KODA KUWA KE KIKA HAIFE SHI, TO BALLANTA NAMIJI A CIKIN GIDANSA
TO AI NI KO LOKACIN DA NAKE KARATUN LITTAFIN HAUSA DAGA NA FARA KARANTA LITTAFI NAGA AN BAWA MACE POWER A KAN MIJINTA NAKE DAINA KARANTAWA DAN NA TSANI LUSARIN NAMIJI WANDA BAYA IYA JAGORANTAR GIDANSA, MEYE AMFANIN POWER MACE A GIDANTA
IDAN YA KASANCE KINA JUYA MIJIN KI TO ME KENAN AKAYI?
AI DUK GIDAN DA KUKA GA MACE NA MULKI A CIKINSA TO TA KAUCE HANYA NE, NI DUK MACEN DAKE MULKI A GIDAN AURANTA TANA JUYA MIJINTA YANDA RANTA YAKE SO WALLAHI BATA BURGENI SABODA NASAN 'KARSHEN TA NADAMA!
MATA SU ZAUNA A 'KARKASHIN MAZAJEN SU KAMAR YANDA ALLAH YACE, SU KUMA MAZAN SU KULA DA DUK WASU HAKKO'KIN MATAYEN SU, AMMA BA WAI INA FIFITA NAMIJIN NOVEL AKAN MACEN NOVEL BA INA SO INA NUNA MUKA ABINDA YAKE FARUWA A ZAHIRI SHINE NAMIJI KO MAI 'KAN'KANTARSA JAGORA NE
*17_18*
Kanta a 'kasa ta shiga dakin da sallama a bakinta, Shi kadai taji ya amsa sallamar dan ko Halisa ta amsa ita dai ba taji ba.
Kusa da Halisan ta zauna tare da sunkuyar da kanta 'kasa, dakin ne yayi shiru na tsayin minti uku kafin yayi gyaran murya kamar yanda ya saba idan zaiyi magana yace." Gabad'ayan ku nasan kunsan abinda yasa na tara ku anan ko."? shuru sukayi babu wacce tayi magana.
Ya kalli Halisa a nutse yace."Tun kafin na kawo miki Naja'atu gidan nan mun gama magana dake ina fatan zaki kar'bi yarinyar nan hannu biyu ki dauke ta a matsayin *'ya* ba kishiya ba, wannan kad'ai za kiyi min ki nuna min ke mai kaunata ce." Halisa ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi, lallai sai ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ba kishiya ba sannan zai gane ita mai kaunarsa ce maganar ma mamaki ta bata sosai kuma ta 'kara tabbatar da cewar namiji bashi da kunya, komai 'kan'kantar kishiyarta yaushe zata dauke ta a matsayin *'Ya* wannan magana ma bai mai yiwu bace.